Hikayar Duniya A Jakin Shehu
Tag: DUNIYA A JAKIN Shehu
Wasu Malaman Kiristoci suna yawo gari-gari suna muhawara da Malaman Musulunci domin suna kuresu sai sukaje garin su Shehu jaha
Bayan sarki ya sauke su, sai ya nemi shawara a fadarsa kan da wane Malami zai hada su,
Mutane mafiya rinjaye sukace a gayyato musu Shehu Jaha saboda yana da hikimar zance,
Sai nan da nan Sarki ya amince, aka kira musu Shehu.
Ko da yazo tun ba’a ce komai ba sai yace a fara amsa tambayoyi,
sai kiristan coci na farko ya mike yace “Inane tsakiyar duniya?”
wannan tambaya ta rikita mutanen wajen, Amma sai Shehu jaha yayi nuni da sandarsa zuwa inda Jakinsa yake tsaye yace “Daidai kafar jakina ta dama inda yake tsaye, nan ne tsakiyar duniya
Sai kirista yace “Yaya zamu tabbatar da haka?”
Sai Shehu yace “Ku auna idan kunga kuskure sai ku karyatani”. Sai kiristan yace Taya zata aunu Sai Shehu jaha yace kasan bazata aunu ba kayi min wannan tambayar Sai ya koma ya zauna jikin shi yayi sanyi
Sai na biyu kuma ya tashi yace “Nawa ne adadin taurarin dake sama?”
Ba tareda wata damuwa ba Shehu yace “Yawansu daya ne da gashin jikin Jakina”
Sai kirista yace “Meye hujjarka?”
Sai Shehu yace “Ka kirga su kazo ka kirga Gashin Jakin kagani, idan kaga kuskure kace min makar yaci Sai mutumin yayi Jim yace
“Ka taba ganin an kirga gashin Jaki ne?”
Sai Shehu yace “A ina ka ta6a ganin an kirga taurarin sama?”. Sai ya koma a sanyaye
Sai na uku ya Mike a fusace da tambayar sa mai zafi yace “Shehu nawa ne adadin gashin Gemu na?”
Sai Shehu yace “Yawansu daya da gashin jelar Jakina”
Sai kirista yace “Ta ya ya zama haka?”
Sai Shehu yace “Ka dinga cizge gashin gemunka daya,
sai kuma cizge na Jelar jakinnan daya bayan daya
Idan ka kammala za kaga idan zai gaza ko kuma zai hau!” Sai yayi Jim Shima ya koma ya zauna a sanyaye
Daga nan sai duk jikinsu yayi sanyi, suka lalla6a suka bar garin su Shehu Jaha!
Sarki da Mutanen Gari sukayi wa Shehu jaha kyauta mai yawa…
Nima ga tawa tambayar nawane adadin Charge din wayata a yanzu.
Leave a Comment