Hoorain mai kusumbi Hausa Novel Complete
HOORAIN MAI KUSUMBI
(The hunch back girl)
🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
#general fiction
#hot love
#scracife
#Hatred
#betrayal
#destiny
_NoorEemaan_📚✍️
The writer of
RAYUWAR FAHEEMAH
MIJIN AMMI NANE SILA
KYAUTAR KODA
PAPI NE
ABRAHAM and now……
HOORAIN MAI KUSUMBI (THE HUNCH BACK GIRL)
_*hoorain zai zo da wani salo na daban wanda ban taba yi ba, novel din na daban ne, ya sha bambam da duk wani Novel nawa, ban ce alkamina yafi na kowa ba, amma alkalamina na daban ne, just follow my pen, and i assure you that you Will never regret*_
Hoorain mai kusumbi (the hunch back girl)
Wanna ba labarin soyayya bane, labari ne ta yanda tsaftataciyyar soyayya bata taɓa mutuwa.
In the name of Allah, most gracious, most merciful.
Chapter 1️⃣⏩2️⃣
*BUKAVU BARRACKS KANO*
Babban barikin sojoji ne mai matukar girma, yana ɗauke da waje je daban-daban, yayinda kabilu mabambamta hadi da addinin ne a cikin barikin, sosai suke zaman lafiya ga hadin kai gwanin sha’awa.
Ko wani soja da iyalan sa da area da suke zama, ya danganta da rank (muƙamin) Mutum.
Misali akwai officers mess, batcher, White House, da sauran su, haka ma akwai asibiti da suke kira MRS duk a cikin barikin.
Zaune yake a officer dinsa, in da aka kawata office din da kayan k’awa irin na sojas…
fuskar sa a murtuke yake amma hakan bai hana kyawun sa buya ba.
Kyakkyawan matashi ne mai shekaru talatin da biyu a duniya, sanye yake da kakin soldier da yayi matuƙar yi wa farar fatar sa kyau, duk da a zaune yake amma hakan bai hana mutum ya gane cewa shi din dogo ne ba, mai fadaddar kirjin, a takaice dai giant wanda ya sha training sosai.
Gashin kansa mai tsayi ne, har parking yake, domin yazo masa har saman kafadun sa, sai dai bai barin shi a baje, always Yana parking gashin.
Sajen sa mara yawa kwantacce ne daya kara masa wani sirrin kyau, zagayayyen fuska ne dashi mai dauke da cikakken gira hadi da eyelashes masu yalwa, hacin sa dogo ne mai tsari, idanun sa madaidaita ne masu ɗauke da eyeball sky blue, sai bakin sa madaidaici red color, a takaice dai he’s damn handsome!
System ce a gaban sa yake operating da hannu biyu at the same time cike da kwarewa, yayinda lokaci zuwa lokaci yana ɗan sipping coffee dake kan table din shi, sam bai damu da abinci ba, mafi yawan lokuta yafi gane wa coffe.
Alamun sako ya gani an Turo ta Gmail din shi, hakan yasa bayan ya gama abinda yake ya shiga.
sunan field marshal ya gani, wanda hakan ya nuna cewa shine ya Turo masa sakon, a nutse ya karanta komai in less than five minutes duk da yawan rubutun…
Hannu ya sa ya shafa kwantaciyyar sumar sa, sanan ya furzar da iska daga bakin sa hadi da lumshe rikitattun idanun sa.
Amsa ya rubutawa marshal da cewa ya gan sakon, sannan ya kashe system din gaba daya
mikewa yayi tsaye… Masha Allah dogo ne sosai wanda ya dace da tsarin halittar jikinsa, hular sa ta sojas ya saka wanda ya ƙara masa kyau sannan ya saka wani brown sunscreen (gilashi) ya dauki wayar sa ya nufi hanyar barin officer ɗin cikin tafiyar sa mai cike da izza, takama, hadi da burgewa…
Jefi-jefi yana haduwa da sojas daya girma a rank suna gaishe shi cike da girmamawa, hannu kawai yake daga musu ba kuma ɗan wulakanci ba, sun san halin shi na rashin son magana shiyasa basa damuwa.
Haraban office din na da matukar kyau an kawata shi da flowers masu ban sha’awa green sai kamshi furanni suke ga Nigerian flag da wasu tambari na sojas da aka kawata Haraban da shi…
Wajen hadaddiyar motar sa kirari Bugatti ya nufa, ya buɗe murfin ya fada ciki, har ya ta da motar ya ji an K’wank’waso glass din motar.
Zuge Glass din motar ƙasa yayi, kasancewar ya rufe kuma tinted ne…
a hankali, ta tsakankanin lips din shi ya furta “Imran” ta yanda babu wanda ya ji, shi ma Imran lips din shi ya karanta da bazai ji ba.
murmushi yayi, domin tun yana mamakin abokin shi ya gane cewa haka halin sa yake sam baya son magana, domin da fari ya dauka wulakanci da girman kai ne, sai da ya zauna dashi har suka kulla abota sannan ya gane cewa halin shi mai kyau ne.
“Yes Captain, ina zaka je ne haka?”
Saurayin nan da aka kira da Captain yace “Ammi…. I wanna see her” ya fada yana jan sunan Ammin.
“Uhmmmm mummy’s boy” Imran ya fada cike da tsokana.
Murmushin da iyakar sa lips kaɗai yayi.
“Sai ka dawo toh, ka gaishe min da ita please” Imran ya fada.
Jingina kai Captain yayi yana rufe Glass din motar, kana a 360 ya bar haraban office din.
*Nassarawa GRA Sultan road*
Had’add’en unguwa ne mai dauke da had’add’un gida irin na masu hannu da shuni, ko ina shiru kowa na cikin gidan sa.
A gaban wani babban gate mai ruwan goro ya danna horn, mintuna biyu kacal aka wangale masa gate din… a guje kamar yadda ya saba tuki haka ya yi parking motar a parking space dake gidan sannan ya bude kofar motar ya fito.
Part hudu ne a gidan, wanda daya na Ammi ne, daya nasa duk da baya zama a gidan, daya na yan’uwan shi, daya kuma babu kowa wanda hasali na mai gidan ne da Allah yayi masa rasuwa.
Part dake tsakiya wanda ya kasance na Ammi ya nufa, gaban hadaddiyar kofar ya tsaya, inda da kansa kofar ta bude ya shiga bakin sa dauke da sallama, da bana tunanin akwai wanda zai ji shi, saboda yadda ya furta sallamar kamar wanda aka yi wa dole.
Macece mai shekaru 50 a duniya, Zaune take cikin shigar less buba Mai kyau da tsada irin na mayan mata, ta sanya medicated Glass, kyakkyawa ce sosai domin kamanin su daya da Captain, kamilalliyar fuskar ta dauke da murmushi mai kyau ganin yaron ta da take matukar so.
“Welcome home My Captain” ta fada tana ware masa hannu.
Cikin tafiyar sa ta lafiyayyen namiji ya karasa gaban ta ya rungume ta, yana fadin
“i miss You first love” hadi da zame kanshi ya kwantar kan cinyar ta.
Murmushi Ammi tayi, ta cire hular kansa, shafa kansa tayi, kullum sai yazo ya ganta amma hakan baya hana shi cewa he miss her.
“Miss you too my jarumin jarumai” ta kira shi da sunan da takan kira shi a wasu lokuta.
Dakin ya dauki shiru kamar ba mutane a ciki, hannun Ammi daya sha jan kunshi ya kama yana kallo, murmushin da bai fito ba Ammi tayi, domin ta fuskanci yayi masa kyau ne amma fada ne ba zai yi ba, girgiza kai tayi, kaf yaranta halin shi ya sha bambam da sauran, komai nasa na daban ne, tun yana karami ta lura yana son kunshi musamman ja. burinta Allah ya bashi mace ta gari, ita kuma tayi alkawarin sai ta sa wa matar ra’ayin kunshi ko da bata da ra’ayin hakan.
Amma abin da kamar wuya domin ko budurwa bai da shi, baya kula kowa, ga kannen shi suna da budurwa amma shi kam sam ba ya son maganar ko wacce mace, duk da kawo kan su da suke gareshi.
Tun Ammi na yi masa magana har ta gaji, domin har cikin dangi ta zabar masa ya nuna baya ra’ayi, haka ta cigaba da yi masa addu’a da fatan Allah ya bashi mace ta gari.
Can ta dago kan shi tace “ka ci abinci?”
Yamutsa fuska yayi, cikin yanayi mai kama da shagwaba daya saba yi wa Ammi yace
“Am full Ammi…”
“Ba wani You re full, kullum haka kake cewa, banason wanna rashin cin abincin naka fa, Ni har mamaki nake duk da baka cin abinci amma ko rama baka yi, oya tashi mu je lemme give you something to eat” ta karasa tana rike hannun shi suka nufi dinining table.
Zaunar da shi tayi kamar karamin yaro Sannan ta shiga serving din shi hadaddiyar fried rice Daya Sha namomi da coslow a gefe, da kanta ta shiga bashi a baki, a hankali ya dinga bude bakin sa yana karba ba dan kuma ɗan yana jin yunwa ba, sai dan farincikin Ammi, a rayuwar baya kaunar ɓacin ranta.
Samari uku ne suka shigo cikin falon suna surutai da alama musu suke a tsakanin su, sai dai ganin Captain a zaune Ammi na bashi abinci sai duk suka nutsu kowa ya tsuke bakin shi domin sun san baya son hayaniya, domin yanzu ne zai yi kasa-kasa dasu.
“Ya Hamdan sannu da zuwa” duk suka hada baki wurin fadin hakan.
Kai ya jinjina musu ba tare da ya ce komai ba, cikin kasa da murya daya daga cikin su mai suna Anas yace “kabeer, Omar, ku kalli yadda Ammi ke bawa ya Hamdan abinci kamar jariri”
Dariya ya bawa su Abbas amma babu halin sakin ta, haka suka kunshe abin su, sannan suka sanar da Ammi zasu fita dubiyan abokin su da bai da lafiya, adawo lafiya Ammi ta musu sannan tace su yi masa sannu…
Ganin Ammi bata da niyyar daina bashi abincin sai ya kama hannun ta ya na yamutsa fuska, yace “Please Ammi”sarai ta fahimce shi, sai ta ajiye cokalin ta zuba masa ruwan gora a Glass cup ta bashi, ya ɗan sha sannan ya ajiye, kan kujerar falon suka dawo…
“Ammmmiiiiiii….” ya kira sunan ta da husky voice din shi.
“Na’am”
Ammi ta amsa tana kallon shi hadi da bashi hankalin ta, numfashi ya furzar ya ma rasa ta yanda zai yi mata wanna bayanin mai tsaho da marshal ya turo masa, domin shine abin da zai bashi wahala.
Wayar sa kirar iPhone 12promax ya mikawa Ammi bayan ya shiga ta Gmail din.
Karban wayar Ammi tayi kana a nutse ta shiga karanta inda karatun ya dauke ta tsahon mintuna bakwai kafin ta gama.
Gwauron numfashi ta saki a lokacin data gama karantawa, hannun Hamdan ta kama cikin nata, tace “na karanta, kai ne zaka jagoranci wasu sojas zuwa kwantar da tarzoma, sam bana kaunar ka zuwa duk wani abu da ya shafi yaki, duk da nan cikin Nigeria ne, zuciya ta cike take da tsoro, amma bani da zabi daga wuce ka je din…”
Kara rike hannunsa da kyau tayi tace “ya Allah! Ka tsare dana daga mugun gani, ka raba tsakanin shi da mugaye azzalumai, ya Allah ka dawo min da shi lafiya, ka basu nasara kan wanna aikin da zasu je yi, ya Allah ka tsare shi da sauran sojoji” ta karasa kwalla na cika idanun ta, amma bata bari ya gani ba, domin ta san cewa matukar ya ga kukan ta, zai ce ya fasa zuwa, ba kuma ta so ta ruguza mafarkin shi, domin tun yana dan karamin yaro yake kaunar zama soja da kuma yi wa ƙasar sa hidima.
Rungume ta Hamdan yayi, har abada yana alfahari da Ammin shi
“Ameen ya rabb! thanks Ammi, i love You so much”
“I love you too my captain” ta faɗa tana shafa bayan sa.
Haka ya cigaba da zama da Ammin har yamma ta yi sosai, ya kuma ji dadi kasancewar su tare, Domin itace mutum mafi soyuwa a duniyar sa, bai san so ba sai a kanta, hakan yasa wasu lokutan yake kiranta da First love.
Sai bayan magriba ya yi mata sallama cike da kewar ta ya tafi, a hanya Isha tayi masa, sai kawai yayi sallar sa a masallacin gadon k’aya sannan ya cigaba da tafiya har ya shigo cikin barracks… bangaren da gidan sa ya ke ya nufa ya faka motar sa, sannan ya shiga cikin gidan, wayar hannun sa kawai ya ajiye ya cire duka kakin jikin sa ya jefa cikin laundary basket, towel ya daura a jikin sa sannan ya shiga had’add’en toilet din sa.
Shower ya sakar wa, kansa, yana dafe da bango inda ruwan ya shiga dukan sa, ya dauki mintuna goma sannan ya fito, short nicker mai zanen soldier ya saka, sannan ya fada kan gado, lumshe ido yayi, iska mai dadi dake kadawa yana shigowa ta window’n sa, hannunsa kan six packs dinsa Yana shafawa, ya dauki mintuna biyar a haka sannan yaji wayar sa na ringing, bude lumsassun idanunsa yayi da suka yi nauyi saboda gajiya da yake tattare da ita kana ya mika hannu ya dauki wayar….
Kamar yanda na fada Hoorain mai kusumbi Naira dari uku ne, haka na siyar da shi a baya, kun san Dalilin dayasa na yi masa raki ya dawo 100? Wallahi saboda jin daɗin yanda kuke son books Dina, da kuma addu’oi’n da kuke min, naji dad’i sosai, da a Free ma zan baku shi, amma sai na fasa saboda wasu dalilai, musamman daga wasu reader’s din, dan haka duk mai son Hoorain mai kusumbi zai biya 100 ta 2261488155 Rukayya Haruna zenith bank.
Ko katin MTN 100
Yan nijer zasu turo Airtel na 200, shaidar biya zuwa ga👇
07082281566
NoorEemaan loves you all habibte’s💞
Tue, 17 2022.
7:38am
Leave a Comment