Hausa Novels

Hausa Novels Complete Documents

Hausa Novels Complete Documents

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

*DR SAIF* Page 12

 

©️Oum Hanan.

 

*HASKE WRITER’S ASSOCIATION*

(Home of expert & perfect writer’s)

 

No 12

 

Fuska yayi

yana wani cin magani, Mukhtar daya k’araso cikin d’akin yana wata shegiyar dariya ya zube kan gadon kusa da Saif yana cigaba da dariyar shi gami da nuna Saif da hannunshi. Saif daya fara k’uluwa ya cillar da wayar akan gadon a fusace yace

“Wai kai mahaukacin inane zaka shigomin d’aki ba sallama uwarka akayi zaka shigo kanamin dariyar hauka”.

Tsagaitawa Mukhtar yayi da dariyar yace

“Malam kaji da abinda ke damunka tabarmar kunya ce dai kake nad’ewa kace yau ta motsa kenan”.

Cije lips d’inshi Saif yayi yana tsaki dan yarasa abin fad’a shidai ba abin ya musa masa ba ya ganshi k’uru k’uru ya juye lemon tsami a bakinshi.

“Wai uwar mi yakawo kama Mukhtar? Ba d’azun muka rabu ba?”. Saif yace yana jefa masa harara.

Kwanciya Mukhtar ya gyara akan gadon ya d’age kafad’a yace

“Normal kwana biyu bamu gaisa da Mamie ba shine nazo, ashe kai kana nan jaraba na cinka”. Ya k’arasa maganar yana k’ara k’yalk’yalewa da wata dariyar.

Baiyi zato ba yaji bammm Saif ya dakar masa baki, tuni yabar dariyar ya dafe bakinshi yana kallon Saif d’in daya maze tamkar bashi ya aikata ba, harararshi Mukhtar yayi yace

“ALLAH ya isana banza mugu, kuma an fad’a d’in jaraba na cinka.

Banza yayi masa bai kulashi ba saboda yadda marar ta k’ara murd’a masa ya runtse ido yana cije baki saikuma tausayinshi ya kama Mukhtar d’in cikin tausayawa yace

” I’m sorry Mr Man ALLAH ya kusa yanke maka na rantse ma ni tausayin Ayshaa nake wllhy idan ta shiga hannunka”.

Duk da halin da Saif yake ciki saidaya bud’e idonshi dayayi jawur ya antaya masa harara. Baki Mukhtar ya gumtse yana y’ar dariya, tsaki Saif yaja ya maida idanunshi ya k’ara lumshewa yana sakin ajiyar zuciya.

Mukhtar dai yana nan bai tafiba sai dayaga Saif ya koma normal suka d’an fara hira duk da duk rabi fad’a ne dai.

Sai bayan wani lokaci sannan ya mik’e tsaye yana shirin tafiya ganin Saif bashida alamun rakashi yasa yace

“Wai S Matawalle ko rakiya babu?”.

“Nina kawoka? Munafurci kazo yi kuma kayi hankalinka ya kwanta”. Yana fad’a ya rufe ido dan wani irin barci keson d’aukeshi.

Murmushi Mukhtar yayi ya fice yana fad’in

“A cigaba da shan lemon tsami Mr Man”.

Bai tankashi ba illa kwanciyar shi daya k’ara gyarawa idanunshi a rufe .

 

 

★★★★★★

Ba k’aramar murna zuhrah tayiba da samun phone number d’in Saif zee kam tasha godiya. Tun a ranar tafara tura masa text message lokacin yana tsaka da duba patients sak’on ya shigo dan haka baibi ta kanshi ba, sai bayan wani lokaci da akayi kiran wayar tashi bayan yayi picking ya gama maganar da zaiyi yana shirin ajiye wayar idanunshi suka sauka kan text d’in kamar zai ajiye saikuma ya shiga cikin inbox d’inshi dan karantawa.

 

*_Amincin ALLAH ya tabbata kan hasken idaniyata fatan alkhairi dafatan kana lafiya ya aiki I hope komai normal Ina maka addu’ar samun nasara a duk abinda kasa gaba kamar yadda nake yiwa kaina addu’ar mallakar ka a matsayin mijina na halal, I love you more baby and I miss my beautiful face._*

_*Z M.*_

Abinda sak’on ya k’unsa kenan, tsaki yaja yana tab’e baki yayi deleting d’in text d’in ya maida wayar ya ajiye saman table d’in inda take.

Ba yau aka fara yimasa irin wad’annan sak’onnin ba saidai sam baya bi ta kansu dan daya gani yake gogewa dan basuda amfani a wajenshi baya ga kiran waya da y’an mata ke damunshi dashi shima d’in dai dayayi picking yaji muryar mace yake kashewa shiyasa some times ma bai cika d’aga bak’uwar number ba dan yasan kwanan zancen ya rasama gidan uban dasuke samun number shi zamani yazo mata ba jan aji ba kamun kai.

 

 

**★★★**

 

Tun daga wannan rana saiya zamana kullum ta ALLAH sai an tura masa text’s zafafa na soyayya time to time ma sau biyu ko sau uku a rana, bai tab’a bi takai ba hasalima daya gani yake deleting yaita masifa shi kad’ai.

 

 

 

*******

Rayuwa nata shud’awa wataran zuma wataran kuma mad’aci dama haka rayuwar ta gada watarana ayi kuka watarana kuma ayi dariya kamar baza’a dainaba, Lokacin biki yanata k’ara k’aratowa ta kowane b’angare an fara tsara yadda bikin zai kasance amma shi uban gayyar ko a jikinshi kuma tun zuwan da yayi Kano sau d’aya bai k’ara zuwaba kuma baya kiranta a waya, to shikam ya kirata ma yace mata me? Mamie tana yawan tambayarshi suna waya da Ayshaa saidai yace mata Eh suna waya sosai ma.

Itama ta b’angaren Ayshaan duk lokacin da sukayi waya da Mamie takan tambayeta suna waya da Saif itama d’in dai duk amsar d’aya ce suna waya dan haka Mamie ta sakankance tafara murnar sun fara saukowa tun kafin akai ga auren(Ayyah Mamie sun kifar dake).

 

 

Suna zaune a parlor Mamie ce da Imaan suna kallon wa’azi a tashar Sunnah Tv ya shigo parlor’n bakinshi d’auke da sallama wadda labb’anne kawai suka motsa alamun sallamar, yana sanye ne cikin bak’in jeans da farar riga sai bak’ar jacket daya d’ora akai ya d’ora bak’ar hula mai kamar ta sanyi akan nashi. Tunda ya shigo parlor’n k’amshin shi ya game ko ina duk ya cika parlor’n dama gana fresheners da turaren wuta dake parlor’n saiya had’u yabada wani sassanyan k’amshi mai dad’i.

Bai cika zaman kujera ba indai Mamie na wajen dan haka yau d’inma k’asan carpet ya zauna yana mata sannu da gida ta amsa cikin kulawa, bai iya zaman hiraba shi sam a rayuwarshi dan haka ya tashi yana shirin wucewa sashenshi kiran da Mamie tayi masa yasa yadawo ya zauna kusa da ita.

Kallonta ta d’auke daga kan TV’n tadawo dashi kan Saif tace

“Biki yanata tahowa banji kafara maganar lefe ba babana”.

“Lefe kuma Mamie?”.

Yace yana wani yatsina fuska.

“Eh, lefe kowani zaiyi maka shi ne?”. Mamie ta fad’a tana masa wani irin kallo.

Jujjuya kai ya fara yana faman b’ata fuska

“Kai nake jira naji yadda za’ayi”. Mamie ta fad’a ranta a d’an b’ace.

“Shikenan zan dubu d’ari biyar ta account d’inki sai a siyo”. Tsakaninshi da ALLAH yayi maganar yana kallon TV Mamie da haushi ya k’umeta saita rasa abin fad’a tayi shiru da bakinta. Imaan kuwa dake gefe kan kujera ta dafe baki cikin ranta tace

“Kan bala’i 50000 ne zasu isa had’a lefe?.

Jin Mamie batace komiba yasa ya juyo ya kalleta yayi karo da muguwar hararar datake jifanshi da ita.

“Lafiya Mamie?”. Yayi tambayar cikin rashin sanin laifin dayayi.

Saida Mamie ta k’ara zabga masa wata hararar sannan tace

“Ai kasan maman tawa y’ar tsanace da dubu d’ari biyar zasu isa had’a mata lefe.

Kai ya karyar yana b’ata fuska yace

“For God sake Mamie ace 50000 bazasu isa a had’a ba me za’a sa a ciki to?”.

“K’aniyarka za’asa, Mamie tace tana jefa masa dak’uwa.

Baki ya d’an tura yayi k’asa da kanshi, Mamie ta cigaba da fad’in

“Idan jikinka ne aika iya fitar da mak’udan kud’ad’e ka siya sutura ko shine dan rashin mutunci zaka kawomin wata maganar banza to wllhy ka kiyaye ni bansan d’iban albarka kaji ko…….ganin yadda Mamie ta d’auki zafi sai faman sambad’a masa fad’a take yasa yace

“I’m sorry Mamie nawa zan bayar to?”.

“2million zakamin transfer”.

Da sauri ya kalleta zaiyi magana yaga fuskar ba alamun wasa sam saiya langab’e kai alamar a tausaya masa yace

“Please Mamie a rage inbada 1.5million”.

“Wllhy karki yadda Mamie Aunt Ayshaan mu mai tsadace dan haka yazama dole duk abinda za’a zuba mata yazama mai tsada”, Imaan ce mai maganar cikin ranta tana matse dariyar mugunta.

“Wllhy ko biyar bazan rage ba saika kawosu ai nasan kanada kud’in wato asara kake gani ka bayar asa mata kaya masu kyau ko kuwa. Kwana biyu nabaka inji alert dan zan turawa Hajia Muneerah k’awata dake Dubai ita zata had’a komi saidai a aiko dasu kawai.

“Insha ALLAH”.

Haka kawai ya fad’a ya tashi ya bar wajen cikin ranshi yanata mitar kayan da za’a zuba har na 2million(Saif mak’o baka irin na mazan novel ne kai😅).

 

Yana barin wajen Imaan tadawo kusa da Mamie ta zauna tana fad’in

“Yawwa Mamie wllhy gara da kikayi masa haka yama za’ayi ace 50000 ta had’a lefe”.

“Ai barni dashi kawai maganinsa zanyi”. Mamie ta amsa mata tana mik’ewa tsaye dan barin parlor’n.

 

 

Tun a washegarin ma da Mamie tayi masa maganar saiga alert taji ya turo mata kud’in dariya tayi lokacin data gani tace “wato da yana dasu d’in yake neman zamewa tana sane tayi masa hakan dan da farko ma Daddy ne yace zai d’auki nauyin yin lefen Mamie tace a,a a barshi yayi kayansa tafiso ya jigatu lokacin bikin yafi ganin matar da mutunci.

A take tayiwa Hajia Muneerah transfer d’in kud’in sannan ta kirata sukayi magana ta fad’a mata yadda take so lefen ya kasance.

 

 

Ba’a d’auki dogon lokaci ba kuwa aka had’a har ankawo kaya ma set biyu na akwatina kai da ganin akwatinan da kayan dake shak’e a cikinta kasan naira tayi kuka kayane masu matuk’ar kyau da tsada na zamani.

A ranar da kayan suka iso da daddare duk suna parlor an baje kayan anata kallo harda Aunt Aisha datazo ranar sai yabawa suke dan kayane duk bana banza ga kalolin ma duk masu kyau ne.

Mukhtar ne ya fara shigowa da sallama kafin Saif yabiyo bayanshi shima da sallamar kamar yadda ya saba a ciki ciki. Ganin kayan yasa Mukhtar washe baki ya k’arasa wajen ya zauna yana fad’in

“Masha ALLAH Mamie kayan sun k’araso kenan?”.

Y’ar dariya Mamie tayi tace

“Aikuwa dai Mukhtar d’azun nan aka kawosu”. Saida suka gaisa da Mamie da Aunt Aisha Imaan ta gaisheshi sannan ya shiga duba kayan yana yabawa.

Ogan kuwa dama tun shigowarshi ya hakimce kan kujera ya shiga sana’ar tashi ta latsa waya ko inda kayan suke bai duba ba sai Aunt Aisha ce tace

“Wai Saifu bakaga kaya bane? Kazo kagani mana”. Mamie kam dama kota kanshi batabi ba ta cigaba da hidimar ta na ganin kaya.

Kanshi a k’asa batare daya d’ago ba yace

“Sunyi”.

Daga haka yaja bakinshi ya tsuke, kai Aunt Aisha ta girgiza tana tab’e baki Mukhtar kam da k’arfi yace

“ALLAH ka shirya mana bawannan naka”.

“Ubanka nayi?”.

Saif ya fad’a kanshi tsaye yana hararar Mukhtar da baisan ma yanayi ba dan kanshi a k’asa yake.

“Oho maka”. Mukhtar d’in ya amsa masa.

Dariya su Mamie sukayi dramar Saif da Mukhtar akwai abin dariya dan mafa Saif d’in bai cika biye masa bane da abinda zasu dingayi ai saiyafi haka.

Tashi ma yayi gaba d’aya yabar suka bishi da kallo gaba d’ayansu Aunt Aisha ce da Mamie suka had’a baki wajen fad’in

” ALLAH ya shirya “.

Murmushi Mukhtar yayi yace

“Mamie sai hak’uri halinne haka”.

“ALLAH ya kyauta to”.

Da Amin suka amsa suna mammaida kayayyakin cikin akwatinan dan sun gama gani Aunt Aisha ma mijinta ya mata waya kan gashi yazo ta fito sallama tayi musu ta sab’a k’aramin yaronta datake goyo sauran yaran suna gida badasu tazoba Imaan ta d’aukar mata jakarta suka fita danyi mata rakiya.

 

A bedroom d’inshi Mukhtar ya sameshi zaune kan sofa ya mik’e k’afafunshi kan d’an k’aramin center table da labtop akan cinyarshi yana dubawa sai fresh milk dake cike a cikin dogon glass cup dayake d’an sha jefi jefi. Mukhtar na k’arasawa ya amshe cup d’in ya kafa kai (Mukhtar ka shiga uku da d’aukan magana😅).

Tankau Saif bai tankaba bai kuma d’ago yabar abinda yake ba dan yasan neman magana ne kawai so yake suyi rigimar tasu da suka saba shikuma yanzu baijin zai biye masa.

Zama Mukhtar d’in yayi a gefen gado yana fad’in

“Wllhy S Matawalle kaji tsoron ALLAH ka daina munafunci”.

Jin kalmar munafunci yasa Saif d’agowa yana kallon Mukhtar kallon rashin fahimta.

“Eh, mana inba munafunci ba dama ashe haka kakeson babyn nan amma kake mana wani alaye kai ala dole matsa maka akayi ko? ALLAH ya toni asirinka to”. Ya ida maganar yana dire cup d’in daya shanye milk d’in a side drawer.

“ALLAH ya baka lafiya”. Abinda Saif yace kawai ya maida kanshi kan wayar da yake dannawa…..

 

 

Mrs Salees Mu’az

 

Oum Hanan

09139964697

Leave a Comment

error: Content is protected !!