Hausa Novels

Hikayoyin Shehu Jaha Masu Ban Dariya da Karantarwa

Hikayoyin Shehu Jaha Masu Ban Dariya da Karantarwa

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Hikayoyin Shehu jaha

1.TSAYA NAN NA GWADA MAKA YADDA ZAN YAUDAREKA

Wata rana shehu yaji wani yaro yana kirarin cewa shi babu wanda ya isa ya yaudareshi ko ya damfareshi. Sai yace dashi: To tsaya nan, ni kuwa bada jimawa ba zan gwada maka yadda zan yaudareka. Sai yatafi yabar shi a wajen yayi ta tsayuwa awowi masu yawa, amma baiga alamar shehu ba, har dai ya gaji da tsaiwa, sai ya rika lanlankwashew. Da abokansa sukazo wucewa sai suka ce dashi kai kuwa tsaiwar me kakeyi a nan? Sai ya basu labarin abinda ya wakana, sai wani abokinssa ya tintsire da dariya yace dashi: Amma ka cika sakarai. To ai gashi nan ya yaudareka, dabara ta kubuce maka. Kai jama’a, shehu sai Allah. Ya wuce tunanin jama’a.

 

 

 

 

 

2.INGANTACCEN LISSAFI

Wani mai kanti yana bin Shehu Jaha bashin
kudi sulai talatin da
uku, sai yazo wucewa ta wajen kantin
mutumin nan, sai ya tsaya yace dashi “Dauko littafi ka nuna min kudin nan da kake bina in biyaka in huta” Mai kanti yaji dadi
ya dauko littafi yana dubawa, Shehu kuma
yana lura dashi, sai Shehu yaga a shafin kusa da nasa Maikanti yana bin limamin
unguwarsu kuma sulai ashirin da takwas, sai Shehu yace da Maikanti “Nawa kake bina Ni?” Maikanti yace “Sulai talatin da
uku” Shehu yace:

 

“To idan ka cire sulai sulai
ashirin da takwas din Liman daga cikin sulai talatin da uku dake Karin, saura nawa
kenan chanji?” Maikanti yace “saura sulai biyar” Shehu yace “To bani sulai biyar, kaga shikenan ba-kare bin- damo, tsakanina da
kai babu sauran bashi” Maikanti yayi murna yaga zai samu bashin da ya dade yana bi, nan da nan ya kawo sulai biyar ya bawa
Shehu, Shehu kuwa yayi tafiyarsa.

 


Sai bayan da ya zauna ya nutsu, sai ya gano
lallai akwai kuskure a cikin lissafinnan, kuskure mai girma! Ya rasa kuma yanda zaiyi ya fita daga wannan gagarumin rikici da Shehu ya jefa shi.

*Shehu gwanin lissalifi anya akwai wanda ya
kai shi iya lissafi kuwa?

 

 

 

 

Sirrin Mata Kashi na Biyu

3. RASHIN LAFIYAR SHEHU

Shehu jaha yayi rashin lafiya aka kwantar dashi a asibiti, kasancewar sa mutun ne mai jama’a yayi ta samun alheri daga wurin jama’a masu zuwa gaisheshi.

 

Sanadiyar haka daShehu ya samu sauki kullum in likita yayi niyyar sallamarsa sai yace “hum humm likita ni kawai nake jin abin da nake ji, to daman gadaje hudu ne a jere, washe gari sai mai gadon farko ya mutu, washe gari na gefensa ma ya mutu, washe gari daman shehu shine a gado na uku, ya zaga kama ruwa a ban daki ya dawo, sai ya tarar da na gado na hudu shima ya cika, sai Shehu yace to layi take bi kenan bata same ni bane shi yasa ta wuje, tunda ta kure layin to lallai zata dawo. Nan take bai jira likita ba, ya tattare kayansa ya gudu.

 

 

 

 

4.Wani Bawan Allah
Wani BAWAN Allah ne da suke kwance da matan sa sai budurwan sa ta Kira shi a waya sai daga,budurwan yace baby kwana biyu sai yace wallahi sai tace yaya gida ya CE lafiya lau sai tace kana lafiya sai kalau sai tace I miss u baby maimakon yace I miss u too budan bakin sa yace mima,sai tace I love u sai ya CE mima,ta sake masa yaya kake ansawa da mima, sai ya sake cewa mima sai tace wanan mima nan bangane sai ya CE sabon salo ne mima a panin so yaiya

5. Wata rana Shehu
Jaha yaje gonarsa tunda safe yake tonon rami
yana biznewa,har zuwa da yamma yana wannan
aiki,yana cikin wannan aiki saiga makwafcin
shehu ya dawo daga tasa gonar,har zai wuce sai
ya hango shehu jaha,sai ya karaso ya gaida
shehu jaha,yace “shehu me kakeyi ne tunda safe
kake tona rami kana biznewa alhali babu abinda
kake sawa acikin ramin?”,sai shehu jaha yace
masa “wallahi kaga kudina na bizne tun shekarar
data wuce(bara),amma kaga yanzu na nemi ramin
dana bizne kudin na rasa,shine kaga ina ta tona
wadannan ramukan”,sai wannan makwabci na
shehu jaha yace masa “kai kuwa shehu baka
sanya wata alama bane?”sai shehu jaha yace wa
makwafcinsa,”na sanya wata babbar alama saitin
wani babban gajimare,amma banga gajimaren

 

5 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!