Hausa Novels

Hayar Mace Hausa Novel

Hayar Mace Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: HAYAR MACE!

_(Destiny and se*ual story)_

 

_Oum Hairan_

 

 

*Note:* _Duk da cewar littafin nan ba free bane amma ina rokon Alfarma kada ki karanta min in kinsan bakida ƙarfin zuciyar ɗaukewa sannan na haramta karanta shi ga yan under 18, ban hana budurwa karantawa ba amma karki zargi Oum Hairan, karki duba ɓarnar dake ciki ki ɗauki sakon dake ciki zaifi miki amfani._

 

 

 

_Page one and two_

 

 

 

Dandazon matasan dake tsaye gindin bishiyar sune suka ɗauki hankalin matashiyar budurwar dake tafe sanye da doguwar riga baƙa tayi rolling baƙin dankwalin a kanta hannunta rungume da takardu da suke alamta da alama daga makaranta take.

Da sauri cikin faɗuwar gaba ta nufi gindin itaciyar har tana tuntuɓe takardun hannunta suna zubewa amma hakan baisa ta dakata daga kudurinta na kaiwa ga inda taga cinkoson matasan ba, can cikin hayaniyar da ba kowacce kalma ake fahimta ba taji ana cewa “Haba Mal Kabiru kai kuwa wanne irin ɗan akuya ne da zaka tuso matarka har kwararo babu ko arzikin kallabi……”

Daidai lokacin matashiyar budurwar ta isa tsakiyar da’irar cikin kaɗuwa ta zube a ƙasa tana cewa “Innanillahi Kumbo meye hakadin me kikayi masa ya dakeki haka Kumbo meye yasa bazaki rabu da Azzalumin……”

 

 

 

 

Rufe mata baki matar dake durƙushe a gurin tayi tare da girgiza mata kai ta buɗe kumburaren bakinta tace “Danku nakeyi Safiyyah kul na ƙarajin kince da mahaifinki azzalumi ba kalmar ƴa me tarbiyya bace, nasani Dani da mahaifinku bamu bawa tarbiyyarku gudummawa ba saidai kuma ban gaza wajen nuna muku girman haƙƙinsa akanku ba Safiyyah akanku ne keda ɗan uwanki, mahaifinku ya sakeni saki ɗaya Kinga saura igiya ɗaya aurena da ubanku ya ƙare, saboda nace bazai turaki aikatau ba sannan bazai tura Safwan Libya neman kuɗi ba…….

Sharrrr idanun Safiyyah ya kawo ruwa me ɗumi ta zame ɗankwalin kanta ta rufawa Kumbon ta ta kama hannunta ta miƙe ta haɗata a jikinta tace “Kumbo ina yawan furta Miki ki daina kula Mutumin nan akan duk abinda yazo dashi idan abune me yuwuwa ayishi kawai idan kuma bamai yuwuwa bane dakansa zai barshi amma bana ganin daraja cikin kulashin da kikeyi kullum kuna gantalar mana da ƙima da darajar da dama ba ita ke garemu ba, muje gida na siyo Miki balangu me ɗumi”

 

 

 

 

Nufar gidan nasu sukayi ginin ƙasa daya gaji da tsufa kwanon da aka rufa saman gidan duk yayi tsatsa gidan gidane na haya me ɗauke da ɗakuna bakwai sai bayi a can ƙarshen gidan sannan Madafi.

Wani dake gefe ɗaya da alamun baikai kowanne girma ba shi suka nufa Saida Kumbo ta zauna sannan Safiyyah ta zaro jakar dake rataye a wuyanta ta buɗe ta dauko ɗaurin ledar ƙarami ta miƙawa Kumbo ta karɓa tana bin ƴar tata da kallo tace “Safiyatu ina kika samu kuɗi keda baki tafi makarantar nan da ko sisi ba har kika siyo nama?”

Zama tayi a gefenta tace “Na faɗa Miki ai muna tarin kuɗi kullum Naira Hamsin to shine yau aka fasa aka raba kowa ya samu dubu uku da ɗari biyar shine na siyo Miki balangu na ɗari biyar ɗin kinga sauran canjin sai musayi taliya ko guda biyar ce sauran ma riƙe muyi cefane…….

 

 

 

 

Da sauri ta ƙunshe kuɗin jin takun mahaifin nasu gabanta ne ya faɗi lkcn da taji yana cewa “ku sarakan ciki ko wato ke Safiyyah ba ƴar arziki bace, kowacce ɗiya tana neman albarkar mahaifinta ke bandake saboda asararriya ce wannan gantalalliyar watsattsiyar uwar taki kika kawowa kuɗi har kina maganar asai abinci nufinki Ni nakasa kenan ko? To bani kuɗin ko naci ubanku dagake har uwar taki…..”

Ƙwace kuɗin Kumbo tayi ta miƙe tana cewa “Aikuwa banga dalilin da zaisa baka taɓa bawa yarinyar nan kuɗin makaranta ba a zubin ƙosan da takewa Hadiza take samu ta biya kuɗin makaranta har tayi rara ta aje abinta to Kabiru koni baci mata kudinta zanyi ba tunda ba wata uwa nake tsinana mata ba in bikin Zuwai ƙawarta yazo ta sai ankon bikin”

 

 

 

 

Hannu ya ɗaga zai zubawa Kumbo mari Safiyyah tayi saurin riƙewa da Muryar kuka tace “Don Allah Bappi ka daina sha’awar dukan Kumbo ya kamata ace ko don darajarmu dake tsakaninku ku rinƙa saurarawa juna, Kumbo ki bashi indai waɗannan canjin ne daya taɓa lafiyarki wataran zai iya sake illataki kina ganin dukan da yayi Miki kwanaki Saida kikaci kuɗi badon Allah yasa Mal me Almajirai ya taimaka ba da bamusan ya zamuyi ba to ina amfanin hakan”

Fusge hannunsa yayi ya sake nufar Kumbo ganin da gaske Mal Kabiru ƙara tara mata gajiya zaiyi yasa babu shiri ta ɗauki kuɗin ta cilla masa tayi waje da gudu tana cewa “Kayi da wata ba A’ishatu ba mahaukaci” da hargowa ya fito yana cewa “A’i Ni kike cewa mahaukaci to wlh yau saina tura Miki takaicin da kika daɗe baki shaƙa ba ina raga Miki saboda yaran nan amma ke baki gani ko? Zaki gane ba tsoronki nakeji ba yau ɗinnan bakar munafuka kinsa mal me Almajirai ya takuramin Saida na dawo dake…….”

 

 

 

 

Tsaki tayi tace “Indai wannan watsattsen auren naka ne ai dashi gara tallan gwanjo nidai cikin shekara ashirin banga uwar abin dana ɗorar ba banda baƙin ciki auren ɗan giya ko asara….”

Safiyyah dake raɓe jikin gini inda sabo ta saba da wannan cece-kucen na iyayenta kullum a haka suke babu me ragawa wani tsakaninsu kowa gani yake ɗan uwansa bai isaba itakam da tanada wajen zuwa da tabar wannan ruɓaɓɓen gidan nasu me cike da hargitsi kala² zame jikinta tayi ta nufi gidan maƙotanmu Mal me Almajirai da matarsa Sahura, tana shiga ta nemi guri kusa da Inna Sahura ta zauna ta rushe mata da kuka, Inna ta saki muciyar tace “Ni Sahura ina ganin rayuwa Safiyyatu ke kullum bakya rabuwa da damuwa da ƙuruciyarki ki rinƙa sawa kanki damuwa…..”

 

 

 

 

Cikin kuka tace “Meye yasa kowanne gida kowanne ma’aurata zaka riskesu cikin walwala da son suga sun faranta rayuwar junansu amma banda Bappi da Kumbona kullum basu da burin da yafi suga sun ƙuntatawa juna?”

Murmushi tayi tace “Safiyyah kenan zuwa yanzu Yakamata ace kin saba da wannan yanayin ƙaddarar taku, iyaye ne kuka haɗu dasu dukkansu babu haƙuri babu kawaicin rayuwa kune haƙuri ya kama mahaifiyarku da tanajin magana da tuni ta daina sauraron Mal Kabiru bare takaisu ga duka amma itama A’isha taƙi bari kedai da kike mace ina horonki da kada ki ɗauki halin mahaifiyarki na rashin haƙuri zakisha wuyar rayuwa da namiji”

Hannu tasa tana share mata hawayen tace “Danma Mal Kabiru yaƙi ne da masoyan nan da suketa zuwa da yabaki dama kin fitar da gwaninkin Yatuh da tuni kin huta da wannan kallon takaicin to yace shi ba kowanne irin namiji zai bawa aurenki ba”

 

 

 

 

Shiru ce ta ratsa can ta miƙe tace “Inna Sahura idan Kumbo ta daina kulashi suma zasu koma irinku a daina jin kansu?” Da sigar tausayawa tace “Abubuwa zasu ragu kam amma a daina gabaɗaya sai a hankali tunda ba’a faro rayuwar da haka ba…..”

“Safiyyah! Ke Safiyyah!! Kina ina ne ko sai na karya Miki ƙauri….” Jikinta na tsuma da rawa ta cire mayafinta ta nufi wajen da gudu, can ta hangeshi jikin wata luntsumemiyar mota ya ranƙwafa da alamun magana sukeyi da wanda ke cikin motar.

Tunda ta nufo motar idanun wanda ke cikinta yake kanta harta iso ta durƙusa tace “Gani Bappi!….” Da zafinsa ya juyo yace “Ke…ke do Allah tashi Yatuh banason shirme Alhaji ka ganta dubeta sosai ka ganta dai babban Molu ce” tana miƙewa na cikin motar yana fitowa, wani farin Balarabe ne a ganin Idanunta sanye Da kayan Hausawa ya ɗora baƙar hula a saman baƙar hularsa.

 

 

 

 

Kallo yakeyi mata irin na ƙurulla wannan yasa Safiyyah yin ƙasa da kanta tace “Bappi…..” Ranƙwashi ya zubanta yace “Alh bakace komai ba wannan harka kasan harkata ce kawai banason wannan arziƙin ya wucceni…..”

Batayi tunanin mutumin ya iya Hausa ba Saida taji yace “Yaronka yayi sosai inason yaro me yawan abubuwa zan ninka maka kuɗin indai yaronka yayi abinda akeso yayi” wata shashashar dariya Bappi yayi yace “Saini Uban ƴan iska kawalin zamani abin kunya gaba na bashi ba baya ba Safiyyah ai kamar ta tafi Fatakwal ta gama maza maza muje ki ɗebo kayanki koda yake tsaya naje na ɗebo miki ke jeki haka ma a siya a can”

Karin wasu littafai da zaku so

 

 

 

 

Tunda ya fara rawar jikin take kallonsa har Saida ya dire tace “Ina zani Bappi?” Daƙuwa ya watsa mata yace “Harkar arziƙi zaki tafi wannan da kike ganinsa bazan tsaya Miki bayaninsa ba a hankali zaki fahimci wanene musu gardama ko taurin kai a matsayinki na ƴar talaka matsiyaci irina ba naki bane, Safiyyah na bawa Alh Urwat hayarki daganan zuwa wani lokaci idan kinje komai da ya kamata ki sani game da ma’anar HAYAR MACE zaki sani….” “HAYAR MACE! Bappi meye hayar Mace?”

 

 

 

 

_Kamar yanda na rubuta a sama ba free bane paid ne saidai yazo da sassauƙan farashi Naira 200 PC 500 zaku iya turo kati MTN ta WhatsApp number 09013718241 ko ta acct 0255526235: gtbank ko ta first bank 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar, ƴan Niger kuma katin Airtel zaku turo._

_Please ina tuni don Allah kada ki biya min littafina kuma ki zageni domin na rubuta a farkonsa bana buƙatar surutu domin bazaisa na fasa rubutashi ba._

Leave a Comment

error: Content is protected !!