Imaan Complete Hausa Novel
Babban compound ne sosai dake dauke da shuke shuke da bishiyoyi masu daukar hankali, kai kana ganin tsakar gidan kasan naira ta xauna, makeken tsakar gidan na dauke da sassa har uku masu fenti iri daya, ko wani sassa kuma akwai tazara mai tsayi tsakaninsa da wani sassan, sashin farko wanda shi xaka ci karo da bayan shigowar ka gate din xamanin dake babban gidan ba dai girma ba don sashin duk ya fi sauran girma, duplex ne babban gaske sai parking space gari guda dake gefe. Durkushe a bakin tap dake babban sashin farko wata farar budurwa ce da baxata wuce shekaru sha takwas ba, duk da a duke take hakan baxai sa aki gane doguwa ce ita din ba, ruwan tap din na ta xuba bucket din da ta tara don ya cika, sai shafa socks din hannunta take kamar mai tausayinsa, daga ves, huluna sai socks kala uku sune kayan da take wankewa a wajen amma ta kusa awa daya, kofar entrance da ta ji an bude ya sa ta kamewa daga inda take durkushe lkci daya ta xaro ido gabanta ya fadi don ita dai a iya saninta babu kowa sashin banda ita da ke wanki tun daxu, occupant din bangaren duk sun tafi biki ta kuma ga fitarsu, wanda da ace suna nan tasan ko hauka take baxata fara xuwa bangaren su tayi wanki ba, a hankali ta juya don ganin wanda ya fito, wani matashi ne dogo sosai wanda baxai haura shekaru talatin da uku ba tsaye dai dai entrance din shiga gidan sanye da jallabiya milk color, Ta dauke kai tana ci gaba da daurayenta, ya rungume hannuwan sa calmly yace “Keee” kamar xata yi kuka ta juya ta kallesa, yace “Me ya kawo ki wanki nan?” Ta buda manyan idanuwanta tace “Tap din mu fa ne ya lalace jiya kuma…..” Ya katse ta yace “Tashi ki bar wajen” Tace “To ai na kusa gamawa fa” strictly yana d’an daga murya yace “Kwashe kayan ki ki bar nan kar ki yarda in iso inda kike” ta dauke kai hade da turo baki ta mike ta xubda ruwan gaba daya ta hade buckets din bayan ta xuba yan kayan da ta wanke ciki ta kwashesu gaba daya ta bar wajen kamar xata tashi sama ba tare da ta sake kallon inda yake ba, ta murguda baki bayan tayi nisa, murya can kasa tace “Allah ya isa” Dai dai part na biyu da ya kasance wani babban hadadden Bungalow ta tsaya, shi ma kuma bangaren na da nasa parking lot din da xai dau motoci uku, ta dinga kallon sauran kayan da bata gama wankewa ba kamar xata yi kuka, to ita yanxu ya xata yi da su, Ammi na ganin bata gama ba sai ta fara mata fada yanxu tace tun daxu me take, kallon hanyar da xata bi xuwa part din karshe tayi, ta tabe baki sanin ba lallai ma mai sashin ta bar ta ta ta6a mata tap ba, tana ta tsaye can kuma dai ta wuce can bangaren karshen, shi ma sashin bungalow ne sai dai bai kai nasu ba, tsarin ma ba iri daya bane, a hankali ta ajiye buckets din hannunta dai dai tap din dake opposite entrance din shiga parlor tana yi tana satan kallon kofar, cikin dubara ta bude tap din yanda xuban ruwan bazai yi kara ba, ta tara bucket din a karkace kar ma aji xuban ruwa ta ci gaba da daurayenta, sosai gabanta ya fadi jin taku duk a tunaninta mai bangaren ce, mutumin daxu ne ke tahowa bata yarda sun hada ido ba ta ci gaba da wankinta, ko kallon inda take shi ma bai yi ba, bai kuma kai ga shiga parlon ba suka ji muryar wata tsohuwa tana cewa “Ni wai ya nake jin kamar ana taba min pampo a wajen nan ne” da sauri ta kashe tap din ruwan xata kwashi kayanta ta gudu sai ga tsohuwar ta fito, Sake baki tayi tana kallon ta kafin tace “Waye kuma wannan, meye kike min kusa da pampo?” Budurwar ta turo baki tace “To inna namu ya lalace…” Inna ta katse ta da sauri tace “Da ya lalace ni na lalata maku?” Budurwar tace “To wai ma ba daxu kika ce in xo in debo maki ruwa in kai maki bayi ba, shine fa na zo xuba maki” Inna na mata wani kallo tace “Ke din? Ke din da na sani ce xaki kai min ruwa bayi munafuka? bayan ba Aisha sunana ba, to wllh ki kiyaye ni a gidan nan ruwana ba na banxa bane kar ki sake xuwa min nan, kin lalata naku nima ki xo ki lalata min nawa saboda mugunta koh, to uwar ki ce xata debo mun ruwan idan na tankin ya kare, haka kawai ki bar ni da diddigin pampo duk tsutsa cuta ta kama ni in bar ‘ya yana da wahala, ke dai wannan yarinya ta Bukar muguwa ce wllh, shegen barnar ki ta fi karfin ki, to wane 6era ma” ita dai Budurwar sai kallon ta take kamar xata yi kuka, inna na xaro ido tace “Maxa dau min ruwana ki tafi ki juye min a bandaki, ni dai a gidan nan duk wanda ya diba da hakkina gaskiya ban yafe ba tunda abun haka ne, don kowa sai da aka dasa masa pamponsa amma don mugunta sai ku wani kwaso shegun bokitan ku duk datti kuna kwashe min ruwa mugayen yara” Ita dai tana tsaye wannan karan ta daure fuska sai kallon ta take, A fusace inna tace “Baxa ki je ki juye min a bandaki ba ko sai nasa an kira min Bukar ya taho duk inda yake yanxu?” Daukan ruwan Budurwar tayi fuuuu ta wuce ciki, inna ta shiga parlor ta dauko wani karamin kwado ta kulle tap din ta wuce cikin parlor tana cewa “Gwara in ta tsayawa ba ruwan nima da a xo ana ta debe min a cuce ni” Tana shiga parlor ta kalli matashin dake xaune kan kujera yana danna wayarsa, ta hade rai ta dau kyallen da take goge goge ta ta fi gun kayan kallo ta ci gaba da gogenta tana cewa “Ka sake dawowa karasa sauran fitsarar da ka mance baka yi ba kenan, wato duk wanda kayi jiya bai isheka ba, to ni dai a fita a bar min parlor ba ruwana, ba katon banxan da zan kula yau ta kaina nake, kaje can kayi ma uwar ka” shi dai bai tanka ta ba sai danna wayarsa yake, Bayan wani lkci ya mike yace “Dama Abba ne yace in xo in baki hakuri” daga haka ya nufi kofa fuska daure, da karfi Inna tace “Imaan tunda mutumin nan ya shigo kinji ya ce min wani abu?? To ni dai ba ni ka ba hakuri ba wllh, idan kuma ba ka yi hankali ba sae in iya fitar har ofis in sami Ahmadu ynxu” Imaan ta rufe babban roban da ta jawo daga karkashin gado tana kokarin daure alkakin da ta cika a leda jin inna ta sake kiranta tace “Gani nan xuwa” window ta bude a hankali ta jefar da ledan ta shiga bayi ta wanke hannunta da sauri ta fito ta shiga parlor fuska daure tace “Meye kike kirana” Inna na nuna sa tace “Ke tunda kika shigo kin ji muryar bawan Allahn can?” Imaan ta tabe baki tace “Wai wa?” Inna tace “Mujaheed” Imaan tace “To ni na sani? Ni da nake cikin daki” daga haka ta bi ta gefensa ta fice a parlon, sauran kayan wankinta ta dauka ta xaga baya da sauri ta dau ledan alkakinta ta wuce part dinsu, a hankali ta bude kofar parlon tana lekan ciki ganin Ammi bata ciki ta wuce bedroom din ta da gudu ta kulle ta ajiye buckets din a bayi. Da yamma Ammi ta shigo dakin ta sameta kwance tana bacci, Ammi tace “Imaan” bude ido tayi a hankali, Ammi tace “Ki tashi daga baccin nan haka, yamma yayi, kin kwaso socks din naki da kika wanke” tana murxa ido tace “Xan kwaso” Ammi tace “Ga hijabs din ki da na wanke can clothe line din su Anty ki tafi ki kwaso su ma sun bushe, don kawai yan gidan basa nan sai ki k’i tafiya makaranta ko?” Ita dai bata ce komai ba, Ammi ta juya ta fita, xaro ido imaan tayi ta mike da sauri ta shiga bathroom din ta ta matse socks din da hula da inner wears ta xuba su a dryer na washing machine ta kunna sannan ta fita, Tana kwashe hijabs din ta a clothe line da Ammi ta ce mai gadi ya bude gate, wani rantsatsen mota ya shigo gidan direct parking space dake babban part din ya taho, sai ga wata motar ta biyo bayansa xuwa parking space din, Mutumin daxu da safe ne ya fito driver seat sanye da kananun kaya daga cikin motar farko, wata yarinya da baxata wuce Imaan ba ta fito front seat din motar, sannan wata mata da baxata haura hamsin da hudu ba ta fito back seat tare da wata yarinya mai shekara ashirin, kana ganinsu kaga yan daki daya, Imaan ta dauke kai tana ci gaba da abinda take, Bude dayar motar aka yi, wani mai kama da Mujaheed Sak ya fito sai dai shi ya fi sa haske, Shima dogo ne kuma Mujaheed ya girme sa da 4 years, mahaifiyarsa ce ta fito bayan motar da kanninsa duk mata hudu su ma, murmushi mahaifiyar tasa tayi ganin Imaan tace “A’ah wanki aka yi yan mata” Imaan tayi murmushi tana boye fuskarta tace “Sannu da dawowa Anty” Anty tace “Sannu Imaan, ya Ammi fa” Imaan tace “Tana gida” Kallon matashin da ke tsaye kusa da Anty yana kallon ta tayi tace “Ina yini ya Yusuf” yace “Lafiya lau, Imaan din daddy, sai dai nasan ba ke kika yi wankin nan ba” ta xaro ido tace “Ni nayi fa” Anty ce “Toh shi xai maki idan baki yi ba banda tsokana, share sa kin ji” tuni Mujaheed ya nufi entrance din shiga part din su mahaifiyarsa Umma dake satan kallon Imaan da ta ki kallon ta ta bi bayansa, Anty ma ta wuce Yusuf na biye da ita yana waigo Imaan yace “In ji yau baki je tsokanan inna ba ta hada ki da daddy” Imaan tayi dariya tace “Ni ina ruwana da ita ai na daina xuwa part din ta” Daga haka ta juya ta wuce bangarensu. Da daddare Imaan na kokarin saka kayan baccinta ta kwanta Ammi ta shigo dakin, tana kallon ta tace “Ki je Abba na kiran ki” xaro ido tayi tace “Abba kuma Ammi?” Juyawa Ammi tayi ta fita, kamar xata yi kuka ta saka hijab din ta ta fita tana tunanin kiran me Abba ke mata da daddaren nan. A hankali ta bude kofar parlon Abba ta shiga bayan ta cire takalmin kafarta, Abba na xaune a 3 seater cikin parlon Mujaheed na xaune shi ma kan lallausan carpet din dake malale kasa, sai Umma dake xaune kan one seater, Anty ma haka, Imaan ta karasa kanta a kasa ta xauna kasa kusa da Anty, murya can kasa ta gaida Abba, Abba ya amsa yace “Ya karatu” tace “Alhmdllh” yace “Imaan discipline din ki kenan rashin gaida na gaba da ke?” Imaan ta daga kai tana kallon sa, ya daure fuska yace “Ita Hajiya sa’ar ki ce da ba kya gaisheta a gidan nan?” Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace “I am talking to Imaan, kuma ki bar kallona my friend” A hankali ta fara 6ata fuska tana jan yatsunta, lkci daya ta fashe da kuka, Abba ya mata tsawa yace “Daman kuka kika samu don ban xane ki ba yanxu” kuka take yi sosai kamar warce aka duka, Mujaheed ya mike ya mata wani raxanannen tsawa ta mike da gudu ta nufi kofa, xai bi ta Abba ya dakatar da shi yace “Rabu da ita M.A, Allah ya shiryeta” Umma ta tabe baki tace “yaran yanxu da ba a sangarta su ba ma ya aka kare ballantana wannan?” Anty ta mike ta fita parlon, Abba dai bai ce komai ba, imaan bata xarce ko ina ba sai sashin inna, tana shiga parlon ta xube kan kujera ta rushe da kuka, inna ta fito daki da sauri, Yusuf ma dake kwance kan 3 seater ya mike xaune da mamaki yace “Me ya faru Imaan” jikin inna na rawa tace “Me ya samu Aishar?” Imaan ta ki cewa komai sai kuka, tuni inna ta nufi kofa, cikin kuka Imaan tace “Ni ba abinda ya samu Ammina” inna ta dawo tace “Ke dai ki dinga jin tsoron Allah, da yanxu xuciyata ta buga ya kike son ‘ya yana su yi, ya zaki shigo da kuka ki janyo min wata fitinar ina xaune” Cikin rawar murya tace “Ko ba Umma bace” inna tace “Wacece haka?” Imaan bata ce komai ba sai kuka, Inna tace “Warcan mata mai kama da zabiya kike nufi wai, ko ba uwarsu fitsararren yaron nan Mujaheed ba?” Imaan ta hadiye abu da kyar tace “Ita” Inna ta share wani xufa tace “Toh xata ga barbadin rashin mutunci yau kuwa, me ta maki?” A hankali Imaan tace “Shine taje ta gaya ma Abba wai ni bana gaisheta alhalin fa ko na gaisheta bata amsawa, shine Abba ya kirani….” Sai kawai ta fashe da kuka, inna tayi wani murmushi tana gyada kai tace “Biri yyi shige da mutum, Sai aka yi ya da ya kira ki” imaan ta kalleta cikin shesshekar kuka tace “Yana min fada…..” Tuni Inna ta fice parlon, Imaan ta saci kallon Yusuf da yyi tagumi yana kallon ta ta mike tana turo baki ta fita. Inna na isa bangarensu Yusuf kai tsaye parlon Abba ta wuce, har sannan Abba na xaune da Umma a parlon sae Mujaheed, gaba daya daga kai suka yi suna kallon ta, inna ta tsaya tsakiyar parlon tana kallon Abba tace “Yanxu yaro tun da sauran numfashin Bukar a duniya zaka sa ma ‘yar sa ido? Yanxu a kan wannan matar zaka ci mutuncin yarinyar da lafiya ma bai isheta ba sai dai godiyar Allah? Yanxu Ahmadu duk son da d’an uwanka ke maka xaka rufe ido a hadu da kai a ci mutuncin yar sa kwaya daya tal…” Kunce ha6ar xaninta tayi tana matsar kwalla tace “Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba…” Abba kasa cewa komai yyi da farko, can yace “Haba inna, wannan wace irin magana kike….” A fusace tace “Ohh yare nake maka da xaka tambayeni wani irin magana nake, to wllh bari ka ji, a kan Fatima a gidan nan ina iya sa6a ma ko wani mahaluki, kuma baxata gaida matar taka ba, ita katuwar gaida mutane take?” Mikewa Mujaheed yyi ya nufi kofa kamar xai tashi sama inna ta bi sa da wani shegen kallo, sannan ta ja tsaki ta maida dubanta kan Abba dake ta kallonta ta daure fuska tace “Ahmadu yaushe rabon ita matar taka ta kai kafafuwanta bangarena gaisheni? Lallai… ni a su wa xata je gaidawa? Ni din banxa xata gaidar?? To hirrrr wllh, kada wanda ya kara sa ma jikata baki a gidan nan idan ba haka ba sai in sa Bukar ya koma daya gidansa dama shi ya nace xama waje daya da kai, tunda yar sa xa a takura gwara kawai ya bar gidan…Dubi fa Mujaheed haushi ya ji yanxu don na ambaci uwarsa, kana gani saura kiris ya bangaje ni in fadi duk cikin bacin rai, to uwa ta fi uwa ne?? don me kai ma baxa ka tattala ni haka ba, duk ka bi ka daure mata kugu bata gani na da gashi a gidan nan, to mu xuba da ita xan ga ko ita ta haifo min kai duniyar, wannan ai raini ne wllh, wai taji haushi Imaan bata gaisheta ba to baxata gaidata din ba, kar ta kuskura ta sake sa min jika a baki tayi ta kanta kawai a gidan nan” shi dai Abba shiru yyi kansa a kasa, Umma ta rungume hannunta daga xaune tana kallon wani direction din, Abba ya dago yana duban mahaifiyar tasa yace “Kiyi hakuri Inna” ta maka masa wani kallo tace “Sai dai ka ba matar ka hakuri tunda na 6ata mata rai” Tana kai wa nan ta fice. Imaan har ta kusa part dinsu taga shukanta na wake da tayi a babban gwangwani a madadin assignment da aka basu a Agricultural science, a yashe duk root din ya fita daga cikin gwangwanin, ta xaro ido ta ta fi wajen da sauri, lkci daya hawaye ya kawo idonta tace “Wllh nasan Rahma ce xata kwabar min da shuka na” sai kuma ta fashe da kuka na takaici ta durkushe wajen, ba ta lura ba har Mujaheed ya iso wajen, ta juya hawaye sha6e sha6e idonta tana kallon sa ta sake rushewa da kuka, ya daure fuska yana kallon kafarta yace “Me ya faru?” Ta mike cikin rawar murya tace “Yaya kalli fa abinda Rahma tayi ma assignment dina kuma ten marks ne, xa muyi submitting ranan Friday, kalli fa har ya girma, don nawa duk yafi nasu sai ta kwabar min” ganin sai hararanta yake ta juya ta wuce tana ci gaba da kuka, fixgota yyi yana mata wani kallo yace “Shi Abban kika tafi kika yi reporting gun Inna?” Lkci daya ta tsaida kukan da take bayan ta gane biyota yyi, ta fizge hannunta ta kwasa a guje, kiris ya rage ya kamata ta shige parlonsu ta banko kofar tasa key, Ammi dake xaune parlon tana kallo ta mike tace “Meye haka Imaan?” Dariya ta fashe da ta wuce daki da sauri tace “Sauri nake in xo in kwanta fa Ammi” tana shiga bedroom din ta ta sa makulli. Har Imaan ta fara bacci wajajen karfe goma Ammi ta bude kofar dakinta, bude ido tayi Ammi ta hade rai tace “Uban me kika debo ma inna a dakinta?” Ta mike xaune da sauri tace “Na debo mata abu kuma? Haka ta ce?” Ammi tace “Kinga na raba ki da xuwa sashinta ki dauko min magana ba ki ji ko? To ki fito mata da duk ma abinda kika daukan mata gata can bakin kofa” Imaan ta turo baki ta sauko daga saman gadon ta bi bayan Ammi da ta fita, ido hudu suka yi da inna da ke tsaye bakin kofa ta tsuke fuska, Imaan ta hade rai tace “Ni me na dibar maki xaki biyo ni cikin daren nan” Inna tace “Duk cikin jikokina babu mai ta6a min kaya ban basa ba sai ke, duk kece mai mugun halin nan don haka maxa ki fito min da alkaki na, don ba a rame na bar sa ba ina sane da abinda nake ba fara haukacewa nayi ba” Ammi dai ta nemi waje ta xauna, Imaan ta 6ata fuska kamar zata yi kuka tace “Wai yaushe naje da har xan dibar maki kayan ki ni da ba ci ma nake sosai ba, to ma ba xaki gansa hannuna da xan fita ba” Wani tsawa Ammi ta yi mata tace “Kin tafi kin dauko abinda kika diba ko sai na mare ki” Imaan ta harari inna ta wuce kitchen sai ga ta ta fito da ledan alkakin, Inna ta saki baki ta warce ledan tace “Naga Ikon Allah ni Asabe, da yake Aisha ce ta xauna ta min tuyar bayan ta kwa6a dole ki kwaso ki kawo maku ku ci, to ni kar in sake ganin kafafuwanki a bangarena don halin ki abun tsoro ne, wannan ai ba tarbiya aka maki ba ki shiga har karkashin gadon mutane ki jawo kwalla ki debe min kayana, yanxu banda jinin ka jininka ne kin xata idan na ja Allah ya isa baxai bi ki ba, ni wllh darajar d’a na kike ci a gidan nan gaskiya, kar in sake ganin ki a parlona ni dai dama baki tsinanamin komai sai dai ki malale kan kujera kina mik’a, duk kin ru6ar min da kujeru” tana kai wa nan ta juya ta wuce, Imaan bata yarda ta kalli Ammi ba ta wuce daki ta rufe kofa tayi kwanciyarta tana turo baki.
Maa sha Allah, I am back by Allah’s grace… daily update in sha Allah, but if schl shud resume anytime soon xan dakata da posting for some weeks coz I will be having exams in sha Allah. Hope you guys will love the *book*, though I know I never disappoint my fans when it comes to writing in sha Allah….
Khaleesat Haiydar…
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
2……
Washegari da safe Imaan ta fito parlor shirye cikin well ironed uniform dinta da beret dake kanta, kitchen ta shiga gun Ammi, Ammi dake juye ruwan shayi flask tace “Yau ma baki yi combing gashin ba koh” ta jingina da kofa cike da shagwaba tace “Wllh Ammi xafi, baxan iya ba” Ammi bata ce komai ba ta gama xuba ruwan a flask ta xuba mata nata a cup dinta ta hada mata shayin sannan ta mika mata, Karba Imaan tayi ta fita xuwa dinning, Ammi ta kai mata dankali da kwan da ta soya mata ta ajiye tana kallon agogo tace “Kiyi sauri kar su jira ki don Allah” Imaan ta xaro ido tace “Ammi kullum fa ni ke jiransu” Ammi tace “Toh kar kiyi saurin” daga haka ta wuce kitchen don yin wanke wanke, imaan na gamawa ta kai plate din da cup kitchen, ta dauko jakarta, Ammi tace “Ki duba gaban dressing mirror a daki na akwai duba daya ki dauka, dakin ta shiga ta dauko sannan ta fito tace ” Ammi sai na dawo” Ammi tace “Ohk Allah ya tsare kiyi addu’a kafin ki fita, and you make sure baki mance ko wani book ba tunda hankali bai ishe ki ba” dariya kawai tayi ta fita gidan bayan tayi addu’a, Can parking space din su Yusuf ta tafi ta tsaya don nan take jiransu, yawanci Yusuf ke kai su wani lkcin kuma Anty ta ajiye su tunda tsohon driver dinsu ya tafi, Tana ta tsaye jikin mota ta hango plant din su Ummi, Rahma da Maimoon don duk ajinsu daya wato ss2, kamar xata yi kuka ta dinga kallon waken nasu da duk ya fito da ganye, ga nata can an lalata mata, kallon entrance din gidan tayi lkci daya ta nufi wajen da plant din suke da kafa ta haure gaba daya biyun banda na maimoon don kowa ya sa sunansa, sai da ta tabbatar roots din sun fita sannan ta koma jikin mota da sauri, Ummi ce ta fara fito sanye cikin uniform irin na jikin Imaan sannan Rahma sai Maimoon, Babu wanda ya kalleta cikin su banda Maimoon da tace “Imaan kin gama maths assignment din ki” Imaan tace “Ehh na gama” Maimoon tace “Toh idan mun shiga mota xan kwafa plss ban yi ba” Imaan tace “Ohk” Mujaheed ne ya fito rike da makullin mota fuska kamar hadari, Imaan ta xaro ido tana kallon Maimoon murya can kasa tace “Shi xai kai mu?” Maimoon tace “Ehh ya Yusuf baya nan ya tafi Zaria daxu, shine Anty tace ya Mujaheed ya ajiye mu, shine yake fushi” Imaan ta turo baki bata ce komai ba yana bude motar ta shiga back seat tare da Maimoon da Rahma, Ummi ta shiga gaba, har suka bar gidan babu wanda yace komai cikin su, Imaan ta bude jakarta ta ciro assignment din ta ba Maimoon, tafiyar minti ashirin ke kai su makarantar su, amma saboda gudun da yyi cikin few minutes suka iso, yyi parking dai dai makarantar yana kallonsu da kyau yace “Dama kuna tashi ku fara trekking din dawowa gida don baxan xo daukan kowa ba” a hankali Ummi tace “Ya M.A ai soon Abba xai dau mana wani driver fa” yace “Sauka malama” bude motar tayi ta fita, tuni Imaan da Maimoon ma suka fita suka shige cikin makarantar. Anty ce ta xo daukan su bayan sun tashi ranan, Anty na kallon Imaan dake ta yamutse fuska tace “Me ya faru Imaan” a hankali ta nuna mata kanta, Anty tace “Toh idan kin koma gida kin ci abinci sai ki sha magani ki kwanta ki huta” to kawai imaan tace, ko da suka isa gida har bacci ya dauketa Maimoon ta tasheta ta bude ido, Anty tace “Toh shiga gida imaan” kai kawai ta gyada mata ta fita ta nufi part dinsu tana dingishi. Ruwan xafi Ammi ta hada mata ta shiga tayi wanka sannan ta ci abinci, Ammi ta bata magani tace “Sai ki daure kiyi shirin tafiya islamiyya it’s too early ki fara fashi this week, today is Monday” Imaan bata ce komai ba, Ammi na fita ta koma kan gado ta kwanta kamar xata yi kuka, hudu da minti biyar Ammi ta shigo dakin jin shiru bata fito ba, ganin har bacci ya dauketa ta kai hannu jikinta taji da dumi, girgixa kai tayi ta juya ta fita, Maimoon ne ta shigo parlorn sanye da uniform din islamiyya, Ta gaida Ammi sannan tace “Ammi imaan muke jira” Ammi tace “Bata jin dadi ku tafi Maimoon” a hankali Maimoon tace “Allah ya sauwake” sannan ta fita, Ammi na girkin dinner a kitchen wajen karfe biyar Imaan ta fito daki, wani internal heat kawai ta ke ji, kuma tana kunna Ac tasan sauran ta dinga lekan kitchen kamar xata yi kuka, a hankali ta nufi kofar fita ta bude kofar yanda baxa aji kara ba sannan ta fice xuwa part din inna don ta je ta kunna Ac, Inna na wanke gun tap dinta da take sa ma kwado ta daga kai tana kallon Imaan tace “Baki tafi islamiyyar bane yau” Imaan ta turo baki tace “Ehh” daga haka ta shige parlon, kunna Ac tayi ta kwanta kan kujera dake kallon Ac din ta lumshe ido, inna na gun tap din har sannan sai ga Mujaheed, ta mike tana kallon sa tace “Baka ji bayana ba Mujaheed kamar xai balle, ko kai baka ga yanda wajen pampon yayi haske ba tun daxu nake ta gurza gashi sai kyalli yake, ai kazanta bata da kyau, yanxu kaga ko tuwo aka xuba a wajen mutum xai iya xaunawa ya ci” Mujaheed dai bai tanka ta ba ya shige parlorn bin bayansa tayi, ya ajiye ledan hannunsa yace “Gashi Abba yace a kawo maki” tace “Toh Allah yayi masa albarka… Dama raina na son kayan marmarin” xai fita Inna tace “Mujaheed kaga yarinya nan abinda ya kawota kenan ta xo ta kunna Ac wata cutar ta kamata ace ai a parlorn inna ne, to ni dai ba ruwana ka kashe min kayana taje can ai su ma suna da shi, duk yanda aka yi kuma uwar hanata kunnawa tayi shine ta taho ta kunna nawa salon ace parlorn inna to Allah ya fi ki babu me sa ni a bakin duniya” Mujaheed ya kalli Imaan da tayi rub da ciki kan 3 seater din ya tabe baki xai fita Inna tace “kai ya ina maka magana xaka fita, idan uwar ka Rukayya ce xaka mata haka Mujaheed?” Fuska daure ya juyo ya xauna yana kallon ta da kyau yace “Wllh idan kina sa mahaifiyata a baki Hajiya xa mu kwashi yan kallo dake a gidan nan, komai sai kice uwata” Inna ta saki baki tace “Kai ni kake daga ma murya” yace “Toh ki daina sako mahaifiyata a xancen ki idan baki son a daga maki murya, ke kwata kwata rayuwarki baki son xaman lafiya daga kice wannan yayi maki sai ki ce wannan yayi maki….” Inna ta gyada kai tace “To ka tara kuma ka samu, xaka san ni ka fada ma bakar magana” Tana fadin haka ta kashe Ac dinta, Imaan ta mike xaune kamar xata yi kuka tace “Meye xa ki kashe min inna” Inna tace “Bukar yasa na kashe, na ku lalacewa yayi xaki taho min nan, ni dai a daina xuwa ana sa ni magana ana min rashin kunya gaskiya” imaan ta marairaice tace “Don Allah inna ki kunna xafi nake ji a cikin jikina” Inna tace “Toh baxa ki ji xafi a jikin ki ba ga magani nan an kawo maki tun daga Nijar kin ki amsa sai yawo kike min da hankali kamar ni xai amfana, duk tashi fadin da nake a kanki ba ki gani, mutum bai san inda xai dace ba, idan an baki magani sai kiyi biyayya ki amsa ki sha sai kiga Allah ya yaye maki wannan ciwace ciwacen da ba a san kansa ba” Imaan tace “Wa yace maki ba a san kansa ba, to ai da shi aka haifeni kuma ba warkewa….” Inna tace “Oh oh Allah, Mujaheed kaji irin fitinar da take ja ma kanta da bakinta ko, kai wannan ‘ya ta Bukar anyi doluwa wllh, ke fata kike kar ki warke d’a na yayi ta cacan kudi, duk cikin jikokina babu mara tunani dama irin ki” Imaan ta hade rai tace “Ehh na ji, ki kyaleni da ciwo na Babu ruwanki, baxan kuma sha maganin ba don ina da na asibiti da nake sha, ni bance ki dinga amso min magani ba dama ai” inna tace “Kada Allah ya sa ki sha, to ni Allah na tuba a haka ma wa xai yi sha’awar aurem ki yau ciwo gobe lafiya duk tattalin arxikinsa ya kare a asibiti, tun kina mitsitsiyar ki nake wahala da ke kan maganan magani shi sa ma kika yi kyan gani, ke da kike kamar kwarangwal da taimakon Allah da taimkona da magungunan da nake amsar maki gun malamai shine kika marmaro, in dan ta uwar nan taki ce ai sai dai ki mutu tana kunshe daki ba fita xata yi ta nemo maki magani ba tana jiran na asibiti, Toh wllh daga yau na fita harkan ku ki ji da ciwon ki nima inyi ta kai na” Imaan ta fashe da kuka tace “Ehh naji, ki kyaleni tunda ba dole bane shan maganin ki” daga haka ta fice daga parlorn da gudu, Inna tace “Duk xa ku yi bayani bari iyayen naku su dawo” Mujaheed ya tabe baki ya mike ya fice mata a parlorn shi ma. Imaan na kwance kan kujera bayan isha Ummi ta bude kofar parlorn tana tsaye daga bakin kofa tace “Abba na kiran ki a bangaren Inna Imaan” daga haka ta fita, Ammi dake cin abinci xaune parlorn ta kalli Imaan da ta wani juya bata dai ce komai ba, bayan kusan minti biyar Ammi tace “Amma dai kin ji abinda tace Imaan” Ta juyo kamar xata yi kuka tace “Wllh Ammi kafana ciwo yake min ban san ko xan iya tashi ba” Ammi ta galla mata wani harara tace “Sai ki rarrafa ai tunda baxa ki iya tashi ba” hawaye cike idonta ta mike ta sa Hijab ta fita tana taka kafar da kyar. A hankali ta bude kofar parlorn Inna ta shiga da sallama, Abba ne xaune parlorn sai Inna da Anty, Imaan ta sunkuyar da kanta ta karasa kusa da Anty ta xauna kanta a kasa ta gaida su, Abba da Anty kadai suka amsa, inna ta wani tsuke fuska, Imaan dai bata ko kalleta ba, Inna tace “Wato shi Mujaheed din jira yake kaje ka ciccibo sa da kanka koh?” Abba ya kalli Imaan yace “Tashi ki tafi can bangaren ki kira min Yayanku” Imaan ta mike ta d’an harari inna ta gefen ido ta fice a parlorn, tana isa part din su Mujaheed ganin bbu kowa parlor sama ta haura ta tsaya corridor tana kallon door din dakinsa har ta mance rabon da ta je kusa da kofar, bude kofar Umma aka yi sai ga shi ya fito, ta matsa da sauri don kusa da kofar dama take tsaye tace “Abba yace in kira ka” ko kallon ta bai yi ba ya fara sauka stairs, ta murguda masa baki ta bi bayansa, har suka isa part din Inna bai juya ba, ya bude kofar ya shiga da sallama, kusa da Anty Mujaheed ya durkusa kansa a kasa, Abba sai kallon sa yake yana girgixa kafa, Imaan ta shigo parlorn ganin inda ya durkusa tace “Waje na ne nan” Murmushi Anty tayi, shi kam ko kallon ta bai yi ba balle ya motsa, Inna tace “Ahmadu na fa gaji da xama nan kamar warce xa a ma gafara, aji da ni in tashi in shiga ciki in kwanta” Abba ya kalli imaan yace “Samu wani wajen my friend” ta harari Mujaheed ta koma wani wajen ta xauna, Abba na kallon Mujaheed yace “Muhammad ita innar ka mayar abar wasar ka a gidan nan?” Inna ta tabe baki tana jijjiga kafa, Mujaheed bai dago ba kuma bai ce komai ba, Abba yace “Am I not talking to Mujaheed” ya dago a hankali yace “Abba kayi hakuri don Allah” Abba yace “Stupid, ni ma kake ba hakuri?” Ya kalli inna yace “Kiyi hakuri inna” dakatar da shi tace “A’a malam a gaban ubanka xaka ce min inna kenan, wllh Ahmadu daxu yana nuna ni da yatsa a can bakin kofar kamar xai make ni Hajiya yace min, ni na ma xata duka xai kai min bayan ya gama kashedin, to gaskiya da sake, sam yaranka basu da d’a’a basu da kunya Ahmadu, isuhu ne kadai dama mai gudun bacin raina duk da shi ma ko aiki xai kashe ni baya taimakona, to ynxu Mujaheed da wani ne da ya xo ya gan ni durkushe ina faman gurje gun pampo ba amsa xai yi ba ya taya ni, to wllh bai amsa ba sai xagina ma ni da yayi daga karshe, a xo har sashina a dinga ci min mutunci, to hirrr don duk ranan da aka isheni tattara kayana xan yi in bar gidan nan kuma sai anyi shekara duba ana nemana” Mujaheed ya d’an daga kai ya kalleta ta gefen ido ya maida kansa kasa, Abba dai bai iya yace komai ba, Anty tace “Kiyi hakuri inna, a yafe masu” Inna tayi kasa da murya tace “Wllh Amina daga nace kai kuwa Mujaheed haka kake ma Mamarka a gida ina ma magana xaka wuce, kuma fa cikin lallami nayi tambayar kawai ba sai ya sakar min aradu a kai ba, ita kuma wancan lankwasasshiyar mai kama da yar tsana bbu abinda ta mance bata gaya min ba daga nace Imaan ga maganin da na amso maki saboda ciwon ki da ba a san kansa ba ba a san dalilinsa ba, wllh Ahmadu sae kaga wanke ni da yarinyar tayi tasss har da ce min ba ruwana da ciwonta kuma ciwon ba me warkewa bane” Imaan ta fashe da kuka har da shessheka, Abba yyi mata tsawa cikin rawar murya tace “Abba xagina fa ta ke yi wai….” Abba ya dakatar da ita yace “Keep shut” ta hadiye abinda xata ce tana hawaye, Mujaheed yace “Kiyi hakuri Inna” Inna tace “Atoh ya xan yi idan ban hakura ba, dama wanda aka cuta ake ba hakuri, amma daga kai har ita kar in sake ganin kafufuwanku a bangarena, tunda kun raina ni, Isuhu da Maimuna sun ishe ni” Fada sosai Abba ya dinga ma Mujaheed da kansa ke kasa, inna sai matsar kwalla take ita a dole an 6ata mata rai, hakuri Mujaheed ya kara bata, Anty ta sa Imaan ma ta bata hakuri, mikewa Imaan tayi da sauri ta fice parlorn tana kuka, Inna tace “Sai ubansa na magana yayi ta sinne kai kamar na kirki alhalin crooo kenan ku ke gani, kar ka sake xuwa min sashi ni dai na gama magana” Mujaheed bai kalleta ba balle ya tanka ta ya mike ya fice parlorn, can kusa da wani flower ya ga Imaan durkushe tana kuka, ya dinga hararanta har ya isa wajen da take, ta mike cikin rawar murya tace “Yaya don Allah kai kaji na xage ta daxu?” Ba tare da ya tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace “Ke ma ai ba dukan ki naga aka yi ba” Ta bi shi da kallo tana shessheka.
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan*⭐🌟
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
3……
Imaan ce xaune kitchen sai faman xuba surutu take ma Ammi dake girkin dinner a kitchen, yar skirt ne jikinta sai ves da yake ranan alhamis ne babu islamiyya, Ammi dake ta saurarenta ta tabe baki daga karshe tace “Aikin kenan sai dai ki cika mutum da surutu ba taimakon fari balle na bak’i” shiru Imaan tayi tana kallon Ammi, Ammi ta kalleta ganin yanda mood dinta ya canxa tayi murmushi tace “Toh ci gaba ina jin ki” sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, Ammi ta karasa kusa da ita tace “I was joking sweetheart, tafi ciki let me fry some onion and pepper” mikewa Imaan tayi a hankali xata wuce Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, Ammi ta jingina da cabinet din kitchen din ta sauke ajiyar xuciya, can ta nufi kofa ta fita don bata son tayi bacci coz shine next abinda xata yi in har ta shiga daki, dakinta Ammi ta shiga ta sameta har ta kwanta, Ammi tace “Baxa kiyi bacci ba yanxu yamma yayi, je dakina xa ki ga leda da atamfa a ciki kan dressing chair ki kai ma su Anty kice ankon bikin Halima” Imaan ta mike xaune tace “Ammi to na mu fa” Ammi tace “Sai ki kirata ki tambayeta ban san ko an fidda naku ba” Imaan tace “Toh, Anty kawai xan nuna ma?” Ammi tace “Ehh sai ki ce mata ta nuna ma Hajiya, na dai fita ai” daga haka Ammi ta fita dakin, imaan ta sa hijab har kasa kan kayana jikinta ta fita ta dau ledan ankon a dakin Ammi, tun da ta shiga parlonsu Anty take yamutse fuska ta dalilin yaji dake tashi sosai daga kitchen, lkci daya ta rike numfashinta, har xata juya ta fita sai ta nufi stairs da gudu don ta shiga dakin Anty, tsarkewa tayi sbda rike numfashin da tayi ga kuma gudun da take, lkci daya ta fara tari sosai breathing dinta na sama, dai dai corridor ta fadi tana kokarin jan numfashi, Maimoon ta fito dakin Anty ganinta ta durkusa gabanta da sauri tace “Subhanallahi me ya faru Imaan” sound din faduwarta yasa Mujaheed ya fito daga bedroom din sa, ganinta a kasa ya kalli kofar Ummarsa kafin ya karasa da sauri ya dagata yana kallon Maimoon da ta rikice yace “Tafi ki karbo inhaler dinta da sauri” da gudu ta sauka xuwa part din su Imaan, Mujaheed ya bude kofar dakin Anty ya shigar da ita ya xaunar da ita kasa ya jinginar da ita da gado ya cire Hijab din jikinta, dai dai nan Anty ta fito daga bandaki, a rude tace “Subhanallahi, Asthman ne, garin Yaya? Ko in amso inhaler dinta” yace “Maimoon taje amsowa” sosai imaan xata baka tausayi saboda ynda take struggling da numfashinta, Mujaheed ya mike ya fita don bin bayan Maimoon suka kusa cin karo bakin kofa, fixge inhaler din yyi ya juya ya koma dakin ya durkusa gabanta ya kai mata baki, dafe hannunsa tayi tana inhaling, Anty dai na tsaye sai kallonta take cike da tausayinta, bayan wani lkci numfashin nata ya fara fita a hankali yana kokarin dawowa normal, Anty ta xauna gefen gado tayi tagumi tana kallonta, Ummi da Rahma na tsaye bakin kofar suna kallonta su ma, Har sannan Mujaheed na duke gabanta idonsa a kanta, muryar Umma suka ji tana cewa “Lafiya me ya faru ku ka tsaya cirko cirko bakin kofa?” Rahma tace “Asthma ne ya tashi wai” Umma ta leko dakin ganin Mujaheed ta wani xaro ido tace “Me Mujaheed yake a nan?” Mikewa yyi da sauri, ta wani hade rai tace “Tambayar ka nake, me ka shigo yi, ko kayi kama da likitan ta ne?” Ya girgixa kai yace “No na xo wucewa ne….” Dakatar da shi tayi tana masa wani shegen kallo tace “Sai ka tsaya aikin da ba lada koh? To ka shiga hankalin ka, Ka guji bacin raina, basu da number likitan ta ne ko kuma neman suna kake?” Shiru yyi bai ce komai ba, Cikin tsawa tace “Xo ka fita malam bana son shishshigi da kwala kai a faranti, kanwar uwar ka ko ta ubanka?” Bai ce komai ba ya kalli Imaan da Anty ke kokarin kwantarwa kan gado ya juya ya nufi kofa xai fita, Anty ta tabe baki tace “Ciwo dai bai wuce kan kowa ba, ita ma ba ita ta doro ma kanta ba…..” Umma ta katse ta da sauri tace “Allah yayi mana tsari da irin wannan ciwo nata, ya tsari jikokinmu da tatta6a kunne, a rayuwar nan ta ynxu wa enda ba sickler ba ma ya suka kare, ae irinsu ne ke tsiyata namiji a sintirin asibiti….” Tsaye Mujaheed yyi bakin kofa yana kallon Umma, Anty ta wani hade rai tace “Kinga ki daina kiranta da sickler ita din ba sickler bace, Allah kuma yyi mata tsari da shi” Umma ta wani tabe baki hade da dariya tace “Kwa dinga boye ma wanda ku ka raina ma wayo, Allah dai ya ba kowa lafiya….” A hankali Mujaheed yace “Umma ba fa sickler bace, she is just a carrier….” Umma ta maka masa wani kallo tace “Meye maraban dambe da fada? And did you have any problem with her being a sickler or not da har kake karyata ni Mujaheed?” Bude kofar yayi ya fita dakin bai ce komai ba, ta ja tsaki ta fice ita ma. Anty ta girgixa kai ta zauna kusa da Imaan da ta lumshe ido numfashinta na sauka a hankali tana mata sannu, sai da ta ga alamar tayi bacci sannan ta mike ta fita, Imaan bata dau lkci tana bacci ba ta tashi ta dalilin ciwo da kirjinta ke mata, ta dinga juye juye kan gadon hawaye na xuba idonta, bude kofar dakin aka yi Mujaheed ya shigo, ya karasa kan gadon yana kallonta, daure fuska yyi yace “Me ya faru kuma?” Kirjinta ta nuna masa ta fashe da kuka, yace “Toh kukan ne xai sa ya daina ciwo, tashi xaune” mikewa tayi ta xauna da kyar, sai ga Anty ta shigo dakin, da sauri ta isa gadon tace “Me kuma ya faru Imaan, are you feeling pain anywhere?” Ta gyada kai tana nuna kirjinta, Anty ta dau Hijab ta nufi kofa tana cewa “Bari in je in kwaso magungunanta dai” Xaunawa Mujaheed yyi gefen gadon, ta koma xata kwanta yace “Kar ki kwanta” ta jingina da gadon tana goge idonta, ba a dau lkci ba Anty ta dawo da ledan maganin gaba daya, Mujaheed ya amsa yana duba maganin ya cire mata wanda xata sha, still yyi jin an bude dakin Umma, sai kuma ya ji muryarta tana tambayar inda yake, tashi yyi da sauri ya tafi bayan kofa ya tsaya, Anty ta tabe baki ta balli maganin ta dau table water ta mika ma Imaan, bude dakin aka yi Umma ta kare ma dakin kallo kafin ta tabe baki ta kulle, Shi dai yana tsaye bayan kofar, Anty ta sa Imaan ta kwanta bayan ta sha maganin sannan ta kallesa tace “Don Allah ka fita min a daki malam, tunda aikin xumuncin ma ba so ake kayi ba, kai ma kuma tsoron yi kake, yau ko da ace baka san Imaan ba a matsayin ka na likita ka ganta a wannan hali ai baxa ka ki taimaka mata ba balle tana yar uwarka halak malak, Allah dai ya shiryi mahaifiyar ka” shi dai bai ce komai ba, bayan karin mintuna uku ya bude dakin ya fita. Anty na xaune kan darduma bayan ta idar da magrib Imaan ta tashi daga baccin da ya kara dauketa, Anty tace “Sannu ya jikin Imaan” a hankali tace “Na ji sauki” Anty tace “Toh shiga bayi kiyi alwala ki xo kiyi sllh” ba musu ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito Anty ta mike kan darduman ta fita, Imaan ta sa Hijab dinta ta hau kai ta tada sllh, tana ta xaune kan darduman bayan ta idar sai ga Anty ta shigo da plate din abinci dakin. Imaan na gama ci ta mike rike da plate din tace “Anty sae da safe” Anty tace “Au baxa ki kwana nan ba” murmushi tayi ta make kafada ta nufi kofa, Anty tace “Toh baki fada min ko na meye atamfar ba” Ta juyo da sauri tace “Lahh, Ammi ce tace in kawo maku ankon bikin Anty Halima” Anty tace “Ashe abu ya xo dai, toh ki ce mata xan shigo gobe” Imaan tace “Toh” Anty tace “Allah ya sauwake Imaan” murmushi tayi a hankali tace “Ameen” daga haka ta fita, tun da ta sakko downstairs umma ke mata kallon tsana tana tabe baki, Imaan dai bata ko kalleta ba ta nufi kitchen rike da plate din, Rahma ce kitchen din ta gama wanke wanke, sai Mujaheed dake tsaye yana xuba ruwan Lipton daga teapot a cikin mug, Imaan xata ajiye plate din, Rahma tace “Kinga plate mai datti a wajen ne malama” turo baki tayi ta dau morning fresh ta bude xata wanke plate din, Rahma tace “Ya M.A in debar maka abincin ne xan fita?” Ya harareta yace “Abincin da ku ka cika yaji ko wanda ba yaji?” Yar dariya tayi tace “Ya Mujaheed yajin fa ba yawa” tsaki yyi yace “Ance maki ban yi tasting abincin bne ku dinga cika ma mutane ya ji a abinci kamar mayyu” Tace “Toh in maka cous cous?” Yace “I will take tea” Imaan ta gama wanke plate din ta juya ta fita kitchen din. Kallonta Ammi ta dinga yi bayan ta shigo tace “Ya jikin Imaan” tayi murmushi tace “Na ji sauki Ammi” daga haka ta nufi dakinta Ammi ta bi ta da kallo. Karfe sha daya saura Ammi ta shiga dakin Imaan, ganin tayi bacci ta tasheta tana mika mata wayar hannunta tace “Me ya sa kika kashe wayar ki” Imaan na murxa ido tace “Kila mutuwa yyi ba charge” Ammi tace “Toh idan kin gama ki maido min wayata daki” Imaan tace “Toh” sannan ta kai wayar kunne tace “Daddy ina yini” Daga daya bangaren ya amsa yace “Why is ur phone switched off” ta langwabar da kai tace “Daddy ban sa a charge ba tun jiya” yace “Toh kiyi kokari ki sa ya jikin?” Tace “Naji sauki, daddy ina missing dinka yaushe xaka dawo?” Yace “Weekend in sha Allah” ta wara ido cike da jin ddi tace “Plss daddy ka dawo week end din kar ka daga, wllh ina son in ganka” kamar xata yi kuka ta kare, yyi murmushi yace “Sure dear, plss ki daina wasa da shan drugs din ki kinji” tace “Ina sha Allah daddy, har yanxu Dr ma bai xo ba” yace “Ehh mun yi waya daxu yace bai dawo ba” Imaan tace “Toh” yace “Sleep tight dear, banda kunna Ac” yar dariya tayi tace “Toh daddy byeee” katse wayar tayi ta mike ta kai ma Ammi daki sannan ta dawo dakinta ta shige duvet. Yau Friday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka tana kokarin saka kayanta taji k’aurin abincin da Ammi ta bar mata a kitchen kan gas don tana shigowa gidan Ammi ta fita kasuwa yin cefane, da gudu ta fita daure da towel don kashe gas din don dama sae da Ammi tayi mata kashedi kan cewar kada ta yarda abincin ta ya kone, muryar inna ta ji a balcony tana cewa “Aa kawai ni dai naga kwana biyu bata shigo bane shine nace in xo in duba ko jikin ne, tunda haka Allah yyi ta mai laulayi, ni jiya ma ko abinci basu kawo min ba wllh, in ma ba ta da lafiya ita Aishar baxata iya takowa ta kawo min abincin ba tunda ba uwarta Habiba bace, abu dai gashi ba tsari da ni fitinanniyar tsohuwa ce ba Bukar xan kira ince matarsa ta bar ni da yunwa ba?” muryar Yusuf imaan taji yana dariya yace “Toh ae an kai maki daga gidanmu naga” da sauri Imaan ta shige daki ta dau Hijab dinta ta fito ta shige kitchen ta kashe gas din sannan ta bude kofar kitchen din ta fice tana murguda baki ta sa Hijab dinta da iyakarsa gwiwa, ko takalmi bbu kafarta ta dinga tafiya har ta zagayo front din gidan, Mujaheed ne xaune kan farin kujera yana waya, ta turo baki ta wuce sa da sauri, ko minti biyar ba ayi da wucewarta ba shi ma ya ji muryar inna tana tahowa, mikewa yyi da sauri tun kan ya bar wajen ta gansa, da karfi ta kwalo masa kira tana murmushi, ya ki juyowa har ya sha corner, Yusuf sai danne dariyarsa yake, Inna ta bude baki tace “Wato ni Mujaheed xai walakanta ina kiransa ya min banxa kai shaida ne ko Isuhu” tana magana tana kunce ha6ar xanin xata goge kwalla, Yusuf ya kasa daurewa ya fara dariya yace “Ke fa kika ce kar ya sake xuwa bangaren ki…” A fusace tace “To shi mahaukaci ne bai san bacin rai ba” Karo Mujaheed ya kusa yi da Imaan dake kokarin lekowa taga ko inna ta taho bangaren, ya hade rai yace “Baki gani ne?” Tana shafa Inda ya bugeta tace “Ko ba inna bace, ta wani biyoni gidanmu anjima tace ina mata rashin kunya” tafiyarsa yyi ya bar ta wajen tsaye, ta turo baki ta bi bayansa, jin tafiyarta a bayansa ya tsaya ya juyo yace “Wai me yasa kike bi na ne” Tace “Ni ba bin ka nake ba tafiyata kawai nake” Tsayawa yyi ya daure fuska yace “To yi tafiyar ki, bana son ganin ki kusa da ni” ba ta ce komai ba ta fara tafiya kamar mai counting steps dinta, yana ta tsaye yana jiran tayi nisa ganin ynda take tafiyar ya girgixa kai ya wuce ta cikin lokaci kankani, sai a sannan ta kara saurinta har ta jera da shi, d’an murmushi yyi bai dai ce komai ba bai kuma kalleta ba, sai da suka kusa entrance din kitchen din part dinsu tace “Yaya ka mance promise da ka taba min 2 years back koh?” Kallonta yayi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Na me?” Ta wara manyan idanuwanta tace “Idan nayi saukan al-quran, gashi mun kusa in few months time” tabe baki yyi xai bude kofar kitchen din yace “I can’t recall….” Ta xaro ido ta rikosa da sauri tace “Wllh nasan baka mance ba” Buge hannunta yyi yana mata wani kallo yace “Keee” Ta turo baki tana kallonsa, yace “Sakeni kar in mare ki” sake sa tayi ya bude kofar kitchen din ya shiga ya kulle, tana ta tsaye wajen bayan few minutes ta murguda baki ta wuce, ta kitchen dinsu ta bi ta kulle kofar sannan ta wuce dakinta ta sa kayanta. Yau tunda Imaan ta tashi take ta murna, gaba daya farin cikin ta ya kasa boyuwa, Kitchen ta shiga tace “Ammi da yaushe daddy xai iso?” Bude baki Ammi tayi tace “Kina kallon agogo kuwa Imaan?” Imaan tace “Ammi wai yau ma da daddyna xai dawo sai naje islamiyya?” Ammi ta mata wani mugun kallo tace “Uwar me xa ki xauna ki min ko yace maki da safe xai taso, common kin 6ace min a nan kin je kin shirya ko sai na 6ata maki rai” a hankali Imaan ta juya a sanyaye ta koma bedroom dinta ta fiddo uniform dinta ta shiga sa wa, sai da Ammi tayi mata jan ido ta amince da yin breakfast da ta hada mata, tana xaune dinning tana shan shayin da kyar Maimoon ta shigo parlon sanye da uniform, Ammi dake goge goge a parlorn tace “Maimoon ku yi wucewar ku kar ta bata maku lkci ko da kafa ne sai ta je” dariya kawai Maimoon tayi ta fita, Imaan ta mike don kanta ganin takwas ya wuce ta dau jakarta ta fita tana matsar kwalla ko ta kan kudin makarantar bata bi, Ammi dai ko kallonta bata yi ba, Tsaye taga Mujaheed jikin motar banda masifa babu abinda yake ma kannin nasa, duk kallonsa kawai suke babu wanda yace komai, “Don samun waje nan nan da islamiyyar ma sai an kai ku a mota ku ga yan gayu ko, to wllh ni ba driver din kowa bane a cikin ku da xa a dinga cewa in ajiye ku a makaranta, Yusuf da ya ga xai iya sai yyi, I won’t tolerate that shittt” A hankali Ummi tace “Amma ya Mujaheed kawai don kana nan ne yasa xaka kai mu ai ba kai ke kai mu ba dama, kuma Abba yace kila Monday xa mu samu sabon driver….” wani kallo ya dinga mata fuska daure, ta sunkuyar da kanta, Imaan da isowanta kenan ta bude motar xata shiga ya dakatar da ita yace “Kee, do I look like drivern gidanku da xaki ajiye ni for the past 15 mins a nan, to ke daga yanxu ma xa ki fara naki trekking din” yana fadin haka ya nuna mata makeken gate din gidan yace “Bi can ki kama hanyar makarantar” ta wani gwalo ido tana kallonsa, lkci daya ta juya kamar xata yi kuka xata koma part dinsu tace “Ni dai ban ta6a tafiya da kafa ba….” Wani tsawa yyi mata yace “Wllh ki ka yarda na takowa har Inda kike sai na sa ki kuka” tsayawa tayi tana hawaye don bata mance last abinda ya mata ba, ya nuna mata gate on a serious note yace “Bi can” Gate din ta nufa tana kuka ya jira ya ga fitar ta sannan ya shiga motar ya bar gidan har ya wuce ta. Tsaye tayi bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab tana kuka, ta kusa minti sha biyar tsaye a haka taji cikin cool voice ance “Are you okay” xame hannunta tayi a hankali daga fuskarta tana lekan ko waye ta cikin hijab dinta, wani dogon matashi ne da baxai wuce thirty two ba, yana sanye cikin kananun kaya idonsa sanye da bakar spec, dogo ne shi din sosai, sannan shi ba baki ba kuma baxa a sa shi a jerin farare ba, kuka ya kara taho mata ta dinga rerawa, yace “Subhanallah, wani abu ya faru da ke ne? Talk to me plss” Cikin rawar murya tace “Yaya ne ya ce baxan shiga mota ba trekking xanyi kuma islamiyyar mu da nisa wllh” kallonta ya dinga yi da mamaki, ta sake lekosa ta cikin Hijab suka hada ido ta yi saurin rufe fuskar tana shessheka, ya d’an yi murmushi yace “Kin masa laifi kenan” girgixa masa kai tayi, yace “Toh mu je in ajiye ki ga ride dina can, while going inside the filling station na gan ki tsaye bayan nayi refilling tank na fito I still saw u the way you were so I decided to check if you are alright” shiru tayi bata ce komai ba yace “Mu je to” tace “A’a” yace “Ohk in samar maki adai daita?” Kai ta gyada masa, ya tsayar da adai daitan ta shiga ya basa kudin, a hankali tace “Nagode” ya mata murmushi kawai mai adai daitan ya ja suka bar wajen, Yusuf ne ya dauko su daga islamiyyar bayan sun tashi karfe sha biyu, tun a mota ya dinga tambayar Imaan me ya faru ganin yanda take yamutse fuska, da kyar tace “Kafana ke min ciwo” yace “Toh sannu, idan muka isa gida sai ki shafa maganin” a hankali tace “Toh” suna isa gidan da kyar ta fito motar, Yusuf ya kama hannunta ya rakata har sashin nasu sannan ya bude mata kofa ta shiga ciki, wanka kawai tayi ta saka doguwar riga Ammi ta shafa mata methylated lotion din da take shafawa a kafafuwanta sannan ta sa ta kwanta nan da nan kuma bacci ya dauketa, dab da la’asar Ammi ta tasheta, Ammi bata mata xancen islamiyya ba Imaan ta wara ido ganin irin girke girken da Ammi tayi tace “Ammi is all this for daddy?” Ammi tace “No it’s for Imaan” murmushi Imaan tayi ta rungumeta ta baya tace “Thanks sweet mum” Ammi tace “Ki tafi kiyi sllh ko baki ga lokacin hr ya gota ba” da sauri ta koma daki, tana idar wa ta fito, Ammi tace “Daddy ya kira yana gate, ki fita ki shigo masa da kaya” da sauri Imaan ta nufi kofa Ammi na kiranta ta xo ta sa hajib don rigar jikinta karamin hannun garesa amma tuni ta fice, dai dai nan mai gadi ya bude gate sai ga motar Daddynta, da gudu ta nufi parking space ta tsaya cike da murna, Mujaheed dake kokarin bude motarsa suka yi ido hudu da daddy da ya fito Imaan ta rungumesa, Daddy ya sakar masa murmushi, hakan yasa ya nufe sa kamar mai kirgan steps dinsa, daddy na shafa kan Imaan yace “Ba kya girma koh Mamata” ta kara kankamesa tace “Don Allah daddy ka daina dadewa haka wllh ina Missing dinka” yyi murmushi yace “To xan daina mamana” Mujaheed ya risina yace “Sannu da hanya Abba” Wani hade rai Imaan tayi tana hararansa ta gefen ido, Daddy na murmushi yace “Thanks Son, ka bar mu a birnin tarayya ynxu koh” murmushi Mujaheed yyi yace “Ae kam daddy” daddy yace “Toh Allah yayi jagora, ya aikin fa?” Yace “Ae ban fara ba sai Monday Abba” Daddy yace “Allah ya kai mu” Daddy ya mika ma Imaan da ta turo baki ledan apples dinta da chocolates don a ko da yaushe tsaraban ta kenan, Mujaheed dai ko kallonta bai yi ba ya dau jakar laptop din daddy da wasu files ya nufi part dinsu, Murguda baki Imaan tayi ta jera da daddynta tana ci gaba da gaya masa yanda tayi kewarsa, Mujaheed ya sunkuyar da kai ya gaida Ammi bayan ya ajiye jakar hannunsa da files, ta amsa ta dau jakar ta wuce daki, Daddy ya xauna yace “Barrister bai dawo ba ko Mujaheed?” Mujaheed yace “Ehh bai dawo ba” Daddy yace “Ohk mun yi magana daxu ma” Mujaheed ya dukar da kai yace “Toh Allah ya huta gajiya Abba” daddy yace “Madalla nagode son” har ya fara tafiya Daddy ya kalli ledan apples da chocolates da Imaan ta sa gaba tana dubawa yace “Son baxa ka Debi apples ba” Da sauri Imaan ta jawo ledan jikinta tana kallon daddy, Mujaheed da har xai ce A’a don he isn’t a fan of Apple ganin abinda tayi yayi kasa da kai yana shafa gashinsa yace “Toh Abba” daga haka ya nufeta, bude baki tayi tana kallon daddy lkci daya hawaye ya kawo fararen idonta, Mujaheed ya jawo ledan yana kallonta da kyau ya cire spare leda ya debi apples har hudu a cikin guda takwas da Daddy ya siya ya xuba a wani ledan yana kallonta har sannan, ya kara bude ledan chocolates din ma ya debi mai yawa ya xuba a ledan hannunsa, har ya mike ya sake dawowa ya dau Apple daya ya sa ka a ledan, daddy ya dauke kai yana murmushi, Mujaheed bai yarda ya kallesa ba yace “Nagode Abba” daga haka ya fice parlon.
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan*⭐🌟
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
4…..
Daddy ya kalli Imaan dake goge hawayen idonta yace “Don yayanki ya debi apples kike kuka Imaan?” Ta marairaice tace “Toh daddy ai ba shi ka siyo ma ba gashi ya kwashe min gaba daya kuma wllh baya cin apple” Daddy yyi murmushi yace “Shi yace maki bai ci” cikin rawar murya tace “Ae nasan baya ci tun da can” Daddy yace “Toh anjima idan na fita xan karo maki” a hankali tace “Toh nagode” yace “Wai amma me ya hada ku da yayan naki all of a sudden Imaan” Ammi da ta fito parlon tace “I am still wondering also, lkci daya aka yi parting” Daddy yace “Ko kin masa wani abun ne dai” ta turo baki ta dawo kusa da daddy tace “Kawai dai naga ya xama mugu ne shi sa na daina kulasa” Dariya kawai daddy yayi, Ammi tace “Har nan ma ai baya shigowa yanxu” Daddy yace “Toh Allah ya kyauta” Imaan tace “Daddy ni dai ka daukan min personal driver dina plss” daddy yace “Ba Abbanku xai daukar maku driver ba, ai mun yi magana da shi bayan tsohon drivern ya wuce” Tace “A’a daddy ni dai nawa daban nake so, kilan ba yanxu driver din ma xai xo ba, yau fa Yaya bai bari na shiga motar ba don na bata masu lkci da kafata na tafi islamiyya shi sa tun da na dawo duk jikina ke ciwo sai da Ammi ta shafa min magani na kwanta da na tashi shine naji sauki”‘ Murmushi kawai Daddy yayi ya mike yace ” Bari in yi wanka daughter ” daga haka ya wuce bedroom dinsa, Ammi tace “Sai ki tashi ki kai ma Inna abinci ko yau ma baxa ki ba” Ta kalli Ammi da sauri tace “Ammi ca tayi bata son sake ganin kafata a part dinta fa, kuma in je yanxu ta gaya ma daddy” Ammi tace “Tashi ki dauki abinci ki kai mata nace” Daga haka Ammi ta bar parlon, mikewa Imaan tayi ba don ta so ba ta shiga kitchen, kusan duk abinda Ammi tayi ma daddy sai da ta dibar ma inna duk ta ajiye a basket, Imaan ta dau basket din me dauke da abincin ta fita, har ta isa part din Inna fuskarta a daure yake irin ko kulata din nan baxata yi ba, ta dinga kallon takalman dake bakin kofa kafin ta bude kofar ta shiga, Mujaheed na xaune yana kallon inna dake bada labari tayi mitsi mitsi da ido, banda murmushi babu abinda yake don da wuya yake dariya, su Maimoon da Rahma kuwa dariya har da kyakyatawa, Inna ta saita hannu sama tace “Ji kawai muka yi ratatatata…. Ba sai kakan ku ya shige karkashin gado ya bar ni da halina da ‘ya yana ba, lkcn Bukar na bayana sai tsala ihu yake, Ahmadu kuwa fitsari ya dinga saki yayi sau uku a wando….” Ganin Imaan Inna tayi shiru ta jawo daya daga apples biyar dake cikin leda a gabanta ta kai baki, Har sannan su Maimoon dariya kawai suke, imaan ta ajiye basket din hannunta tana kallo chocolates din da Daddy ya kawo mata a hannunsu Maimoon, ta saci kallon Mujaheed ta juya xata fita Inna ta tabe baki tace “Ga dambun naman ki can a daki ni dai na ajiye maki bana bi ta halin ki ba” ba tare da ta juyo ba tace “Bana ci” inna na ci gaba da cin apple dinta tace “To wa yayi asara?” Mujaheed yace “Yana ina a dakin?” Da sauri Imaan ta juyo ta shige dakin, Inna tace “Ya xaka ce yana ina bayan ka ci rabon ka da wanda ma ka dauka ban baka ba” yace “Haba” tayi tsaki tace “Yana nan cikin roba xa ki gansa a rufe, duk naki ma ya fi yawa” Imaan ta fito rike da uban dambun naman da inna ta ajiye mata a bowl mai murfi ta nufi kofa, inna tace “Wannan liyafar hala Bukar ne ya dawo?” Imaan tace “Bai dawo ba” daga haka ta fita, Inna tace “Duk ta ma fige kamar bata cin abinci” Rahma tace “Mu dai ci gaba da ba mu labarin da kike yi don Allah inna” inna ta gyara xama xata ci gaba, mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon. Imaan na komawa bangarensu ta tadda Yusuf ya shigo gaida Daddy, Ya bi ta da kallo ta boye bowl din hannunta tana wara masa manyan idanuwanta tace “Nasan ka ci naka dai” fitowar Daddy parlon yasa Yusuf bai ce mata komai ba, daddy yace “Engnr ashe kana gari” Yayi murmushi yace “Ina nan daddy, da fatan kun iso lafiya” yace “Alhmdllh My son, ya aikin fa” Yace “Mun gode Allah Daddy” daddy ya xauna kujera yace “Madalla, kowa dai lafiya koh?” Yusuf yace “Duk lafiya” Yusuf bai wani dade ba ya mike yace xai wuce, daddy yace “Baxa ka tsaya mu ci abinci ba” Yace “Alhmdllh daddy na ci abinci” Ammi dake dinning tana jera abincin tace “Anya Yaya Yusuf” dariya yayi yace “Ammi wllh na koshi” tace “Toh shikenan” sallama yyi ma daddy ya fita. Bayan magrib daddy xai je gaida inna babu yanda bai yi da Imaan su je ba ta ki, har hakan ya basa mamaki ya tafi shi kadai, inna na goge tiles din parlonta daddy ya shiga da sallama, ta mike tace “Amma dai gaskiya Bukar ka dinga kwa6a ma yar ka ta daina karya, ce min fa tayi baka dawo ba” Ya xauna yana murmushi yace “Sannu inna, ina yini” ta shimfida tabarma ta xauna tace “Lafiya lau, amma ai karya ba shi da amfani kuma a gaskiya Imaan ta iya karya” Shi dai bai ce komai ba, tace “Toh ya hanyan?” Yace “Alhmdllh mun baro hanya” tace “Wannan karan kuma kamar baxa ka sake dawowa ba” yace “Aiki ne yyi yawa Inna” tace “Toh Allah ya bada sa’a ya tsare mana ku a duk Inda kuke, ya maka albarka” yace “Ameeen inna” Tace “Toh ya xa ayi, Allah ya kaddara a can abincin ka yake, banda haka na tabbata da kana gidan nan da ka dinga share min hawaye daga bakin cikin da nake fuskanta” Daddy na kallonta da mamaki yace “Bakin ciki kuma Inna?” Inna tace “Yo bakin ciki mana Habu… Kaga yayanka baxai fito daga masallaci ya tako nan tun asuban ba ya gaisheni sai ina jin wajen karfe tara xai taho da safe ya duka can bakin kofar ya gaida ni a gurguje ya kara gaba, bana sake ganinsa Bukar sai ina kokarin kulle kofa ta da daddare shi ma Allah yasa ya yi minti biyu xaka ga yace sai da safe daga haka ya wuce, Kaga matar nan tasa Rukayya take ko wa? Uwarsu Mujaheed dai wllh kaji rantsuwar musulmi tafi wata biyu ina ga bata tako ta xo nan ta gaisheni ba sai ta gan ni a tsakar gida ko a can bangaren, ita kuma dayar mai kama da fulanin Bararoji wato Amina da suke ce ma Anty sai ta bushi iskarta xata kwaso kafafuwa ta xo gaisheni, ita wnn farar wa take da suna? Uwar wannan yarinya Imaan d’an wankin da take min da duk ta watsar sun xugeta, in kuwa wannan ‘ya taka Imaan borinta ya tashi ta ki kawo min abinci to ranan fa da yunwa xan kwanta a gidan nan, Aisha ta fi karfin ta taso takanas ta kawo min da kanta, to me yafi wannan bakin ciki Yaro? Gashi gaba daya ‘ya yanku sun rainani sun maida ni ba bakin komai ba, sun maida ni kakarsu tun ma ba wannan katon Mujaheed ba da ramammiyar ‘yar ka, sai wannan kazamar Ummi, ni nasan da sun ga ido wllh taka ni xasu dinga yi suna wucewa, isuhu kadai ke raga min a gidan nan sai wannan yarinya Seeyama, Imaan idan ta fara balbale ni wlh shiru nake, haka ma Mujaheed yaron da aka haifa a gabana, to ina dalili ina da gata na ta ko ina don dai d’an abincin da ake yarfa min a kwano sai a maida ni bola” Daddy dake ta saurarenta ya dago kansa a karo na farko yace “Kiyi hakuri don Allah inna” a fusace tace “Na gaji da jin wnn axxalumin kalman, ayi ta baka hakuri ana cutan ka, ni dai a fita harkata, don idan tsiyata ta debeni wllh sai an fita har kasashen waje ana nemana” Daddy yace “Xa a gyara Inna, duk ki yafe masu, ita Imaan xan sameta yanxu, shi ma Mujaheed din xan gamu da shi” Tace “Atoh, sai ka xaunar da su ka tambayesu kaji ko xaman gidan ne basa son inyi, ka tambayesu dalilin da yasa basa fitsaran su a waje sai a cikin gida cikin gidan ma a kan uwarka, kayi masu jan ido ka nuna masu bacin ranka Yaro” Daddy yana murmushi yace “In sha Allah” nan suka ta6a hira amma kusan hiran gaba daya na complain ne daga karshe daddy yace mata xai wuce masallaci don an kira isha. Daddy na dawowa masallaci ya dinga kallon Imaan dake xaune parlor tana cin abinci, ya xauna yace “Imaan yanxu ita innar kika mayar abar wasar ki a gidan nan?” Kallonsa ta dinga yi kamar zata yi kuka, ya hade rai yace “would you take ur eyes off me silly girl, haka kike ma uwar ki? I warned you the last time a kan haka shine kika sake repeating foolishness din yanxu ko?” Ta sunkuyar da kanta, ya gyada kai yace “Nasan maganin ki, tashi ki bar min parlor” tashi tayi da sauri ba tare da ta bi ta kan abincin ba ta shige bedroom dinta ta kulle, ita dai Ammi bata ce komai ba, Daddy yace “I don’t like this nonsense character of her, ita innar abokiyar wasanta ce, ke kuma Aisha baki taka mata burki, a kan me xata dinga rainata, I don’t like that, and I am going to teach her manners soon” Ammi ta tabe baki ta mike ta dauke abincin da ta bari ta kai kitchen ta rufe, ta tsaya kitchen din tana wanke plates da ke sink. Washegari wajen karfe bakwai da rabi Imaan ta fito sanye da uniform din islamiyya, kanta a kasa ta gaida Ammi dake jera breakfast a dinning, Ammi dake kallonta tace “Wato ke ba isa a maki fada ba shine kika kwana kuka ido ya kumbura koh?” Ta fashe da kuka tace “Ni Ammi don Allah kar ki sake ce min in kai mata abinci kullum sai tayi ta ma mutum sharri alhalin ba abinda nayi mata” Ammi tace “Ko ban baki abinci kin kai ba ma da kanki naga kike kwasan kafafuwanki kije can din ko da kuwa koranki tayi” Imaan ta hade rai tace “Yesterday was the last day da xan je part dinta, har abada baxan sake xuwa ba” Ammi tace “Toh bari dai ya ji ki gashi can ya fito, ni ba ruwana” shiru Imaan tayi tana juya shayin da Ammi ta hada mata, Daddy dake tsaye parlon yace “Madam me yasa ba a kai ma Inna breakfast ne wai?” Ammi tace “Breakfast kuma?” Yace “Ehh ai ya kama ta ne” tace “A’a don Allah yallabai kar ka hada ni da ita, kullum sai Abba ya tura mata bread, tana da kayan shayi kuma tana da heater ta iya amfani da shi, meye breakfast din dama idan ba shayi da bread ba sai kwai wani lkcn, lunch da kanta tace bata so a daina kai mata wai jagwalgwalon yara ne” Tuni Daddy ya xauna ya sa news channel, Ammi ta shiga kitchen ta ci gaba da abinda take, Imaan ta gama breakfast din ta mike ta iso cikin parlor ta durkusa ta gaida Daddyn nata, sau daya ya kalleta ya amsa ya ci gaba da kallonsa, ta mike ta tafi kitchen ta amshi kudin makarantar ta gun Ammi ta fito ta dau jakarta bayan ta sa takalmi da safa tayi ma daddy sallama ba tare da ta kallesa ba ta fice daga parlon, kiranta daddy yyi ta juyo ta dawo ta sunkuyar da kanta tace “Ga ni” room freshener har biyu ya nuna mata dake ajiye yace “Dauka ki kai ma Inna kafin ku wuce” shiru tayi tana kallonsa kamar xata yi kuka, bata dai ce komai ba ta durkusa ta dauka sannan ta fita xuwa part din inna, Inna na ta goge goge bayan ta gama share ko ina fesss, banda kamshin turaren wuta babu abinda ke tashi a parlon, imaan bata kalleta ba ta ajiye abun hannunta fuska daure tace “Ina kwana” xata fita inna tace “Me ya sami idonki ni Asabe? An umaki wani abun ne” Imaan da har ta kai kofa ta juyo lkci daya ta fara kuka tace “Kawai sai kije kice ma daddy ina maki rashin kunya yaushe rabon da in xo nan….” Tana fadin haka ta fashe da matsanancin kuka, Inna da ta saki baki tace “Shine ya maki me?” Cikin kuka tace “Fada ya dinga min mana yace zai yi magani na” Inna ta dau dankwalinta ta fita parlon imaan ta bi ta da kallo tana share idonta, Ko sallama babu inna ta bude kofar parlon, daga daddy har Ammi suka daga kai suna kallonta, tace “Bukar dama yaro ba lallabasa ake yi ba a rayuwar nan, daga mun yi magana tsakanina da kai sai ka taho ka far ma yarinya da bala’i, to ae gwara ita sau dubu a kan sauran, Imaan bar ta da son jikinta amma wllh wllh bata da matsala, haka kawai ka ja mata wani cutan dama gata mai cuta iri iri kamar ta kashe d’an mutum, yanxu da kasa ta kwana tana kuka idan wani abun ya sameta me xa ka gaya ma Allah, kai dai wllh ka cika bala’i, ba haka yayanka Ahmadu yake ba, ba ruwansa da irin wannan hali, to wai ma me ta min da xafi haka da xaka sa ta kuka haka, ga abun duka can Mujaheed me nuna ni da yatsa, mai ce min Hajiya, ni tunda nake wllh xan iya kirga sau nawa Imaan ta mayar min magana shima kuma duk laifina ne…..” Ammi dai tuni ta shige kitchen, Daddy kuma ya kasa cewa komai, Inna ta juya ta nufi kofa tana cewa “Wannan dai ba yi bane, kamar ba kai ka haifeta, yar gata daga ita sai ita amma kuma ka takurata, da wanne xata ji da rashin karo mata kanni da ba ayi ba har yau ko kuma da fitinar mahaifinta, kuma ka tashi ka kawo min turaren bature da ko kamshi babu wai in fesa a daki, to uwata bata ce min je ki kya gani ba turaren wuta tsadadde mai kamshi nake nufi, sai ka ba matarka mai kumewa a daki kamar matar liman ta fita kasuwa ta siyo min” daga haka ta fice ta kulle masu kofa. Dama imaan direct gun mota ta nufa bata yarda ta ma bi ta part dinsu ba. Yusuf ne ya ajiye su islamiyyar, karfe sha biyu Anty ta dauko su, A hankali Imaan ta bude kofar parlonsu tana lekan ciki, babu kowa hakan yasa ta shiga ta rufe kofar ta nufi bedroom dinta da sauri, tana kokarin cire Uniform dinta Ammi ta bude kofar, Imaan ta gaisheta kanta a kasa, Ammi tace “Amso min card waje kafin ki cire uniform din” Imaan ta amsa tana kallonta tace “Ammi daddy fa?” Ammi tace “Yana daki” Imaan ta marairaice tace “Ni fa ban gaya ma inna ya min fada ba, kawai taga idona ne haka” Ammi tace “Wannan ya rage naku ke da shi, ni kiyi sauri ki amso min card din” imaan ta maida Hijab dinta ta fita, kiosk din is just a house from theirs, ta amso card din ta juyo ta shigo gida, Umma ta gani tsaye parking space alamar xata fita, Mujaheed ya iso wajen ya bude mata back seat, sannan ya shiga driver seat, Imaan na hada ido da Umma dama ta dauke kai tayi wucewarta, Mujaheed ya bi ta da kallo ta madubi, Umma ta shiga cikin motar tace “Wllh duk ranan da ka gaida uwar yarinyar nn ko da mistake a gidan nan ban yafe maka ba Mujaheed, duk kanninka ma na karanta masu haka nasan kuma sun dauka….” Yana kallonta ta madubi yace “Haba Umma kema kin san…..” Ta karasa masa da sauri tace “Baxa ka iya ba ko? tunda ga ta kanwar Ahmad ko kanwata, Mara tunani kawai da bai san ciwon uwarsa ba, to mu xuba da kai wllh, ba dai makiyana su ne mutanen arxikin ka ba a gidan nan, ka ci gaba, a ta dalilin munafukar uwar yarinyar nan na bar gidan ubanka for good 5 years, ta hade kai da kishiyata suka yi ta kulla min makirci har ubanka ya sakeni, da yake akwai sauran xamana a gidan na dawo few years back na tarar baka da masoya da ya wuce makiyana, ka maida Aisha uwarka, ka nuna duk gidan nan baka da kanwa da ya wuce yarinyar Aisha, yarinyar da bata gaisheni a ynxu ko idona xai makale a nata saboda uwar ta hanata, da kyar da siddin goshi da rokan Allah na rabaka da su, ni da ba a kan idona na haifeka ba kuma ina haihuwar ka aka ajiye min kai a gefe na da wllh bbu abinda zai sa baxan ce canjen ka aka min a asibiti ba, sam baka san mutunci na ba, ace makiyana su ne masoyan ka Mujaheed? Anya kana son gamawa lfya kuwa?” Shi dai ya kasa cewa komai, ta gyada kai ta bude motar ta fice tana cewa “Ga ka ga su ai, daga ynxu ma ka tatttara yanaka yanaka ka koma bangaren nasu” a hankali yace “Umma I have avoid a lot of things a gidan nan kema kin sani, wllh ko kadan bani son abinda xai bata maki rai, don Allah kiyi hakuri….” Ko saurarensa bata yi ba ta fice daga compound din ya sauka ya bi bayanta da sauri. Washegari har Ammi ta gama hada breakfast ta fito daga kitchen imaan bata fito daki ba, ta kalli agogo ganin bakwai da quarter ta nufi dakin ta bude ta shiga, kwance ta ganta ta dukunkune cikin bargo, Ammi ta karasa da sauri ta cire bargon tace “Are you okay Imaan?” Ta bude ido kamar xata yi kuka, Ammi ta dinga kallonta don jikinta ya dau xafi sosai, a hankali tace “Ina ke maki ciwo kuma?” Kafafuwanta ta nuna mata da kai, hawaye cike idonta tace “Ammi duka jikina ciwo, jiya ban yi bacci ba” Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace “Ba ki sha magani ba jiya da daddare ko daughter” ta nuna ma Ammi magungunanta a side drawer tace “Na sha Ammi” saketa Ammi tayi ta mike ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka ta fito tace “Toh shiga kiyi wanka sai ki kara shan maganin” da taimakon Ammi ta sauka kan gadon, Ammi na rike da ita suka shiga bathroom, bayan ta wanke baki Ammi ta taimaketa tayi wanka ta fito, barin ta tayi ta sa kaya ta tafi hado mata shayi, Daddy na xaune parlor yana dube dube a laptop, ta tsaya bayan kujerar tace “Yallabai jikin imaan fa kar ya rikice mana ko xa aje asibiti tunda likitan ma baya nan” daddy ya mike yace “Bata jin dadi ne” Ammi tace “Nima yanxu na shiga ganin bata fito ba, her temperature is high tace bata yi bacci ba” daddy ya d’an yi shiru, Ammi tace “Kwanakin baya ciwon ya lafa sosai, as from some weeks ago yanxu duk sai ya tasar mata ga xaxxabi da ciwon kai kuma tana shan drugs dinta” Daddy yace “Toh ta shirya mu tafi asibiti” Ammi tace “Toh” komawa yayi ya xauna, ita kuma ta wuce dinning don hada mata shayi. Kwance ta sameta bayan ta sa abayar da ta fiddo mata, da kyar Imaan ta sha shayin, Ammi ta fesa mata turarrukan ta ta bata veil din abayar sannan suka fito parlor, kwanciya tayi kan kujera tana gaida daddy dake rike da makullin mota yana jiransu, ya amsa yace “Sannu mamana, tashi mu je to” mikewa tayi ya kama hannunta suka nufi kofa Ammi na masu Allah ya kiyaye hanya, A hanya daddy ya hadu da Abba ya taho daga part din Inna, gaisawa suka yi, Imaan ma ta gaishesa a hankali, Abba yace “Jikin ne ya tasar mata?” Daddy yace “Wllh kuwa, xa mu je asibiti ne yanxu” Abba yace “Subhanallah tana shan magunguna kuwa” Daddy yace “I think so” Abba yace “Toh likitan ta fa?” Daddy yace “Yayi tafiya ne” Abba yace “Toh tunda Muhammad na nan ba sai ya dinga dubata ba kafin likitan nata ya dawo, ko gwara a tafi asibitin?” Daddy yace “Noo in xai dubata shikenan, dama don likitan baya nan ne xa mu je asibitin” Abba yace “Let me give him a call, na barsa sashin inna, idan ma asibitin xa a sai ya kai ta kawai” Yana kokarin kiran Mujaheed suka hangosa yana tahowa, Abba ya maida wayarsa, har Mujaheed ya isa parking space da suke tsaye kallonsu kawai yake, Ya risina ya gaida Daddy, ya amsa masa da fara’a, Abba yace “Imaan xaka duba Mujaheed, bata jin dadi” Sosai gabansa ya fadi ya kalli Imaan dake jingine da mota duk ta wani langwabe.
I appreciate my fan’s love always, ina yinku fisabilillah😘😍
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_✍🏻