Hasken Makafi Hausa Novels Complete

Hasken Makafi Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

“Banyi rayuwa da mutane ba nayi rayuwata tare da giwaye ban san yaya na kasance tare da wad’anan dabbobin acikin wannan dajin ba, na dai wayi gari na ganni acikin su ina rayuwa.

ba irin halittar da bana iya sarrafawa inhar acikin dajin *k’arfafa* take kuma ba halittar da ta tab’a cutar dani, saboda suna matukar ji dani fiye da y’ay’an da suke haifa, shiyasa kaga sun taso maka har suka cutar dakai saboda tunanin su zaka cutar dani, su kuma inhar suna gani to ba zasu bar mutum ba kuma ba kanka aka fara ba, da yawa in sun shigo yawon su suna yunk’urin keta mini haddi na Allah ne gata na kuma wad’anan nan dabbobin sune gatana, da badan taimakon Allah ba da taimakon su bazan kawo yau ba da bazaka sanni ba.”

 

Na k’arashe ina saka wani k’yalle ina daure masa ciwukan dana gama shafa masa magani akai, d’ago dara daran idanu na nayi na same sa yana kallo na kamar ma bayajin zafin ciwukan daya samu, mik’ewa nayi na juya masa baya ina gyara mad’aurin daya rufe mun surar jikina, domin dai ba kaya ne normal nake sawa ba wasu kyallaye ne nake rufe jikina dasu, ina daure kirjina sannan na nad’a kyallen na rufe k’uguna zuwa duk inda al’aura ta take, amman cinyoyina zuwa kafafuna duk a waje suke, haka nan ma daga cibiyata zuwa sama banda kirjina suma abud’e suke, sai kuma babban mayafin da nake yafawa nakeyin sallah.

 

Maganarsa kawai naji tamkar saukar aradu yace,

 

“Kin amunce mun na tafi dake?”

 

Saurin jiyowa nayi ina kallon sa cikin ido, lumshe mun su yayi sannan ya bud’e kamar wani dan maye, ya sake cewa “zuciyata bazata barni na tafi ba muddin kina nan”

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Daina kallon sa nayi ina juyawa ina tattakawa zuwa bakin wata bishiya na zauna ina wasa da wani icce dake hannuna nace masa, “Bawan Allah karka b’ata yawun bakin ka ni bazan tab’a binka ba, anan ka ganni kuma anan zaka barni”

See also  Matar wani Hausa Novel part 1

 

Idasa kwantawa yayi bisa ciyayi dake wajen yana cewa cikin isa da iko, “ni kuma kin mani, kuma bazan tafi ba tare dake ba, saidai idan giwayen naki da sauran namun dajin naki su cinye ni”

 

Saurin kallon sa nayi ya jinjina mani kai alamun tabbacin abunda ya fad’a nai saurin mik’ewa na dauk’i yar sanda ta nace, “sai idan ka sake gani na sannan zaka tafi dani d’in ai”

 

Na surd’ad’a ta wani kogo na yanke hanya ina jinsa yana kwalla kiran na dawo saboda bai iya mik’ewa balle ya biyoni yai mun ta karfi, inajin sa nai gaba abuna wata giwa da ba ajima da yaye ta ba ta biyoni da gudu na biye mata mukai ta gudu ina dariya…………….

 

Runtse idanun sa yayi cike da jin zafin ciwukan da ke jikinsa aman guduwa ta tafi masa rad’ad’i fiye da wad’anan ciwukan, kafin ya wani yunk’uri guard d’in sa har sun iso wurin ta hanyar bincike da location, cikin sauri da azama suka yunk’ura zasu kamashi ya d’aga masu hannu muryar sa cikin bada umurni da izza yace, “bazan bar wannan dajin ba tare da ita ba, don haka ku ba zama duk wani sak’o da kungu na wannan dajin ku nemota, inba haka ba ina nan babu inda zani”

 

Sanin halin sa na kafiya da taurin kai da tsaya wa akan magana guda yasa ba tare da wani jinkiri ba suka kasu, wasu gabas da yamma wasu kudu da arewa koma wa yayi ya kwanta yana rufe idon sa, yana sake ba zuciyar sa tabbacin muddin ba da ita ba bazai bar dajin ba.

 

(Tabdijam ji karfin hali ga dan mutum🤔)

 

*******

 

“Ishaq na gaji da ganin ka haka kana yawo ba aure, kai baka ganin kayi girman da ya dace ka zab’i abokiyar rayuwa? Me kake jira? Kana da aikin ka kana da gidan ka to meya rage ka Ishaq?ka tsaida hankalin ka waje guda”

 

Kanshi a soke k’asa yana d’an shafa sumar sa irin ta fulani kwantacciya cikin jin kunya da nauyi yace, “Baffa insha Allah ina nan ina duba wacce zata dace dani, bana son nayi garaje inzo ina dana sani”

See also  Ali Dan Tsoho Hausa Novel Download

 

Baffan ya ce, “anan kuma kayi hankali amma hakan bashi zai bka lasisin cigaba dazama haka ba, idan ma matar ce ka kasa zab’a ni ka bani dama zan zabar maka wadda zakaji dad’in zama da ita”

 

Daman kwata-kwata baida wadda ya fidda, da dai a ishe shi da ga wannan ga wannan gara ya barma Baffa zab’in yasan bazai zab’a mashi wadda batai mashi ba, yafi kowa sanin halin sa zai samar mashi wacce tayi dai-dai da halayen sa.

 

Cikin jin kunya yace “to shikenan Baffa hakan ma ba laifi, na baka zab’in Allah ya tabbatar da Alkairi”

 

Har cikin ran Baffan yaji dad’i sosai yace, “Allah yai mak Albarka Ishaq, naji dad’in jin haka daga gareka insha Allah ba zan baka kunya ba, saidai abu guda ne nake son sani shin kana da ra’ayin Auren zumunci ko kafison na waje?”

 

Ya ce, “Baffa duk wacce aka samu daga cikin dangi har na wajen indai tayi maka, kuma kaga zata dace dani ba wata matsala”

 

Albarka yai ta sanya mashi sannan ya tashi ya fito ya shiga wajen mahaifiyarsa.

 

********

 

“Yallab’ai kayi hakuri ko tant a had’a maka ba girman ka bane ace ka kwana acikin wannan dajin wanda kowa yake jin tsoron sa, yarinyar nan idan da rabon zaku sake had’uwa zaku had’u tunda ba inda bamu duba ba acikin jejin bamu same ta ba”

 

Muftahu kenan na hannun damar sa acikin guard d’insa, wanda shi kad’ai yake gaya mashi yaji, amman yau ya rufe idon sa a yau bayaji baya gani har sai ya sake arba dani………….

 

“Yallab’ai kayi shiru duhu k’arayi yake………..muftahu!!!

 

Ya daka mashi tsawar da duk saida sauran suka zabura ya fara magana cikin bala’i ya ce, “na riga na gama magana bazan canza ba, daga nan har mahady ya bayyana inhar ba ku nemota ba ana zamu dawwama daku”

 

Tsitt sukai sannan kowa ya nemi ruwan sallah don lokacin magariba ya wuce ma, muftahun ya taimaka mashi yayi alwallah yai salla saman shimfid’ar da akai mashi da darduma, atakaice dai nan suka kwana baci ba sha sai insunji kishirwa akwai ruwa mai kyau acikin jejin cikin wani rami shi suke sha, idon sa biyu har akai asuba…………….

See also  Wasa Da Nonon Amarya A Daren Farko

 

Ina ganin alfijir ya fito na fito daga in da naje na b’uya, ban nufi ko ina ba sai wajen giwaye na na duba lafiyar su, sannan na yanki hanya don koma wa inda nake zama da tunanin wannan mayataccen mutumin ya tafi, kwata-kwata ban zaci zai iya zama anan ba har iyanzu shiyasa cike da kwarin guiwa ta na doshi wajen, motsin da naji yasa na waiga a zabure ashe abokiyata ce wadda muka tashi tare kusan shekarun mu guda da ita, har suna na samata watau Aminiyata duk cikin namun dajin jejin munfi shak’uwa saifa iyayen ta sune ma suka fi daukar zafi idan aka tab’ani, hayewa samanta nayi muna tafiya ina mata surutu in zata ban ansa sai tayi mun kuka,har bakin d’an kogona da nake rayuwa aciki ta sauke ni nace mata, “zanyi sallah saiki dawo ki daukan muje naga kifaye na,ban basu abinci da dare ba”

Ta mun kukan su na dabbobi sai ta juya ta tafi tafiya ta babu ko dad’e wa naji anyi caraf dani ban k’asa aguiwa ba na dage cicin karfina na fasa wata irin k’ara data karad’e baki d’aya dajin,kan kaceme kukan giwaye da sauran dabbobin dake kewaye da dajin sun saki nasu kukan sun fara bazowa da gudu domin cetona, yadda nake jiyo sautin gudun giwayen bana jin kafin suzo ba’ai nasarar guduwa dani ba, kuka kawai nake saboda nasan shikenan nayi bankwana da dajin *karfafa* nayi nisa da dabbobina da suke sona nake son su, tunda nake rayuwata ban tab’a fitowa daga wannan dajin ba sai yau don wata iska na shak’a wadda ban tab’a shak’arta ba, kafin na sake tantance inda nake naji an jefani cikin wani abu an rufe da karfi,sannan an fizgeta atsiyace kamar za’a tashi sama………………..

 

*WANNAN SHINE ASALIN BARINA CIKIN JEJIN,KUMA SHINE MAFARIN FARA SABUWAR RAYUWA WADDA BAN ZACI AKWAI WATA RAYUWA BAYAN WADDA NAYI CIKIN DAJIN KARFAFA BA*

 

*Labarin HASKEN MAKAFI na kudi ne, ki biya ki karanta cikin lumana, a dari 200 ba wani tsanani*

 

 

 

MOM MUHSEEN✍🏻

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top