ILLAR GOYO HAUSA NOVEL

ILLAR GOYO HAUSA NOVEL

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*ILLAR GOYO*

 

*STORY WRITING BY*

*HAUWA S ZARIA*

(MMN USWAN)

 

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

 

_Affuwa affuwa please, mistake nayi 49 zansa nasa 50, idan baku mance ba a 48 mu tsaya a inda Yusuf ya ɗauki jiddah zuwa asibiti ne, duk mebin littafin zai gane._

 

 

_Hussain Mijin Aljana Episode 4 Latest Hausa Novels._

 

 

 

 

*PAGE  50*

 

Tana hurgi da jiddah ta rarumi zanin gadon da jiddah ta rufe jikinta dashi tai hurgi dashi gefe. Cikin kaukausar murya da tsanani tashin hankali jiddah ta kwarrrrrma ƙara gami da furta innallahi wainnailahin raju’un,hannu tasa ta shako wiyar mama kome ta gani kuma oh ta sakin” mana dake tsaye gami yanda takai mata shaƙa yasata cewa”ai! danbe zakiyi sani?” fashewa da matsanancin kuka jiddah tai gami da zubewa ƙasa

tana furta na shiga uku na lalace wannan wacce irin rayuwace haka?”

 

Mama tace”au! fasawa kikai kuma?eyye!?nace fasawa kikai kuma? Duk mama na maganar ne gami da kaiwa jiddah duka”kuka jiddah keyi sosai babu”mama dake tsaye kanta duka sosai take kaiwa jiddah gami da tokari” cikin tsanani kuka da zafin rai jiddah ta kamowa mama bakin zani tana faɗi ki kasheni nace ki kasheni mama”

 

Yusuf dake jingine jikin bango kuka yake sosai,gani har a lokaci tsirara jiddah take, yasashi ɗaukar zani gado yazo ya rufeta dashi…..kafin ya cire hannu tuni jiddah tai hurgi da zani”mama tai dariya da shewa gami da furta yo ina kunya ga ragowar gayu? Wacece ta gama rabawa kazan kanta ina taga kunya, karuwa kawai karuwa!karuwa!!karuwa!!!…….no-no-no mama Please”cewar Yusuf kenan”Cikin tsanani ihu jiddah ta miƙa gami da kaiwa mama shaƙa tana faɗi ni ba karuwa bace,ki daina kirana da karuwa….shaƙar da jiddah taiwa mamane yasata daɗi a gado jiddah ta haye kanta.

 

Zafin shaƙar da jiddah taiwa mama ne yasa ta kasa katabus, sai faman zazzare ido take yi.

 

Gani haka yasa Yusuf sanya hannu ya fara kokarin ɗaya jiddah daga wiyar mama, a lokacin ne mama tasamu Sa’ar kama jiddah da danbe,duk inda ta kama cizo takeh kai mata”duk yanda jiddah taso da Yusuf ya saketa ta kwaci kanta daga cizon da mama ke mata yaƙi.

 

Gani Yusuf yaƙi sakinta mamarsa kuma bata daina cizo da kai mata duka ba yasa jiddah ɗaukar abin saini hankali, kama Yusuf tai da fadi mama na dukanta ita kuma tana dukan Yusuf, da haka har suka isa bakin kofa, shi dama a tasa tunani idan ta fita tabar ɗakin Dole mama ta fita tunda dama don ita ta shigo.

 

Gani Yusuf ya fitar da ita daga ɗakin yasa mama komawa a guje taje ta ɗauki takardan aikin hajjin sannan ta koma wajan wardrobe ɗin jiddah ta fara watse kayanta tana furta yau sai kinbar gidan nan tunda ba gidan ubanki bane.

See also  Aisha Indo Hausa Novel Complete

 

Daƙyar Yusuf ya kwaci kansa daga rikon da jiddah tai masa da sauri ya fice daga ɗakin, yana fita yasawa kofar key ta waje ya rufe,yana cire key ɗin sulalewa yai a ƙasa ya faɗi yana me fashewa da kuka, gami da tambayar kansa wani wacece irin mahaifiya Allah ya bashi, shin shi kaɗai ke fuskantar Irin wannan matsalar? ko kuma kowama na iya fuskantar irin wannan matsalar?kuka yake sosai gami da Allah wadai da halin mama.

 

Jiddah dake kulle a ɗauki sosai take buga kofa gami da barazanar in har be buɗeta ba zata kashe kanta.

 

Yusuf dake zaune yana kuka duk hargowar da takeyi yana jinta amma Besa ya tsorata da barazanar kashe kanta da tai ba.

 

Nan yaci gaba da kukansa.

 

Mama dake ɗakin jiddah bata fito ba saida ta fidda da kayan jiddah ta watsar a ƙasa kaf, sannan ta fito daga ɗakin tana me cewa”in har na haifu cikin uwata da ubansa yau sai kin bar gidan.jin ihu jiddah a dakin Yusuf ga kuma Yusuf zaune yana kuka yasa mama rafka salati gami da cewa shi kenan ta shinyemi shi,yanzu kuma kaki don nace tabar gidan? “Banza Yusuf yai da’ita yaci gaba da kukansa.

 

Duk abinda suke ciki jiddah na jinsu, jin haushin bezo ya budeta ba yasa jiddah ɗaukar silver cups dasu kan Frish ta fara halbi dasu..ƙaran fashewar Glass da Yusuf yajine yasa shi mikewa ya razane key yasa ya buɗe kofar,yana sa kai mama nasa kai, hankaɗeta yai ta koma baya kana yameda kofar ya rufe da key.

 

Tun daga bakin kofa Yusuf ya fara taka kwalba har ya isa inda take”mama dake bakin kofa kuka tasa gami da furta jiddah ta fini kenan Yusuf? Wallahi in har baka budemi kofa na shigo ba saina tsine maka kabi duniya”banza yai da’ita be ranka mata ba”jin zafin hakan yasa mama furta”tunda Ni ka wulakanta saboda wance banzar insha Allah laima sai ‘ya’yanka sumaka,in har nina haifeka bazaka gama da duniya lafiya ba,motace zatai ajalinka gawarkama bazai ɗauku ba…kowani  wani kalma da mama zata furta tamkar mashi Yusuf jeji a zuciyarsa, duk zafin sukan Glass da yakeji bekai zafin kalaman mama a zuciyarsa ba.

 

Hawaye kawai yake yi wani kebin wani, ƙarisawa inda jiddah take hannu tasa ya fisgota jikinshi da ƙarfi ya rumgumeta, duk irin wutsila-wuntsilar da takeyi nesa ya saketa ba.da ƙarfi sosai ya matseta batare dayace uffan ba, har sai da ta rage hargowa da ihu sannan ya ɗauketa zuwa gado, nanma tayi yunƙurin tureshi da sauri ya haye kanta, zama yai bisa cinyoyinta”Gani haka yasa ta kai masa zuba masa mari a ƙirji.hannu yasa ya haɗa hannayeta ya dannesu a ƙirjinta.yana me furta ke wacce irin yarinya ce eyye?duk da masana haka ba halinki bane amma kiyi haƙuri mana,..mama dake bakin kofa ke tsine-tsinenta a fusace ta juya zuwa ɗakin jiddah, katanya ta kwaso ta fiddasu waje tsakar gida (compound) ta zuba kayan sannan ta sake komawa ciki ta kuma ɗibo wasu tana me faɗi kunbar kwana cikin gidan ga, da haka saida ta kwashe kayan jiddah kaf ta fiddasu waje tsinkenta bata bari cikin gidan ba sannan ta dawo tasawa kofar key ta rufe sannan ta koma palo ta zauna.

See also  Hausa Novel Whatsapp Group Link

 

Daƙyar Yusuf ya samu ya lallashi jiddah ta haƙora, jallabiyarsa ya sanya mata sannan yasa tsitsiya ya share glasses ɗin data fasa ya kwashi a Paka ya dauka zuwa inda suke zuba shara, ko kallo inda mama ke zaune beyi ba yazo yai wucewarsa yana fita daga Palo can ya hango dumin kayan jiddah zube a tsakar waje, da sauri ya ƙarisa inda kayan suke,ije Paka ɗin dake hannusa nan ya fara tattara kayan, be damu da bincike wanda ya aikata hakan ba domin yasan ba kowane zai aikata ba irin mama.

 

Yana ɗiban kayan ya nufi hanyar shiga nan mama ta kasa ta tsare tace”bazai shiga dasu ba, babu irin rokon da Yusuf bewa mama ba amma taki, gani haka komawa yai yaje ya haɗa kayan waje ɗaya ya kullesu, sannan ya ɗauki sharrarsa yaje ya zubar. Fita harkanta yai be kuma bi takan kayan ba sai da ya bari ta mance sannan yaje ya kwashi kayan yabi ta kofar baya ya shiga da kayan.

 

Ya tura kofar jiddah da niyyar shiga kenan ya jita gami rufe da key, uhmm kawai yace”kana ya juya zuwa ɗakinsa nan ya zuba kayan sannan ya dawo Palo inda mama take, guiwa bibbiyu yana rokon ta da yabawa jiddah key ɗin ɗakinta.

 

Babu irin rokon da Yusuf beyi ba mama taƙi,gani bata da niyyar yasashi miƙewa ya koma ɗakin, ranar ko masallaci befi ba a gida yake sallar ba,tsabar tashin hankali yasa Yusuf mancewa yai da gilasan da suka sokesa har saida ƙafar tai masa tsami sannan, zama yai da kansa yake cire gilasan”Jiddah dake ɗakin juya masa baya tai.

 

Duk yanda yaso shige mata ƙin bashi fushi tai, har safe, yana fita sallar asuba itama ta tashi ya ɗauki abinda zata ɗauka ta fice daga gidan.

 

Sauri-sauri dugu-dugu jiddah keyi domin gani tabar layin.

 

Kofa Yusuf yaje sallar beja dogaye sura ba hakan yasa yai saurin idarwa yana sallama a gabgabce yai addu’a ya shafa sannan ya fice daga masallaci, yana isa kofar gida yaga gate buɗe hakan yasa shi ƙarisawa ciki da sauri. Kai tsaye ɗakinsa ya shiga, gani bata ciki yasashi leƙa toilet nanma bata ciki, fitowa yai ya fara duba katanga, gani babu wasu daga ciki yasa shi fahimta cewa”barin gidan tai.

See also  Duk So Ne Sila Hausa Novel

 

A guje ya fice daga gida ya fara bin layin yanayi yana dube-dube can ya hangota ƙarshen layi a guje yai kanta gami hannu tasa ya riƙeta yana me rokonta da tai haƙuri da koma gida.

 

Kuka jiddah tasa gami da furta babu inda zata, babu yanda Yusuf beyi da jiddah da tai haƙuri yazo su koma taƙi”gani yanda ya rike kayan hannuta yasa jiddah sakar masa kayan…da sauri shima ya saki kayan ya riƙeta.

 

Daƙyar Yusuf yasamu jiddah ta bishi suka koma gida,suna shiga mama dake Palo ta kwashe su da harara,tun daga lokacin ta daina kula Yusuf ba magan dashi duk wani hanya da yasan zaisa tai magana ko wani abu ya haɗata dashi ta datse.

 

Duk da beji daɗin wannan matakin data ɗauka ba, a wani ɓangare kuma yace”Gara su zauna haka da ace gidan tabari.

 

Tun daga lokacin da mama ta fahimci basu magana yasata jawosa a jikinta,Abinci ruwan wankansa abin brekft ɗinsa duk mama ke haɗa masa, da safe kafin ya fita zata shiga kitchen ta haɗa masa breakft tana gamawa jerasu take yi a trey takawo masa Palo, yana fitowa zai zauna yaci, idan ya gama kuma har bakin mota take rakashi,bayan ya shiga ta rufe motar gami dayi masa addu’ar dawowa lafiya.

 

Yana tafiya ta dawo ta kwashe kayan zuwa kitchen ta wanke, bayan wasu awowi yana fama da aiki a office saiga kiran mama, cike da mamaki ya ɗaga wayar gami da gaisheta”yaya aiki ta tambyesa”alhamdullilah yace”sannan ta kuma tambyrsa abinda yakeso a dafa masa kafin ya dawo.

 

Cikin rashin fahimta yake bata amsa, yana faɗin kalar abincin da yake da ra’ayin ci sannan sukai sallama.

 

Jiddah dake ɗaki kejin kunnani maganganu da mama keyi, mamaki ne ya kamata gami da tambyr me mama ke nufi da hakan?”

 

Gani ɗaya saura yasa mama shiga kitchen, tuwo shinkafa da miyar alaiyahu ta ɗora”jiddah dake ɗaki jin motsin mama a kitchen yasata leƙawa gani yanda ta tsaya take aiki yasata komawa cikin ɗakin, kasa zaune tai, sai fama rally take yi a tsakar ɗakin.

 

Kafin Yusuf ya dawo kuwa tuni mama ta gama, jerasu tai a foodflast kana ta sanya su a trey ta ɗauka zuwa Palo.

 

Yusuf na dawowa mama ta miƙa ta amshi jakar hannusa gami sayi masa sannu da dawowa,ije jakar tai sannan taje ta bugawa jiddah kofa, jiddah na budewa mama tace”fito tunda bana ubanki bane.

 

A sanyaye jiddah ta fita daga ɗakin, tana fita mama ta hurga mata key ɗin ɗakinta sann taje ta kwaso kayanta ta watsa mata su waje….

 

 

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top