Hausa Novels

Hatsabibiyar Yarinya Hausa Novel

Hatsabibiyar Yarinya Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Hatsabibiyar Yarinya Hausa Novel

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

*HATSABIBIYAR YARINYA*

 

 

 

 

 

 

 

Zainab Habib(Mom Islam

 

 

 

 

 

 

 

 

 

I’m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I’m

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 08066268951

 

 

13-14

Iyya ta haƙura akan gobe insha Allah dole ta koma gida.

Tunda Alhj yaji Iyya zata tafi yaji ransa babu daɗi sam ,

Washe gari ta a kunnenta akayi kiran sallah ,ta miƙe zumbur taje tayo alwalah tayin sallah ko dogon adu’a bata ƙara ba ta ɗauki jakar kayanta ta fito palo  ,zama tayi har gari yayi haske ,lokacin Alhj yayi sallama ya dawo daga masallaci ya sameta zaune yace “haba Halimatu kodai laifi mukayi miki ne ? Iyya tana murmshi tace “inajin kamar akwai abinda ke faruwa a ƙauye ne shiyasa “Alhj yace “amman dai zaki ci abinci ai tukun ?Iyya tace “banacin abinci idan zanyi tafiya “Alhj ya wuce ɗakin Hjya Wasila ,ya samu ta idar da sallah ya faɗa mata ai ga Halimatu can ta gama shiri “da sauri Hjya ta fice taje gurinta ta tsaya tana ƙare mata kallo , tace “ki faɗamin gaskiya ko a cikinmu wani ya ɓata miki rai ne ? Iyya tayi shiru kafin tace “ko ɗaya nidai burina inje inga su baba “hjya Wasila tace “kodai kiga mijinki ?”Iyya tasa dariya kafin tace “Allah ya kyauta .

Ƙarfe 11:am Alhj ya dawo daga siyowa Iyya tsaraba ,sosai ya haɗo mata harda kayan tea da sabulai da omo da kayan kwaliya , Hjya Rabi tayi masa godiya ,itama Iyyan tayi masa godiya , daga nan suka rakata parking space ta shiga mota drivernsu ya wuce da ita ƙauyensu ,

Tasha bacci a mota ,dan tunda suka fara tafiya take bacci har Allah ya kawosu ƙauyen .

Suna isowa yara suka cika ƙofar gidan da driver yayi parking suna cewa “oyoyo Iyya oyoyo Iyya “malam har yana tuntuɓe sbda tun daga gidansu yaji kuwwar yaran ya rugo da gudu yaga ko da gaske ne , a yanayin shigar da tayi da kuma kyau data ƙara yasa malam ruɗewa yama rigata shiga gidan .

Tana shiga ta sami baba zaune a gaban iyayenta yana gaishesu , ko kulasa batayi ba tayi wucewarta ɗaki . bayan driver ya gama shigowa da kayan sukayi masa godiya tare da yi masa Allah ya tsare ,

Baba ya daɗe a gidan babu wanda ya kulashi ,sai ma ɗaki da suka shige daga mahaifiyar Iyya har mahaifinta sunata murnar kayan da tazo dashi.

Malm daya gaji da zamansa ya fice yana zuwa ƙofar gida ya hau cewa “shegu ƙananan mutane mugaye ,mutum da matarsa amma an hanashi rawar gaban hantsi ” ya ƙarasa gidan nasu yana mita .

Inna ta ɗauka wani abunne ya faru har tana tahowa gurinsa da sauri tana cewa “lafiya malam ?” Baba ya harareta kafin yace “na gyayyaceki kul ki rufamin baki ina Tinene ? ” Inna tayi tsit bata kulasa ba , Tinene dake ɗaki tana zane fuskarta da bakin kwalli tace “gani baba ” Baba ya ruƙo hannunta tare da sunkuyawa dai-dai saitin kunnenta yace “Halima ta dawo ɗazu “Tinene ta tsala ihu tayi waje da gudu tana dariya ” tana zuwa gidansu Iyya ta zube a kan tabarma tana cewa “Iyya dan Allah ki fito “tausayin Tinene ne ya kama Iyya ta fito tana sharar ƙwallah kafin tace “ni yanzu bazan koma gidanku ba ,kinga kayana nan ma da aka kwaso tunda malam yace wai koda na dawo sakina zaiyi “Tinene ta rufe bakin Iyya kafin tace “,dan Allah kidaina faɗar haka kiyi haƙuri dan Allah kidwo walahi amaryar baba dukana take .

Iyya ta baban Iyya ya fara magana cikin nasiha yana cewa ”

Ke Halima kiyi haƙuri ki koma gidan mahaifinta ” Iyya ta juyar da kai alamun zancen baiyi mata ba ,

Tinene da taga yamma tayi dole ta haƙura ta koma gida ,da niyar gobe zata kwaso kayanta ta koma gidansu Iyya ,

Washe gari , baba rabonsa da wanka yakai kwana 5 yau kam yayi fess ya shirya cikin yadinsa na shadda roba ,wanda ya gaji da duniya , ɗakin da yake ajiyar fatanyu ya shiga ya ɗauko takalminsa ya fito tare da kallon Inna dake shara a tsakar gida kafin yace ” karki kuskura ki biɗamin ƙura ƴar baƙinciki kawai “Inna ta kawar da kai har ya wuce sannan taci gaba.

Kai tsaye ƙofar gidansu Iyya ya nufa ya tsaya ,yana ganin yaro yace “kiramin Halima “yaron yace “ace injiwa? Baba ya gyara zaman hular kansa kafin yace “,inji masoyinta ” yaro ya wuce kiran Iyya ,cikin sa’a ya sameta zaune tana gyaran shinkafa , ya durƙusa tare da cewa “wai ana kiran Iyya “Iyya ta juyo kafin tace “wai inji wa?” yaron yace “masoyinki “mahaifiyar Iyya dake jin maganar tasu tace “maza tashi amma karki manta kinada aure ” Iyya ta miƙe cikin bin umarni ta ɗauki mayafi ta fita , mutum ta gani a tsaye ya juya baya har wani ƙwambo yakeyi waishi ɗan gaye , juyowar da zaiyi idonsu ya sarƙe a na juna ,cikin sanyaya murya baba yace “haba Halimatu kiji tausayina mana ki nunamin soyayya irinta lokacin da muke amare “Iyya zata juya ,baba ya ruƙo hannunta kafin yace “,har yanzu baki haƙura ba ?”dan isar annnabi ki yafemin “darajar manzon Allah tasa Iyya cewa “na yafe maka ” baba jiki na rawa yace “yaushe zaki koma to ” kai tsaye Iyya tace “sai nayi shawara.

Baba kam bai tsaurara ba sbda ya sami abinda ya keso ya koma gida ,yau shine harda biyawa gurin mai tsire ya siyo tsinke biyu ya kawowa Inna da Tinene .

Kwana huɗu da faruwar hakan , aka dawo da kayan Iyya gidan baba , Tinene tayi murna sosai , malam kam ranar fara’arsa ta dabance .

Tunda Iyya ta koma gidan ya gyaru yayi fes ,a maimakon da Inna bata cika gyara gidan ba , Tinene kullum sai tayi wanka .

 

Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah , cikin ikon Allah Tinene nada shekaru 14 ƙirjinta ya fara cika da dukiyar fulani , ga gaɓɓanta daya ƙara buɗewa ,ta ƙara kyau ,amma a sokonci sai abinda yayi gaba .

 

Wata ranar juma’a bayan an sakko daga sallahar juma’a Tinene ta kwanta bacci har waje la’asar bata farka ba , sai ƙarfe biyar ta farka taji ɗumi a jikinta , da sauri ta miƙe dan ta ɗauka fitsari ne , tana zuwa bayi taga jini nabin ƙafarta , ta tsala ihu tana kiran Iyya , Inna ta fito da gudu Iyama ta fito suka shiga bayin cikin tashin hankali ” ganinta da sukayi a tsugunne ne ya sasu tsayawa turus suna kallonta ,Iyya ta ƙarasa gurinta Inna ta koma .

Bayan Iyya ta tayata gyara jikinta suka koma ɗaki , Iyya tayi mata bayanin rabe-raben haula da niyar wanka.

Bacci ne ya ɗauketa har magrib , sannan ta tashi tana mutsike ido , iya ta kuma yi mata nasiha akan duk namijin data yarda ya taɓata to tabbas ciki zata samu ,kuma ta dena yawan rawar kai ,

Bayan sati ɗaya.

Tinene tayi wanka lokacin har tafara sallah ,ranar asabar da daddare yaro yazo yace ” wai ana sallama da Tinene , cikin turo baki Tinene tace “uban waye ni bazani ba “Inna tafito kafin tace “haba Tinene ba’a wulaƙanta ɗan adam gara ki fita kiji da me yazo ” Iyya dake tsaye tace “tadai gama kore samarin shikenan…!

 

 

Mom Islam

Leave a Comment

error: Content is protected !!