Hausa Novels Complete Documents
​
Tag: Hausa Novels Complete Documents
”’Manzon Allah mai tsira da aminci, ya yi mana bayani a kan sallah da abin da Bawa yake iya samu. Cewa ya yi, “Yana yiwuwa mutum ya kawo sallah ga baki É—ayan ta amma a ba shi lada wadda ba ta wuce sudusin ta ko ushurin ta ba.” Abin da yasa haka kuwa shi ne rashin nutsuwa cikin sallah.
Allah yasa mu dace.”’
.
*EPISODE Forty Two*
Kyakykyawar parlor’n tabi da kallo, a ranta tana ayyana tsantsan kyawun sa da tsaruwan sa, duk da ba kaya ne me yawa a ciki ba, saboda kun san yanayin tsarin tura wa, basu cika saka karikitai kamar mu a gida ba, amma haÉ—uwar sa sai kin yi kamar zaki zubar da yawu tsaban kallo. Hotunan sa ne har guda uku a Æ™usurwa-Æ™usurwa na É—akin, babu me cewa shi ne sai idan ka yi masa kallon tsab, sabida mugun haÉ—uwar da yayi, tamkar dai É—an Æ™asan; ba É—an Nigeria ba, uwa uba ga shi da skin irin nasu, ga kyawu da ya haÉ—a, ga kuma kayan da ya saka duk nasu ne.
Ɗahira ta saki baki tana kallon Parlor tamkar wata ƴar ƙauye. Sai jin takun takalman sa tayi daga bayan ta, da sauri ta waiga tana kallon sa
Ba ita yake kallo ba, da alamu ma har ya shiga É—akin sa, duba da har ya cire rigan saman Jikin sa; yana sanye da Singlet da dogon wandon da ya zo da shi, fuska babu walwala ya nemi wuri ya zauna a É—aya daga cikin tsararrun kujerun parlor’n
ÆŠauke kai tayi tana haÉ—iyar yawu a hankali sabida jin maÆ™oshin ta ya bushe, tsayuwan taci gaba da yi a inda take, tunda be ce mata ga inda zata shiga ba, sabida ba wani É—akuna ne da yawa a gidan ba, daga É—akin sa sai irin sa na baÆ™i, sai kuma kichen me haÉ—e da store har biyu da Æ™ofa ta baya da zai kai ka Garden É—in gidan, sai kuma Toilet a parlor’n guda biyu shima.
Hausa Novels Complete Documents
Tana nan tsaye ya Æ™i ya ce mata komi, dole ta ajiye wani Æ™yaliya nata ta kalle sa tace, “ina ne É—akin da zan zauna?”
Uffan be ce mata ba, ya ci gaba da latsa wayan sa, har sai da ta cire rai da zai yi magana, sannan ya ce, “baki da muhallin zama a gidan nan, taimako É—aya zan miki”. Sai ya É—ago kai yana kallon ta, hakan yasa suka haÉ—a idanu, kallon kallo kawai suke wa juna, ko wanne na cike da juriyan kallon É—an uwan sa, domin yanda gaban su ke wani irin bugawa a tare sai ka É—auka suna jin bugun zuciyar junan su, shi nashi har da wani tsoro ne ya mamaye sa, wanda duk idan dai ya kalli Æ™wayan idanun ta masu Colour’n nan, to sai hakan ya ziyarce shi
Wani irin ɗaure fuska ya sake yi, sai tayi saurin sad da kanta ƙasa, domin itama ta kasa ci gaba da kallon sa
“Ga lungu can, nan zaki riÆ™a kwana”. Ya nuna mata wajen kichen da hannun sa, sannan ya ci gaba da magana, “ko a parlor’n nan ban yarda in ga Æ™afafun ki ba”.
Sosai zuciyar ÆŠahira ke suya da maganar nan nasa, sai dai ta kasa cewa komi illa sake duÆ™ar da kanta da tayi, take hawaye suka soma sintiri a saman kyakykyawar fuskar ta sabida jin rainin hankalin sa da baza ta iya É—auka ba, “wai me yake nufi ne? Ni ce zan riÆ™a kwana a can kamar almajira?”
Shi kuwa tuni ya miƙe ya shige cikin ɗakin sa, ko a jikin sa. Wanka ya shiga yayi ya soma rama sallolin da ake bin sa. Tunda kwana suka yi a hanya.
Tamkar gunki haka Ɗahira ta ƙafe a inda ya bar ta, ko motsin kirki ta gaza yi, lumshe idanu kawai tayi hawayen ta na ci gaba da zubo mata. Har ya fito tana nan tsaye a wajen bata jirga ba
Kallon ta kawai yayi ya taÉ“e baki, sai da yaje kichen ya haÉ—a tea kafin ya dawo cikin parlor’n, zama yayi yana harÉ—e Æ™afafu, sai ya É—auki wayan sa ya soma latsa wa yana sipping coffee É—in.
Babu daɗe wa aka yi Nocking a bakin ƙofan, sai ya bayar da iznin shigo wa
Wani matashi ne ya shigo, shi ne me kula masa da gidan, kuma shi ne ya gyara gidan tun da ya kira sa yace “zai zo” har girki shi yake masa
Gaishe sa yayi bayan da ya durƙusa a gaban sa alamun girmamawa
Hausa Novels Complete Documents
Cikin miskilanci tamkar bazai yi maganar ba ya amsa mishi, kana ya Æ™ara da cewa, “daga yau ka zauna ka huta, ina da me aiki”. Yayi maganar cikin turanci
“Ok sir thank you”.
“You can go”.
“Ok sir”. Ya sake faÉ—i yana me miÆ™e wa tsaye ya fice.
Ɗan ɗago kai yayi ya kalli setting da Ɗahira take, sai ya taɓe fuska yana ci gaba da sipping coffee ɗin sa, kamar shuɗewar mintoci a ƙalla goma, ya ajiye Cup ɗin a saman table, kana yaci gaba da latsa wayan sa. Daga ƙarshe ma kwanciya yayi saman kujeran yaci gaba da abinda yake yi.
Yanda Æ™afafun ta ke zugi nan da nan suka soma rawa sabida gajiya, dole ta janye Æ™afafun ta ta isa inda ya nuna mata, ajiye Trollyn ta tayi a wajen, sannan ta buÉ—e Æ™ofan da take kyautata zaton Toilet ne, ta shige. Zama tayi a ciki tasha kukan ta ma’ishi, kana ta share hawayen ta tare da É—auro alwala. Tana fitowa babu shi cikin parlor’n, Æ™arisa wa tayi wajen Trolly É—in ta ta zuge ta ciro Hijab, sannan ta zare gyalen da tayi Trollyn dashi ta saka Hijab É—in, cikin parlour’n ta Æ™arisa ta soma sallah saman tattausan carpet É—in dake shimfiÉ—e a wajen, rama sallolin da ake bin ta tayi. Har ta idar ta soma kwararo addu’a tana kai wa Allah kukan ta, bayan ta ida sai ta shafa tayi zaman ta a wajen, ta jima tana zaune a wajen ga zafi ya ishe ta, dayake ba’a kunna masa Gen ba, sai ta tashi ta cire Hijab É—in ta ninke, ta nufi Trolly É—in ta taja shi zuwa É—akin kusa da nashi, sai dai a kulle yake, hakan yasa ta tsaya tana tunanin mafita, domin baza ta iya kwana a inda ya nuna mata ba tamkar wata almajira, ko bata da gata sai haka
Juya wa tayi ta mayar da akwatin, sannan ta shige Toilet É—in, wanka take son Yi Amma babu ruwa me zafi tunda babu wuta, sai ta fito ta nufi kichen inda taga ya bi É—azu, tana shiga kuwa ta sami komi a dai-dai, ta kunna gas ta matsa ruwa a famfon kichen É—in; ta É—aura. Sai da yayi zafi ta sake tare da sirka wa, har ta koma ta shige Toilet bata sake jiyo motsin sa ba, wanka tayi ta fito. Ta duba kayan ta cikin Trollyn ta ta koma Toilet É—in ta saka, riga da skert ne Æ´an kanti, sun yi mata kyau sosai sun lafe a jikin ta, kasancewar bata da jiki
Ta rasa yanda zata yi da kayan da ta cire, sai ta fito dasu ta ninke ta mayar cikin akwatin nata, janyo akwatin tayi ta nufi cikin parlour’n, tayi zaman ta kan kujera, sai dai gaba É—aya tunani ya addabe ta, ga yunwa da ta soma ji, amma rashin jin daÉ—in yanayin yasa baza ta iya girki ba.
Tana nan zaune kamar mintuna 20, sai ta jiyo buɗe ƙofa, sai dai bata motsa ba tunda ta san shi ne
Kallo É—aya yayi mata ya É—auke kai, ba tare da ya ce komi ba ya sanya Æ™afan sa ya fice, a ransa yana murmushin mugun ta, “tabbas zai koya wa yarinyan nan hankali, bata san waye shi ba har yanzu. Nan gaba ko yace kar tayi wani abun; to baza ta tsallake umarnin sa ba”.
Tana ganin ya fita, sai kuma ta tashi ta nufi kichen ɗin, dube-dube ta hau yi, wasu abubuwan duk bata taɓa ganin su ba, amma dayake tana karanta wa sai ta gane amfanin su, nan tazaƙulo indomie ta dafa, daga mai sai gishiri ta saka, saboda duk sauran kayan girkin su ba iri ɗaya bane, ta san ko da ta saka ba daɗi za su yi mata ba, sai dai a hankali zata soma gwadawa ta ga ko zata iya ci, amma yanzu yunwa take ji baza ta zauna tayi abinda baza ta iya ci ba.
Tana gama wa ta fito Parlor tayi zaman ta tana ci, sai da ta gama sannan ta koma ta wanke komi ta mayar muhallin sa, still ta sake koma wa Parlour tayi zaman ta, tunanin rayuwa kawai take yi tare da kewar gida, ga shi babu waya a hannun ta bare ta sa ran zata kira su, shiyasa ta yanke shawaran yana dawowa zata ce “ya bata wayan ta”, tunda dai ba nashi bane.
Ganin duhu ya soma yi ta duba agogon hannun ta taga magriba tayi, sai taje tayi alwala ta dawo, ta tayar da sallan ta, tana idar wa ta duÆ™ufa addu’a, ta jima a wajen har lokacin isha’i yayi, ta gabatar. Ga duhu ko ina dole ta soma jin tsoro, tunda ba inda ta saba da shi ne ba, nan ta Æ™udundune a kujera ta rufe idanun ta ta hau karatun Alqur’ani a hankali da muryan ta me tsananin daÉ—i, a haka har ta soma jiyo motsin buÉ—e Æ™ofa, tayi shiru tana buÉ—e ido tare da kallon wajen
Usman ne ya shigo riƙe da wayan sa yana haska wa, tunda ya shigo ya ƙyalla hasken kanta idanun sa suka sauka cikin nata idanun, yanda ya ga idanun suna wani ƙyalli sun sauya kala sai yayi saurin ɗauke kansa gaban sa na matsanancin faɗi, rufe ƙofan kawai yayi ya nufi ɗakin sa, domin so yayi tun yau ya soma mata tijara, amma ganin ƙwayan idanuwan ta bazai iya zuwa ba
Yana shige wa ta rufe idanun ta, “wai da gaske dai mutumin nan be da imani anan zai bar ta ta kwana?” TafaÉ—a a ranta. Numfashi taja ta gyara kwanciyar ta tana sake Æ™udundune wa, bata sake motsi ba illa tunani da take ta faman yi, sai daga baya ta samu barci daÆ™yar ya sumfice ta.
Hausa Novels Complete Documents
Washe gari ta farka a makare, ƙarfe 07:00am. A lokacin, shaf-shaf tayi alwala ta gabatar da sallan ta, ta zauna nan tana ta lazimin safe, sai da gari yayi haske sosai kafin ta miƙe ta nufi kichen, a tunanin ta ko ya fita ne tunda bata ji motsin sa ba, ga shi har sha biyu tayi, amma haka nan ta soma haɗa musu Breakfast har da shi, ruwan tea ta haɗa sai arish da ta soya, ta kwashe ta kai saman dainning, ta zo ta sake duba kichen ɗin ta ɗauko kayan haɗa tea ɗin, duk ta kai kan dainning ɗin. Sai da taje tayi bruch kafin ta zo ta haɗa tea ɗin ta sha da arish ɗin, tunda babu ko bread bata gani ba
Bayan ta gama ta tashi ta je ta É—aura ruwan zafi, yana É—umi ta sake tayi wanka ta shirya a Toilet É—in, yau ma riga da skert ta saka na kanti, rigan t.shirt ne me gajeren hannu ja, ta zauna mata É—as ta yi mata matuÆ™ar kyau, sai ta saka skert Robber light green, irin me tsagin nan ta baya, sai da ta É—an yi kwalliya kaÉ—an tunda sabon ta ne, gaskiya tayi mugun kyau matuÆ™a, musamman yanda take kyakykyawar nan. murmushi kawai tayi tana zaro siririn gyale ta yafa a kanta zuwa wuyan ta, sai ta zauna a kan kujera, a ranta tana tunanin ko ta tashi ta gyara parlor’n ne?
Buɗe ƙofan da Usman yayi na ɗakin sa, shi ne yasa ta ɗago manyan idanuwan ta ta sauke a kanshi, tare da dakata wa daga miƙewan da tayi ninya
haka zalika shima kallon ta yake yi, lokaci É—aya ya É—auke kai yana cin magani, da alamu dai fita zai yi saboda a cikin shirin sa yake
Littafan Hausa Guda 1000 Download
Takowa yayi ya isa wajen kujerun
Duƙar da kanta tayi kawai tana jin gaban ta na faɗuwa
“Keee”. Yayi maganar a maÆ™oshi yana ja
ÆŠago kai tayi tana kallon sa, yanda ya tsare ta da ido da fuskar sa tamkar hadarin kaji, daga gani ba mutunci a tare dashi, hakan yasa ta É—auke kai itama tana shan kunu, domin bata san da me ya zo ba
Zama yayi be sake cewa uffan ba, don be san ma ta ina zai fara ba tsaban miskilanci, ga shi matsanancin haushin ta yake ji, tare da sake jin tsanar ta me Æ™arfi a ran sa, “ko uban wa zata yi wa kwalliya?” Ya faÉ—a a ransa yana sake kallon ta
“Ki tashi ki je ki É—auko min Trolly É—in ki”. Yayi maganar tamkar ba shi ba
Sai da ta kalle sa kafin kuma ta ɗauke kai tana me mamaki. Amma bata ce komi ba ta miƙe ta nufi wajen kayan ta, janyo wa tayi ta kawo masa har gaban sa
“BuÉ—e shi”. Ya sake bata umarni
Ita dai bata ce uffan ba sai mamaki da ke son kashe ta akan “me zai yi mata da kaya?”
Tana buÉ—e wa ya sake ce mata “ta fito da duk komi dake ciki”.
Hakan kuwa ta sake yi
Ɗaya bayan ɗaya ya saka ta tana ɗaga kayan, don shi bazai iya saka hannun sa ya taɓa kayan ta ba
Idan ta É—aga sai ya ce “ta ajiye gefe,” wani kuma yace “ta mayar cikin akwatin”. Karkatakaf sai da ya gama zaÉ“e Æ™ananun kayan dake ciki, sai atamfa da Abaya kaÉ—ai da yace ta zuba cikin akwatin
Ita dai duk yanda yace tayi hakan take yi, arziƙin ta ɗaya bata biye wa miskilancin sa ta fito da under-Wears ɗin ta ba, da yanda ya saka take ɗai-ɗai da kayan ta; da ta sha kunya
“WaÉ—annan kaÉ—ai kike da damar saka wa a gida na, nan ba gidan karuwan ki bane da zaki zo kina saka min Æ™ananan kaya, and daga yau aikin gidan nan gaba É—aya ya dawo kanki, ko ina na cikin gidan nan kullum Ina son ki share shi tsab, ko alamun datti ba na son gani, zan bar miki keeys É—in É—akunan, kuma daga yau inda nace ki koma nan zaki koma, kar in sake ganin Æ™azantaccen jikin ki ya zauna min a cikin parlor. sauran aiki ya rage naki, ki bi ko kar ki bi, idan ba haka ba zan baki mamaki Wlh”.
Tun sanda ya soma magana ta É—ago kai tana kallon sa, sakin baki kawai tayi tana bin sa da ido domin mamakin sa ma ya kusa kashe ta. Ganin yana shirin tashi tace, “ban gane me kake cewa ba fa? Ni fa matar ka ce ba baiwar ka ba. fine naji aikin gidan zan yi tunda dama aiki na ne, amma meye haÉ—in ka da kaya na da sai ka zaÉ“a min waÉ—anda zan saka? Kuma da kake cewa ba gidan karuwai na bane, amma ai naga Gidan Mijina ne, kuma idan ma nayi karuwancin iyawa ne, kasan da haka ka aure Ni, so ba abun damuwa bane”.
Sosai yayi mamakin furucin nata
Ita kuwa ƙarfin hali ne ta azawa kanta har ta iya faɗan waɗannan kalaman, domin ba ƙaramin tsoro ne cike a zuciyar ta ba, amma kuma tana gani idan har taci gaba da shiru ba ta mayar masa da amsa, tabbas ya samu damar kullum yana sakar mata magana yana cusa mata baƙin cikin sa.
Kallon ta yayi da idanun sa da suka soma sauya kala, domin maganar nan ma da yayi me yawa ba Æ™aramin dauriya yayi ba, amma kuma tsaban rashin mutunci irin nata take maida masa martani, “ke nan baza ta bi umarnin sa ba?” Ci je leÉ“en sa yayi yana bin ta da kallo, sai kuma ya É—an saki guntun murmushi yace, “me yi ba ya faÉ—a, don Allah idan kin cika ke Æ´ar uban ki ne, ki tsallake umarni na”.
Sosai ranta ya É“aci da zagin uban ta da yayi, sau biyu kenan hakan ke faruwa. Shiyasa cikin É“acin rai da baÆ™in cikin sa tace, “ba dai uba na ba wlh, domin ya fi Æ™arfin ka har da zaka zauna kana zagin sa..”
Bata ajiye numfashi ba ya É—aga hannu ya falla mata marin da sai da taga taurari suna shawagi a idanun ta, É—if tayi kawai ta dena gane abinda ke duniyar.
Name: | [Hausa Novels Complete Documents] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | June, 2022 |