Crypto

How long does it take to mine 1 Bitcoin

How long does it take to mine 1 Bitcoin

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: mine bitcoin

Bitcoin da Altcoins:

Me yasa duk lokacin da Bitcoin yake tashi sauran Altcoins ma sai su tashi, idan Bitcoin ya fadi sai suma su fadi?

Kamar yadda muka sani a Crypto Bitcoin shine babban Coin mafi girma a duniya wanda yake da Market dominance mafi yawa, duk Coin din da ba Bitcoin ba ana kiran sa da Alt, ko (Alternative), idan suna da yawa ana ce musu “Alts” wato (Altcoins), so duk Coin din da yazo bayan Bitcoin toh yana cikin Alts a asalin yadda aka faro tafiyar Crypto a 2009.

 

To amma a yau an samu sauyi, ko ‘kari a kasuwar Crypto, akwai Bitcoin, akwai Altcoins, akwai Shitcoins.

Sai dai da aka ce Altcoins ba kowane Crypto bane ake kiran sa da Altcoin, saboda wasu Coins ne wasu kuma Tokens ne.

Menene bambancin Coin da Token?

Watanni 9 ko 10 da suka wuce nayi rubutu akan haka, amma a takaice:

 

1. Coin shine Crypto din da yake da Network din sa mai zaman kansa, wato Crypto din da yake da BlockChain din sa, ba akan BlockChain din wani coin yake ba, wannan shine Coin.

 

2. Shi kuma Token shine Crypto din da baya da Network din kansa, aron Network yake yi, akan Network din wani Coin yake.

 

Dan haka shi Coin ana iya gina Smart Contract akan sa, ana iya samar da wasu aiyuka akan sa ko a kirkiro wani Token akan sa, amma Token kuma ba’a iya samar da smart contract akan sa.

A saukake idan kaje kan Trust Wallet, idan ka hau kan SafeMoon ko FEG, daga hannu hagu ta sama zaka ga an rubuta BEP20.

Toh duk Crypto din da kaga an rubuta Masa haka toh Token ne, ko kaga an rubuta ERC20, idan Coin ne toh zaka ga an rubuta Coin a wannan wurin da kaga BEP20 ko ERC20, idan ka duba Bitcoin da Ethereum da BNB zaka ga an rubuta Coin, su ba Tokens bane.

 

Toh me yasa idan Bitcoin ya tashi sai sauran coins da token su tashi, idan ya fadi kuma sai suma su fadi.

Wani lokaci Sai Bitcoin yayi ta tafiya amma sauran Coin din suna tsaye?

Wannan tambaya ce mai matukar wahala ga Injiniyoyi da sauran masana Computer a harkar, har yau ba zaka samu wata amsa kwara daya tak da zata gamsar da kai ba daga cikin dukkan maganganun da masana suka yi.

 

Amma binciken da nayi da nazarin wasu abubuwa a harkar, naga wasu bayanai da dama, wanda sun kai guda biyar (5) amma a ciki babu wanda nafi gamsuwa da ita kamar wannan

Abinda ya sabbaba haka shine “Open Sort Code” na Bitcoin, barin Sort Code din Bitcoin da aka yi a bude a lokacin da Satoshi Nakamoto ya kammala kirkirar Bitcoin a 2008.

Da kuma Entry code na Bitcoin da aka rufe, har yau anki a bayar ma wani, ko a 2019 babban mai kudin duniya na yanzu wato Elon Musk ya nemi ya mallaki Entry code na Bitcoin an hana shi.

 

Wanda har yau yana fatan ya mallaki Entry code din.

Barin Sort Code din Bitcoin a bude shine ya bada dama aka dinga kwafar code din (Copy) aka dinga kirkiro sauran coins a duniya.

Sunce, da ace an rufe sort code din da Bitcoin ba zai samu wannan karfin jan ragamar kasuwar Crypto ba, domin duk Wanda zai kirkiri coin zai nemo sort code din sa ne daban wanda baya da wata alaqa da Bitcoin.

.

Wasu masana kuma suna cewa, idan ana so Bitcoin ya daina jagorantan kasuwar Crypto sai an kure Mining din sa, daga 100 percent ya koma 0 percent, wanda yanzu haka anci kaso 90 cikin ‘dari, so daga yanzu zuwa shekaru biyar masu zuwa Bitcoin zai kai matsayin da ake so, wato Digital Gold, daga nan kuma zai tsaya da jan ragamar kasuwar Crypto.

Wasu na cewa idan ya kai Dala dubu 500 ya kure, tare da market cap na 5 trillion dollars.

.

Daga baya kuma za’a zo a wuce Bitcoin a kudi, dama wannan kam sanannen abu ne a wurin duk wanda yake bincike akan Crypto yasan za’a je lokacin da za’a wuce Bitcoin kudi, wata kill Ethereum ko BNB su zasu jagorancin kasuwar bayan Bitcoin ya kai geji.

Tabbas za’a wuce shi, amma still dai yana da wasu manyan abubuwan da sai an koma gare shi.

Sai dai wata matsala guda daya da muka baro a sama wurin batun Sort Code din Bitcoin, da ace an barshi Close wato a rufe, toh da yanzu babu coins guda 50 ma duniya.

.

Domin samun wadanda zasu iya aikin kirkiro Coin ba tare da kallon aikin da Satoshi Nakamoto yayi ba za suyi wahala, kenan da yanzu duniya bata san ma da batun Crypto ba, sai ‘yan kadan.

Sai dai wasu suna cewa da gangan aka sake sort code din Bitcoin.

Domin kasuwar Crypto mutane take so, da an rufen da yanzu babu mutane a cikin ta kamar yanzu.

.

A wani gangaren kuma, daga cikin abubuwan dana gano, shine a tsarin kirkirar Bitcoin an bude kofofi uku, wanda idan an cike su da tsari irin na Bitcoin toh Bitcoin din shi zai yi nasara akan harkar.

Bayanai sun nuna cewa an rufe kofa ta farko da Bitcoin Cash ne, wato BCH, kofa ta biyu da Ethereum, ko ETH, sai ta uku da XRP, wasu kuma sunce da ADA ne (Cardano).

Akwai wadanda suka ce “Doge Coin” ne ma, amma wannan maganar bata da karfi.

.

An kirkire su ne asali domin suyi aiki ma Bitcoin, su karfafe Shi, ba dan suyi aiki irin nasa ba, even though Bitcoin bai cika dalilan yin sa ba.

A wannan gabar zan so na alaqan ta bayanin da wasu tsare tsaren da aka yi acikin Pi Network, wanda suke kusan kama da gyara ma Bitcoin, a rubutu na gaba zan kawo bayanan in sha Allah.

Toh amma har yanzu masana suna cewa dole a samo mafita akan wannan matsalar ta Bitcoin.

.

Kuma bincike yana kan gudana a fadin duniya, watakil tsarin Pi Network ya sauya tafiyar Crypto Currency a duniya gaba daya.

Tare da kawo mafita ma matsalar high volatility da kasuwar take dashi, even though nayi analysis akan wasu abubuwa guda biyar wadanda zasu kawo saukin volatility, wato yawan faduwar kasuwar Crypto nan da shekaru uku masu zuwa in Sha Allah, last week na rubuta su a group din mu na Whatsapp, na tabbata wasu sun gani.

.

Akwai wata alaqa wacce nake so na tabbatar da ingancin ta itace alaqar masu Pi Network da Satoshi Nakamoto ko kuma alaqar Bitcoin Core Team da Pi Network Core Team, ko kuma hannun masu Pi Network a lokacin kirkirar Bitcoin, wanda har yanzu ban kai ga samun tabbacin abinda nake son sanin ba.

Amma tabbas jijjigar da Bitcoin yake yi ma kasuwar Crypto abu ne da ko jiya ka shiga harkar zaka tabbar da akwai gyara a technology din Bitcoin, wanda ada is good, amma yanzu needs some modifications.

Allah yasa mu dace.

.

✍️

Abdul-Hadi Isah Ibrahim.

Leave a Comment

error: Content is protected !!