Hausa Novels

Iffah ko Hibbah Hausa Novel Complete

Iffah ko Hibbah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*IFFAH KO HIBBAH*

 

 

NA

R.HUSSAIN (Zinariya)

 

 

Marubuciyar

 

So halitta ne

Masarautarmu

Ɗaukar fansa

now

Iffah ko hibbah.

 

 

 

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

_ƊANƊANO!ƊANƊANO!!ƊANƊANO!!!_

_MIJIN DARE_

_(Spiritual story)_

 

_Tunda Abban Ansar ya bar gidan ta ji hankalinta ya kwanta, tun bayan da tayi arba’in Khaleesat ta sauya gaba ɗaya,Mijinta Ibrahim ya kasa gane kanta, a haka suna zaune lafiya amma da zarar ya bujiro mata da buƙatarsa ta auratayya za ta ce bata san zancen ba.Tsawon wata biyu kenan yana cikin matsananciyar damuwa._

 

_Haba kullum sallah,kullum sallah idan na dawo daga party’n na haɗa nayi_

_Kwalliyarta ta ke ta tsarawa,dan tafi kowa kyau a wajen bikin, INTEESAR kenan, tafiya take sai taji kamar ana bin ta a baya, idan ta juya sai ta ga ba kowa, a haka har ta isa gidan ɗan Hausa inda za’ayi kamun ƙawartasu_

 

_Ita ce ta fara buɗe wajen da rawa, babu abin da ke tashi a wajen sai ihu da tafi kawai rap!rap!rappp!!!! ka ke ji, DJ ne ya nemi da suyi rawa tare, 9ja music aka sa musu, tare su ka fara irin rawar waƙar,taɓe-taɓe da rungume-rungume su ke yi, ihu da hargowa kawai ke ta shi dan sun burge guys da ladies ɗin wajen_

 

_Gida ta dawo kusan goma na dare, raɓe-raɓe ta farayi, ta shiga da sallama,Mahaifinta na zaune ya na cin tuwo_

 

_Ya tsani ya buɗe ido yaga INTEESAR a gidan, duk ƙannenta da sa’anninta sunyi aure, amma ita har yau babu wanda ya zo da sunan ya na sonta_

 

_Bacci ta ke ba tare da ta yi sallolin da ta tara ba, underwears kawai ke jikinta, Wata Mummunar halittace ta bayyana MIJIN DARE baƙin aljani ne mai mummunar siffa_

_Cikin bacci ta ji an fara….._

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
_HUMMM MASOYA KARKU SAKE AYI BAKU,MIJIN DARE YA NA NAN TAFE VERY SOON, DAGA ALƘALAMIN✍🏼 R.HUSSAIN (Zinariya)_

 

 

 

Ga waɗanda su ke so suyi joined a face book ku bi ta wannan link ɗin👆🏻

 

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

 

 

 

 

FREE BOOK

 

 

Page 93 – 94

 

 

 

 

_________Dukan tsohon yake da ƙasan bindigar da ke hannunsa, “ka ga ni ko, su ma iyalan naka sun gaji da rayuwarka,shiyasa su ka kasa fansar ranka, kashe ka za mu yi dan mun gaji da ajiyarka” Ali boy wanda ya ke real name ɗinsa shine Ashiru, ya ke faɗawa sarkin noma bayan ya yi masa jina- jina,ko motsi ba ya yi.

 

Ɗaya daga cikinsu ne yace”oga ya kamata a ƙara kira, idan ba su kawo ba kawai sai mu aika shi ƙiyama”

Ali boy da ya ke zaune a kan dutse yace” wacce dama ce ba mu ba su ba, tun ina cikin garin har na gama aikina,yau kwana na nawa da dawowa, kullum sai mun ciyar da shi to ni nagaji wallahi idan ba su kawo yau ba” Ya harba bundiga sama, ƙarasa suma sarkin noma ya yi tsananin razanar da ya yi.

 

A gidan sarkin noma kuwa ana ta ƙoƙarin haɗa kuɗin fansa,an siyar da kadarorinsa da yawa an haɗa kuɗin, jiran kiransu kawai ake su faɗi inda za’a kai kuɗin.

 

Rashida da ta ɗan saki jikinta da mutane dan ta fara dangana da ƙaddarar da ta faɗa mata, ta haƙura da MAHEER tunda ta ji ya auri IFFAH ta sanyawa ranta ruwan sanyi, yanzu gaba ɗaya ma ta cire rai da aure gani take ma ba mai aurenta.

 

Har su Mommy su ka gama kintsawa, MAHEER bai shigo gidan ba, Hajiyan birni ce tace” wai kenan wannan kafurin Yaron ba zai shigo ya yi wa matan gidan sallama ba, sai dai mu same shi waje ko ya ya yake nufi?”

babu wanda ya amsa, su HIBBAH da su ka gano kiwon IFFAH mashaAllah akuya ta yi ƴaƴa ga shanuwarta ma ta girma da ɗan maraƙinta wanda shanuwar ta haifa, ta na dawowa take tambayar ina nata, Umma tace na ta ya na nan zuwa ita ma,ai IFFAH aka fara haifa shiyasa a ka fara siya mata,ita ma nata ya na hanya.

 

 

Sosai HIBBAH ta yi murna, har su ka shirya tsaf, amma IFFAH ta yi zuru-zuru duk da ta daina kukan, ba ta daina jin haushin MAHEER ba. MUJEEB ne ya shigo ɗakin dan kiransa.

Samun sa ya yi ya na kuka, tamkar ƙaramin Yaro, da sauri ya nufi wajensa ya na tambayar lafiya me ya faru.

Hannun MUJEEBB ya riƙe ya na cewa ya taimaka masa, rasa taimakon da zai yi masa ya yi, cikin damuwa yace” sannu ka daure ka yi breakfast bro, may be alser ce tunda ciki ke maka ciwo” kunun ya zuba a cup ya bawa MAHEER a hankali ya ke sha ya haɗa uban gumi sosai, a hankali-a hankali ya ji ya fara dawowa normal.

 

 

Tare su ka ci abincin da MUJEEB sannan suka fito, gidan su ka shiga, sashe-sashe su ka shiga su ka yi sallama, sashin inna Hansa’u su ka je ganinta su ka yi a hargitse, sanar da su Hajiya su ka yi sannan aka je dan ganin mai ya faru.

 

Da kanta kawai take kuka tun jiya, HIBBAH ce ta kalli IFFAH, ɗauke kanta IFFAH tayi ganin haka yasa HIBBAH tasan ramuwar abin da tayi mata IFFAH tayi.

Umma ce tace”sannu Inna Hansa’u Allah ya sauwaƙe”

MUNEEBA ta kalli IFFAH tace” in faɗa?” kallonta aka yi Hajiyan birni tace “au, au wata kitimurmurar ta ƙulla ko?”

MUNEEBA tace” wallahi IFFAH ce ta sa mata ciwon kan nan, saboda sharrin da ta yi wa HIBBAH”

Kallon IFFAH kowa ya ke, tare da alamar tambaya.

 

MUJEEB yace” *IFFAH KO HIBBAH*” MUNEEBA tace”jiya da daddare lokacin da abun ya faru, naji HIBBAH ta na cewa bazata yarda ba, sai IFFAH take cewa, ai ta rama mata, ko bacci ba za ta yi”

“la’ilaha’illahu…….IFFAH wai ke me ya sa kin cika mugunta ne?” Hajiyan birni ta faɗa ta na riƙe kunnen IFFAH, Inna Ma’u tace”au wai har yanzu ba su daina kama mutane ba, kai gaskiya wannan abun yafi ƙarfin ƙwari sai dai mu kira shi da maita”

Umma da ta kasa magana ta shammaci kowa ta kamo IFFAH da HIBBAH ta yi sashinta da su, sa bo da ranta ya ɓaci, sanadin su ake alaƙanta mata dangi da maita, MUJEEB ne ya bi ta, yana bata haƙuri hakama su IFFAH da su ka fara kuka su na cewa tayi haƙuri.

 

Mommy ce ta kira Daddy a waya ya na ƙofar gida tare da su Baba tare su ka shigo gidan jin abinda Umma za ta yi su ka nufi sashin, MUJEEB ya riƙe dorinar da Umma ta ɗauko za ta yi duka, ana haka Daddy da Baba su ka iso, “haba Halima me kike shirin aikatawa haka?” Daddy ya faɗa ya na riƙe dorinar hannunta, kuka ta sa tace” nagaji da abinda Yaran nan su ke janyo min, sanadinsu ne ake alaƙan ta ni da maita,wa ye yace su yi mata ƙwari, su barta da Allah mana” ta na ta kuka abin tausayi.

 

MAHEER kuwa tunda Inna Ma’u ta faɗi haka ya ji ya tsaneta, ganin Umma ta ja ƴaƴanta tayi fushi ya sa shima ya ce”mu tafi”

Hajiyan birni tace” ina za mu tafi ba su sa kar mata kanta ba, kai ni wannan ƙwarin ya ishe ni, sun riƙe min ido,sun riƙe wa Yaro magana da ji, yanzu kuma sun riƙe wa Hansa’u kai “sai ta fashe da kuka.

 

Hansa’u ce ta buɗe idonta, jin kan nata ya yi sauƙi, ta miƙe aikuwa ba ta tsaya ko ina ba sai sashin Umma ganin yanda ake drama akan su IFFAH ya sa Hansa’u hanawa, haƙuri ta bawa

HIBBAH.

Da ƙyar su Baba su ka sasanta komai, Umma tayi masu addu’ar Allah ya tsare ya kai su lafiya.

 

Mommy ma ta nuna rashin jin daɗin abinda ya faru,haƙuri su ka ba ta, su ka nemi yafiya sannan su ka ɗau hanyar Kano.

 

 

BAYAN SATI BIYU

 

 

 

Tunda su ka koma gida,babu wanda ya ke shiga harkar kowa tsakanin MAHEER da IFFAH, duk inda tasan za su haɗu ba ta bin hanyar,Hajiyan birni na kula da takunsu, kallonsu kawai ta ke.

 

Daddy ne ya fito domin zuwa office, da sauri MAHEER ya tare shi, dan ya na son akai IFFAH boarding school. “Daddy” MAHEER ya kira shi yana ƙarasowa durƙusawa ya yi ya na soshe-soshe Daddy yace” ya aka yi ne MAHEER?”

“Uhm dama ko, da…ma Daddy akan wancen Yarinyar ne?”

Daddy yace”wacce Yarinya kuma”

MAHEER yace”wai da ma cewa nayi mai zai hana a sauya mata school, akaita boarding school,kamar za ta fi karatu”

Daddy ya yi murmushi yace” sai corner-corner ka ke wa za’a kai boarding ɗin wai”

“wannan IFFA ɗin, dan na ga kamar idan ba tsayawa aka yin sosai akan ta ba, wallahi Daddy za ta sa aji kunya nan gaba, kaga acan su na tsare dole ta mai da hankali tayi karatu”

Kai Daddy ya gya ɗa alamar gamsuwa da wannan shawara.

 

“Gaskiya ne, ka yi kyakyawan tunani, to yanzu abun da za’ayi shi ne zan sanarwa Hajiya kasan ƴar ɗakinta ce, idan ta ta amince shikenan, sai a kaita”

Da jin daɗi kuwa MAHEER yace” ai za ta amince ma, Daddy ni zan ma je in sanar da ita”

“to shikenan” Adawo lafiya yayi wa Daddy ya nufi sashin Hajiyan birni.

 

 

IFFAH na can sashin Mommy su na soya wainar fulawa, da su MUNEEBA. Haka nan yau take sha’awar ci.

Gabanta sai faɗuwa yake kar dai ciki ne,ga shi mugun kwaɗayin wainar takeji. Jiki a sanyaye ta ke komai, idan ta faki idon su HIBBAH sai ta share hawaye. MAHEER ya cuceta, shikenan rayuwarta ta kusa ƙarewa, shawara take da zuciyarta ta faɗa ko kar ta faɗa? Tun ta na tunani har HIBBAH ta fuskanci akwai damuwa, a fuskar IFFAH jira take su gama wainar ta tambaye ta.

 

 

 

MAHEER ya isa sashin Hajiyan birni yana jin daɗin ya haɗowa IFFAH mugunta, zai rabata da kowa nata, akaita boarding inda ba ta san kowa ba.

Tana zaune a parlour ta na kallon Saudiya kamar kullum Atine na gyara mata ƙumba, su na hira sama-sama, MAHEER ya shigo da sallama daga shi sai three-quarter da wata armless ta Maza,kallon uku saura Hajiya tayi masa.

“Assalamu alaikum” ya yi musu sallama.

“wannan sallamar kaɗai ya sa za’a san kana sallah, ba dan haka ba, ba ka da maraba da kafurai yanzu wannan kaya kasa ko kuwa tsirara kake?” Hajiya ta faɗa ta na nuna wandon da ke jikinsa.

 

“Ni kinga ba wai abin da ya kawo ni kenan ba, na zo miki ne da very important issue ne about…….Kai dalla ba na son wannan yaren na kafurci,me ne ne?” Atine ce ta ta shi domin ba su guri. Farko kamar abun arziki ya fara tsara ta sannan ya kawo mata hujjoji, kafin ya faɗi dalilin zuwansa.

“watu kun Hajiyata kinga ne, idan aka kaita can ko, za ta fi nutsuwa da kuma karatu nasan idan ta dawo sai dai ki ji tana larabcin da ki ke so, boarding school ɗin nan ta na gyara marasa kunya”

Hajiya tayi dariya tace” ai kuwa za’a kaita MAHEERU, idan UMARU ya dawo za muyi maganar” da sauri MAHEER yace” ai ya amince sai da na sanar da shi ma sannan ya ce sai abinda kike ce”

Hajiya tace ” ai na amince, tun kafin ka zo da wannan shawarar na yanke shawarar kai ta babbar makaranta,wacce take cike da ƙalubale kala-kala”

“very good my Hajiya, shiyasa na ke son ki, kinga munyi tunani ɗaya kenan”

Da murna ya bar sashin ya na jin ya haɗa mugunta kuma ta karɓu.

 

 

 

Hajiya ta bi shi da kallo” hmmm Yaro yaro ne, ai kuwa ƙafarka ƙafarta a can za ta yi bomin ɗin dan Ubanka, za ka san da ni kake zancen, kai ka kawo shawara kuma ta karɓu MAHEERU.

“Atine,Atine!! zo ki kira min Nafisa” da hanzari kuwa Atine ta fito ta na amsawa ta tafi ta kira Mommy.

 

Tana can ɗaki ta na ta tunanin ko dai an bar zancen tafiyar IFFAH ne, ganin har yau ba’a ƙara maganar ba.Atine ce ta shigo ta sanar da ita kiran Hajiyan birni. Tare su ka koma, ta gaishe da Hajiya tace” ga ni Hajiya”

Hajiya ce ta ɗaga baki sama ta turo shi, ta harɗe ƙafa tace”yanzu MAHEERU ya zo yace min ya na son akai IHU bomin wai anfi karatu, sa bo da zalunci shi, to za’a kai ta bomin ɗin amma ta can ƙasar da ya ke karatunsa, tunda shi ma ai bomin ɗin yake, sai su yi tare acan ko”

 

Mommy tace” yanzu shi ne ya ce akai IFFAH boarding Hajiya”

“a’a Nafisa ba shi ne ya faɗa ba, ƙarya na yi masa” Hajiya ta faɗa ta na galla mata harara, Mommy tace” Allah ya ba ki haƙuri,amma Hajiya ni a shawarata kama ta ya yi a…….” Ta shi ki koma gidanki Nafisa,ko yanzun nan in ci mutuncinki”

ta shi Mommy tayi ta na bata haƙuri,ta koma saahinta.

 

“Ai na kwan da sanin ba kya son auren nan kuma Allah ya haɗa, sai dai ki haɗi yi zuciya ki mutu Nafisa, tare za su tafi in ya so ke ma ki bar gidan, ƴar nema mtswwwww………..

 

 

 

 

*Zinariya ce*





Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022



Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram



Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!