Tunatarwa

Hukunci akan ranar Eidel Fitir ga Musulmi

Hukunci akan ranar Eidel Fitir

Musulmi mu na da idi guda uku, biyu daga ciki su na maimaituwa duk shekara: 1. Idin Babbar Sallah wanda ya ke maimaituwa duk ranar goma ga watan Zulhijjah; 2.  Idin Ƙaramar Sallah wanda ya ke maimaituwa duk ranar ɗaya ga watan Shawwal, 3. Idin Jumma’a wanda ya ke maimaituwa duk sati.

Babu wani idi a Musulunci bayan waɗannan.

KALMAR IDI

Abin da kalmar “idi” ta ke nufi shi ne duk abin da ya ke maimaituwa, ya ke dawowa, ya ke komowa da farin ciki a wani lokaci sananne.

Anas Ɗan Malik (ra) ya ruwaito cewa lokacin da  Manzon Allah (saw) ya shigo Madina su na da wasu ranaku da su ke yin idi a ciki wanda su ke tunano abubuwa da su ka faru a zamanin Jahiliyya, sai ya ce, “Allah ta’ala ya musanya muku da wasu ranaku da idin Fiɗir (Ƙaramar Sallah ranar ɗaya ga watan Shawwal) da kuma idin Adhha (ranar goma da watan hajji).

Imam Ahmad da Abu Dauda da Nasaiy duba Sahihu Abi Daawud. Ibn Hazmin ya ruwaito ijma’in malamai akan haka.

HIKIMAR SALLAR IDI

Allah ta’ala cikin hikimar sa ya ware wa Musulmi wata rana bayan sun ƙare ibadar azumi za su shiga cikin watan hajji, su yi sallah su yi farin ciki su girmama Allah bisa hore musu dama har su ka ga ƙarshen azumi lafiya, kuma kwanakin hajji su ka fara.

ABUBUWAN DA AKE YI A RANAR SALLAH

1. Yin sallar idi
2. Fitar da zakkar kono kafin sallah.

3. Sada zumunta.

4. Girmama Alalh da yi masa godiya.

5. Shagulgulan Sallah ga mata da yara waɗanda ba su ƙetare iyaka ba.
6. Bayyana farin ciki da yafiya da kyautata wa al’umma da maƙota.

HUKUNCIN SALLAR IDI

1. Alƙur’ani mai girma.

2. Sunnar Annabi (saw).

3. Haɗuwar kan malamai.

An samu maganganu guda uku daga malaman Musulunci game da hukuncin sallar idi, gwargwadon kowa daga cikin su dalilan da su ke hannun sa:

1. Wajibi ne zuwa sallar idi. Abin da ake kira wajibi shi ne duk abin da shari’a ta nemi a yi shi dole. Idan an yi shi yadda ta ce za a sami lada, idan ba a yi shi ba an aikata laifi, wanda azaba ta na iya sauka a kan haka.
2. Mustahabbi ne zuwa sallar idi. Abin da ake kira mustahabbi shi ne idan an yi za a sami lada, idan ba a yi ba babu alhakki.

Fardu kifaya ne zuwa sallar idi. Abin da ake kira Fardu kifaya shi ne abin da ake nema wasu daga cikin al’umma su yi domin su ɗauke wa ragowar, amma idan babu wanda ya yi to duk al’umma ta yi laifi.

Musulmi a wajen sallar Idi ta bara

Sallar idi ta bambanta da sauran salloli ta fuskoki da dama:

1. Ba a yi mata kiran sallah ko iƙamah.

2. Ba a yin nafila kafin ta ko bayan ta.

3. Ba a yin huɗuba sai bayan an gama sallah.

4. Ana yi mata ƙarin kabbarori guda bakwai a raka’ar farko har da kabbarar harama, da kabbarori guda biyar a raka’a ta biyu.

5. Ana canza hanya wajen tafiya da wajen dawowa.

6. Duk Musulmi maza da mata yara da manya, har da masu jinin al’ada da jinin biƙi da amare da marasa hajabi, duk sai su aro daga maƙota domin su zo sallar idi saboda muhimmancin ta.

7. Waɗanda su ke da larura ta rashin yin sallah sai su koma gefe su na kabbara, domin su dace da addu’ar wannan rana da albarkacin ta.

8. Za a tafi ana kabarbari cikin nutsuwa.

9. Yin wanka da ado, kwalliya da shafa turare a ranar sallah domin zuwa sallar idi.

10. Yin asuwaki da gyaran jiki, da tsafta da kauce wa maganganu na batsa da rashin kangado.

11. An so a tafi a ƙafa a dawo a ƙafa, idan tafiyar ba wahala.

12. Ana so a ci ɗan dabino kafin a fita zuwa idi na Ƙaramar Sallah.

13. Ana so a yi sammako zuwa sallar idi, musamman na Babbar Sallah, domin a dawo da wuri a yanka abin layya.

14. Idan kuwa sallar idi ce ta Ƙaramar Sallah, an so a yi jinkiri domin a sami lokacin fitar da zakkar fidda kai.

YADDA AKE SALLAR IDI

13. Raka’a biyu ce.
14. Karatun ta a fili ake yi.

15. Za a yi kabbara bakwai ban da kabbarar harama a raka’ar farko.

16. Za a kabbara biyar ban da kabbarar ɗagowa a raka’a ta biyu.

17. Ana karanta Suratul A’ala a raka’ar farko bayan Fatiha, ko suratu Ƙaaf.

18. Ana karanta Suratul Gashiyati a raka’a ta biyu bayan Fatiha, ko Suratu Ƙamari.

19. Bayan an gama sallah sai a gabatar da huɗuba guda ɗaya, ba biyu ba, domin Hadisin da ya kawo huɗuba biyu ba shi da inganci, don haka masu fassara huɗuba sai su  haɗe su a tsayuwa guda.

20. Ba a hawa mumbari lokacin yin huɗuar sallar idi, a ƙasa ake yi.

21. Kada a yi doguwar huɗuba, domin a ba wa mutane dama su koma gida da wuri.
22. A wajen kabbarorin za a iya ɗaga hannu, amma idan idan ba a ɗaga ba babu laifi.

23. Sahabbai su na yi wa juna fatan alkhairi da addu’a tagari a ranar idi,Allah ya karɓa, mana, ya maimaita mana da alheri.

*Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban malami ne a Kano

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Leave a Comment