Hotunan Gaban Mace Da Namiji

Hotunan Gaban Mace Da Namiji

 

 

 

 

 

 

Bayani kan yadda Hotunan Gaban Mace Da Namiji Yake…

CIKAKKEN BAYANI AKAN BUDEWAR GABAN MACE DA YADDA ZAA MAGANCHE HAKAN.

Hotunan Gaban Mace Da Namiji

Yanayin halittar farji tamkar robar danÆ™o ce wacce zata iya buÉ—ewa idan aka yi mata talala, haka kuma zata iya komawa ta haÉ—e, wato ta tsuke bayan buÉ—ewa. Tsokokin bangon farji masu motsi ne kuma zasu iya tsukewa ko buÉ—ewa idan mace tayi yunkurin tayi hakan, wato idan ta motsa su ko matse su ta ciki. BuÉ—aÉ—É—en farji (loose vagina) ko buÉ—ewar farji (vaginal looseness) wani yanayi ne dake shafar mata da yawa musamman lokacin juna biyu da kuma bayan haihuwa inda farji ke canza yanayin halittarsa ya Æ™ara girma, wato ya zama buÉ—aÉ—É—en wuri kasancewar naman dake zagaye da farji mai yiwa zakari zobe lokacin jima’i ya saki , tsokokin sun saki basu iya damÆ™ar zakari yanda ya kamata lokacin saduwa. Kamar dai yanayin halittar fatar jikin mutum, wasu mutanen fatarsu nada tauri kamar roba marar sauÆ™in budewa idan aka jata, wasu kuma fatarsu nada laushi da sauÆ™in yin talala idan aka jata, kusan haka itama halittar gaban mace take. Wurin haihuwa jinjiri na fitowa ne ta farji inda wurin ke buÉ—ewa sosai domin jinjiri ya fito. Bayan wani lokaci da haihuwa farji na komawa ya tsuke.

Salon So Hausa Novel Complete

Duk da haka , farji ba zai taɓa komawa ba kamar yanda yake ada ko kamar na macen da bata taɓa haihuwa ba (ko budurwa) , koda kau anbi hanyoyin magani , farji zai zamanto ya ƙara girma kaɗan ko da yawa.

Yawan haihuwar mace, budewar gaba saboda tiyatar likita/Æ™arin kofa a lokacin haihuwa (tear) da yawan yin jima’i yau da gobe, na daga cikin dalilan dake haddasa budewar gaban mace. Idan buÉ—ewar farji tayi yawa yana zama kalubabale ga ma’aurata. Zaya iya zama matsala a rayuwarsu ta jima’i . Saboda wannan yanayi na sanya raguwar É—anÉ—anon jima’i ga mace da mijinta koma ya hana macen jin Æ™oluluwar daÉ—i (orgasm) lokacin saduwa. Dalilin faruwar haka shine , farji baya matse/riÆ™e zakari da kyau, ta yanda za’a samu É—anÉ—anon gugar fata-da-fata tsakanin ma’aurata biyu wanda jin wannan guga shine zai kai ma’auratan biyu ga gamsuwa mai Æ™arfi a lokacin jima’i. Bugu da Æ™ari, wannan matsala na iya saka mace cikin damuwa da jin cewa bata amsa sunanta na cikakkiyar mace ba saboda bata jin dadin saduwa kuma bata iya gamsar da mijinta da kyau. Hakan kuma zai iya sanya maigidan ya Æ™ara wani aure domin biyan buÆ™atarsa. Hakika gamsuwar aure itace saduwa mai daÉ—i tsakanin ma’aurata da zata samar da soyayya da zaman lafiya mai É—aurewa. Matsatstsen gaba (tight vagina) bakin gwargwado, yanayi ne mai kyau da zai iya Æ™arawa mace gishirin soyayya mai Æ™arfi tsakaninta da mijinta.

See also  The sexy boss Romantic and Comedian Story

 

YAYA ZA’AI KI GANE CEWA KO KINA DA

BUÆŠAÆŠÆŠEN GABA?

 

1. Mafi yawan mata masu fama da matsalar buÉ—aÉ—É—en gaba na fama da matsalar rashin riÆ™e fitsari , wato É—igar fitsari. Digar fitsarin zata iya faruwa a lokacinda kika É—auki wani abu mai nauyi, ko lokacinda kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace cewa mace nada budadden gaba.Yawan shekaru, yawan haihuwa , yawan jima’i, tiyatar likita (Æ™arin kofa) ko wani rauni a gaban mace, ko tsayawar al’ada (menopause) saboda karancin sinadarin “estrogen” na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga Æ™arshe zai iya haddasa buÉ—ewar tsokokin bangon farji masu matse zakari .

2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da gaba mai faÉ—i itace: ki saka É—an yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa’annan kiyi Æ™oÆ™arin matse dan yatsan da tsokokin farjinki. Idan har ki gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji to zaya iya zama kina da babban wuri. Bugu da Æ™ari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo) , kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to yiwuwar itace kina da buddden farji.

3. Idan ya zamanto yana da wuya kamin kiji ƙololuwar dadi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar budadden gaba ne. Haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima na iya zama alamar.

4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan buÆ™atarta kuma tafi sha’awar ta saka wani babban abu a gabanta akan Æ™arami – wato bata jin dadin Æ™aramin abu idan ta saka a farji sai babba. Shima alamace cewa mace nada girman farji. A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga lafiya da rayuwar auren ‘ya mace. Don haka sai a kiyaye.

See also  Shareef Hausa Novels Complete

5. Idan ya zamanto kina shan wahala kamin ki gamsar da mai gidanki wajen jima’i ba kamar daba.

6. Idan ya zamanto sai kin matse ko haÉ—e cinyoyin ki biyu sosai sa’annan kike jin dadin jima’i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda Æ™aramar al’aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi budewar gaba.

7. Idan ya zamanto kina jin Æ™arar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake , iskan kamar fitar “tusa” amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa lokacinda maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da budadden farji.

 

MINENE HANYOYIN TSUKE FARJI ?

 

Akwai hanyoyi da dama na matse gaba musamman bayan haihuwa wanda sun hada da hanyoyin magani, motsa jiki (exercise), tiyatar likita domin rage girman farji da sauransu. Wasu hanyoyin nada illa ga lafiya , wasu kuma hanyoyin basa da wata matsala ko hadari kamar dai yanda likitoci ke bayani. Wasu daga cikin hanyoyin:

1. Motsa jiki , hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa (such as kegel exercises) da sunaye. Motsa jikin ya shafi horo da mace zata iya bawa jikinta domin ya zamanto tsokokin gabanta masu motsi sun kara Æ™arfi da tsukewa. Misali, wata kwararriyar likita a India Dr. Sangeeta Gomes ( Consultant Obstetrician and Gynaecologist) , ta nuna cewa mace zata iya inganta tsukewar gabanta idan tana yin motsa jikin dauke numfashi (breathing exercises). Zaki dauke numfashinki na tsawon ‘yan daÆ™iÆ™oÆ™i (seconds) kadan sannan ki tsuke (tsokokin) farjinki matakam na tsawon wani lokaci a lokacinda kike mai dauke numfashin. Za kiyi hakan a kowace rana, sau 10 ko 15. Zaki iya yin hakan a kicin lokacinda kike aiki, a ofis, a tsaye ko a zaune , a ko ina kuma a ko wane wuri bata tare da ma wani yasan abinda kike yi ba. Sa’annan zaki yawaita cin ƳaÆ´an itatatuwa (kayan marmari) da abincin ganye (vegetables). Wannan ko shakka babu zai taimakawa mace wajen matse gaba domin gyara aurenta. Wani nau’in motsa jikin kuma shine ake cema “Kegel exercise”. Toh yaya ake yinshi? Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fitsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki riÆ™e fitarin, ki danne sa na tsawon daÆ™iÆ™oÆ™i 10 , wato ki Æ™irga 1 zuwa 10 sa’annan ki saki fitsarin a hankali a hankali. Zaki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za kiyi fitsari. Shima wannan nau’in motsa jikin na tsuke gaban mace.

See also  Ya zanyi da auren Adnan Hausa Novel Complete

2. Hanya ta biyu shine wanke gaba da ruwan sanyi mai Æ™ankara. Yana taimakawa wajen matse gaba amma sai an hada da motsa jikin da muka yi bayani. Wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana. Amma zaifi dacewa ace sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwatakwata sa’annan tayi amfani da ruwan sanyin , wato bayan ta koma “normal”. SaÉ“anin yanda al’adar Bahaushe tayi imani dashi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace ,wasu likitocin a wasu al’adun na ganin yana matse gaba.

3. Yin amfani da aluf (alum). Aluf yana matse gaba sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin hakan saboda da sinadarin kemikal ne.

4. Yin tiyatar likita domin rage budewar farji. Wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yin hakan saboda wasu dalilan lafiya.

5. YunÆ™urin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacinda mijinki yake kaikawo. Zaki yawaita yunÆ™uri domin tsuke gabanki domin mijinki yaji alamun ana riÆ™e masa al’aura tamkar zobe zagayen gabansa. Idan mace na yawaita yin da haka to zai zama É—abi’arta kuma nan gaba ba zata san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta, kuma hakan zai inganta jin daÉ—in mijinta sosai. Allah Ya taimaka.

6. Da sauransu.

Za’a iya neman taimako na musamman daga cibiyar mu domin magance wannan matsala wacce za’a haÉ—a da bayanan da mukayi anan domin samun sakamako mai kyau, da yardar Allah.

0 thoughts on “Hotunan Gaban Mace Da Namiji”

  1. Pingback: Bakar Waskika Hausa Novel Complete - Hausa Novel

  2. Pingback: Bakar Waskika Hausa Novel Complete - Hausa Novel

  3. Pingback: Amfanin Hulba Ga Budurwa - Hausa Novel

  4. Pingback: Amfanin Hulba Ga Budurwa - Hausa Novel

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top