Illar Alamajiranci hausa novel
: *ILLAR ALMAJIRANCI*
*NA LANTANA JAFAR*
_Shafi na ÆŠaya_
“Wallahi ba zai yiwu ba, karatun allo zan turaku domin ba ni da karfin da zan ciyar da ku, ku tafi can ko na huta. Ku zama cikin shiri, a duk lokacin da malam Sidi ya iso tafiya za ku yi.” Malam Bako ke fadi ma ya’yansa, cikin kakkausar murya.
“Malam don Allah ka yi hakuri ka kyale mun yarana a gabana, na yi alkawarin daukar nauyinsu, ba tare da na nemi taimako daga gareka ba.”Cewar Kulande, wacce ke durkushe bisa gwiwowinta gaban malam Bako, cike da jimami.
“Sai ki yi, in dai nine ubansu na gama magana, kuma na rufe wannan babin.” Ya karkaÉ—e rigarsa tare da ficewa daga gidan.
Ba ta da zaɓi, dole tashi ta yi ta koma cikin ɗakinta jiki babu kwari, kuka take yi kaman ranta zai fita, tunanin yadda almajirai ke gararamba ya hana zuciyarta sukuni, tana hango ita ma haka yaranta za su rika bulayi gida-gida suna neman abinci. Babban ɗanta ya shigo Mudi, dan kimanin shekaru sha biyu a duniya, yaro ne mai tunani da hangen nesa. Allah ya yi masa basira, idan ya yi magana kamar wani babba, ya kasance mai tausayin mahaifiyarsa. Shi ma ransa duk a jagule, ba sa kaunar hukuncin da mahaifinsu ya yanke. Ganin halin da mahaifiyarsu ke ciki ya kara daga masa hankali.
Gefenta ya zauna cike da tausayinta, cikin dakiya ya fara magana,
“Inna ki yi hakuri ki bar kukan nan, ba shi da amfani kin san halin baba idan ya furta babu makawa sai ya aikata, don haka ki yi mana fatan alkairi don Allah.”
Ɗago jajayen idanunta ta yi, wadanda suka kara ƙanƙancewa saboda kukan da take yi.
Ta ce, “Ba za ka gane abunda nake hango wa ba Mudi kai yaro ne, ba ka san illar dake tattare da kai yaro al’majiranci ba, a sanadin haka na rasa dan’uwana jigon rayuwata, wanda hakan ya sani cikin maraici da rashin gata, tunda na taso har yau.” Ruwan hawayenta suka cigaba da gudu kan fuskarta, ta sanya hannu ta share sannan ta gyara zamanta sosai tana fuskantarshi.
“Babu wanda ya dauke ni mutum sai ku ya’yan da na haifa, ku kuke saka ni farin ciki har in yi dariya. Zan shiga wani hali idan na bude idona, ban ganku a kusa dani ba Mahmoud.”
Cikin mamaki ya dago kansa, wanda tunda ta fara magana yake kallon kasa. Tunda yake bai taɓa jin ta kira sunanshi ba.
Ba ta damu da yadda yake kallonta ba, ta cigaba da fadin,
“Ina son ka goya mun baya duk runtsi kar ka yarda da hukuncin mahaifinku, a wannan karon ba zan yi shiru ba, na É—auki aniyar sai na Æ™watarwa kaina yanci, cin kashin ya isa haka. Amma hakan ba zai samu ba sai ka goya mun baya, zan kai kara gidan maigari koda igiyar aurena za ta tsinke.”
Cikin hanzari ya ce, “A’a Inna, ki bi komai a hankali, yin hakan ba abun da zai haifar fa ce kara É“ata lamarin, kin san halin baba kaifi É—aya ne, ba zai taÉ“a janyewa ba, ki yi mana addu’a da fatan alkhairi. Burin kowanne É—a idan ya shigo gidan ubansa ya ga mahaifiyarsa a ciki, kina nan bamu tsira ba ina ga ba kya nan? Zamanki shi ne rufin asirinki damu ba ki É—aya. Ki yi hakuri.” Ya karasa cikin murya mai rauni, wani abu ya ji ya turnuke shi a makoshi, da kyar ya hadiye domin kuka ke shirin kufce masa. Cikin azama ya tashi ya fice.
Wasu zafafan hawaye suka zubo mata, tabbas Mahmoud ya fadi gaskiya, tashin hankali ba zai kaita ga cin nasara ba.
*ILLAR ALMAJIRANCI*
*NA LANTANA JAFAR*
_Shafi na Biyu_
Rabe aboki ne ga malam Bako, mafi yawan lokuta suna haɗuwa a wata majalisa karkashin bishiya, inda suke hira. Yau ma kamar kullum, sun hadu sai dai su biyu ne a gurin ba kamar yadda suka saba taruwa ba, bayan sun taɓa hirar yau da kullum, nan malam Bako ke shaidawa abokin nasa cewa zai kai yaransa karatun allo.
Rabe ya ce, “Almajiranci fa kenan Bako.”
Ya amsa masa da eh, a takaice. Rabe ya ce,
“Ka yi wa Allah ka dubi darajar mutunci da abotarmu, ka janye wannan kudirin na ka, al’majiranci kana da rai da lafiya, amma ka tura yaranka can wata duniya neman abinci. Ba ka tunanin yadda za su tsinci kansu?”
Bako ya ce, “Rabe wallahi na riga da na yi niyya babu fa shi.”
“Duk da haka kana iya janyewa tunda ba kai sun ka yi ba, yaran yau sai a hankali, suna gabanka tarbiyyarsu ya aka kare, ballantana kuma an kai su wani guri inda babu mai kwaba masu gara dai suna gabanka yafi. Yanzu ka duba dan gidan Lado Manga, al’majiranci aka kai shi, wanda ya yi sanadin lalacewarsa ba ki daya, ban da shaye-shaye da dauke-dauke ba abunda ya koyo, menene amfanin irin wannan karatun? Jiya nan bayan mun fito sallar asuba, yake koka mun yaron ya addabesu da dauke-dauke, hatta danyen hatsi ba su isa su bari a fili ba kai ka ce bera ya haifeshi; shi kansa uban dana sani ya ke yi. Tunda akwai tsangayu a nan garin, mai zai hana ka kai su mafi kusa, ka ga ai yafi ace sun tafi wata uwa duniya.”
“Ba za ka fahimta ba ne Rabe, ni fa wallahi nauyi ne ya yi mun yawa, gara dai su tafi can za su fi yin karatun. Ka ga na samu sauki su ma yan’matan aurar da su zan yi kakan bana, ka ga nauyi ya ragu sosai. Sai in samu yarinya danya shakaf ma malam in aura.”
Dariya su kayi hadi da tafa hannu. Rabe ya ce, “Ba ka da dama abokina.”
“Ai sunna ce ta ma’aiki, hudun nan sai na cike su ras! Dama annabi ya fada, idan talauci ya yi ma yawa to ka kara aure.”
“Haka ne kuwa, sunna kan sunna.”
Nan ma dariya suka yi hadi da tafa hannu. Malam Bako ya yi gyaran murya ya ce,
“Me zai hana ka hada da yaranka? Idan malam Sidi ya zo ya tafi da su tare.”
Nan da nan fuskar Rabe ta sauya, cikin dakakkiyar murya ya ce,
“Ka ga ni bani da ra’ayi, akwai masu son yin karatun zamani, don haka zan karfafa masu gwiwa ne In Sha Allah, don ganin sun samu ilimin addini dana zamani cikin sauki ba tare da sun wahala ba. Kai ma don ba ka jin shawara ne, na so ace ka sa yaranka makarantar zamani don su samu rayuwa mai inganci musamman ‘ya’ya maza, tunda su biyu ne wadanda suka tasa, dama su ‘ya’ya mata da gidan aure su ka fi dacewa.”
Malam Bako ya ce, “Mu da ba mu yi karatun zamanin ba wani abu ya same mu ne? Ba ga shi muna rayuwa yadda muke so ba.”
Kada kai kawai Rabe ya yi, ya san wannan ko za su kwana anan yana fada mai ba zai fahimta ba. Don haka ya ce,
“Allah ya kyauta. ka ga an kira sallar la’asar muje mu samu jam’i.”
[26/06, 6:42 am] Auwal Novels: *ILLAR ALMAJIRANCI*
*NA LANTANA JAFAR*
_Shafi na Uku_
3.
Bayan kwana uku da maganar tafiyarsu Mudi. Kwatsam! Ranar da safe sai ga malam Sidi ya yi sallama a kofar gidan Malam Bako, cikin shigar manyan kaya, wato jamfa, kansa sanye da hula, wuyansa rataye da rawani yayin da hannunsa ke rike da carbi, wani katon asuwaki ne a bakinsa yana tattaunawa. A lokacin su Mudi suna dakin Innarsu Kulande, suna tsaka da karya kumallo. Jin sallamar da Malam Bako ya yi ya sa shi fitowa daga É—aki, koda ya ga takalma a kofar dakin Kulande sai ya hasala ya nufi dakin, a waje ya tsaya ya kama dan tsumman labulen dakin ya daga.
“Kai Mudi, dama kana ciki ana sallama ba za ka fita ka duba ba, har sai na fito?”
“Ka yi hakuri baba wallahi ban ji ba ne.”
“Eh ai ba za ka ji ba, kuna nan ta taraku tana hure maku kunne.” Ya ja tsaki, kana ya nufi kofar gida don ganin mai sallama. Koda ya fita Malam Sidi ya gani tsaye, yana ta goga asuwakinsa.
Ya ce, “Aha Malam Sidi ashe kai ne? Maraba da malamai magada annabawa.”
Cikin sakin fuska, Malam Sidi ya mika masa hannu hadi da sallama. Bayan sun gaisa ne, ya ke cewa,
“Na zo ne a kan maganar yaran da za a tafi da su karatu.”
“To to da kyau, ga shi ko ka zo a daidai, domin suna ciki ba su riga da sun fita ba. Bari na kirawo su sai ku tafi.” Ya fada cike da murna, tare da juyawa zai shiga gida.
“A’a dakata saurin me ka ke yi ne? Ba fa yau zamu tafi ba sai nan da jibi idan Allah ya kai rai, dama yanzu zuwa na yi na shaida ma domin su zama cikin shiri, yanzu ma kauyukan da muke makwabtaka da su zanje na shaidawa iyayensu tafiyan.” Malam Bako ya ce, “To hakan ya yi, Allah ya sa a dawo lafiya.” Suka yi sallama Malam Sidi ya wuce.
Koda Malam Bako ya koma gida, bai ce masu komai ba shiru ya yi da bakinsa.
Kulande ke zaune a dakinta bisa tabarman kaba, dakin ciki daya ne babu wani wani kayan a zo a gani ciki. Gadonta na karfe waya sha biyu da wata yaloluwar katifa, zanin gadon duk ya yayyage, sai wani tsohon akwati kwaya daya da wasu jakunkuna na gana masgo, wanda ke dauke da kayansu ita da yaranta, a gefe guda kuma wasu tsofaffun kwallaye ne manya guda biyu, nan take sa yan komatsan kayan aikinta na yau da kullum, ledan kasa kuwa rabonta da ita tun ta aure. Sumintin dakin duk ya fashe, haka labulen dakin duk ya sha faci, haka take rayuwa cikin talauci da tsangwaman miji da na kishiya da ya’yanta. Kodayaushe tana cikin kunci da É“acin rai, yanzu ma haka tunda ta yi sallar isha’i take zaune tana faman tunanin rayuwa, musamman hali da rayuwar da yaranta za su shiga na al’majiranci da mahaifinsu ke shirin kai su. Jife- jife ta kan yi ajiyar zuciya, Sadiq na kwance jikinta.A wannan yanayin Mudi da kaninsa Sabi’u suka taddata, sallama su ka yi, ta amsa cikin karfin hali.
Ta ce “kun dawo?” Suka amsa da “eh.” Leda ya ajiye mata a gabanta.
Ta dauka tana cewa, “Menene wannan din?.”
“Tsire na siyo miki Inna.” Cewar Mudi.
Ta kalleshi kallon tambaya, ya dan yi gajeran murmushi. “Kudin iccen da na yi yau ne.”
“To shi ne ka kaso su? Maimakon ka adana?”
“Ba duka na kashe ba Inna, akwai saura.”
“To Allah ya yi albarka, ya tsareku gabaki dayanku.” Suka amsa da amin.
Ta ce, “Ku diba ku ci, sai ku bar min kwaya biyu sun isheni.”
Sabi’u ya yi saurin mika hannu domin ya dauki ledar, Mudi ya yi saurin kabar mai da hannu yana harararsa.
“Ba ka ci na ka ba?”
Ya sunkuyar da kai yana dariya kasa-kasa.
“Inna don Allah ki daure ki ci, na lura kwanakin nan kina yawan zama da yunwa ka da ta illataki.”
“Wa ya fada ma? Ko dazu na sha koko.” Ta ce a sanyaye.
“Inna ba zai rike miki ciki ba. Ko in amso miki ruwan zafi ne sai ki hada wurin mai shayi?”
Kai ta girgiza, “Ba sai ka amso ba, wannan ma ya isa. Na gode.”
Ya dan karkace, ya fito da kudi daga cikin aljihunsa ya mika mata, “Inna ga wannan ki rike a hannunki koda wata bukata za ta taso miki, tunda baba ya ce ko wani lokaci muna iya tafiya da zarar malam Sidi ya zo.”
Kudin ta karewa kallo, kana ta komar da kallonta gareshi. “Wannan kudin fa masu yawa?”
“Kudina ne wanda ake biyana idan na yi aikatau ko icce, na dade ina tarasu gurin Hadadde me nama, na so inyi jari ne da su, to amma kuma…” Sai kuma ya yi shiru.
Sauke numfashi ta yi, “Ba komai kwai Allah.” Sun dan taba hira kadan, kana su ka yi mata sai da safe.
Ranar tafiya ta zo ba tare da sun sani ba, safiya ce bayan sun kammala kalace, kamar kullum suna dakin Innarsu, hira suke yi wanda ya zame masu al’ada, duk sadda suka gama kalace, sai sun zauna sun taba raha kafin su fice daga gidan. Dariya suke yi sosai harda Innarsu, kai ka ce ba su da wata matsala ta rayuwa, kwata-kwata ba su ji shigowar malam Bako ba, sai ganinsa suka yi tsaye a kansu yana huci kaman wani kububuwa, koda suka ankara da shi nan da nan kowa ya shiga nutsuwa, yayin da suka hada baki gurin furta kalman baba ina kwana.
Tsaki ya yi ba tare da ya amsa ba ya ce, “Dube ki don Allah ko kunya ba kya ji, kin zauna cikin yara kina ta sakarci, to malam Sidi ya zo ku yi maza ku shirya.
Idon Kulande ya yi rau-rau yana shirin zubowa, cikin wata siririyar murya wanda ita kanta ba ta san tana da ita ba ta ce,
“Malam amma dai ya kama…” Ya katseta ta hanyar daka mata tsawa
“Ki shiga hankalinki, bana son jin wata magana daga bakinki.”
Wani kallo ya yi wa yaran, ba shiri suka fice daga dakin. Sabi’u ya fara kuka kasancewarshi mai kawazuci, haka shi ma ya bi bayansu ya fice daga dakin. Kukan baÆ™in ciki ya kufce mata, takaici ya isheta kullum ba ta da iko akan ya’yan da ta haifa, haka idan rashin kirkinsa ya motsa, gaban ‘ya’yanta zai mata zagin cin mutunci ba ta isa ta yi magana ba, da wanne za ta ji? Kishiyarta da ‘ya’yanta duk sun rainata, wannan baÆ™in cikin har ina? Yaranta da take jin dadinsu za a rabata da su, a kai su wata uwa duniya. Hannu ta daga sama,
“Ya Allah ka yi mun agaji cikin lamurana, ba domin halina ba.” Haka har suka shirya suka nufo dakin innar.
Malam Bako ya yi masu magana cikin karaji,
“Ina kuma za kuje bayan ana jiranku?”
Mudi ya ce, “Zamu yi ma lnna sallama ne.”
“To maza ku yi ku fito.”
Koda suka shiga ta kasa daina kukan, ballantana ta boye masu don su samu kwarin gwiwa. Ta kama hannayensu duka ta rike, musamman na Sabi’u wanda kuka yake yi. Cikin muryar kuka ta ce, “Mahmoud ga dan’uwanka nan, ka kula mun da shi amana, na san kai yaron kirki ne, za ka yi abunda na umurceka da shi.” Mudi bai amsa ba, saboda kuka.
“Sabi’u ka yi biyayya ga dan’uwanka, ka zama yaron kirki mai jin maganar na gaba da shi.”
Ya gyada kai. Ta ce, “Kuma ka zama mai girmama na gaba da kai ka ji? Na san duk kana yi ka kara a kan wanda ka ke yi ka ji. Allah ya yi muku albarka, ya tsareminku.”
Suka amsa da amin. Kudi ta mika wa Mudi.
“Ga wannan ka boye su koda za kuci abinci.”
Kai ya girgiza mata.
Ta ce,
“Bana son musu ka kara da na hannnunka.”
Malam Bako ya shigo, “Wai me kuka tsaya yi ne? Ku fito sallamar ta isa haka.” Ya leka É—akin. Shi kanshi ya ji wani iri, amma da yake namijin duniya ne sai ya basar. Da kyar ya bambare Sabi’u a jikin Kulande, ihu yake yana fadin, “Innarmu! Innarmu! Wayyo.” Ihun da yake yi ya ja hankalin mutanen gidan. A guje Aisha ta fito daga É—akin Innarsu, ganin abunda ke faruwa, yasa ta fashewa da kuka.
“Baba don Allah ka yi hakuri.”
Ko kallonta bai yi ba, ya sa su gaba. Mudi ya durkusa a gaban Innarsu Aisha ya ce,
“Inna zamu tafi.”
Cikin fara’a ta ce, “To Mudi, Allah ya ba da sa’a.” Har da daukar kuÉ—i ta ba shi, wai su sha ruwa a hanya, in gari banza ne ko kallo bai isheta ba, ballantana ta basu kudi. Innarsu kuwa, ko lekowa ba ta yi ba har suka bar gidan.
Auwal Novels: *ILLAR ALMAJIRANCI*
*NA: LANTANA JA’AFAR*
_Shafi na huÉ—u._
Zaune take zaman dirshan a tsakiyar É—akinta, tun bayan tafiyar Æ´aÆ´anta. Takaici da baÆ™in ciki suke addabarta, ta ma rasa mai za ta yi, dan kukan da take yi ta samu sauki yau kwata-kwata ya ki zuwa, sai ajiyar zuciya da ke sauka lokaci bayan lokaci. Haka ta zauna, ba ta san iya lokacin da ta kasance a cikin wannan yanayin ba, sai da karamin É—anta ya shigo yana kuka, da alama yunwace ta koroshi daga gurin wasa. A sa’ilin hankalinta ya dawo jikinta, mikewa ta yi ta dauko raguwar kokon da suka rage na karin kumallo.
“Amshi ka sha kafin indora sanwa.” Ta mika mishi kofin kokon.
MaÆ™ale kafaÉ—a ya yi, “Ni ba na son koko, abinci na ke so.” Ya karasa maganar cikin kuka.
Hannunsa ta riÆ™o ta ce, “Ka yi hakuri ka sha kokon, kafin in dafa abincin ka ji?”
Zama ya yi ya saka sabon kuka, hakan ya sa ta dauko nairan talatin ta mika mai.
“Ungo ka je gidan Inno ka sawo awara ka ci.”
Abun ka da yaro, nan da nan ya share idanuwanshi yana dariya ya fita a guje. Kai kawai ta gyada, ko da ta fito tsakar gida Innarsu A’isha ta shiga yi mata habaici, ko kallon inda take ba ta yi ba domin inda sabo ta saba.
A daren ranar idanuwanta ba su runtsa ba, tsananin tunanin halin da Æ´aranta ke ciki ya hana mata sukuni.
‘Da wahala in raba rayuwata da matsaloli, matukar ina raye a wannan duniyar. Daga wannan sai wancan, a haka na taso. Ni Hauwa Kulu! na ga ranar da da zan wuni cikin farin ciki ba tare da an É“ata min rai ba.’ Ta yi maganar a zuciyarta.
TUSHEN LABARI
Malam Bako haifaffen garin Cutar Biki ne, da ke karamar hukumar Sumaila ta jihar Kano. ÆŠa ne ga Malam Rabo, sana’arsa siyar da fata, hakan ya sa ake yi masa laÆ™abi da Rabo mai fata. Matansa biyu, Huraira ita ce matarsa ta farko, sun shekara bakwai da aure sai dai Allah bai ba ta rabon haihuwa ba, hakan yasa shi karo aure. Inda ya auri Halima É—iyar goggonsa Ba’arufa, watanni biyu tsakani ta samu juna biyu, malam Rabo ya yi farin ciki haka ita ma Huraira ta yi farin ciki da hakan kasancewarta mace mai hakuri da nutsuwa, shi ya sa ma zamansu gwanin ban sha’awa, ba zama ka ce zaman kishi suke ba.
Bayan wata tara, Halima ta haifo É—anta namiji da taimakon abokiyar zamanta, kowa na gidan na cikin farin ciki, ranar suna aka sanya masa Abdullahi, sunan mahaifin malam Rabo, saboda kawaici suke kiranshi da Bako. Bako ya taso cikin gata da kulawa, kodayaushe yana gurin Huraira, yunwa da barci kaÉ—ai ke rabasu. Sai da Bako ya shekara uku, kafin Halima ta sake haihuwa, wannan karon ta samu É—iya mace aka sanya mata suna Hindatu, amma suna kiranta da Hinde. Tun daga lokacin duk shekara Halima take haihuwa, sai da ta jero mata hudu kana ta sake haihuwar É—a namiji. Asiya ke bi ma Hinde, sai Uwa wato takwarar Huraira, sai Abu sannan Auwal shi ne karaminsu ana kiransa da Tanko, kasancewar ya biyo mata.
[26/06, 6:42 am] Auwal Novels: *ILLAR ALMAJIRANCI*
*NA: LANTANA JA’AFAR*
_Shafi na biyar._
Auwal bai shekara ba ta sake samun wani cikin, wanda ya zo mata da laulayi sosai, hakan ya sa ta cireshi daga nono, kulawarsa kacokan ta koma hannun Huraira. Halima ta sha fama da cikin, kasancewar ya zo da matsaloli ba kamar na baya ba. A haka har cikin ya isa haihuwa, wata ranar Laraba tunda safe Halima ta fara jin nakuda, kamar wasa har kusan azahar ba ta haihu ba, hakan ya sa aka kira unguwarzoma. Sai gabanin la’asar kan É—a ya fito, shiru babu uwar jiki, anyi-anyi abun ya gagara hankula duk sun tashi.
Unguwarzoma ta dubi Huraira cikin damuwa ta ce, “Gaskiya wannan abun ya fi karfina, ya kamata a sanar da malam Rabo halin da ake ciki, domin ayi gaggawar kaita asibiti.”
Cikin zafin nama Huraira ta miÆ™e za ta je waje, domin sanar da Malam halin da ake ciki. Halima ta riko hannunta “Yaya Hure ki yafe mun, ni nasan ba zan tashi ba. Ga amanar Æ´aÆ´ana nan ki kula da su.”
“Ki daina fadin haka, In Sha Allahu za ki tashi, ki rayu da Æ´aÆ´anki har ma ki ga aurensu.” Huraira ta ce a sanyaye.
Da sauri ta fice kofar gida cikin tashin hankali, ta iske malam Rabo tsaye ya jingina da garu ya yi nisa cikin tunani.
Cikin haka ya ji muryar Huraira tana fadin, “Malam! Malam! Har yanzu fa tana kan gwiwa, ya kamata mu tafi asibiti.”
Ba tare da ɓata lokaci ba ya tafi nemo mota, jimawa kaɗan ya dawo. Da hanzarinsa ya shiga gidan yana fadin su fito ga motar an samo. Koda aka cewa Halima ta taso ankawo mota, kai kawai ta kaɗa.
“Ba sai mun je ba, ku barni na cika a É—akina.”
Juyin duniya amma taki, ta ce sam! Babu inda za ta je. Suka yi ta ba ta baki, amma ba ta sauya zani ba. Har sai da Malam ya nuna ɓacin ransa, sannan ta amince za ta je.
“Hure ku kimtsa sai ku fito, bari na koma wurin mai mota kar ya ji shiru.”
Allah sarki! Rai baƙon duniya, yana ba da baya ta ce ga garinku. A lokacin Huraira ta je ɗakinta dauko mayafi, tana shigowa ta ga unguwarzoma tana kokarin lulluɓeta, bakinta ɗauke da salati. Juyawa ta yi cike da sanyin jiki ta dubi Huraira ta ce,
“Sai dai muyi hakuri Allah ya yi mata cikawa.”
Wani duhu ne ya ziyarci idanuwanta, tun daga lokacin ba ta sake tantance halin da take ciki ba. Hinde dake bayan Hure ta kurma ihu, ta diba a guje ta yi waje, hakan ya jawo hankalin malam Rabo ya rikota.
“Ke lafiyarki kike mana ihu?”
Kofar gidan take nuna mai, kuka na cinta. Ta ce “Cewa aka yi Innarmu ta rasu, shi ne Inna Hure ita ma ta fadi kasa.”
“Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un!” Ya rika maimaitawa cikin tashin hankali. Ba tare da sanin abun yi ba ya nufi cikin gidan, bai yarda ba har sai da ya ganewa idanunsa. Ya shiga tashin hankali marar misaltuwa, ga wannan ta rasu ga kuma wannan a shimfide ga Æ´aÆ´a suna ta kuka, ya kasa jurewa duk yadda ya so ya daure sai da kuka ya kubce masa.
Nan da nan labari ya ba za gari, cikin Æ™anÆ™anin lokaci jama’a suka cika maza da mata, aka yi jana’izarta. Hure kuwa har lokacin ba ta farfaÉ—o ba, hankula sun tashi sosai, sai bayan magriba ta farfaÉ—o, shi ma da taimakon malamar asibiti. Ta yi kuka kamar ranta zai fita, dan sun yi zama na amana, babu munafurci balle ha’inci. Jama’a sun yi ta ba ta baki hadi da nasihohi, kana ta É—an sausauta. Yaran kuwa kodayaushe suna rabe da ita, gwanin ban tausayi. A haka har aka yi bakwai, yan’uwan Halima sun so daukar wasu daga cikin Æ´aÆ´an, amma Hure ta ki yarda, sanin zaman da suka yi ya sa suka hakura ta ci gaba da rikon yaran.
[26/06, 6:42 am] Auwal Novels: *ILLAR ALMAJIRANCI*
*NA: LANTANA JA’AFAR*
_Shafi na shida._
Haka yaran suka tashi ƙarƙashin kulawar Inna Hure, ba tare da wata matsala ba, duk wani abinda ɗa zai nema a gurin Uwa suna samu daidai gwargwado. Shi ma mahaifin nasu yana iya kokarinsa, don ganin rayuwarsu ta inganta.
Bayan wasu shekaru, yaran duk sun girma anyi masu aure, Hinde tana nan acikin garin Cutar Biki, Asiya kuma a DumDum, kauye ne dake ƙarƙashin karamar hukumar Ajingi, sai Uwa dake garin Dall, wanda shi ma ƙarƙashin Sumaila yake, yayin da Abu take cikin garin Sumaila tana auren wani tsohon ciyaman din garin.
Bako da Æ™aninsa Tanko sun gado sana’ar mahaifinsu, wato noma da siyar da fata, sai dai shi Bako ya fi karfi a É“angaren noma. Tanko ya riga shi yin aure, yana da Æ´aÆ´a biyar maza uku mata biyu, saÉ“anin Bako da bai yi aure da wuri ba, har sai da Æ™annensa mata suka rigashi. Ya auri matarsa Hama suna zaune a gidan mahaifinsa, inda ya keÉ“e musu É“angarensu. Zuwan Hama ya kawo sauye-sauye da dama, domin kuwa ba ta da kunya ballantana ganin mutuncin iyayensa, hakan ya janyo rashin jituwa da yan’uwansa. Dama-dama mahaifinsa, tana dan shakkarsa ba kamar Inna Hure ba da ta gama rainata. In ya yi magana, ta ce ai ba ita ta haifeshi ba, kishiyar Uwace. Sau da dama ya yi yunkurin rabuwa da ita, sai dai mahaifinsa ke danneshi, ya kan fadi masa ya yi hakuri, iyayenta mutanen kirkine kowa ya shaidesu, ita ma kuruciya ke damunta za ta daina watarana. Haka ya ke hakuri da ita kodan darajar mahaifinsa, da kuma Æ´aÆ´an da ke tsakaninsu, yanzu haka suna da Æ´aÆ´a hudu mata, akwai mai sunan Innarsu wato Halima suna kiranta da Ummi sai takwaran Hure, ana mata lakabi da Inna karama sai Maryama sai A’ishah.
*****
Hama wata iriyar bahaguwar mace ce, ta kasance mai son zuciya da ƙwadayi ga rashin hakuri kamar zawo. Fitinarta tasa Tanko yin nesa da su, sai dai kullum zai zo ya gaida iyayensa. Watarana Malam Rabo ya je gona shi da ɗansa Tanko, sai bukata ta kamashi.
Ya dubi Tanko dake zaune kasan wata bishiya, ya ce, “Zan dan kama ruwa, in na dawo sai mu tafi gida, ina so na kaiwa Malam Bawa ziyara, kwana biyu ba mu hadu ba.”
“To Baba.” Tanko ya amsa tare da miÆ™ewa yana haÉ—a sauran kayansu.
Ratsawa ya yi ta gefensa ya wuce yamma da gonarsa, cikin ciyayi ya tsugunna, bayan ya kammala sai ya ji kamar abu ya cakeshi a kafa, dubawan da zai yi ya ga maciji.
“Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un.” Ya furta a sanyaye.
Komawa ya yi gonarsa a hankali, ya ce ma Tanko mu je gida ba tare da sanar da shi komai ba. Har suka isa gidan da yake a babur ne ba su ba ta lokaci ba,Tanko ya ajiyesa a kofar.
“Baba zan karasa gida sai da yamma.” Cewar Tanko yana kokarin juya kan mashin din.
Cikin dakiya ya ce, “Tanko ka je ka kira min Bala mai wasa da maciji, dazu da na za ga, na ji wani abu ya cakeni ina tunanin maciji ne, amma ban tabbatar ba.” Ya fadi haka ne dan gudun ya tayar masa da hankali.
Mutuwar tsaye Tanko ya yi yana duban mahaifinsa, zuciyarsa na yi masa wani karatun da ba ya fahimta.
Sai da malam Rabo ya ce, “Ka kuwa ji abinda na ce?”
“Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un.” Ya furta. Yayin da tsoro da tashin hankali suka bayyana Æ™arara a fuskarsa, a guje ya fusgi babur din cikin rashin hayyaci.
Malam ya girgiza kai, tare da fadin, “Allah ya tsare.” Ya shiga gida.
Hure tana ganinshi ta san babu lafiya, alamu sun nuna Æ™arara a fuskarsa dauriya kawai yake yi. Ta saki butar dake hannunta, wacce fitowarta banÉ—aki ke nan. Da sauri ta cimmasa, hannunsa ta riÆ™o, “Malam lafiya na ganka haka?”
Ya ce, “Babu komai.” Ya ba ta amsa a takaice.
“A’a da komai mana, ga alamu sun nuna babu lafiya.” Ta nufi inuwa da shi inda tabarma ke shimfide, ta zaunar da shi ya jingina da garu.
Cikin sauri ta tashi, ta debo mai ruwa a randar kasa ta kawo mai. Ya karba ya sha da bismillah tare da hamdala, ta karbi kofin ruwan. Ganin yadda zufa ke tsatsafo mai, ya sa ta shiga daki ta dauko mafici tana mai fifita.
“Sannu Malam, Bari na leka waje ko zan samu yaro ya dubo Tanko, in yana nan sai ya kai ka nan asibitin shakatafi.”
Kai ya girgiza, “Tare muke, ya tafi kiran mai magani.”
Haka ta cigaba da mai fifita tun yana amsawa da baki, har ya koma yi da kai. Koda Tanko ya je gidan Bala ya aika yaro ya yi mai sallama, jim! kaɗan ya dawo ya ce baya nan ya je bayan gari dibo magani, haka ya kara buga babur din ya nufi bayan gari. A hanya ya hadu da Bala yana dawowa, ya shaida masa daga gidansa yake, hawa babur din ya yi suka tafi. Koda suka isa gidan Malam Rabo ya fara galabaita, sai zufa kawai ke keto mai.
Bala ya kalle shi ya ce, “Subhanallah! Tanko ya aka yi kuka yi sakaci haka? Har ya fara fita a hayyacinsa, kamata ya yi ku daure dan saman gurin don gudun yaÉ—uwar gubar a jikinsa.”
Cikin hanzari ya ciro kullin magani, dake cikin jakar dake rataye a wuyansa, dama da ita yake yawo dan gudun karta kwana. Ya bukaci a ba shi ruwa, babban dan yatsansa dana tsakiya ya sa ya debo garin maganin ya zuba, kana ya sa babban dan yatsan ya gauraya ya mikawa malam Rabo.
“Ka shanye duka.”
Ya karba ya shanye kamar yadda ya umurcesa, ya mika masa kofin. Guntun wanda ya rage ya shafa masa a wurin tare da yi masa tofi.
Ya ce, “Sannu ka ji Allah ya tashi kafaÉ—a.” Ya karasa haÉ—i da mikewa.
“To, ni zan koma, na dawo zuwa anjima. Allah ya kara lafiya.”
Sai a lokacin Hure ta samu damar bude baki ta yi magana, “To mun gode a sauka lafiya.”
Tanko ya ce, “Mun gode. Mu je na mayar da kai.”
“Wallahi na yafe, koma ka kula da mara lafiya.” Ya yi gaba.
“To na wa za a ba da sadaka?” Ya tambaya yana bin bayansa.
Bala ya ce, “Haba in dan wannan ne ka barshi, babu wani abu fatanmu Allah ya ba shi lafiya.” Ya fita cike da fatan samun lafiya ga Malam Rabo.
[26/06, 6:42 am] Auwal Novels: *ILLAR ALMAJIRANCI*
*NA: LANTANA JA’AFAR*
_Shafi na bakwai._
Godiya ya yi masa suka yi sallama ya tafi, shi kuma ya koma cikin gida. Radadin da malam Rabo ya ke ji ya dan lafa, har wani gyangyadi ya fara ji hakan ya sa suka gyara masa kwanciya.
Bako ya shigo da sallama, ya yi turus! Yana kallon mahaifinsa dake kwance bisa tabarma. Cikin mamaki ya kalli Inna Hure da ke zaune gefensa.
“Lafiya na ga malam na kwance a wannan lokacin?” Tanko ya labarta masa abinda ya faru da shi.
Bako ya ce, “Subhanallah! Me ya sa ba ka aika aka kirani ba, ina nan majalisarmu.
“RuÉ—ewa na yi, fatanmu dai Allah ya ba shi lafiya.”Suka amsa da amin.
Tanko ya kalli gidan, sannan ta maida dubansa ga Bako.
“Ina mutanen gidan ne? Na ji shiru.”
“Wai sun tafi bikin Safare É—iyar ‘yar Hama, gobe daurin aure.”
“To ko dai ita dan gidan Halilu zai aura?”
“Eh! ita ce.” Bako ya ba shi amsa.
“Aikuwa an gayyaceni daurin auren.”
Sun dan taÉ“a hira kadan tsakaninsu, Inna Hure dai ba ta sanya musu baki ba. Tanko ya ce, “Tunda ka dawo zan je gida na yi wanka, zan dawo ba da jimawa ba.” Ya yi masu sallama, Inna Hure ta ce ya gaida iyali.
Bayan wani lokaci malam Rabo ya dan ji dama-dama, har ya fita sallar magariba a cikin jam’i, ya jira lokacin isha’i dama al’adarsa ce haka, ba ya shigowa gida har sai ya sallaci isha. Koda ya dawo gida nan ya tadda Bako da Tanko har da iyalinsa suna hira a tsakar gida, tare da Inna Hure. Shi ma guri ya samu kusa da Æ´aÆ´ansa ya zauna, sun ji dadin yadda suka ga jikinsa ya yi sauki.
Saude matar Tanko ta yi mashi ya jiki tare da fatan samun sauki, haka ma ƴaƴanta. Hira suke yi mai dadi cike da raha, Malam ya sa Tanko ya kira masa sauran yaransa mata, da yake shi yana da waya. Sun gaisa cikin jin dadi da kulawa, tare da jajanta masa, ya yi mamakin yadda aka yi suka sani. Tanko ya ce shi ya sanar da su.
“Ai da ba ka sanar masu ba, tunda ba wani babban abu ba ne, kar hankulansu ya tashi.” Ya ce yana duban Tanko.
“Yana da kyau a sanar da su, yanzu ba ga shi kun gaisa ba? Na tabbata ka ji dadin hakan.”
“To, Allah ya yi muku albarka ya sa ku gama lafiya.”
Dukkansu suka amsa da amin. Akasarin hirar da suke yi shawarwari yake ba su, mai kama da wasiyya. Ya kalli Bako ya ce,
“Kai Abdullahi kai ne babba, kuma don haka ka yi hakuri da yan’uwanka haka ma iyalinka, koda kasa ta rufe idona ban yarda ka rabu da iyalinka ba. Ka yi ta hakuri kodan zuri’ar dake tsakani.”
Mafiya lokuta in sun zauna, haka yake yawan yi masu nasihohi. Lokaci mai tsawo suna hira, daga bisani su ka yi sallama da juna kowa ya nufi makwancinsa.
Cikin bacci Hure ta jiyo nishinsa, a lokacin karfe uku da kwata na dare. “Subhanallah! Malam jikin ne?”Ta tambaya a ruÉ—e.
“Eh.” Kawai ya iya furtawa.
“Sannu bari in taso Bako ya je ya kira Bala.” Ba tare da ta jira amsawarshi ba ta fice da hanzari.
Kira É—aya ta yiwa Bako ya amsa. Yana fitowa ya ce, “Inna ba dai jikin malam ya tashi ba?”
“Shi ne wallahi, cikin barci na jiyo nishinsa. Ka yi gudu ka kira Bala.”
Ya tafi da hanzari, cike da tausayin mahaifinsa. Ita kuma ta koma É—aki, fifita da sannu ta dinga yi mishi. Jimawa kaÉ—an Bako ya yadawo da Bala, Tanko biye da su a baya. Magani ya jiÆ™a ya ba shi, ya sha sannan ya shafa masa. A hankali ya dan lafa har barci ya kwasheshi, wanda bai wuce minti biyar ba ya farka da azababben ciwo. Nan suka ta yi masa adduo’i, can ya yi ajiyar zuciya.
“Allahu Akbar! Malam Rabo ya amsa kiran Ubangiji.” Cewar Bala cike da sanyin jiki.
Dukkansu sallati suka dinga yi hadi da, ‘Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un!’
Bayan sallar asuba aka sanar da rasuwarsa a masallaci, wasu da dama sun yi mamakin rasuwar, domin tare suka yi sallar magriba har da isha, sai dai kuma babu mamaki da ikon Allah. Tun a daren Tanko ya sanar da yan’uwansa mata, duk sun hallara. Kasancewarsa mutumin kirki, ya samu jama’a da kuma shaida ta gari, iyalansa sun yi kukan rashinsa, suna kallo aka tafi da shi zuwa makwancinsa. Gidan cike yake da jama’a yan gaisuwa, Hama ta yi ta rashin mutunci kala-kala, sai dai babu wanda ya kulata hatta wa’inda suke zuwa gaisuwa da ita suke tafiya a bakunansu. Haka har aka yi bakwai jama’a suka watse, saura na jiki. Washegarin bakwai aka kira liman da malam Habu, shi ne babban malami a garin aka raba dan abinda ya bari na gado, bayan an kammala Hure take shaida musu za ta koma garinsu BAJI da zama, sun yi kokarin hanata domin ba su da uwar da ta fita tun bayan tasowarsu.
Ta ce, “Ina jin ku har cikin raina, ban taÉ“a daukanku a matsayin Æ´aÆ´an kishiya ba, nima kaina zan yi kewa da baÆ™in cikin rabuwa da ku, ba zan iya jure zaman gidan nan ba musamman na bude ido na ga babu Halima babu malam.” Ta fashe da kuka. hakan ya sa sauran yin kuka har da Tanko, inka cire Bako shi ne mai karfin zuciya hakuri ya yi ta basu hadi da nasiha, kana su ka yi shiru.
“Yawan damuwa da tunani ka iya haifar mun da ciwo.” Cewar Inna Hure.
Sun fahimceta tare da rokon ta bari sai tafita takaba, kana ta tafi, suna yi matsaya akan hakan kuma ta amince.
ILLAR ALMAJIRANCI
NA LANTANA JA’AFAR
Shafi na takwas
8.
Bayan shuÉ—ewar wasu watanni, wata ranar juma’a malam Bako sun je daurin auren abokinsu Naliti a garin Kanawa, nan ya ga Kulande. Kulande na É—aya daga cikin kawayen amarya wato Jamila, tun daga lokacin yake ta bin diddiginta, ya yi kokarin yi mata magana amma ta Æ™i sauraransa, haka ya hakura ya shaidawa ango wato Naliti,
Ya ce, ” Tsuntsu daga sama gasasshe abokina, kar ka damu, aminiyar jamila ce, Hauwa’u kenan yarinyar kirki tana da hankali da natsuwa In Sha Allahu zan yi iya kokarina don na ga ka mallaketa a matsayin mata.”
Bako ya washe baki, ya ji dadin maganar abokin nasa. Bayan dawowarsu da daddare, Bako ya je bakin tasha ya siyo yan daƙwalan kaji guda biyu, ya biyo ta shago ya siya lemun kalbansa guda uku kana ya nufi gidan abokinsa ango Naliti, ya kuwa taki sa a domin a waje ya taddashi suna magana da wanshi. Sallama ya yi masu, bayan sun gaisa ya tsaya nesa da su. Sai da suka yi sallama kana ya nufo gurin Bako suka sake gaisawa.
Naliti yana dariya ya ce “Na ga alama da gaske kake malam.”
“Eh mana. a bari ya huce shi ke kawo rabon wani.” Cewar Bako cike da zumuÉ—i.
“Kana da gaskiya abokina, da zafi-zafi akan bugi karfe.”
Bako ya yi dariya yana gyara tsayuwa, “Kwarai ma kuwa. Yanzu dai ba wannan ba, ga wannan, a kaiwa amaryata ta more.” Ya mika mai ledar hannunsa.
Baki sake Naliti ya karbi ledar. “Au! Har ta zama ta ka?”
Bako ya yatsina fuska, ya ce “Abokina yan magana kan ce fata nagari lamiri fa.”
“Haka ne, Allah Ubangiji ya tabbatar da alherin. Yanzu dai ka bari sai gobe in Allah ya kaimu ka ji koma menene.”
“Allah ya sa na ji alheri.”
“Amin.”
Suka yi sallama cike da nishaÉ—i.
Koda ya shiga gida, kai tsaye ya wuce bangaren amaryarsa, ya yi sallama suka amsa.
Ya ce, “Ina Hauwa’u jidda? (Dama haka yake kiranta, idan ya je zance gurin Jamila ita ke mata rakiya)”
Ta amsa da sanyi a muryarta, dama kwance take cikin uwaddaka tunda ta yi sallar isha. Waje ya fita ta biyoshi a baya, suka tsaye kusa da tagar É—akin, ta gaidashi, ya amsa tare da kulawa.
Leda ya miko mata. “Ungo sakonki ne aka ce na ba ki.” Saroro ta yi tana kallonsa, iya saninta babu wanda ta taÉ“a sani a garin Cutar Biki, ballantana ya aiko mata da sako.
“Na san kina mamakin wanene ya yi miki aike ko?” Muryarshi ta katse mata tunani.
“Amshi tukun, sai in yi miki bayani.” Ya ce yana sake mika mata ledar.
Hannuwanta biyu ta sa ta karɓa, zuciyarta cike da zullumi. Ta kuma tsinkayo amon muryarsa yana fadin,
“Abokina Abdullahi shi ne ya ce a ba ki.”
Cike da mamaki take kallonsa, bakinta har rawa yake wurin fadin, “Abdullahi? gaskiya ban sanshi ba.”
Gajeriyar dariya ya yi kana ya ce, “Abokina ne ta yiwu dazu kin ganshi, wani mai farin yadi É—an dogo haka, yana da duhun fata amma ba sosai ba.”
“Oh! na gan shi.” Ta ce a hankali.
“Yauwa! To shi ya ce a ba ki, idan Allah ya kaimu gobe ya ce zai zo ku gaisa. Kuma shi mutumin kirki ne, sai dai dan’uwana ne damin yana da mata daya da yara. Idan Allah ya yi muna fatan ki shigo a ta biyu, kin ga ga ki ga Æ™awarki a kusa abun ya yi kyau.” Ya karashe maganar da zolaya.
Hjabinta tasa ta rufe fuskarta, murmushi ƙunshe da bakinta.
Ya ce, “Shi ke nan, ki je sai da safe.”
Godiya ta yi, ya tafi ita kuma ta koma cikin É—akin. Jamila ta fara tsokanarta da yake ta san da zancen, ita dai ba ta ce komai ba, ta baje masu nama da lemun kwalba, dama su yan’mata uku ne da dattijai guda biyu su shida har da amarya sun ci sun koshi har suka rage.
Washegari da hantsi, malam Bako ya yi wanka cikin shiga mai kyau, ya feshe jikinshi da turare É—an duwala sai ba za kanshi yake. Hama tana kallonsa, tana so ta yi magana sai dai babu fuska, tun bayan rasuwar malam yake fushi da ita saboda rashin da’ar da ta yi, tana kallo ya yi ficewarsa. Kai tsaye gidan Naliti ya nufa, yaro ya aika ya yi mai sallama jim! kaÉ—an ya fito, gaisawa suka yi.
“Da kyau abokina, irin wannan kamshi haka sai ka ce alhajin birni.”
“Kai haba mutumina?” Cewar Bako yana sake duba jikinsa.
“Allah ina fadama, na Hauwa kulu mai tagwayen suna, ka ba da kanka a sare ka je gida ka ce ya faÉ—i.”
Dariya suka yi su duka cike da nishaÉ—i.
Bako ya ce, “Yanzu dai shiga ka turo mun mutuniyar, baccina rabi ne cike da mafarkinta.”
Hannu suka tafa suna dariya.
koda ta fito sallama ta yi mai, ya amsa cikin fara’a da annuri. Bayan sun gaisa ya gyara tsayuwa cike da muradin samun zuciyarta. Ya ce, “Malama Hauwa ina fatan Naliti ya yi miki bayani, duk da haka bari in kara gabatar miki da kaina. Sunana Abdullahi an fi sanina da Bako, ni haifaffen nan garin ne haka iyayena, amma Allah ya yi masu rasuwa.”
Cikin jimami ta ce, “Allah ya jikansu da rahma.”
“Amin. Na gode.” Ya É—an tsahirta, kallonta yake yi yana Æ™ara nazari a kanta. Kamar an ce ta É—ago kai, aikuwa suka haÉ—a ido ta yi saurin dukar da kan
[26/06, 6:42 am] Auwal Novels: ILLAR ALMAJIRANCI
NA LANTANA JA’AFAR
*shafi na tara*
9.
Murmushi take tana wasa da gefen mayafinta. Shiru na wasu mintuna, ya sake maida hankalinsa kanta.
Ya ce, “Ban sani ba ko Naliti ya faÉ—a miki ina da iyali ba.”
“Ya fada mun.”
“To ya kika gani?”
Shiru ta yi ba tare da ta furta komai ba.
Ya ce, “Malama Hauwa’u ni fa da gaske na ke, ina son ki ba ni dama.”
Shirun dai ta sake yi, shirun da ya haddasa bugawar zuciyar Bako, wani sashen na sanar da shi ba za ta amince ba. Hakan yasa shi jefa mata tambaya,
“Ko akwai matsala ne malama Hauwa Kulu?’
Cikin jin kunya ta girgiza, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da furta,
“Alhamdulillah! Allah ya tabbatar mana da alkairi.”
Ya sa hannu cikin aljihunsa ya fiddo sababbin kudi yan naira dari- dari.
“Ga wannan ki sha ruwa a hanya.”
Kai ta girgiza, “Ka bar shi na gode, zan koma ciki sai anjima.”
“ÆŠan tsaya mana, kin san dai babu kyau maida hannun kyauta baya. Idan ki ka Æ™i karÉ“a ba zan ji daÉ—i ba, ungo.” Ya sake miÆ™a mata karo na biyu.
A wannan lokacin ba ta ƙi ba, hannu biyu tasa ta karba har da ɗan rusunawa.
Ta ce, “An gode Allah ya saka da alheri.”
“Ba komai, Idan Allah ya kaimu mako mai zuwa rana ita yau asabar kenan ko?”
Ta gyada kai.
“Muna nan tafe tare da Naliti In Sha Allahu.”
Godiya ta kara yi mai kana suka yi sallama, ta koma ciki. Shiru ta yi ba ta sanar da kowa ba, sai da suka keÉ“e da Jamila a cikin uwaddaka, lokacin sauran yan’matan sun fita ganin gari, sauran kuma suna zaune a falo. Ta kwashe duk yadda suka yi da Abdullahi ta fada mata, har ma da kyautar da ya yi mata. Jamila ta karba tana Æ™irgawa, sabbin yan É—ari-É—ari ne guda goma sha biyar, ta mika mata.
Ta ce, “Ni babu abinda zan yi da su Jamila, ki bar su a gurinki.”
Dariya Jamila ta yi, “Kyautar masoyi ne fa, a’a ki tafi da abinki in ya so sai ki kaiwa Innarmu ta aje miki in bikinki ya tashi ko wani abun a siya miki.”
Ta ce, “Ke ma dai da taya Bera bari, kamar ba ki san halin da na ke ciki ba. Ina ga ba zan taÉ“a samun mijin aure ba, ko wannan jinshi kawai na yi, amma na san da yaje gida sai dai wani ba dai shi ba.” Ta aje maganar cike da Æ™unar zuciya.
Jamila ta dafa kafadarta cike da rarrashi, “Ki daina faÉ—in haka, babu abinda ya fi Æ™arfin Ubangiji addu’a za mu yi ta yi Allah ya yanke miki wahala.”
“Amin. Ni a halin yanzu kowanne irin mutum na samu zan aureshi ko don in samu yanci.”
Haka suka cigaba da tattaunawa. Bayan an yi komai na al’ada idan aka kai amarya, lokacin tafiyarsu ya yi Jamila ta yi kuka sosai ita da amiyarta barin ma Hauwa’u wacce ke kuka kamar ranta zai fita, tana bakin cikin rabuwa da kawarta kuma aminiyarta, wacce ta kasance jigo gareta a rayuwarta, haka suka yi sallama babu dadi inda suka yi bankwana da kauyen Cutar Biki suka nufi garinsu Kanawa. Sai yamma likis! Suka isa saboda lalacewar da mota ta yi masu a hanya, koda suka sauka, kai tsaye dattijan nan ta bi zuwa gidansu Jamila, yayin da sauran yan matan suka nufi nasu gidajen.
Isarsu suka tarar da gidan akwai sauran baÆ™i na nesa, bayan sun gaggaisa da tambayar ya suka baro amarya, suka ce lafiya kalau. Kulande ta É—auki buta ta yi alwala domin sallar la’asar, don a hanya ta riskesu ga kuma magriba tana karatowa, ta shiga can cikin É—akin Innar Jamila wacce suke kira da Innarmu. Bayan ta idar da sallah tana zaune tana lazimi, Inna ta shigo ta sameta suka sake gaisawa.
Ta ce, Innarmu kina da maganin ciwon kai?”
“Subhanallah! Kai ke miki ciwo? Babu amma bari na aika Anas ya anso miki a shago.”
“A’a ki bar shi ba sai kin aika ba, in na yi bacci zai daina.”
“Bana son shirme Kulande, za a yi in bari bayan ba ki jin daÉ—i.”
Sallamar Anas suka tsinkaya kamar an jefoshi.
Inna ta kwance haɓar zaninta, ta ciro kudi.
“Ruga shago ka amsomin maganin ciwon kai.”
Bayan fitarsa ta dawo da dubanta ga Kulande ta ce “Anya Kulande ba kuka ki ka yi da yawa ba?”
Kai kawai ta girgiza, ta daga rigarta ta ciro kudi a karkashin zaninta ta mikawa Inna.
“Ga shi Innarmu.”
“Wannan kuma daga ina?”
“Abdullahi ne ya ba ni.” Cewar Kulande, nan ta kwashe labarin yadda suka hadu duk ta fada mata. Inna ta yi murna sosai.
“Allah ya tabbatar da alheri, kin ga in kika yi nesa ma yafi miki, babu ruwanki da gutsuri tsoma, kema za ki fi jin daÉ—i da sakewa, ga kuma yar’uwarki a kusa dake.”
Kulande ba ta bar gidan ba, har sai bayan sallar isha kana ta nufi gidansu cike da zullumi.
*****
Bayan sati ɗaya Abdullahi da Naliti suka ziyarci garin Kanawa, kamar yadda ya yi alƙawari. Kai tsaye gidansu Jamila suka fara zuwa, wannan tsarin Jamila ne domin ta yi masu bayanin komai game da Kulande, ba ta ɓoye masu wani abu ba. Hakan ya sa ta ce su fara zuwa gidansu, domin su nemi jagorancin iyayenta. Ba su yi kasa a gwiwa ba, can suka nufa, an yi musu tarba mai kyau cikin mutuntawa, bayan sun gaisa da mutanen gidan ne aka kawo masu ruwa da abinci. Jim! Kaɗan bayan sun kammala ne Innar Jamila ta zo ta taddasu, cikin ɗakin Hamidu ɗanta in da aka yi masu masauki. Suka sake gaisawa, Naliti yayi mata bayanin abinda ke tafe da su, ta yi farin ciki da jin hakan.
Ta ce, “Ina fata, Jamila ta fada maku wasu abubuwa game da Hauwa’u?”
“Eh! Duk ta fada mana, hakan ne ya ba mu karfin gwiwar zuwa.”
“Madalla! Yanzu dai ya kamata a sanar da iyayenta zuwanku, kar muyi abu cikin duhu.”
Suka ce haka ne, mikewa ta yi, “Ba ri in je gidan na su in yi muku iso.”
Cikin sa a kuwa ta samu Dahe a gida yana shirin fita, bayan sun gaisa ne ta ce, “Wurinka na zo dama.”
“To! To! Allah ya sa lafiya.”
“Lafiya lau sai alheri.”
Ya yi kiran mai É—akinsa Altine, wacce ke cikin É—aki ta fito.
“Salame ke ce? Maraba.” “Yauwa.” Suka gaisa.
Dahe ya umarci Altine da ta kawo tabarma, ta yi musu shimfida suka zauna ita ma ta zauna gefe. Innar Jamila Salame ta yi masu bayanin abinda ke tafe da ita, ya karÉ“i maganar haka ma matarshi ta yi na’am sai washe baki take yi abu ya yi kyau, sanadiyar Æ™awance ita ma ta samo nata Masha Allah. Salame ta tafi gida domin ta taho da baÆ™i, fitarta ke da wuya Altine ta matso kusa da ÆŠahe.
“Baban Habu, ai wallahi koma wane irin mutum ne a ba shi tunda ka ji ance É—an kauyen Cutar Biki ne, ta yiwu matsiyaci ne bai da mamora.”
“kin ji fa har mata da yara garesa.” Suka sheke da dariyar mugunta. Dahe ya tsagaita dariyar,
“Kin san wani abu?”
Ta girgiza kai, “Sai ka fada.”
“Ba dan kada a ce na yi gaggawa ba, da sai ince yana komawa ya turo magabatansa a zarga musu su tafi can su Æ™arata.”
“Shi ke nan ma, mun zubda kwallon mangwaro mun huta da Æ™uda.” Cewar Altine.
Ta É—ora da fadin,
“Wallahi kuwa, ai kawai ka ba su mako biyu, koma daya ya fito.”
Dariya yake cike da jin dadi,
“Kai amma wannan shawara ta…” Bai ida furtawa ba, suka ji sallamar Salame.
Ta ce, “To ÆŠahe bismillah, gasu nan a soro.”
Ya ce, “A yi haka? Ai bai kamata su tsaya a waje ba, su shigo daga ciki ai yafi. Ke Altine tashi ki karo shimfida.” Cikin rawar jiki ya nufi soro.
“Marabanku da zuwa, ku shigo ciki.”Ya yi musu jagora har kan shimfida. Altine ta shiga É—aki ta dauko kwanon sha ta kamfato r
[26/06, 6:42 am] Auwal Novels: ILLAR ALMAJIRANCI
NA LANTANA JA’AFAR
Shafi na takwas
8.
Bayan shuÉ—ewar wasu watanni, wata ranar juma’a malam Bako sun je daurin auren abokinsu Naliti a garin Kanawa, nan ya ga Kulande. Kulande na É—aya daga cikin kawayen amarya wato Jamila, tun daga lokacin yake ta bin diddiginta, ya yi kokarin yi mata magana amma ta Æ™i sauraransa, haka ya hakura ya shaidawa ango wato Naliti,
Ya ce, ” Tsuntsu daga sama gasasshe abokina, kar ka damu, aminiyar jamila ce, Hauwa’u kenan yarinyar kirki tana da hankali da natsuwa In Sha Allahu zan yi iya kokarina don na ga ka mallaketa a matsayin mata.”
Bako ya washe baki, ya ji dadin maganar abokin nasa. Bayan dawowarsu da daddare, Bako ya je bakin tasha ya siyo yan daƙwalan kaji guda biyu, ya biyo ta shago ya siya lemun kalbansa guda uku kana ya nufi gidan abokinsa ango Naliti, ya kuwa taki sa a domin a waje ya taddashi suna magana da wanshi. Sallama ya yi masu, bayan sun gaisa ya tsaya nesa da su. Sai da suka yi sallama kana ya nufo gurin Bako suka sake gaisawa.
Naliti yana dariya ya ce “Na ga alama da gaske kake malam.”
“Eh mana. a bari ya huce shi ke kawo rabon wani.” Cewar Bako cike da zumuÉ—i.
“Kana da gaskiya abokina, da zafi-zafi akan bugi karfe.”
Bako ya yi dariya yana gyara tsayuwa, “Kwarai ma kuwa. Yanzu dai ba wannan ba, ga wannan, a kaiwa amaryata ta more.” Ya mika mai ledar hannunsa.
Baki sake Naliti ya karbi ledar. “Au! Har ta zama ta ka?”
Bako ya yatsina fuska, ya ce “Abokina yan magana kan ce fata nagari lamiri fa.”
“Haka ne, Allah Ubangiji ya tabbatar da alherin. Yanzu dai ka bari sai gobe in Allah ya kaimu ka ji koma menene.”
“Allah ya sa na ji alheri.”
“Amin.”
Suka yi sallama cike da nishaÉ—i.
Koda ya shiga gida, kai tsaye ya wuce bangaren amaryarsa, ya yi sallama suka amsa.
Ya ce, “Ina Hauwa’u jidda? (Dama haka yake kiranta, idan ya je zance gurin Jamila ita ke mata rakiya)”
Ta amsa da sanyi a muryarta, dama kwance take cikin uwaddaka tunda ta yi sallar isha. Waje ya fita ta biyoshi a baya, suka tsaye kusa da tagar É—akin, ta gaidashi, ya amsa tare da kulawa.
Leda ya miko mata. “Ungo sakonki ne aka ce na ba ki.” Saroro ta yi tana kallonsa, iya saninta babu wanda ta taÉ“a sani a garin Cutar Biki, ballantana ya aiko mata da sako.
“Na san kina mamakin wanene ya yi miki aike ko?” Muryarshi ta katse mata tunani.
“Amshi tukun, sai in yi miki bayani.” Ya ce yana sake mika mata ledar.
Hannuwanta biyu ta sa ta karɓa, zuciyarta cike da zullumi. Ta kuma tsinkayo amon muryarsa yana fadin,
“Abokina Abdullahi shi ne ya ce a ba ki.”
Cike da mamaki take kallonsa, bakinta har rawa yake wurin fadin, “Abdullahi? gaskiya ban sanshi ba.”
Gajeriyar dariya ya yi kana ya ce, “Abokina ne ta yiwu dazu kin ganshi, wani mai farin yadi É—an dogo haka, yana da duhun fata amma ba sosai ba.”
“Oh! na gan shi.” Ta ce a hankali.
“Yauwa! To shi ya ce a ba ki, idan Allah ya kaimu gobe ya ce zai zo ku gaisa. Kuma shi mutumin kirki ne, sai dai dan’uwana ne damin yana da mata daya da yara. Idan Allah ya yi muna fatan ki shigo a ta biyu, kin ga ga ki ga Æ™awarki a kusa abun ya yi kyau.” Ya karashe maganar da zolaya.
Hjabinta tasa ta rufe fuskarta, murmushi ƙunshe da bakinta.
Ya ce, “Shi ke nan, ki je sai da safe.”
Godiya ta yi, ya tafi ita kuma ta koma cikin É—akin. Jamila ta fara tsokanarta da yake ta san da zancen, ita dai ba ta ce komai ba, ta baje masu nama da lemun kwalba, dama su yan’mata uku ne da dattijai guda biyu su shida har da amarya sun ci sun koshi har suka rage.
Washegari da hantsi, malam Bako ya yi wanka cikin shiga mai kyau, ya feshe jikinshi da turare É—an duwala sai ba za kanshi yake. Hama tana kallonsa, tana so ta yi magana sai dai babu fuska, tun bayan rasuwar malam yake fushi da ita saboda rashin da’ar da ta yi, tana kallo ya yi ficewarsa. Kai tsaye gidan Naliti ya nufa, yaro ya aika ya yi mai sallama jim! kaÉ—an ya fito, gaisawa suka yi.
“Da kyau abokina, irin wannan kamshi haka sai ka ce alhajin birni.”
“Kai haba mutumina?” Cewar Bako yana sake duba jikinsa.
“Allah ina fadama, na Hauwa kulu mai tagwayen suna, ka ba da kanka a sare ka je gida ka ce ya faÉ—i.”
Dariya suka yi su duka cike da nishaÉ—i.
Bako ya ce, “Yanzu dai shiga ka turo mun mutuniyar, baccina rabi ne cike da mafarkinta.”
Hannu suka tafa suna dariya.
koda ta fito sallama ta yi mai, ya amsa cikin fara’a da annuri. Bayan sun gaisa ya gyara tsayuwa cike da muradin samun zuciyarta. Ya ce, “Malama Hauwa ina fatan Naliti ya yi miki bayani, duk da haka bari in kara gabatar miki da kaina. Sunana Abdullahi an fi sanina da Bako, ni haifaffen nan garin ne haka iyayena, amma Allah ya yi masu rasuwa.”
Cikin jimami ta ce, “Allah ya jikansu da rahma.”
“Amin. Na gode.” Ya É—an tsahirta, kallonta yake yi yana Æ™ara nazari a kanta. Kamar an ce ta É—ago kai, aikuwa suka haÉ—a ido ta yi saurin dukar da kan
ILLAR ALMAJIRANCI
NA LANTANA JA’AFAR
*Shafi na goma*
10.
Ruwan randar Æ™asa mai sanyi, ta dire a gabansu. Bayan sun gaisa ne Salame ta sake gabatar da su da kuma Æ™udirin son auren Hauwa’u wato Kulande. Nan take ÆŠahe ya amince, har ma ya ce ya ba shi Kulande kowanne lokaci yana iya zuwa, koma ya turo manyansa a tsaida magana. Sun ji dadin hakan sosai, Bako bakin nan a washe kamar gonar auduga, murnasa taki É“oyuwa.
Ana haka sai ga Kulande ta shigo, kanta dauke katon tire cike da gwangwanayen alale, wanda aka daure da ledar suga. A nitse ta shigo tare da sallama, kai tsaye gurin wanke-wanke ta nufa ta ajiyesu, zuwa ta yi ta tsugunna har kasa ta gaishesu kana ta miƙe zuwa ɗakin Gwoggo wato Altine. Jim! Kaɗan ta shigo, cikin rawar jiki ta mika mata kudin hannunta. Tsareta ta yi da ido dama ga su dara-dara kamar na mujiya.
“Kin san waÉ—ancan?” Ta tambayeta.
“Eh.” Ta ba ta amsa a tsorace.
“Munafuka, tun tsawon wanne lokacin kika sanshi?”
“Da… Zuwan bikin um… bikin Jamila ne.”
“Da yake ke makira ce, shi ne da kika dawo kika yi gum da bakiki.”
“A’a ba haka ba ne.” Ta ce tana hawaye.
“Ya ya ne?” Ta tambaya a tsawace.
“Kawai ni bai yi mun ba ne.”
Baki sake ta zuba mata idanu, kafin ta kwashe da dariya.
“Au! Ke nan har wani zaÉ“i gareki? To bari ki ji, mun riga da mun ba shi ke ko ya miki ko kar ya miki oho! Dabara ta rage ga mai shiga rijiya.” Ta karasa fadi tana zuba kudinta a talita.
“Ma za ki yi ki fito ku gaisa.” Ta yi ficewarta.
Durkushewa ta yi tana zubar da hawaye, kaico! da wannan rayuwa mara yanci, wannan shi ne silar auren Kulande da malam Bako wato Abdullahi.
*****
Duk da suna cikin tsananin baÆ™in ciki da Æ™ewar gida, hakan bai hanasu kallo da bayyana mamakinsu ba, ganin kyawawan gine-gine wanda babu irinsu a kauyensu, musamman benaye komai abin sha’awa hatta mutanen birni su ma abin kallo ne, shigarsu da dabi’unsu daban ne, lallai birni wata aljanna ce. Wani abin mamaki kowa harkarsa yake, babu ruwan wani da wani, tunda suke ba su taÉ“a tsallake Æ™auyensu ba.
Mudi na daga cikin tawagar yaran da za a kai almajiranci, sun yada zango a garin Kano ta dabo mai mata mai mota, tabbas haka abun yake domin kuwa, an sha fama wajen tsallake titi, motocine kala-kala wanda ba su taba tunanin akwaisu a duniya ba. Sun zama abun kallo gurin jama’a, haushi da takaici sun ishi malam Sidi fada yake ta yi, kauyancinsu ya yi yawa da kyar da taimakon jama’a ya samu suka tsallaka titi. Koda suka tsinkayi makarantar malam Babba azahar ta Æ™arato, don haka malam Sidi ya umarci kowa ya yi alwala su yi sallah.
Bayan sun idar da sallah suka sake gaisawa ta hanyar yin musabaha, malam Sidi ya gabatar wa malam Babba da sabbin daliban da ya kawo.
Malam Babba ya ce, “Sun yi yawa ba zan iya karbansu duka ba, sai dai a rabasu biyu akwai Æ™anina malam Haladu, dake can garin Lukoro.”
“To, daman dan’uwanka ne?”
“Eh, kanina ne, domin É—an wajen Baffana ne shi, ashe kawaye shi?”
“Kwarai ma kuwa, wani lokacin ina kai masa dalibai.”
Sun taÉ“a hira kadan, daga bisani ya yi mai sallama ya tafi da sauran yaran. Sun nufi tasha inda za a hau mota, su Mudi suna cikin wa’É—anda za a kai Lukoro. Sabi’u ya riÆ™e ciki alamar yunwa yake ji. Koda Malam Sidi ya gan shi murmushi ya yim
“Sabi’u ya aka yi ne na ga kana riÆ™e ciki ba dai yunwa kake ji ba?”
“I Malam.”
Malam ya yi gajeriyar dariya ya ce, “Yaro dama ka koyi hakuri, domin ilimi za ka je nema, ka ga dole ka koyeta.”
Fadin hakan ya yi daidai da isarsu tasha, abinci ya fara siya masu kana suka hau mota kirar Bus, malam kujerar gaba ya zauna shida wani inda aka loda yaran a kujerar baya duk sun yi goyo. Sun shafe rabin sa a kana suka tashi, ba su isa ba sai gurin magriba da ke motar irin sauki daura din nan ce, tafiya kaɗan a sauke a dora. Koda suka isa duk sun gaji barin ma yaran abinda ba su saba ba. Da suka iso tsangayar yara ne cike ana ta kokarin yin sallar magriba, su ma suka bi sahu aka yi da su.
Malam sidi sun gaisa da malam Haladu cikin aminci, ya kuma gabatar masa da daliban da yake tafe da su daya bayan daya. Malam Haladu ya kira wasu daga cikin É—alibansa ya haÉ—asu domin su nuna masu guri, yadda a hankali za su san ko’ina ya kuma yi masu nasiha, da su zama masu biyayya ga wadanda ya haÉ—asu daga karshe, ya umurci daya daga ciki mai suna Yusufu da ya kai su zaure haka suka bi bayansa. Koda suka shiga zauren babu kowa a ciki, sai shinfidaddun taburmai da kuma buhuna, sai dai kuma babbane zai iya daukar mutum arba’in ko ma fiye da haka, kowanne bangon É—akin an buga mai Æ™usa jakunkunan bakko ne da na leda a sagale.
Yusufu ya nuna masu guri kusa da tagar É—akin, ya ce “Kusa taburmanku anan.”
Shi dai Mudi tunda suka shigo yake ta ƙarewa ɗakin kallo, yana mamaki yanzu a ce duk yawan daliban nan anan suke kwana.
Yusufa ya ce, “Kana mamaki ne?”
Juyawa ya yi ya kalli Yusufa, wanda ya cigaba da fadin,
“To a ha kama an ragu.”
Mudi ya riÆ™e baki, “Kana nufin ko lokacin haka kuke cakuÉ—uwa?”
“A’a idan zafi ya zo ba mu fiye kwana a ciki ba, kowa daukan shimfidarsa yake yi zuwa waje.” Yusufa ya ba shi amsa.
Mudi ya jinjina kai lalle akwai aiki gabansu.
Yusufa ya ce, “Ni zan tafi neman abinci.”
Mudi ya ce, “Ka jira bari mu ajiye kayanmu sai mu tafi tare.”
Kallonsa ya yi cike da mamaki, “Daga zuwanka? Mu ko ka ga lokacin da aka kawo bamu je bara ba, mun taho da guzuri shi muka ci.”
Sakin baki Mudi ya yi yana kallonsa. “Wani irin guzuri kuma?” Ya tambaya.
“Kana nufin ba ka san ana kawo mutum da guzuri ba?”
“Wallahi ban sani ba.”
“To bari ka ji, in dai mutum É—an gata ne, to sai anyi mai siyayya kafin a kawoshi.”
Mudi ya kara tambayarsa a karo na biyu, “Kamar me da me ake kawo yaro da shi?”
Ya ce, “Kamar bushesshen kanzo, garin rogo, mangyada, sukari, tasshi, magi da gishiri.”
Shiru Mudi ya yi yana nazarin maganar Yusufa, kenan su ba su da gata shi ya sa ba a kawo su da komai ba.
Ina son cigaban illar almajiranci?