Hausa Novels

Hausa Novel Wattpad Documents

Hausa Novel Wattpad

 

 

 

 

 

 

 

 

Hausa Novel Wattpad

hausa novel 2020,hausa novel 2022,hausa novel audio mp3 download,hausa novel batsa,hausa novel complete,hausa novel furuci,hausa novel masu dadi,hausa novel only,hausa novel wattpad,hausa novel wattpad 2021

 

Karin wasu littafai da zaku so

 

MIJIN TACE *1*

Humaira! Humaira!!humaira!!!bata jin wanannan kira ne ko kuwa? Daga can cikin gidanmu nake jiwo wadannan maganganun.Abunda yayi dalillin dana fasa shiga cikin gidan na kara da baya na tsaya ina sauraron mai maganar.
Cikin takaici da bacin rai na yanda ita kullum babu dama ta kira wani ta dan sa shi wani abu don in huta komai sai dai ne humaira.

Can cikin zuciyata na sake jan tsaki lokacin da haushinta ya sake kamani adalilin zuba ma kwanon dake hannuna ido danayi,cikin takaici saikace ba ita ta aiken ba harta mance tana sake nemanado sake aikana kamar nikadai ce agidan.
Maimako in shiga gidan inkai mata aiken nata musannan yada takasa daina kwala wa sunan,sai na makale jikin bango ina sauraro tare da yin tsokaci kanwasu al’amura dasuka addabi zuciyata.
Ko yaushe ne ma zan huta irin sauran yaran gidanmu?a lokacin ina yarinya na zaci halin danake ciki na takura da kunci yasameni ne saboda nice karama cikin yaran da suka kai munzalin moro.

Dunhaka nayita dua na bayana su kawo dun su karbe ni ,amma daga baya nagane ba haka bane tunda akwai was kannen nawa da tazarar watanni 10 ne tsakanin na dasu,Kamar su Suwaiba,kumasu din ba ayi musu irin aiken nan da ake min,abinda yafi komai bata min rai shine ko a gida daya abubuwan da ake bukata suke baza a hada aiken ba saina dawo a maidani.duk a dalilin kar a ganni zaune ina hutawa gakuma wasu kenen nawa da su sunada yancin a aike su suce baza su ba.

Babana mal Surajo mazaunin U/jahun ne dake jihar Bauchi ne kuma sananne dan kasuwane saboda haka mutane da yawa sunsan shi da kuma gidanmu.na bude ido na tarar da babana da matanshi na aure 2 da haj Majadan wace koma har a Unguwa ke kira da Mama sai kuma Innata wace nasha tabka akan kokarin sakaya sunnanta wanda a dalilan haka na hakura a shiga sahun kiran sunanta kamar kowa wato Gambo.

Mama ce Uwargida dun aure saurayi d budurwa sukayi dun haka take jindadi da gadara da haka,zan ma iya cewa gani take duk wace bata auri saurayi ba to aure na matar d mijin ba na sosai bane dun ko yayan dasuka fito da Amaryar ganitake gasunan ne amma ba ya’ya masu yanci ba. Shiyasa ma da yaran ta su isa munzalin aure ta kasa ta tsare tayi kememe taki yarda da mazan d babana kawo su aura. Dalili kuwa,saboda kada yaranta suyi bauta da diyan wasu, sabo dahaka samari gal a leda suka aura kuma a dole baba yayarda ya daura wa auty Sha’a awa da anty Kaltume aure da samarin da mama keso.
Mama mace ce mai son gadara da mulki,dun da kar rana tafito ha ta fadi batayi ma kanta kirari ba “Alh mijinane aure saurayi mukayi da budurwa cikin soyayya tun baya da ko kwabo, tun wanduna sakawanshi basu wuce biyu ba saboda haka ba wace zata shigo man gida a dalili iyayenta sun hangi arziki Tace zata kawo mani fi’ili.

Baba baya iya musa ma mama kullum a to yake wurinta gashi kuma tayi sa’a yana matukar gudun bacin ranta.Innata Kuwa zaman hakuri take yin dun in banda tanada iyyaye wadanda suke da tasiri mai karfi kanta da bata iya yinshi ba
Innata yar gatace dun yar autace wurin Mal mai babban allo a wurin mahaifiyarta kuwa itace kadai mace. Mal. Mai babban allo Mal ne ma karantarwa ga yara da manya ya na da mata 2 Haj Yar dubu itace 1st kuma uwar manyan yaran gidan duk sun girme Innata nesa ba kusa ba Don ma yayansu sune sa’o’inta wasu masun girmeta. Haj Turai ita ce 2nd kuma uwar Hasan d Husaini sai Gambonsu.

innata taso cikin Shagwaba da rashin kwaba da sagarcewa shiyasa Alh Maikudi baban dan Mal ya Dauke ta ya maida gidanshi gaban matarshi Kubra wace ke da yara 3 alokacin wato Abdullahi(abba) Auwal da Ahmed.
Haj Kubra kuwa tayi mata riko na gaskiya da amana shiyasa ta taso tamkar itace babar yar alh Maikudi mace dunhaka itama baba take kiranshi. lokacin d innata ta girma tazama budurwa manema tayi sosai duk da Alh bai yarda anje guntaba dun ya tsaya kan cewar Karatu zata yi duk d Mal. Bai goyi bayan haka ba,hasali ba shi yabada Umarnin Auranta ga baban mu saboda kamun kafar da baba yayi gun almajirin Mal mai babban allo wato Alh Yahaya wanda shi kuwa aminin babana ne , tare suka taso tun suna yan yara.
Alh maikudi ya aurar da innata lokacin shekarunta 15 gashi kuma gaba daya ansan mama da irin matan da takora a gidanmu da kuma raden-raden da ake yi na fin karfin mai gidan da aka cewa tayi. kowa cewa yake za a yiwa karama yar karamar yarinya sanadin Zawarci bai hana A.Maikudi kashe dukiya mai yawa gun hidimar auren nata ba.H Kubra ce tatsaya aka ba Inna daki 3 da falo mai dauke da toilet cikin shi kasancewar baba na matukar son auren yasa yayi musu yada suke so duk da irin tashin hankalin da ya fuskanta daga mama.Alh M wasan jika da kaka yake dani don kuwa ya dage kan inna yarshi ce shiyasa na dade bangani cewar bashine mahaifin Innata ba sai a wani lokaci da cikin dare na farka dakin yaran innar mu naji maganar Baba cikin yanayi mai karfi da alama akwai bacin rai cikin maganar tashi da na saurara sai naji yana tuhumar ta kandalilin da yasa mama tasata aiki bata yiba?banjin maganar innan sabo da shikin murya mai sanyi takeyi sai dagabaya ne naji tanacewa to tunda kace ita bata karya maiyasa intagaya maka magana ba zaka yi hukunci ba kawai sai ka tuhumaini? Baba yace haka zaki ce? Sai tace saboda inta fadi magana ko na musa baka yarda ,yace to kar kice an zalunce ki,tace zalunci kam ai Cikinshi nake sai dai kuma nasan da sannun mai sakayya zai sakamin dun kuwa ba zan yafe ba.saukar dukan baba a jikinta naji wai tamasa Allah ya isa shida mama.

Tuni jikina ya shiga rawa inata karkarwa kan gado narasa yanda zan yi in taimaki innata,Nayi kamar in mike in fito falo ko ya ji motsina ko zai saurara sai kuma na tuna da mama ta gaya mishi wai ni zamana a wannan dakin labe nake musu,komai suke yi shi da innata ina jin su,don haka ya hana ne kwana a nan ya fito dani tsakar gida saboda son tarage karfin mu”amallar dake tsakanina da mahaifiyata wacce ta tabbatar cewar ni ce farin cikinta.bisa dalilin yasa nayi shiru nasake komawa na kara labewa kan gadon namu sai dai hawaye suka ta gudu kan kumatuna.bansan dalilin dayasa innna ta ki kuka wanda da tayi da dukan bai yi tsanani haka ba, don watakila yaso tayi kururuwa yarda mama zata ji abinda ke faruwa tasan yayi hukunci kan karar da ta kawo mishi.Duk da baba ya daina dukan bankuma jin motsinta ba ,kwana nayi ido 2 ina kuka,dunhaka ina jin bude kofar da yayi ya fita sai nima nayi maza na diro kan gadonmu na shiga wurin inna. Cikin rawar jiki d rawar murya saboda kuka nace mata “sannu Gambo” bata amsa min ba sai ta kalle ne shikin natsuwa tace “Dauki Aliya da Sa’adatu ki dora su suyi fitsari ki wanke masu baki”. Nace to naje nayi yarda tace din,har na idar da sallah na gaisheta bata motsaba ,ban dade a wurin ba sai ga H.Kubra cikin Zurmemen Hijabinta.da alama daga idar da sallah Asuba ta fito kuma inna ce tayi amfani da wayarta ta kira ta.
“Inace ko dai lafiya fadimatu? Sunnan da take kiranta dashi Kenan, tace eh lafiya Umma” na gaisheta najuya na fita na kuma dakinmu na zauna ina tunani. Kan kace meye wannan? Tuni yan uwan innata sun cika gida wasu na kuka wasu nasakin maganganu a tsakar gida don neman a tanka ayi wacce. Za’ayi a wannan lokaci.

Tuni Mama tabar tsakar gida ta koma falonta ta kuma kama bakinta tayi shuru bata tankawa bakaken Maganganun da wasun suke saki ba don tasan karonta dasu.ana cikin haka nasake jin sallamar baba Yahaya tsakar gidanmu,H. Kubra tafito cikin natsuwa ta nemi wuri ta zauna a kasa cikin yanayin girmamawa,na cewa alh ya gaya maka ina nemanka ne saboda in bi umarnin da ka bani na duk abin da ya faru a cikin gidan nan,kai ne farkon wanda zan gayawa ba shi alh ba.
Ina bin umarni naka ne kamar yanda nake bin na baba da ya hana ni fitar da Fadima daga dakinta ba da izinin mijinta ba.ya gyada kai alamar gamsuwa d maganar tata Kafin ya tambaye abin da ya sake faruwa, ta ce “eh to ni kam bansan komai ba tunda baya kai kara kan laifukan da ake yi mishin, sai dai yayi hukunci na ganin dama saboda ganin komai yayi ana sharewa.in banda haka me fadima zata yi wa mutumi yayi mata iri abinda ake yi mata a gidan nan. Nan da nan ta shiga share hawaye tana fadin a rokan man shi kawai ya bani ita muji gida, inna yi jinyarta ta warke musan abin da muke ciki.Haj shi babba fa da hakuri aka san shi,kin kuma sani sarai ita mace komai gatanta bata da wata darajar da ta wuce dakin aurenta.tace “haka ne” ya ce to ina dalilin komai kankantar abinda ya faru a gidan nan baza kubar maganar a tsakaninsu ba sai kun shiga?sai kuyiwo gayya ku cika mishi gida? Ita Gambo bata laifi ne ? Kuma don yar gata ce a danginta da ke da Alh Maikudi sai ace ba shi da iko a kanta .Haj Kubra ta soma kuka tana fyace majina tace in tayi laifi sai ayi mata duka har targade?kuma menene laifin taki yiwa matarshi aiki?mai aiki na kawo mata ne?Inna Hajara taleko ta na sannu da zuwa Mallam,ya na daga ido ya kalle ta yace ia kuma duk kunzo ne kuna ciki?to duk ko fito koma ciki ki gaya musu nace duk ku fito ku bar gidan.in na bar nan kuma zan je in gaya wa mallam har da ku a rura wutar fitinar dake aukuwa a gidan nan.nan da nan suka fito suna tafiya soboda sanin matsayin baba yahaya wurin Mal mai babban allo,matsayin da tuni ya maida shi yazama dagida.yatsaya har suka gama wucewa ya kalli H.kubra ya ce haj kiyi hakuri kiyi hakuri na roke ki kar kije ki ce zaki gayawa wa Alh Maikudi munin Al’amarin tunda shi ma bai san hakuri ba.
MIJIN TACE *2*

Gambo da ke da ya’ya mata 4 a jere,kubra in aka barku da mijinki kuka yi yarda kuke so din kun mata adalci?I ke uwa ce ba sai na tsaya yi miki dogon bayani ba,kin san komai zai yiwu ne ku kaita inda zaku mantar da ita wadannan yayan nata?to kiyi hakuri kawai ki kuma rinka kwabarta duk da dia kin ki yarda da cewar yarki mai laifi ce,amma hakan ba zai sa kullum ki rinka goyan bayanta ba,don gyara kayanka kubra ba fa ya zama sauke mu raba,haka nan kana kin naka ne dun duniya taso maka shi.tace Alh nagode Allah ya saka da alheri ya ce amin ya wuce ya fita ita kuma ta koma daki Innata ta gyara abubuwan da ke bukatar gyara. Duk d watsewar da dangin inna suka yi aka bar H.kubra ita kadai,mama ta kama kanta sosai daga yawan zirga zirga balle aje ga sakin maganganu.baba yaya ya sake dawowa tare da wata dattijuwa Sidiya kowa yasanta da da mijinta gyaran taegade da karaya suke yi, ta shiga ta gyarawa inna targaden da babana yayi mata ta fito ya maida ita.
Ranan Haj Kubra sai magariba aka zo aka dauke ta.inna ta wuni a kwance shi yasa na wuni rannan hidimar dakinmu bata yi ta addabata da yawan aike ba balle aje ga tabkata da dukan da aka saba yi mani kullum.
Washegari sai ga baba yahaya da A. Maikudi ga dukkan alamu kuma daga masallaci suke tunda sudin makwabtan juna ne.Baba Yahaya ne ya fara shigowa gidan babana ya fito daga falon mama wanda dama nan ne wurin zaman shi ko da kuwa shi din a dakinmu yake.
Sannu da zuwa alhaji baba Y ya amsa kafin yace ni da A.maikudi ne ” nan da nan yanayin baba ya sauya yace to bari in bude muku falona mana ya ce mishi A’a izini yace in zo in rokar mashi yanaso zai shiga ya duba Gambo.

To, to ai shi kenan ,Baba ya sake fadi cikin wani yanayi ya kuma wuce ya shiga wurinshi. Har tsakar gidanmu A.maikudi ya shiga innata ta fito ta durkusa tana gaishe shi,bai wani tsaya wajen amsa gaisuwar tata ba,zuba mata ido ya yi yana kallonta.
Sunnu Fadimatu sannu kin ji,sannu da kokari”shi kuwa baba yahaya yana gefe yana kallon shi,shiga ciki Gambo ta mike ta kuma ciki suka kama hanyar fita waje yana cewa Yahaya baka yi min adalci ba,ka zalunce ne ka sani na kawo yarinyar nan inda ba za a yi mata adalci ba bayan kasan komai amma duk da haka kaje ka hadani da mahaifina.to nima nace ban yafe ba,ku hadu ku rufen da duka tunda itama abinda ta fada kenan aka yi mata wannan zaluncin.
Rashin jituwa mai tsanani ne yashiga tsakanani Alh maikudi da Alh Yahaya sai da Mal mai baban allo ya tsawatar. Mama tashiga sakin maganganu masu zafi a tsakar gida saboda taga baba ya dau matakin daina duka sai dai kawai yayi magana in an kawo kara Inna,”ni fa kar mutum yaga wasu gutayen iyayenshi marasa girma da sanni darajar surikunta sun zo su ma alh burga ya tsorata yayi zaton ko in ma a tsoracen nake” ta tabe baki tace “ko kadan ni din nan a gidana rashin jini ne rashin tsagawa,baka shigo sabgata ba ba ruwana da kai,amma kana doso ni da rashin mutuncika to kama ka zan yi in nada maka duka,ba mai kudi ba mai dala ne ma ina daidai dashi”inna bata daga ido ta kalle ta ba balle ta tanka mata.Amma duk da haka bata tsira rannan akan ruwan bunu ruwan tin da babu komai cikin shi sai ganyen tea mama tace wai Innata kwashe wa yayanta ita ta basu dan kankani. Nan ta shiga zagezage baba ya leko ya na tambaya menene ta galla mashi uwar harara tace “ai don kaji ina cewa zan bata kashi ka zaburo ka fito kana tambaya?I ko kana tsaye zan mata hakan don nagaji da irin cin kashin da ake yimani a cikin gidannan zan yi in gani ko nima za ayi min wujuwujun da aka yi da kai.ta zubawa iNna ido tana mata kallon wulakanci.ke nan yar gwal kizo gidan mutune kina masu rashin kunya saboda iyayenki basu maki tarbiya ba a tabaki suce za suyi ma mutane iskanci to ni ba Alh bace babu ruwana da iya shegensu maganinki zan yi ba Maikudi ba a turo min Mai babban allo in ya tashi zuwa kar ya zo da allon katako yazo da na karfe.

Inna ta kasa hakuri “A’a me iyayena suka yi maki?in dai kan ruwan tea ne to gashi nan na juye maki.garin juye ruwan tea wani ya dallu a kafar Mama nan ta fusata wai Inna ta kona ta ta shiga dura wa iyayenta ashar.Inna ta juya ta shiga dakinta tana fadin kiyi ta zage zagenki In kowa ya ji abunda kike fada yasa bada iyayena kike ba tunda kowa yasan su yasan ba mutanen banza bane. I ko mama ta jawo ta tana tambayarta nasu waye ne banzan?bata kai gabada amsa ba ta rufe ta da duk ta turmushe ta a kasa ta hau ta danne tana ta naushinta da kyar baba ya dagata ya kaita dakinta ta huci da zage-zage.haka kawai kaje ka dauko masifa ka kawo gida ba dole in tsaya in yi maganinta ba tunda kai kasa”yana fitowa daga dakin mama ya kai min maka kafin ya daka min tsawar da ta katse min komai.”Me aka yi da kike kurma wannan ihun kina nema tara min jama’ar Unguwa a gida? Shiru nayi na bi baba da kalo har ya shiga wurin shi,an daki innata an farfasa mata baki da hanci amma ina kuka ya make ni yace wai ba ayi komai ba.na faki idon mutane na fita na bar gidan na taka da kafata har makama extension na gaya wa Haj.Kubra abinda ya faru tace “duka” to ba laifi zauna ki karya kiyi wanka ki sauya kayan jikinki sai ki koma gidanku nace “To”ina dawowa nasamu inna cikin wani yanayi ko dukan da baba ya yi mata dangin Inna suka yi ta kai kawo akai da fadin maganganu bata ji jiki irin wannan ba.ciki zuciyata nace wato ba banbanci tsakanin dukan miji da na kishiya? Da yamma sai Ga baba Yahaya agaban Baba mama tayi wa Baba Y wankin irin na babban bargo,ko dama can ta dade tana da cikinshi do bata ambatan sunanshi sai dai tace Mishi Munafuki.haka bata zuwa hidimar gidanshi wai shi da matanshi sunci amanarta. Baba Yahaya na ganin haka ya juya ya fita ya bar gidan ya barta tana zage-zagenta tana hadawa da baban namu har tana cewa tunda ya kasa ita zata yi maganisu,wai tananan tana jiran A.Maikudi zata nuna mishi bai da wayo har baba ya gaji ya fita. Mama bara gaji ba,sai fadi take kan ki na fara ganin kishiya?guda nawa akayi mani? Ke ce ta 6 ke ki ka fi kowa?shafaffiya da mai,kizo min gida ki gallabe ni ke din banza! To zantasa ki gaba zan ga yanda za’ayi kiyi zaman gidan nan,sai dai ko mai kudi ne zai tayaki zaman ko.
Ana haka sai ga Haj kubra ,ina ja’ira. Mama mara mutuncici to dun kin daki fadima sai me? Sau nawa kika haife ta? girman da take baki kina rainawa yau ya kara zubewa,haka kuma ba zai hanata sake hada shinfida da mijinki ba,tsohuwar banza kawai.a fusace mama ta fito tacewa ke ce kikazo baki turo Maikudin ba?Haj kubra tace ai sai abinda yafi karfina ne kike ganinshi kekuwa ni ce zanyi maganinki sakarya banza wacce uwargidancinta bai amfani mijinta da komai ba,tsohuwar da ta rasa masu zaunar da ita su gaya bata gaskiya
Bansan yada akayi ba sai naga Haj Kubra tayi jifa da gyalen da take yafe dashi kankace meye wannan tuni danbe mai tsanani ya kaure a tsakanin su sai ji kake didim didim!!!
Dun kuwa dukkansu ma’abotan kibane sai dai kan kace meye Haj Kubra ta kai Mama kasa tim! Abinda ya firgita gida gaba daya. Habiba ta kasa hakurin kayan da a ka yi wa Uwarsu ta sunkuto tabarya tazo zata rafkawa haj Kubra cikin kuskure da rashin dace sai kawai ta sake timawa mama tabaryar a gefen fuska da iya kacin karfinta.

Habiba tayi waje a kidime neman tai mako,Haj Kubra najin za sushigo tayi maza ta daga mama da ke kwance jijajina ta sulale tayi ficewarta tabar mama na wa makwabta ransuwar alkali ne zai raba su da mama sukuwa sai fadi abin kam baiyi dadi ba a gefe kuwa sai dariya mama suke don babu wanda bai san abin da gidanmu yake ciki bama.
Jinya sosai mama tayi da su zuwa asibiti, da su hoto duk rantse rantsen da ta yi na daukar mataku da zuwa koto duk yatashi a banza,iyaka sake tasa babana ta yi da fitina wai anshigo har gidan shi anci mutunci iyalinshi bai yi komai ba,kan haka har iyayenta sukazo suka sa baba gaba ina jinshi yana mayar musu da yanda aka yi duka,sudinma basu yarda da shirrun da baba yayi ba sunce in yana haka a gidanshi ai sai ayi abinda babu kyau,duk dai sun gaya wa mama rashin kyautawarta kan cin mutunci abokin mijinta da tayi gaban mijin nata
Tun rannan kuwa ban sake ganin yunkuri dukan Inna ba dun H.kubra ta gaya mata in ta yi maki laifi ki fadi amma duka tsakaninki da ita babu inkuwa kikayi ganganci kikayi to zan maki irin wanda na iya,dun ba baiwarki bace matar mijinki ce irin amfanin da kike yimashi irinshi take mashi ba kuma sai nace miki yana sonta ba tunda kina ganinta da ciki da goyo,dun haka kiyi kadan fitinarki taraba ta da mijinta. wadanan maganganu sun sosawa mama rai dun har baba ta rika nanata wa yafi saunawa.

“Ni ina Humaira taje ne?maganar da na sake jiwowa kenan daga cikin gidanmu wacce tayi dalilin katse min tunanina nadawo kan abinda nake ciki a lokacin bakin ciki da takaicin mama suka sake lullube ni,don kuwa kuwa kowa ya sani zan yi mu’amalla da mama ne kawai bisa tsoro amma ba don so da kauna ba.wannan dalili ne ma yasanya ni na zamo mai iya kwaikwayon mama da al’amuranta duka babu wani abin da yake yin shi dabi’ar ta ne da bana kwaikwayon shi.ko a yanzu ma na shiga kwaikwayon maganar tata, Humaira maam zo ga wanki,to na yi, Humaira naam zo ga shara, to na yi. Humaira na,am zo ga …..
Mama kike kwaikwayo?da iyakaci karfinta tayi min tambayar,nayi maza nabar abinda nake yi cikin kaduwa na zuba mata ido alamun tsoro ya bayyana a fuskata.Habiba ce yata da nake bi ta dakin mama wata 20 ne tsakanin mu abinda kullum mama take nanata gaya min kenan duk sanda abu yashiga tsakanin mu zata jaddada min ko sada uwarki tazo gidannan ta samu Habiba na da wata 11 kekuwa wata 9 daidai tayi ta haife ki do ko kamar a hannunta ta shigo dake, ba wannan bayyanin ya zama dole in yi wa habiba ladabi da biyayya irin wanda bata ba uwata 1/10 tunda zata aike ni ta sani aiki ta mani hukunci ita kuwa Innata bata isa tayi mata ba, ni har suwaiba kanwar habiba dake dakin mama wada na girma da wata 9 dukana take yi,bankuma isa ince zanrama ba sai mama da habiba su rufeni suce wai cin zalinta zanyi
Mama kike kwaikwayo za ki gamu da gamonki kema kin san saura ta yi magana cikin yanayin jinjina.

Na zobara baki na bata rai sosai abinda nayi ya bata haushi ta kawo hannu da nufin buge min baki nawa na maza na kebe hannu nata tare da fadin “A’a me nayi ban yafe ba tayi maza ta sake kawo min bugun nima nasake cewa banyafe ba muguwa kawai azzalumu.Ado ya leko cikin zaure Mama na kiran ku,Ado kanin mamane uwarsu daya uba kowa da nashi, ta dauko shi ne daga kauyensu ta kawoshi gidanmu. Ita d da baba suka maidashi gatan gidanmu saboda irin son da mama take mashi.lokacin da yazo shi din ba kowa bane face dan dogo yaro dan sirriri dan baki,dan bagidaje bagidaje kana ganin shi kasan daga kauye yake,ko gajiya da aiki bai yi don ya saba yin wanda ya fishi.in kuwa aka cika mashi kwano da abinci ya cinye shi tas amma sannu a hankali aka wayi gari Ado ya murje ya zama kosashe ya zama wankan tarwada dan gaye ba zaka taba ganinshi ka gane bai dade da fitowa daga kauyensu ba. Kankace mai har ya murje yazama dan birni santalelen saurayi,saboda ya samu ya dare kan dukiyar babana ba wannan ne abin da yafi komai. Kona min rai ba sai iri zuwa gidan mu da yayi da takardarshi ta kammala secondary wacce ko credit din da ake nema bai gama samu ba amma ya gyara jarrabawar a gidanmu ya tafi Fed Poly yayi diploma yasake dawowa ya shiga ATBU yayi digiri amma gaba daya yan uwan na maza wayanda maman ce ta haife su suna zaune gida suna sakarci sunki karatu suna ki tsayawa kan alamuran Baba

Komai na gidanmu Ado ne yayi matukar shiga ran babana bai gajiya da yabonshi,mutane dasuka san gidanmu sunsan mama da dan uwanta Ado sune babar matsalar da babana ke fuskanta amma ba rashin kasuwa ba.sai dai mama kullum na danganta matsalar kasuwar baban nawa da yawan aure-auren da take cewa yayi,musamman wai aure shi na bayabaya wanda aka rufe mishi ido yayi ta kwasar dukiyarshi yana bayarwa.
Tun farko zuwan ado gidanmu ba jituwa nake yi da shi ba saboda bai taba shiga harkar innata ba bai taba samun lokacin daga ido ya kalle ta balle yasamu na lokacin gaisheta hakanan yayanta bai mu’amaLla da su iyakar shi mama da yaranta.itama mama mai yanuwa da yawa ce sai dai ba wata mu’amalla ta kuzo ku gani take da su ba sai dai yan uwanta da ta hada uwa dasu.bisa wannane ma yan uwanta na uba ba kasafai suke zuwa mata ba saboda komai nisan garuruwasu nata yarda bakuntar su ta wuce kwana 3 sai kaji tanace wa sai da ka zama mutumne fa ake nemanka amma kana karami menene baka gani ba?
Muna shiga gida habiba tace “Kwaikwayonki take yi mama” Kwaikwayo kamar yaya ? Dun bukatar karin bayani Habiba ta samu damar da ta tsaya bayani sosai da sosai na abida ta tarar ina yi. Maman take wa iya shege?babane ya kara yin tambayar, na kalle shi tamkar yau ba wurrin inna yake ba dun ran girkin inna sai ya faki ido yake shiga in dai bakarta aka kawo ba zai shiga yayi mata hukunci nan ne zaka ga yashiga kai tsaye baruwanshi da hakki saboda mama bata yardar mashi baiwa mai hakkin hakkinta
Abubuwan da habiba ta kwatanta suka bayyanawa baba abinda nayi dun haka ya baiwa babana takaici ya zuba min ido,yana kallona cikin takaici da bakin rai mai yawa shiyasa na waiwaya baya do ganin wadanda suke tsaye.Ado da Habiba wadanda su dukan su biyun ana cewa za’a kama ni zasu yi sanadin da za a yi haka.to ba dole ta yi kwaikwayona ba I gata gareta mai yawa a gidan ‘yar lelen Baba’

Baba ya ce ‘ bafa naso kina min haka gaban yara ni nace miki ina da yar lele ne?mama tace Alh kenan bari naja bakina kawai in yi shiru tuda bani da ikon yin magana sai ka hayayyako gaban yara tunda nice marainiyar wayonka amman in banda haka iya shegen da yarinyar nan take yi da wani ne wanda ba a tsoron uwarshi da danginsu ai da nai kwashe kalay ba,sai dai ne ma bani ganin laifinka da azo ana tuhumarmu kan abin da bai taka kara ya karya ba ai gara muyi ta hakuri.da irin wadannan Kalaman mama Ke tuzura baba tasa shi yayi abinda take so yayi min hukunci irin na azabtarwa,shikuwa ya kasa tunawa kanshi cewar su dangin inna basu taba zuwa sun same shi kan wani abin da shi ko mama ko wani can daban yayi min ba duk kuwa da sun saba ganina da tabo,mikewa da naga babayayi yasaya ni juyawa da gudu na ko banke habiba dake bayana,shi kuwa Ado na kwantara mishi kwanon dake rike a hannusa, man gyadan dake ciki kuma ya kware mishi a fuska da jiki gaba daya. Mama ta kama salati,baba yace kamo min Ita Ado kamo ta maza in baka bulala ka hukuntata ja’ira mara kunya.mama tace wannan shi ne wani zance kai baka hukunta al’amarin gidanka ba sai Ado salon kaja mishi karin bakin jini, itada ba so suke su bude ido suganshi ba a cikin gidan nan. Baba ya biyo ni tsakar gida inda nake tsaye ina ta faman bari, ina kuma kuka saboda na riga na tsorata da abinda zai same ni.innata kuwa na sunkuye tana wankin kayan yaranta Ba ta daga ido ta kalle ni balle tace meke faruwa? Baba ya shiga cewa shakiyancin banza shakiyancin wofi mu nan gidan ba a kawo mana shakiyanci dama kin yi maza kin bari do wahala kawai zasi yi ta ja maki, ya shiga shira min bulala wacce yasa Suwaiba miko mashi ina ihu ina buga tsalle ina faduwa kasa don tsananin gigicewa, sai da mama ta tabbatar na jigata ne ta fito daga daki tana “ni fa bana so irib wannan ja mini maganan da kake yi kasan halin ja’ira yarinyarnan ba a tabata ma ihu take yi don dai ta kulla wa mutane sharri a Unguwa ace gatanan ana azabtar da ita tunda tasan da yan sa ido to balle nantaba ta”yana huci yana to ina ruwana zafu hanani yin hukunci a gidana ne? Mama tasa hannu ta karbi bullalat ta na fadin ai kuwa dai magana abin a guje ta ne,ne bata kudi man gyadan ta sayo min tunda wancan din a gabanka ta kifar dashi, nawane kudin? Ya tambaya yana fido kudi a aljihu shi tace “kwalba 2 ne” daga ni har shi barin abinda mike yi muka yi muka kalli mama dole na bar kuka na zuba mata ido shi kuwa ya tsaida hannu a aljihunshi ya bar zaro kudi.

Kwalba 2 ne? Ya bukaci sani? Tayi maxa ta daura fuska tace to zanyi mata karya ne ba gata ba? Tambaye ta mana,ne kam da baba bai yi kuzarin tambayata ba kiris ya rage in bude bakina in karyata mama in ce gongoni ne 2 ne ba kwalba na. Sai naga yinhaka bazai amfane ni da komai ba tunda ba zai hana babana biya kudin kwalba 2 ba ni kuwa insake shiga wani matsanancin hali dun cewa zatayi na karyatata a gabanshi yana kallo ko a ce innata tasani yin haka tunda kullum laifina na innata ne “ke da masu koya maki iya shege zan yi maganin ku zansa kafar wando 1 daku”abinda ya ci gaba da gayamin kenan.bayan ya ba mama kudi ita kuwa ta kerbe su ta juya tafiyarta bata sake aiken nawa ba wa kar insake kifar mata cikin zuciyata kuwa nasan ba saye zata kara yi ba,a kullum irrin kaamun Baba kan furta an koya min halin tsiya ,hudumar banza,an cusa min dabi’ar da bazata anfanene ba alhali shi bai taba kama wani ko jin wani yana min daya da ga wadannan abubuwa ba da ke faruwa,illa iyaka mama take gaya mishi nayi,kan haka ne ma magana baya yi wada ta shafi muhimmain abu ne a gabana sai tanuna mashi ne ta hanyar zunde ta ce dama kayi shiru tunda ga yan baka nan a kusa.Amma ta yarda yayi a gaban su habiba wadanda a wajenta wasa zaka ji suna fadin babanmu yace kaza yace kaza in magana zatafito bace akesun ji bane sai mama tace I tahana shi sakin bakinshi gabana yakine shiyasa tasa mashi ido.
Gidamu anyi karancin yara maza dun ko dakin ina 3 ne mata 5 to bale dakinmu da ko namiji 1 babu sai mata 4 ne,to amma mazan da sun ci ace sunyi nisa Baba da ibrahim don sune a gaban su aunty anty Kaltume sunki karatu kuma mama na kallo su babu bako babu arabi sai gata a gabanta ado yazo yayi karatu wanda har yau kuma ba barin karatun yayi ba ga kuma kasuwance ya tsunduma kanshi shikin al’amarin babana wanda mutane ke ce wa jaruntakarshi ita ce kan gaba wajen saman mishi fada mai yawa,shi ne aika shine wanken kayanshi ya goge dun zuwan ado ne baba ya daina kai wanke da gogar kayanshi,ga wanke mota ya share gida ya sare bishiyoyi wanda ganye yayi yawa,bakuma sashi ake ba she kesa kanshi.gashi ya iya girmama babab da dattawan ungwarmu duka.amma ya Ibrahim ankale su suna yawo kan baburan da mama tasaya musu da kudinta da baba yayi magana ta ce kai alh kai baka saiwa yara ba bayan ga sa’oinsu nan sa ma wanda basu kaisu ba wasu har da motoci iyayensu suke sai musu yace da suka tsaya suna yiwa kansu abin arziki ba? Suna bin umurin iyayensu suke basu suma sun tsaya kan karatunsu kamar yanda wadancan din suka tsaya me zai hana in saya musu ai taimakon kai ne da kullum ka baiwa yaro kudin motar makaranta da kasuwa I gara kabashi abun hawa to su wadanna basu sa komai gabasu ba sa la…..”Tayi maza ta katse shi ta hana shi karasawa ta ce “a’a kar kayi musu baki gara yauwa she karatun boko ai ba shine kadai hanyar arziki duniya ba dun da shi kadai ne da baka samu ko kwabo ba”

Ta juyar da fuska can gefe ta daina kallon inda yake,gashi kaida ne kuma wanda ya kai musu abinci ya kuma ya kwaso in sun gama ci akuma yi musu shara,ga abokanasu sun fi kowa mutunci wurin mama,ana cikin haka suka tasa mama gaba wai su a bar su su koma daya gidan na baba wanda Ado ke ciki tunda Baba baya so abokansu suna shigowa gida, daga farko baba bai yarda ba amma mama ta dage to menene ba gashi manne jikin wannan ba ga kuma Ado a ciki?dole ya hakura suka koma nima na dan ji dadi duk da Dai ana tura ni kai musu abinci in debo kwanuka sa musu shara,a fili yake gaba daya yara mama mata da mazan dama ita kanta basuso na ba halin in dan zauna cikinsu sai ka ji suna cewa haka kawai muna zaman zaman mu baba ya auro wannan matar ta haifan mana wannan shegiyar da zan kalle su don sanni ni da uwata suke zagi ka ji sun daka min tsawa dai na kallo na in ba haka ba in buga miki rankwashi, wata ranna ko nayi maza na daina sai sun bi ne da rankwashi. daka Da tsanar da a kemani a gidan mu wurin dagin inna fari jini ne da ni tun ma ba Alh mai kudi da Haj Kubra ba dakuma mal mai babban Allo Haj Yardubu ita kam Haj turai yarda bata kula innata haka nima.
Kwata kwata shekaran inna 13 da aure yayanta 6 wanda Ni da atika da aliya jere muke sai Zainab d kubra su babu su sa’a Sa’ada2.yawan haihuwar inna ba karamin damun mama yakeyi ba wanda a wannan lokacine ta kawo ka’ida in kana goyo to bakada girki kuma makazuwa gun miji ko she ya zo wurin ka,kowa yasan dun taga haihuwa ta tsaya mata ne yasa ta fito da wannan ka’ida amma tunda wanda akayi dominsa ya yarda shiyasa innata bata tanka ba sai dai inna ba girki ne bata yi ba kamar yarda ka’idar take wai don kada yaro yayita kazanta to amma mama kusan kullum sai tayi cefane ta ajeye ta fita Unguwa.
Da ina tasowa nayi zato kwatakwata so inna ne baba bayayi ina soma wayyo na na gane shakku ne mai yawa tsakaninshi da mama na kare yarda da hakanne a dalilin ganewar da nayi cewa mama tana sanya kafarta waje tabar gidan dun kusan kullum sai taje unguwanninta to shikuwa zai bar kasuwarshi sai ta tabbatar ta kusa dawowa sannan zai fice ya bar gidan yana shigowa gida kuma wurin inna zai nufa wurinda bai rabuwa da tsabta da kamshi dub iyayanta masu yimatane bata nema komai tarasa ba har turaren daki na jiki namu na yara kawo mata ake yi.

Baba na shigowa gida in dai mama bata nan to zaka ji yana magana cikin natsuwa ina fatima take? ko kuma ke Humaira ina mamanku?ina gaya masa sai ya nufi inda take sai dai inna bata sauraron shi,innata mai kyau ce gata da kwalliya ga tsabta duk da nasan ta ne a shekarun da tayi matsalolin aureta haka bai hanani sani kwaliyarta ba
MIJIN TACE *3*

Ranna mama bata nan tun safe ta bar gidan ita da su suwaiba baba ne ma ya dauke su a motarshi ya tafi dasu wai anyi mata haihuwa in da inna ne kawai a gida sai ko sa’adatu su atika. Suna makarantar allo ni ta taimaka ma inna ta gama aikin abincin rana da mama ta fita ta bar mata ta shiga dakinta dun yin wanka bayan mun gama ni kuwa na tsaya gyara kicin din da muka yi aikin ciki. Ke Humaira ina Innarku take? Nayi maza nace sannu da zuwa baba ta shiga wanka,Ado ya shigo ya ajiya cefanen da yazo dashi baba ya kalle shi ya ce koma shago sai an yi sallah sai kazo ka dauke ni cikin ladabi yace mishi ti ya tafi baba ya shiga wurin inna bai dade ba naji inna tana cewa ina kike? Kawo min ita nace to nage zankaita tana zaune kan kujerarta ta kwalliya ta ga ban mudibi baba na tsaye bayanta yana magana a hankali tare da kallon abunda take. Na garan gashi.ke fa halina dake kenan kenan ba halin in dawo gidan nan saboda ke sai kin bata min rai,to ka daina dawowa mana nayi maza na ce gatanan susan nashigo dakin har ta mika hannu zata karbe ta sai kuma ta ce min shiga ban daki kiyi mata wanka don kar ta bata min jike nace to na je yin abinda tace duk da kukan sa’a ina cikin mata wanka nage baba Yana cewa me kike nufi ne?tace abinda nake nufi kenan mun zauna kamar yanda aka ce mu zauna. Ya fara magana kamar zai yi fada cankuma ya canza yana cewa ke baki da wayo tace iai nima nasani. Zo ki ji abinda zan gaya maki nafito da sa’adatu zan bata har lokaci bata gama shafe jikinta da mayukan kan madubi nata ba wanda ne nakawo mata su daga gida Alh Maikudi,ke fita da yarinyar nan baba yayi maza ya daka min tsawa na bar dakin na fito tsakar gida ina rarrashinta na goyata na nufi zaura naja na tsaya ni kadai zikina na bari tsoro abinda zai faru tsakaninsu tunda na fara jin baba na ce wa tunda kince baki jin rarrashi to kuma wannan abin da ya shafe kine kinsa baki isa ba.

Lokaci mai tsawi baba ya dauka bai fito daga dakin na tun ina tsorace har na hakura na shiga sobgogina tunda ita ma sa’ada2 tayi barci.zuwa can naga ya fito ya shiga wurin shi ya dan dade kafin ya sake fitowa yazo zai wuce mu a zaure ya kalle ni yace min kai mata ita ta shimfide ta nayi maza nace mishi to,ina shiga shiga daki gabana ya fadi saboda kukan da na same ta tana yi gashi gaba daya kwaliyar da gyaran gashinta sun lalace,tasa hanu ta karbi Sa’a suka kwanta tare tana bata nono ni kuma na fita dun bin umarnin da tabani na dora sanwar abinci dare. Kullum ka’idar baba kenan mama tana barin gida zai dawo yasamu inna ko da dawowar na shi zai zama dalilin fadansu yatafi ya barta tana kuka ya gwanmace yin hakan
Wurin dangin baba INna ba wanni farin jinni ne da ita ba saboda saboda mama ta riga ta saye si da yan kyaututuka gashi kuma ita innan a cikin kulle mai tsanani take don ko nan da can baba bai barinta taje koda ko abida ya shafi dangintane sai dole takai dole.yan uwan baba da suke so inna sune na suka hada uwa da uba wadanda mama kuwa ke mu’amalla dasu sune na uba daya dun dun a cewarta na uwa daya uba daya su da uwarsu ma’ana kakarmu basu nufinta da komai sai sharri dun sunfi kowa son gani baba na aure,
Wata rana kawar Mama Haj Anwama tazo sai naji suna maganar inna inda har suke ta maganar inna da tsaftar ta wai da ta samu wurin sakewa sai yaya? can naji Haj anwama dake ka kallon Inna tana taje gashin kanta da tagama tsefewa tace uhun ni kam da za’a barni da nace yarinyar nan ciki ne da ita. Mama ta zabura da sauri cikin kaduwa tace ciki? Kai haba wani irin ciki to aina ma ta ganshi? Ita ba fita take ba balle ince suna haduwa a wani wuri shikuwa ba dawowa gida yake yi ba in bana nan tunda ai ko da nake fita unguwa da yaran don bana barin su balle ace sune zasu girkin dana bari ai kullum ina tambayar Ado da bana nan kun zo gida ne? Sai yace min ni dai nazo na kawo cefane innace Alh fa? Sai yace a’a shi bai lura ba cikin zuciya nayi mamakin jin yanda duk da baiyananniyar kiyayyar da ado ke yiwa innata ya ki yarda ya gayawa yarshi gaskiyar abinda yake faruwa tsakanin baba da inna in bata nan,mama ta sake cewa aminiyarta kinsan ita din bata rabuwa da shafe shafe kullum a shi yasa nake cewa ita din ba wata fara bace mai ne kawai ya maida ita haka.

To bazan miki musu ba amma ni dai nasan matar da aka hana miji ya kama hannu tsabtarta da bantake da irin ta wannan yarinyar.kalli kyan kitson da tsefe ke da kike da mijin kalli kitson da yake kanki. cikin zuciyata na amince da cewar ita haj Anwamu mata ce mai auna komai a mizanin hankali,don kuwa ni da kunnena nasha jin babana a irin tanakun da yake dawowa wurin inna in mama bata nan yana cewa inna. nafa gaji da ganin wannan kitson a canza min shi a kuma zizara min lalle in gani in dan ji dadi,wani lokaci ma zan gan shi yana bata kudi masu dan auki yana cewa ki sayi sabbin under wears ki kuma ki kuma bada sabin gunkuna tunda nasan kinada sabbin zannuwan da ba a dinka ba,kuma a lokacin ko bata tanka ba zakaga tayi abinda yace din zata kuma nuna mashi in an kawo dunhaka nayarda yawan kwalliyar ina har da kulawar baba.

Sai dai duk wannan hannunka mai sanda da aminiyar tata tayi mata do ta lura ta sa idoko zata gano abinda ke gudana ta ki yarda ta mace taja ta tsaya kan cewar ai shi babana ba ma zai kwatanta wani abu makamancin abinda ake zaton ba don yasan karonsu da ita.ban da haka ma ta riga tayi sa’a ba binda ya ke tsoro kamar bacin ranta in ban da haka ai zama da wadannan bai zamo mai sauki ba a wurin kullum fa sai tsohon nan ya zo gidannan wai yazo ganinta sai kace shi kadai ne ya haifi ya duniya,haj Anwamu ta rike baki nuna alamar mamaki tace ai fa da walakin goro a miya kinsan shi fa yayanshi da jikokin shi da ake aurarwa inda duk suka je ai karbe gida suke yi in banda nan din. Mama ta gyada kai alamar jindadi cewar da aka yi ita kadai ce ta gagara.

Mama da yaranta sun tsani ace ni din ina kama da baba balle ma idan baban ya yi subutan baki yace ai duk gidan nan babu mai kama da Alh Surajo sai humaira sai kaga tana fadanta kuma da iyakacin gaskiyanta rai bace wai wannan ai wulakanci ne ace duk yayan gidannan ba’a samu mai kama da alh ba sai wannan mummunan yarinyar to ta ina kamanni nasu yake ku nuna min do in ganni.sukuwa inna da danginta sundage kan ban dauko komai na innata ba.
Ko kadanni din bana kama da innata do kuwa ita farace sol ni din baka ita mai dogon gashi ni kuwa matsaikaici Sai dai akwai laushi da santsi da cika,ita dara-dara idanuwa in kuwa madaidaita ne.

Rannan muna kwqance ni da innata nace mata kamar ki bani gashin ki ta maza ta juyo ta kalle ni cikin yanayin murmushi ta ce na ki fa? Nace nawa ba mai yawa bane irin naku ke da su atika su kam sun ji dadi kama dake suke su masu kyau farare sol-sol ni kuma baka mumm…..kan in karasa tayi maza ta daure fuskarta nima nayi maza nayi shiru,wayace miki baki muni ne?ta zuba min ido tana kallona sannan ta dan saki fuska kadan ko kadan baki da muni kuma bazaki yi ba, ko kin ji ana ce maki mummuna kar ki sake damuwa ki dai sa maranki natsuwa da zama mutuniyar kirki mai kamun kai da natsuwa,mai girmama na gaba da ita mai jin maganar iyaye mai maida hankali akan karatu mai jin tausayin kannenta kinji ko? Nace inna, can kuma tace kin fara girma yanzu kuma ke din mai manyan barage ne, amma duk da haka ina so kiyi karatu tunda ni ban samu damar yi ba don haka kar ki yarda ki kula kowa kiyi karatunki kawai nace to.
Yawan maganar karatu da inna ke mani yasa na zamo ko a bani kudin makaranta ko kar a bani to zan taka da kafata in tafi makaranta secondary ta kofar Fada inda muke karatu in an tashi sai I karasa gidan mallam Mai babban allo in ci abinci in huta in na yi sallah in zo gabanshi in biya Alkur’ani da kuma littaatafan sannan ya bani kudin motar in shiga in dawo gidaa.kan haka mama take cewa baba wai ba ina zuwa makaranta don nafi kowa so karatun bane a’a ina zuwa ne saboda inazuwa ne saboda gidan mai babban allo su kuwa Habiba basuda kowa a wurin shi yasa suke fashin zuwa.

Rannan na dawo gida daga makatanta da yamma cikin gida sai innata sai kuma baba shi kuwa ya dawo ne a dalilin yasan mama da yayanta basa zama,nayi zan shiga falon inna na ji baba yanacewa kai kukan mata sai a barku, wato ashe duk ta sani a gaban nan da aka yi a kanki bin ta bai ishe ki ba? Ke kin fi son dai kiyi ta ganina cikin fitina?ki boye ciki a jikinki wata 7 baza ki gaya min ba sai yau? Alhalin kuma na tambaye ki yafi sau nawa in akwai shi ki fada don a san yanda aka yi dashi tunda ina anfanin fitina? Inna tace babu, to yanzu yaya za’ayi kenan? Ta sake ce mashi ai ban sani ba kai nake sauraro yace to kinga ni banaso abinda zai tayar min da hankalo, ina ga asibiti kawai zamu tunda kema gashi ko yaye yarki baki yi ba, bata ma tafiya,uhun sannan ana ganewa sai ace baki da miji amma ga ki da ciki ya kenan? Inna tace kana nufin acire?ya ce eh to kinsan wani abin dole kan saka kayi shi ba don kana so ba ni fitina ce bana so. Tace to sai ka gaya mata kawai ba naka bane yayi maza yadaka mata tsawa ta hanyar tambayarta wane irin zancen banza ne wannan?nan take ta soma kuka tana fadin ita ya maida ita gidan su ya taimake ta ya mayar musu da ita tunda ita bata da halin zuwa da kanta su barta ta zauna,inna ta urunce da kuka gaba dayanta tana fadin ya mayarwa iyayenta da ita tunda akan tsoron kar matarshi tasan tana da ciki zai kaita wurin haluka hankalin baba yayi matukar tashi. Ya shiga fadin ni binta?ni da bakina nace ki zubar da ciki?na ce muje a san menene abin yi? Nayi sallama a bakin kofar sau 2 kafin ya amsa na shiga ina wucewa zauwa dakinmu shi kuwa yayi maza ya fita watakila dama zaman ya ishe shi?
Washegari kuwa da safe sai kuwa ga katon cikin inna ya baiyana tanfar dai dama wani abu take sawa tana daure shi dun ko mainyan riguna da hijaban da take sanyawa yau taki zani da riga ta saka da tayi wanka ta gama kwalliyarta ta fesa turare ta kuma shiga zirga zirga da kaiwa da kawowan da ta saba ba a dauki lokaci mai tsawo ba kuma na ji mama na wani irin firgitaccen salati a tsakar gida

Wannan menene ki ke son nuna min shi Fatima? Ciki kuka yi bab sani ba? Lalle yau za’ayi abinda za’ayi a gidan nan,dama cin amananata kuke yi kuna satar Kwanana?inna kam bata tanka mata ba,ailinta kawai take yi mama kuma sai faman zuba ashar take yi tana fadin su habiba duk su fito su kira mata baban duk inda yake”inna ta bar tsakar gida ta dawo dakinta tayi zamanta na kuwa san in ban da tasan ba zata taba inna ta kwana lafiya ba da ta gwada yin hakan. Ranna cikin dare ba mu san abin da ya faru ba iyaka dai iyaka dai da sassafe naga baba ya shigo dakin inna na ji shi yana ce mata to bukatarki ta biya binta kin nunawa mama cikinki kin tayar mata da hankali kin yi sanadin da tayi yaji ta bar miki gidan shi kenan ko? Inna tace tana da gata ne tana da wurrin zuwa ni da bani da wurin zuwan ba gashi “yayi maxa ya katse ra muje can dakina sai muyi magana inna ta ce wa?tafdijan
Rannan baba ko tsakar gidanmu bai leko ba yana dakin inna suna ciki su 2 gaba daya hidimar gidan ni aka bar wa har abinci rana sai bayan azahar na fito ya shiga wurinshi yayi wanka ya tafi masallaci da ya dawo a ci abinci ne na ji yana cewa bari in je kasuwa in ga abinda suke ciki tace mishi a dawo lafia” har washagari mama bata dawo ba a dalilin baba bai je biko ba duk da aiken da aka yi na ana neman shi, gidanmu ya zama gwanin dadi sai murmushi yake yi yana hirarshi maimakon da da kowane lokaci fuskarshi a daure. Kwanan mama 2 sai ga baba Yahaya ya dawo da ita. Da alama shine yaje bikon ta kuma ta biyo shi duk da cewa da take yi shi din munafuki ne. Mama ta dawo gida cikin wani karin zafin ita kanta dai kana kallonta kasan tana cikin bacin rai mai tsanani ban da haka kuma kollo daya zaka yi wa fuskarta ka gane ashe ba karamin gumurzu suka yi da baban namu ba kafin ta tafi.
Tsakar gida baba suka zauna shi da baba yahaya da maman suna maida magana don maman ce ta nemi ayi hakan duk da shi da ya kawo ta cewa yayi to ni na tafi Allah ya kiyaye na gaba” tace A’a ai gara ka tsaya ka ji abin da abokin naka yake yi” mama ta maida bayanin komai dalla dalla na yanda aka yi taga inna da ciki alhalin ita din bata da kwanan miji,baba yahaya ya kalle ta yace bata da kwanan miji kamar yaya? Ta mishi bayanin har dai ya fahimci komai.sai dai maimakon yayi magana kan cin amana da zaluncin da ta tace anyi mata na satar kwana sai reshe ya juya da mujiya. Baba yahaya ya soma yiwa baba magana cikin bacin rai mai tsanani yace ba laifin Haj Majadan bane duk abinda ke faruwa a gidan nan Alh laifinka ne. Da ka kasa tsayawa da kafafunka ka zama Kaine mai zartar da hukunci a clkin gidanka.yanzu ace an zartar da hukuncin hana ka baiwa Binta hakkinta na kwana har sai ka saci jiki ka shiga wurinta don kawai bata girki?Girkin me nene? Ita mace dole ne sai tayi girki kafin aure da ita? Yarinyar nan guda nawa take da kake mata irin wannan zaluncin? Har yau din nan fa bata cika shekara 30 ba tana da 16 ne aka baka ita.yazaka rika gana mata azaba ana wulakantata kana kallo?maimaikon ayi maganar da zata zamo mai dadi ga mama sai kawai aka shiga yin wadda hakurinta ya kasa jura , ta shiga gaggayawa baba yahaya maganganu ya kalle ta yace ba laifinki bane shi ya bar ki ki ka zame mishi haka da har ki ke ganin matarshi da ciki kina tuhumar shi yanda aka yi” yayi ficewar shi ya bar su nan a zaune

Mama ta shiga borin da zage zage tana fadin wasu irin maganganu tamkar dai ba daga bakin baban mai shekarun suke fita ba,babana yana jin ta bai ce komai har lokazin mai tsawo.ban san ya aka yi ba sai kawai na ji ya daka mata tsawa mai karfi yace ya isa haka.ya kuma ishe ki haka kin gane? Abin mamaki sai kawai na ji mama tayi dib,tayi shiru cikin zuciyata na ce a’a ashe dai itama tana dan tsoronshi ina ma dai ace kullum irin wannan tsawar yake yi mata da wasu abubuwan da yawa, ashe da bata yi su ba. Baba ya shirya ya fita ya bar gidan ni ma naci gaba da abin da nake yi ban san abin da nayi ba sai kawai na ji mama to zo ta fincike ni tana jana zuwa gakinta. Tuni na saki kwanon dake hannuna ya fadi na shiga kuka ina magiya ina bata hakuri don kuwa nasan karonmu da ita a kullum nakan gwannace ta hada ni da baba ya buge ni duk da tsananin dake dukan nasa don shi duka kawai yake yi min baya shake ni.mama kuwa bayan shaka ma sai ta ce sai ta ce sai ta hau kai na ta zauna,can cikin gakinta ta kai ni ta shaga gana min azaba ta yi kuma tana cewa wai ke shegiya ko na bar muku gida kuna murna ke da uwarki to na dawo zan kuma yi maganinku”gajiya mama tayi ta kyale ni don kanta babu wanda yazo ya kwace ni tunda ba ma kowa a cikin gidan in banda inna da sauran yara gida ita kuwa ina ko meye za a yi bata yin magana.
Da kyar na fito na dawo dakin inna na kwanta ban iya fitowa sai wajen yamma ina fitowa su habiba suka kalle ni suka kwashe da dariya suna fadin ta ji jiki ba kula su ba.tunda mama ta dawo baba yasake kama fuskarshi ya tsuke tamkar ba shi ne ya wuni murmushi jiya da shekaranjiya. yana dawowa ya shiga dakin mama Suka yi maganganunsu kuma ya fiti yazo dakin inna ranshi a daure “to ai sai ki fito kizo ki dara abincin dare ko shima ba za kiyi ba ne zaki bar mutane da yunwa kamar yanda kika barsu da rana? Inna ta kalle shi tace a’ah ni ce kuma mai girkin ba gata ta dawo ba ? Ya yi maza yace A’a baza ta yi ba karbi girkinki kawai tunda dai taimakonki da aka yi aka hana ki hirkin ya zama laifi a kanshshi ake kiran mutane azzalumai”

Inna ta kalle she kawai ta juyar da fuskrta gefe bayan taja mishi wani irin mumunan tsaki sai dai kafin takai ga gama tsakin nata yayi maxa ya wafce bakin naya da duka.a kidime nayi tsalle nayi waje ina kurma ihu saboda razana.inna da ta wuni cikin wanni yanayi da na kasa fahimtarta za kuma a buge ta ban san yanda aka yi ba na gan shi ya fito yana cewa in ba zaki fito kiyi girki ba sai a zauna haka waye mai kananan yara a gidan in ba ke ba?
Rikici yayi yawa a gidanmu gaba daya an daina yi girki mama ta ki yi itama inna yaki,gaba daya gida ba dadi,ni kaina na kara shiga wani yanayi na tsoro saboda irin kallon da mama ke yi min,baba sai jin haushin inna yake yi yana fadin wai dama abin da take son ganni ya same shi kenan shi yasa tayi abin da tayi gashi kuma ya ce ta karbi girki ki ta ta ce ba zatayi ba tunda dama can ba a bata girkin ba sai yanzu. Rannan da safe ya shigo dakinmu bai tsaya amsa gaisuwar da take mashi ba yace mata shirya kije gidan ku” tace kai madallah ya juya ya fita ni kuma na soma kuka yayin da ita kuma ta shiga shirya dakinta tana kwashe kayayakinta masu daraja tana kai su dakin kwananta tana kuma gaya mini abinda take son ina rinka yi ma kannena ni kam ko amsawa ba na yi saboda kukan da na ke yi. Tagama kintsawa ta kulle wuri ta jefa dan makullin a jakarta sannan tayi shirinta tamkar wacce zata unguwa,ta dauki jakarta ban sani ba ko kukanda taga ina tayi ne yasa ta ce dauko min jakar ki rakani sai kiyi sauri ki dawo ke Atika kar ku fita ko ina suka ce to”muka fito sai da muka yi wa mama sallama bata wani amsa ba muka wuce muka fito kofar gida muka shiga taxi zuwa gida Alh maikudi,ashe kararta ya kai wajen Alh fada ma tsanani Alh mai kudi yayi mata tayi ta kuka bai fasa fadan ba bai bata wata dama ta cewa ga abinda aka yi mata ba.sai bayan fitarshi ne ta yi wa Haj kubra bayanin komai ta yi ta dariya ta ce in baka iya tsiya ba ka yi wa kanka tace ashe kema kin iya iya shege?to amma ai da ya baki umarnin karbar girki sai ki bi ba kema ki bijire ba wato shi ba wacce zai tankwasa ta tankwasu kenan?baki kyauta ba ai kin rama abinda tayi miki yaushe rabon mama da jayi in ban da wannan karon?muka koma hanya muka dawo gida muna shiga dakinmu inna tace min in je in gyara kicin ban kuma san abinda ta tuna ba ta ce ke dawo taje ta kama aikin da kanta ta gama girki aka kaiwa mama tace ta koshi suma su habiba haka.ta gama komai ta dawo dakinta tayi magariba taja carbi sai da tayi isha’I sannan ta shiga tayi wanka ta fito ta shafa mai su Atika suka kwanta mu ma muka hau gado zamu kwanta sai ga babana ya shigo.Fuskarshi a dan sake yana dan dube dube kina fa jin dadinki Binta sai kawai ki kalelece jikinki da dakinki ki tasa yayanki a gaba kuyi kwanciyarku cikin kamshi babu abinda ya dame ki da miji ba kya nemanshi saboda baki damu da shi ba.In dai yayanki suna kusa da ke to shi kenan zance ya kare musamman ace ga Humaira,tace eh to su na mallaka sune nasan da wuya ace an yi nasarar rabani da su a zahiri da badini amma miji fa? In na kwallafa rai a kanshi ai sai in yi ta wahala tunda ba zan same shi a lokacin da nake so ba,yayi murmushi yace karya kike yi kice in kin neme ni baza ki same ni ba,baki neme ni ba ina kawo miki kaina duk da bata min ran da kike yi ban taba bari kin rasa ni ba,wurin girki kawai aha hana ki amma ba a hana ki mijinki ba kuma da aka hana ki girki da kwanan ai ba kiyi magana kin ce baki yarda ba,shiru kika yi nima na taya ki shirun.

Inna ta ce kai dai ai sha’ani yace to shi kenan ai sha’anin zance dai kuma ai ya kare tunda gashi yau kin karbi girki ga ni kuma a dakin naki.ban san yanda aka yi ba watakila sai lokacin babana ya ganni a bayan inna don tsawa na ji ya daka min ya kuma shiga yiwa inna fada ina dalilin da take barina ina shigawa nan dakin ina kwanciya bayan ga sauran yan uwana a can sum sum na tashi na fita.tuni aka koma wani zama tsakanin mama da baba sai su suka san irin shin duk kuwa da cewar shi din baya iya shiga dakin inna akan idonta ko da kuwa girkin natane ko da daddaren ne ma yakan shigo ne bayan ya dan faki idota.amma duk da haka bata gamsu ba tunda dai tasan yana shigan,a wanna lokaci a wannan lokacin bata da wani zance da ya wuce na kowa ya ji tuwo-tuwo da ita miya ya sha. Ai wannan cin mutunci da aka yi mata in bata rama shi ba to ba iyayen da suka haife ta ne iyayenta ba.inna bata kulawa ko dama can kuwa ba dabi’arta ba ne tunka maganganun mama sai in ya zame mata dole haka nan kowane lokaci babana ya shigo dakinta bata ce mishi do me? Ko kuma sai yanzu? sai dai kawai tayi amfani da wannan damar wajen ganin ta kyautata mishi kamar yanda haj,kubra ta mata umarni.
Inna tayi girki kwana 2 ta fita girki Ada ya kawo cefane babu alamar mama zata karbi girkin tayi na fito daga daki zan je aikan da inna tayimani na ji Ado yana ce mata Haba! Mama gidan nan fa ko an so gidanki ne yaya za ki rika yin abubuwan dakowa zai gane akwai matsala tsakaninki da baba kin ce zaki yi maganinta na ce eh,yana da kyau kiyi hakan to kumasai kiyi ta kin girki? Bayan kinsan babu abinda baba ya ki irin hakan to kuma sai kiyi ta kin yin girki?

Leave a Comment

error: Content is protected !!