Imara Hausa Novel Complete

*Chapter 3:*

 

“Get out!” Abinda kawai ya furta kenan yana kafeta da manyan idanunsa ɗan turo baki tayi sai kuma ta ce”ni bazan iya kwana ni kaɗai ba wlh saidai na kwanta a nan a ƙasa” buɗe idanunsa ya yi a kanta yana yi mata wani mugun kallo cikin kakkausar murya ya ce”idan nayi kamada abokin wasanki to ki cigaba da zama anan” da haka ya juya mata baya yana rufe gaba ɗaya jikinsa da duvet, bayansa Imara tabi da kallo hawaye na zubowa kan fuskarta me Maheer yake nufi da ita?, Wane irin mutum ne shi?.

 

***A nutse ya turo kofar ɗakin yana sanye cikin wasu suit black colour as usual idanunsa maƙale da glasses, lumshe idanunsa ya yi saboda ƙamshin turaren daya daki hancinsa kusan 2mins kafin ya buɗe idanunsa akanta sanye take cikin wata Abaya black colour ta yi rolling veil ɗin abayar a fuskarta ƴar ƙaramar round face ɗinta ta fito sosai gwanin sha’awa ɗauke idanunta tayi daga kallonsa fuskanta a haɗe babu walwala bai ce mata komai ba ya kamo hannunta ya matse cikin nasa ya tallafi fuskarta akan tafin hannunsa yana bin ta da kallo hannunsa ya sanya ya gyara mata gashinta wanda yake kwance gefen fuskarta ta yi saurin lumshe idanunta tana ƙamƙame jikinta waje guda batayi aune ba taji dungure mata kai tayi baya zata fadi ya sanya ƙafa ya tareta yana yi mata wani irin kallo ya ce”ke har abada bazaki ji magana ba ko?” Ɗago idanunta wanda suka sauya kala tayi tana kallonsa da rashin fahimta ta ce”me kuma nayi maka?” Ta faɗa tana dafe goshinta, harararta ya yi bai sake ce mata komai ba ya juya ya bar ɗakin. A dinning area ya samesu duka kowa na cin abincinsa cikeda nutsuwa wajen Shamma ya ƙarasa ya rungumeta yana murmushi ya ce” Barka da safiya Shamma” murmushi ta yi ta ce” ka tashi lpy?” “Alhamdulillah” ya ƙarasa wajen Ameer sunkuyawa ya yi a gabansa ya ɗora kansa bisa cinyarsa yana sakin wata ajiyar zuciya wani yalwataccen murmushi Ameer ya yi yana shafa sumar wacce tasha gyara ya ce”Ka tashi lpy?” ɗago kansa ya yi yana murmushi ya ce”Alhamdulillah Ameer” jinjina kai Ameer ya yi yana zamesa daga jikinsa ya mike tsaye dai-dai lokacin da ta shigo dinning area ɗin kallo ɗaya Ameer ya yi mata ya ɗauke kansa yabar parlon zuciyarsa na ayyana masa abubuwa dayawa da idanu kawai Imara ta bisa sai kuma ta sunkuyar da kanta ta ƙaraso wajensu Shamma ta gaishesu kamar yanda ta saba. Kujerar gefensa ta zauna sai juya abincin gabanta take ta gagara kai shi bakinta kallonta Shamma ta yi ta ce” ki ci abinci mana daughter ko bakison school ɗin?” ɗan murmushi ta yi tana girgiza kanta ta kai abincin bakinta,

“Maybe bata saba irin wannan rayuwar ba shiyasa ta fito daga ƙabilar matsiyata dole ta dinga kasa cin abinci”

Cak! Imara ta tsaya da tauna abincin da takeyi ta zubawa Immi idanu wanda suka gama sauya kala ba ita kaɗai ba kowa ma na wajen kallon Immi yake, ajiye spoon ɗin hannunsa ya yi ya miƙe tsaye bai kalli kowa ba ya kama hannunta suka bar wajen da idanu Joda ta bisu sai kuma ta taɓe baki.

 

*Education City, Doha, Qatar*
_DOHA INSTITUTE OF GRADUATE STUDIES (DI)_

 

Fitowa ya yi daga office ɗin yana kallonta ya ce”idan har kika aikata wani abu wanda za’a gane ke ba Katalina ba ce wlh sai na saki dana sani” kallonsa kawai tayi sai kuma ta taɓe baki tana kallon wani wajen bai sake ce mata komai ba ya fice daga wajen ita kuma tabi wanda zai nuna mata class ɗin nasu. Babban class mai matukar kyau da ɗaukan hankali komai na amfanin student an tanada a cikinsa a hankali take wara idanunta tana kallon tsirarun mutanen dake cikinsa wanda basu fi 20 ba suna ganinta suka tashi suna ihu sai murna suke

“Welcome back friend kin dawo?” juyawa Imara tayi tana kallon wacce take mata magana ganin yanda take dariya yasa ta yi murmushi itama wanda yake iya laɓɓanta ta gyaɗa mata kai dukda bata gane inda ta dosa ba hannunta taji an kama ta juya tana kallonta bata ce komai ta zaunar da ita gefenta tana kallonta ta ce”munyi kewarki sosai Katalina yanzu kin ji sauƙi?” da idanu kawai Imara ke bin ta tama rasa abin da zata ce gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta gaza gane abin da suke nufi shin wa ce Katalina? Meyasa suke zaton ita Katalina ce? kuma ina Katalinan?, Jijjigatan da akayi ya sanya ta ɗago manyan idanunta tana kallonta ta ce”Eh I’m fine” murmushi tayi ta ce”Allah ya ƙara lafiya Ina Maheer?” ” Ya tafi” Imara ta ce da sauri tana sunkuyar da kanta, da gudu ta ƙaraso zata ta ɓata tayi saurin riketa ganin yanda ta ɗora kanta kan desk idanunta a rufe ta ce”bari Nora inaga bata jin daɗi na ganta wani iri” kwaɓe fuska ta yi ta ce”Rania na ƙagu nayi magana da Katalina wlh nayi kewarta ki barni ko sau ɗaya ne nayi mata magana” girgiza kai Rania tayi tana gyara gashinta da ya rufe mata fuska ta ce” ki bari sai anjima please” numfasawa tayi ta ce”shikenan Allah ya kaimu” “Ameen”.

 

*** Tunda ta shigo gidan take zaune a fadar tayi shiru tunani ne kala-kala cikin zuciyarta jira take Maheer ya dawo ta tambayeshi amma har yanzu shiru bai shigo fadar ba, fitowa tayi tana sanya da wata riga iya gwuiwa ta gyara gashin kanta sai sheƙi yake hannunta riƙe da wayarta tana dannawa hankali kwance tana zuwa ta nemi waje ta zauna a kujera ta ɗora ƙafarta saman kujerar tana cigaba da danna wayarta da kallo Imara ta bita sai kuma tayi tunanin ta tambayeta tunda taji rannan ta fara maganar da wannan tunanin ta daga ta kalleta sai kuma ta ce”daman kince za ki faɗamin wace Katalina to ki faɗamin yanzu” tayi maganar tana langwaɓar da kanta gefe ɗaya, tamkar tana magana da kujerar gabanta haka Joda tayi mata bazaka taɓa cewa da ita take maganar ba ganin tayi mata banza ya sanya Imara ta harareta tana ala wadan hali irin nata. Tana ƙoƙarin tashi ya shigo hannunsa riƙe da wata kwalba ƴar ƙarama sai tangaɗi yake a matuƙar tsorace Imara ke kallonsa ganin yanda ya yo kanta tashi Joda tayi tana kallonsa sai kuma ta girgiza kanta da gudu Imara ta nufi stairs ganin yanda yake ƙoƙarin cimmata da sauri shima ya hau saman duk inda tayi yana bin ta, karo tayi da Ameer da yake ƙoƙarin shiga nasa apartment ɗin yana dogara sandarsa cikeda nutsuwa bayansa tashige tana kuka cikin tashin hankali take faɗin

“Dan Allah Ameer ka taimaka mini wayyo Ummana zai kasheni dan Allah Ameer!” Cikin wata murya irinta bugaggu Dameer ya ce” babu wanda ya isa ya hanani gamawa dake a wannan daren dole sai kin mutu ni ne zanyi ajalinki…” Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin yin inda take. Ƙara ta saki tana riƙe alkyabbar jikin Ameer ba tareda tasan tayi hakan ba, wata irin ajiyar zuciya Ameer ya sauke jin yanda jikinta ya haɗu da nasa ya runtse idanunsa yana jin wani abu na taso masa tun daga ƙafafunsa, baisan sanda Dameer ya fincikota daga jikinsa ba ya haɗata da jikin bango ya shaƙe mata wuya tuni idanun Imara suka firfito waje sai miƙa hannunta take hawaye na zuba daga idanun da gudu Joda tazo ta dinga dukansa amma hakan bai sa ya saketa ba saima sake shaƙeta da yayi yana wani irin cije leɓe ihun da Joda keyi ne ya sanya mutanen fadar suka jiyo da gudu kuma suka ƙaraso wajen ana masa magana amma kamar ma ba dashi ake ba.

 

Hannu ɗaya ya sanya ya fincikeshi daga jikinta ta faɗi ƙasa nan sumammiya ya juyo da fuskarsa ya wanke shi da mari har biyu bai gama buɗe idanun ba ya sake masa wani ya shaƙe masa wuya yana kallonsa da idanunsa wanda sukayi jajur dasu ganin yana ƙaƙarin mutuwa ya sanya Immi ta ƙaraso gabansu tana kallonsa cikin kwantar da murya ta ce”yi haƙuri magaji ka rabu dashi kaga ƙaninka ne sake shi” tamkar tana magana da dutse haka Maheer ya yi mata madadin ya sake shi sai ma sake shaƙesa da ya yi above 5mins kafin Ameer ya ƙaraso gabansa ya kama hannunsa bai ce masa komai ba suka bar wajen.

 

***A hankali ta shiga buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi kallon inda take a kwance tayi sai kuma ta miƙe zaune tana shafa wuyanta saboda wani raɗaɗi da taji yana yi mata ɗan turo bakinta tayi tana tuno yanda ya shaƙe mata wuya kwaɓe fuska ta yi ta ce”mugu kawai” ta faɗa tana tura baki gaba, shigowa ya yi hannayensa zube a aljihun trouser ɗin jikinsa ya tsaya a kanta yana kallonta kwaɓe fuska ta yi ta “kaga abinda ya yimin ko?” jin ya yi shiru yasa ta sake cewa “kuma da zafi sosai kamar zan mutu wayyo Allahna…” sakar baki Maheer ya yi yana kallonta ganin yanda take abu kamar ƙaramar yarinya girgiza kansa ya yi bai ce komai ba ya juya zai fita. Da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce

“Yawwa daman ina ta jiranka xan tambayeka” tsayawa ya yi ba tareda ya juyo ba tana wasada fingers ɗinta ta ce”daman yau a school ne aka dinga cemin Katalina kuma wai ya jikina? Daman ita Katalina kamar mu ɗaya? kuma itama fara ce? Tana ina yanzu? Wai batada lafiya nag…”

 

“Hyyyyy yimin shiru aku kawai kin fiye surutu karki sake tambayata wani abu kawai duk wanda ya ce miki Katalina ki amsa sannan koda wasa idan kika ce ba sunanki bane sai ranki ya ɓaci!” Ya fice daga ɗakin cikin tafiyarsa ta isa, buga ƙafarta tayi a ƙasa kamar za tayi kuka ta ce” kullum baya bani amsa wai ni ce aku?” Sai kuma tayi murmushi tana gyada kanta tuna wasu lokuta da suka shuɗe, komawa tayi ta kwanta kan gadon idanunta a buɗe tayi nisa cikin tunanin da take taga mutum tsaye a kanta cikin sauri ta tashi tana ja da baya akan gadon fuskarta a kwaɓe kamar zatayi kuka tana kallonsa zama ya yi gefen gadon har sannan idanunsa na kanta kusan 2mins kafin ya numfasa cikeda nutsuwa ya fara magana”Lolo narh! Ya jikin naki?” cikin rawar murya ta ce”naji sauƙi Ameer” jinjina kansa ya yi yana ƙoƙarin ɓoye abin da yake cikin ransa ya ce” har yanzu ina nan akan bakata ki yarda da Ameer bazai cutar dake ba, ba sai kin faɗa min ba nasan ba daɗin zama da Maheer kike ba saboda haka ki bani dama zan fitar dake daga cikin halin da kika shiga…” Ya ƙarashe maganar yana kallon fuskarta to see her reaction. Ɗan turo baki Imara tayi tana langwaɓar da kanta gefe ta ce”ka rufamin asiri Ameer wannan maganar ka daina yin ta dan Allah…”

See also  Hukuncin Allah Hausa Novel Complete

 

“Wace magana?”, Maheer ya faɗa yana shigowa ɗakin hannunsa riƙe da system, a ɗan razane Imara ta ce”bab…ba komai kawai akan abin da Dameer ya yimin ne” ajiye system ɗin hannunsa ya yi a kan wani table ya zauna gefen Ameer yana murmushi ya ce” karka damu Ameer babu abinda ya sameta ai” murmushinsa mai kyau ya yi yana kallonta ya ce”haka tace min ai” sunkuyar da kanta tayi jin zuciyarta tayi wata kyakkyawar bugawa bai sake cewa komai ba ya miƙe tsaye yana dogara sandarsa ya yi hanyar waje.

 

“Maheer ka bata shawara taso wanda ya ke sonta a rayuwa karta wulaƙantashi yin hakan babban zunubi ne” Ameer ya faɗa yana ƙoƙarin barin ɗakin, murmushi Maheer ya yi ya ce”In sha Allah Ameer”.

 

 

***Tana danna masa kansa da towel ta ce”koda wasa karka sake yin irin abin da kayi yau Dameer akan me kasan ka bugu zaka shigo gida? Sannan mene haɗin ka da ita da har kake neman kasheta? kuma dan rashin hankali a gaban kowa” ture hannunta ya yi daga kansa yana wuci ya ce”Ni Immi ki daina wani yimin faɗa dole sai ta mutu dan banason ganinta a cikin fadar nan kuma babu wanda ya isa ya dakatar dani!, sannan…”

Wasu lafiyayyun maruka Immi ta sauke masa a fuska tana kallonsa fuskarta a haɗe babu alamar fara’a ta ce”to kasani kanayin wani kuskure Udaid zata kwace maka shashasha!” Dafe kuncinsa ya yi yana kafeta da idanunsa sai kuma ya yi kwafa ya tashi ya fice daga bedroom ɗin kamar zai tashi sama.

 

JODA.

***Tsaye take jikin motarta tana sanye da English wears riga da wando ta tufke gashinta waje guda tana danna wayarta, tun daga nesa yake kallonta yana murmushi har ya ƙaraso gabanta kallonsa ta yi bata ce komai ba ta shige motar ganin haka ya sa shima ya shige ɗaya site ɗin da wani irin speed taja motar suka bar wajen, a wani restaurant tayi parking suka fito a tare ya kalleta sai kuma ya yi murmushi harararsa tayi bata ce komai ba tashige ciki hakan yasa shima ya bita sai da ta zauna sannan ta kalleshi cikin nutsuwa ta ce”ka daina yawan dariya dan Allah haba!” murmushi ya sake yi yana kallonta ya ce”oh tanan kuma kika ɓullo?” ɗan ƙaramin tsaki tayi tana kallonsa ta ce”bar wannan maganar akwai abinda yasa na kiraka kuma yanada amfani saboda haka ka saurara kaji abinda zan ce please” ganin ya bata full attention nasa ya sa tayi murmushi a karo na farko wanda ya yi matuƙar ƙara mata kyau cikin siririyar muryarta ta fara magana

“.

*Chapter 4*

 

 

 

 

“Nan da ƴan kwanaki zai dawo ƙasar nan kuma shigarsa Udaid na nufin abubuwa masu yawa, saboda haka na shirya komai kuma ina buƙatar taimakon ka, Rasheed!” Gyara zaman glasses ɗin fuskarsa ya yi yana kallonta ya ce”ina tare dake a kowane lokaci kawai ki sanar dani abin da kika shirya” wani cute smile tayi ta cigaba da magana.

 

 

 

 

***A hankali take taka stairs din benan dan gaba ɗaya a tsorace take, “Habibty” a dan firgice ta juyo ta saki wata ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta ta ce”Sabahul khair Shamma (Barka da safiya Shamma), murmushi Shamma tayi tana kama hannunta ta ce”why are you scared?” Ta marairaice fuska tana kallon Shamma bata ce komai ba, a gefenta ta zaunar da ita bayan itama ta zauna tana kallonta ta ce”kar ki saka damuwa a ranki babu abinda Dameer zai yi miki, ki cire incident din jiya a ranki kinji baby” jinjina kanta tayi hawaye na kawo idanun nata ta ce” in sha Allah Shamma” shafa kanta tayi tana murmushi ta ce”good girl” murmushin Imara ta mayar mata sannan ta tashi tsaye tana kallonta ta ce”zan tafi school” “Allah ya kiyaye” Ameen ta ce tana gyara zaman veil ɗin ta. Sound ɗin takalminsa ya sanya ta ɗago kanta tana duban inda hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗin jikinsa ya sakko fuska babu wata walwala yana zuwa ya gaisheda Shamma ta amsa cikeda fara’a bai cewa Imara komai ba ya yi waje ta bi bayansa tana murguɗa masa baki.

 

 

 

Yana ƙoƙarin shiga motarsa yaga shigowar wata baƙuwar mota hakan yasa ya tsaya yana kallon motar har tayi parking, waro idanunsa waje yayi ganin wacce ta fito daga motar sanye take da wata riga irin mai kama jikin nan wacce ta tsaya iya cinyarta fararen cinyoyinta duk sun fito waje sai gyara gashin kanta wanda ya ke ƙoƙarin rufe mata fuska take tana ganinsa ta washe baki ta tawo da gudu da niyyar shigewa jikinsa saurin matsawa ya yi yana kallonta hakan yasa ta dakata tana tsuke fuska ta ce cikin wata siririyar murya

 

 

“Haba Akhii yaushe rabon dana ganka baka missing ɗina?” tabe bakinsa ya yi yana ƙoƙarin buɗe motarsa ya ce”wane ya baki shawarar ki dawo?” watsa hannayenta tayi alamar bata sani ba ya kalleta sai kuma ya shige motarsa, Imara tabi da kallo sai kuma ta juya tabar wajen. Sun yi nisa da gida ta kalleshi ganin yanda yake tuƙinsa cikeda nutsuwa ta tura baki gaba ta ce” kuma yau idan suka min magana me zan ce?” Jin bai ce komai ba yasa ta ci-gaba da faɗin”ni wlh zan ce musu ba sunana Katalina ba kuma ni ba ƴar ƙasar nan ba ce har ƙasarmu kaje ka ce aurena zaka yi ashe kai mugu n…” Cak taji ya tsayar da motar ya juyo a fusace ya shaƙe wuyanta yana kallonta da idanunsa wanda suka gama sauya kala ya ce” kina iya aikata duk abin da kikaso a sanda kikaga dama amma ki sani Maheer bazai taɓa lamuntar tunon asiri ba dole ki ɓoye sirrin sannan kiyi abin da na ce miki ki manta da cewa ke Imara ce! Ki manta da cewa ke ba ƴar ƙasar nan ba ce! Ki manta da wata rayuwa ki sanya a ranki ke Katalina ce!! Idan kuma ba haka ba…” Ya cije laɓɓansa sannan ya hankaɗata tsananin azaba ya hana Imara furta wata kalma ta riƙe wuyanta wanda takejin kamar har yanzu hannunsa yana kai wasu zafafan hawaye ne suka shiga sakkowa kan kuncinta lokaci ɗaya kuma wani irin tari na azaba ya ziyarceta, tsawon lokacin data ɗauka a haka Maheer bai kalli inda take ba har ya yi parking a compound ɗin makarantar

 

 

“Get down!”

 

 

Abinda ya furta kenan ba tareda ya kalleta ba, cikin sanyin jiki Imara ta sauka daga motar ta shiga tafiya toward direction ɗin class ɗin su har sannan bata daina jin zafin shaƙewar da Maheer ya yi mata ba. Koda ta shiga class ta tarar har lecturer ɗinsu ya shiga hakan yasa kawai ta zauna tana sauraran abin da yake cewa duk da rabin zaman nata tunani take har ya kammala lecturen ya fita Rania ce ta kalleta tana murmushi ta ce”yau kin makara meyasa?” kallonta Imara tayi sai kuma ta kwabe fuska ta ce”bansan lokaci ya tafi haka ba” jinjina kai Rania ta yi ta ce”yanzu ya kike jin jikin naki?” lumshe idanunta tayi nan take hawayen da yake kwance cikin idanun ya zubo kan kyakkyawar fuskarta da mamaki Rania ta ce”ya Ilahi, meke damunki? ko ciwon ne? Ina ne ke miki zafi?” hannunta ta sanya ta goge hawayen sai kuma ta kalli Rania tayi murmushi cikin sanyin murya ta ce”ba komai fa I’m fine kawai wani abu na tuna” girgiza kai Rania tayi ta ce”wannan ba halin ki bane Katalina, bamu ɓoyewa juna komai dan Allah ki sanar dani abin da yake damunki kinji” ta ƙarashe maganar cikin rauni shiru Imara tayi tana kallon Rania tabbas tana buƙatar wanda zata faɗawa damuwarta, tana buƙatar wanda zata kwanta jikinsa tayi kuka amma ba Rania ba! “Imara think idan kika ce zaki faɗa mata abin da ke zuciyarki to tabbas zaki fallasa kan ki kuma Maheer ba zai kyale ki ba dole ki danne abin da kike ji kiyi kamar yanda ya umarce ki” wani ɓangare na zuciyar Imara ta faɗa mata haka, da sauri ta dafe saitin zuciyar tata jin yanda take bugawa da ƙarfi.

 

 

 

“Katalina!”, Rania ta kirayi sunanta a ɗan firgice ta kalleta sai kuma tayi murmushi tana kokarin ɓoye damuwarta ta ce”karki damu friend ina lafiya kinji babu komai” shiru Rania tayi badan ta gamsu da abin da Katalina ta ce ba.

 

 

****

 

 

*LONDON*

 

*Royal Brompton and harefield hospital specialist care*

 

*7:30pm*

 

Kwance take akan gadon marasa lafiyar, a hankali take jan cazbahar hannunta. Wata mata farar tsohuwar mata ce kana ganinta kansa ta manyanta amma kuma da gwarinta yanda take komai a nutse ne zai tabbatar da hakan, turo ƙofar ɗakin akai wanda yasa ta maida hankalinta ga ƙofar tana ganin wanda zai shigo likita ta gani hakan yasa ta ɗan tsuke fuska tana ɗauke kai murmushi kawai likitan ya yi sanin halinta ya ƙaraso gabanta cikin fara’a ya ce” how are you feeling maa?” kallonsa ta yi sai kuma ta sake ɗauke kanta tana kallon gefe, girgiza kansa ya yi ya ce cikin harshen turanci” zan miki allurar yanzu” da sauri ta kalleshi sai kuma ta galla masa harara cikin wata kamilalliyar murya ta fara magana da larabci

 

“Ya Ilahy, wane ya ce maka bani da lafiya? A’a ni nasamu sauƙi Ana-bikhair Shukran laak” ta haɗe hannayenta alamar godiya. Daman ya rigada yasan haka zata yi yasa ya yi murmushi kawai ya ce”I’m sorry maa dole a miki kodan lafiyarki” wangale baki tayi tana kallonsa sai kuma ta ce” yau naga abin da ya isheni to na ce na warke ai sai a barni haka ko kuma…” Shiru ta yi da maganar ganin ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo jin takun tafiyarsa ya sanya doctorn yin murmushi ya juya ya kalleshi, sanye yake da wata riga t-shirt fara jikinta da stickern hoton Damisa sai wani cargon 3-quater black colour sai canvas fari a ƙafarsa yanada tsayi sosai haka kuma yanada faɗi yanayin jikinsa zaka kalla kasan ma’abocin gym ne saboda yanda duk wani ƙashi na jikinsa yake a murɗe kallo ɗaya ya yi musu ta tsakanin gashin da ya rufe fuskarsa sai kuma ya ɗauke kai yana gyara zaman Bluetooth ɗin kunnensa ya shiga takawa har wajen window ɗin ɗakin da alama waya yake da wani. Ganin ya juya musu baya yasa ta yafito likitan da hannu cikin ƙasa da murya ta ce”kaga wannan azababben ya zo dan Allah ka tafi idan ya fita zan nemeka da kaina kaji”

 

 

“Min Fadlhik(Excuse me)”

 

 

Tsit tayi shiru da bakinta tana kallonsa ganin har sannan wayarsa yake yasa ta sake kallon likitan ta ce”ka ji yaro” jinjina mata kai ya yi sannan ya juya zai fita, “wait” ya faɗa yana juyowa murmushi doctorn ya yi yana kallonsa ya ce”sir You need something?” bai ce masa komai ba ya zauna gefen gadon yana ƙarewa hannunta kallo above 2mins kafin ya buɗe bakinsa cikin cool voice ɗinsa ya ce” zo ka mata injection ɗin” da sauri ta kalleshi sai kuma ta hade ranta tana huci ganin haka yasa likitan ya dawo har ya yi mata allurar ba ta ce komai ba sai kallo da ido tana ganin ya fita ta bisa da harara.

See also  Zuciya Kowa Da Irin Tasa Hausa Novel

 

 

“Da kin daina harararsa Jadda tunda bashi ya sa kansa ba” a fusace ta ce”koma wane ya saka shi ya je shi da Allah babu wanda zai dinga cutata yana azabtar dani wlh” jin ya yi mata shiru yasa ta yi kwafa ta ce”tunda ga mahaukaciya na magana dole ayi min shiru to uwarka Fateymarh ita ka yiwa shiru ba ni ba” tamkar tana magana da gadon da take kai haka ya yi mata daga ƙarshe ma ya tashi ya fice daga ɗakin, girgiza kanta ta yi cikin faɗa ta cigaba da magana ” yaro sai shegen miskilanci da jin kai wai shi wani wannan matarsa ta shiga uku a wajensa wai KA SAUYA HALI!” Jadda ta faɗa tana cigaba da jan cazbahar hannunta.

 

 

 

Kai tsaye office ɗin likitan ya shiga bayan ya zauna doctorn ya kalleshi fuskarsa ɗauke da fara’a ya ce cikin harshen turanci” she’s getting better yanayin jikinta ya nuna tana samun sauki sosai” shiru ya yi for some second sai kuma ya numfasa “zuwa yaushe za’a iya discharging nata?” Ya faɗa yana miƙewa tsaye, “maybe by next week” jinjina kai ya yi ya juya ya fice daga office ɗin yana wata irin tafiya mai nuni da isa.

 

 

 

*UDAID*

 

 

Murmushi Shamma tayi tana kallonta ta ce”shine kika dawo?” kwaɓe fuska tayi ta ce”wlh Shamma na gaji akwai wahala sosai acan shiyasa na dawo kuma wai ina Ameer?” bata rufe bakinta ba ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama, da gudu ta tashi tana zuwa ta shige jikinsa tana dariya shafa kanta ya yi da murmushi a fuskarsa ya ce”kaifa-al-hal?(ya ya kike?)” tana sake riƙe shi ta ce” Ana-bikhair Ameer” jinjina kansa ya yi sannan ya janye ta daga jikinsa, akan royal cushion ɗin dake parlon ya zauna ya lumshe idanunsa, kallon Shamma tayi sai kuma ta sake kallonsa ta zauna gefensa da mamaki ta ce”Shamma Ameer bashida lafiya ne?” numfasawa Shamma tayi tana kallonta ta ce”nima bana ce ba Maha haka kullum yake yanzu kamar akwai abin da yake damunsa” hannunta na dama ta ɗora akan fuskarsa ya yi saurin sakin ajiyar zuciya yana buɗe idanu, sosai ta ji zafi a jikinsa hakan yasa ta kwaɓe fuska tana kallonsa ta ce”Ameer ka je asibiti kuwa?” jin ya yi shiru yana kallonta yasa ta cigaba”ka ji jikinka akwai zazzaɓi please ka je asibiti ko a kira doctor ya duba ka?” tayi maganar tana sake kallonsa. Ɗan murmushi ya yi yana jan kumatunta ya ce” ina lafiya fa” turo baki tayi tana kallonsa ta ce”a’a ni dai ka shirya gobe muje asibiti” jinjina mata kai ya yi bai sake cewa komai ba ya tashi ya bar parlon. Da kallo ta bishi har ya shige apartment ɗinsa sannan ta kalli Shamma dake zaune har sannan ta ce”Shamma wai ina Akhii?” murmushi ta yi ta ce” bai shigo ba har yanzu” taɓe baki tayi ta ce”wacce na gansu tare ita ce matar tasa?” gyaɗa mata kai Shamma ta yi, tayi murmushi ta ce”she’s beautiful” girgiza kai Shamma ta yi saboda sanin surutun Maha kawai ta tashi ta bar wajen. Tana tashi Joda ta fito hannunta riƙe da system ɗin ta as usual kallo ɗaya Maha ta yi mata ta ɗauke kai dan ko kaɗan basa shiri itama Jodan zamanta tayi wajen kamar batasan da mutum a gurin ba, above 5mins kafin Maha ta tashi zata bar wajen har tayi gaba sai kuma ta dawo tana kallon Joda ta ce cikin harshen larabci

 

“Ina mai baki shawara ki gyara ɗabi’unki tun kafin lokaci ya ƙure miki, akwai lokuta da dama da bamu gane masoyanmu da kuma maƙiyanmu musamman idan mutum ya kasance yana rangwamin sanin ya kamata kamar dai ke ɗin nan. Ki sani lokaci na nan da za kiyi danasanin abubuwan da kika aikata kuma danasani mara amfani, it’s better for you to change your attitude or else…” Ta juya fuu ta haye sama. Sai a sannan Joda ta ɗago idanunta wanda suka kaɗa sukayi jajur tabi bayanta da kallo wani irin tafarfasa zuciyarta ke yi tashi tsaye tana sake duban inda Maha ta yi sai kuma ta daki glass table ɗin dake gabanta nan take ya tawarwatse hannunta ya fashe kallon fararen hannunta wanda suka jiƙe da jini tayi sai kuma ta fasa wata irin ƙara ta zube a wajen sumammiya.

 

 

 

***Zaune ta sameshi a gefen gado ya jingina da jikin fuskar gadon idanunsa a rufe amma ba bacci yake ba, zama tayi gefensa ta kama hannunsa ta riƙe, buɗe runannun idanun nasa ya yi yana kallonta sosai abun ya bata mamaki dan ta daɗe bata ga Ameer cikin irin wannan yanayin ba, cikin sanyin murya ta ce”yallaɓai idan da abin da ke damunka ka sanar damu ko zamu iya maka maganinsa, idan kuma ba zamu iya ba mu tayaka da addu’a amma wannan damuwar bata dace da mai irin Shekarunka ba” da idanu kawai Ameer ya bita ganin hawaye na zuba a idanunta, hannunsa ɗaya ya sanya ya jawota gefensa ya riƙe haɓarta yana kallonta sai kuma ya yi murmushi yana girgiza mata kai da sauri ta shige jikinsa tana fashewa da kuka, shiru Ameer ya yi mata yana jin yanda take kukan. Saida tayi shiru dan kanta sannan ya ɗago fuskarta ya goge mata hawayen cikin kamilalliyar muryarsa ya fara magana

 

“Zan so a ce kunada damar warwaren matsalata da nafi kowa son na sanar daku, saidai abin da ke cikin raina ya shige tunanin mai tunani. Saboda haka ku tayani da addu’a kawai” kallonsa Shamma tayi sai kuma ta girgiza kanta tana kallonsa ta ce”.

 

 

 

# *Imara*

# *Lolo*

# *Joda*

# *Nanameera*

# *Fashion gurl*

*Chapter 5*

 

“Wace irin matsala ce da har zata gagara sanar da iyalinka?, Ameer kodan lafiyarka ka daure ka sanar mana, kowa ya damu a fadar nan, ka daina walwala kullum saidai kana ɗaki why?” Ta ƙarashe maganar cikin rauni. Bai ce komai ba ya sanya hannunsa ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya fice daga ɗakin hannunsa goye a bayansa, baki buɗe ta bisa da kallo har ya ɓacewa ganinta a hankali ta miƙe tsaye ta shiga zagaye ɗakin tana saƙe-saƙen wasu abubuwa a ranta. Library ɗinsa ya nufa dan akwai muhimman abubuwan da yakeson gabatarwa duk da baya jin daɗin jikinsa. Akan wata royal cushion dake gefensa ya zauna hannunsa riƙe da Alqur’ani mai girma, a hankali fuskarta ke yi masa gizo akan idanunsa yana hango ɗan siririn bakinta wanda take masa tsiwa dashi, saurin runtse idanunsa ya yi a hankali ya ɗora hannunsa bisa ƙirjinsa yana jin yanda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.

“Astgfirullah!”

Shine abin da ya samu damar furtawa yana sake rufe idanunsa a karo na babu adadi, above 10mins yana zaune a wajen ba tare da ya samu damar aiwatar da abin da ya kawo shi ba, kwakwalwarsa gabaɗaya ba a wajen take ba, tunaninsa da zuciyarsa sun karkarta zuwa gare ta.

****

*Al-Udaid Kingdom, North part, backyard*

*9:30pm*

JODA

Tsaye take ta jingina da jikin wani bango, sanye take da wata riga t-shirt milk colour sai wandon jeans Blue colour gashinta ya zubo ta gefen kafaɗarta, idanunta maƙale cikin glasses black colour mai ɗan faɗi, yanayin wajen ya taimaka wajen ƙarawa backyard ɗin kyau. Furzar da iska ya yi daga bakinsa yana kallonta cikin harshen larabci ya ce” ?Limadha tanẓur ilayya (Meyasa kike kallona?”. Finger ɗinta ta sanya ta ɗan janye glasses ɗin fuskarta ya dawo kan tsinin hancinta tana kallonsa da sexy eyes ɗinta ta ce cikin harshen turanci” like how? (Kamar yaya kenan?” ɗan basarwa ya yi sanin halinta ya yi murmushi har saida beauty point ɗinsu suka loma ya ce” just move on ” jin tayi shiru yasa ya ce”yanzu mene ne plan A?” Kyakkyawan murmushi Joda tayi ta ɗan cije lips ɗinta ta ce”zan tura maka later ” jin jina kansa ya yi yana kallonta ya ce” shikenan ina jiranki ” . Juyawa yayi ya fara tafiya hannayensa zube cikin aljihu.

“Rasheed!”

Juyowa ya yi yaga bashi take kallo ba sai ya zuba mata idanu, “Kun hadhiran (Ka kula)”, ɗan murmushi ya yi wanda ya fito da zallar kyansa ya ce “then you care about me?” Wani kallo ta watsa masa sai kuma ta juya tabar wajen, girgiza kansa ya yi yana jinjina hali irin na Joda kafin ya juya ya tafi shima.

 

*** Zaune take gefen gadon ta zuba uban tagumi, tunani ne kala-kala cikin ranta gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta nema take ta gaza ɗaukan abubuwan dake tunkaro ta, dole ta nemawa kanta mafita. Agogon dake maƙale jikin kusurwar ɗakin ta kalla, 9:45 ta gani a jiki ta sauke idanunta ƙasa tana tunanin wani abu, mene makomar aurenta?, me Maheer yake nufi da ita?, wacece ita a wajensa?. Rashin sanin amshoshin tambayarta ya sanya ta fashe da wani raunataccen kuka ta kwanta kan gadon ta ƙanƙame pillow tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, kuka ne wanda yake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta, kuka ne wanda yake fassara how sad she is, kuka ne irin kukan komai ya ƙare mata. Meyasa sai ita?, Meyasa ƙaddararta ta zaɓa mata haka? Yaushe zata yi farin ciki?

 

“Sanda kika aminta da Ameer matsayin mai sonki, sanda kika yarda da soyayya da kuma ƙaunar da nake nuna miki, sanda kika buɗe zuciyarki har ta karɓi saƙon da Fahad ke aiko mata a kowace rana, ki yarda dani Lolo, ki ƙaunaceni kamar yanda nima nake ƙaunarki na faɗa kuma zan sake faɗa, billahil-azeem nafi Maheer sonki, ni ne na dace dake ba Maheer ba, ki karbi soyayya ta hannu bibbiyu nayi miki alƙawarin farin ciki mara yankewa, zan zame miki garkuwa, zan baki farin ciki, zan kula da lamuranki, zan tsaya miki. Ki karbi ƙaddarar ki yanda take, ni ne ƙaddarar ki IMARA!”

Ameer ya faɗa yana ƙarasa shigowa ɗakin hannunsa riƙe da sandarsa as usual, a firgice ta ɗago tana kallonsa da idanunta wanda suka yi jajur, ta miƙe tsaye tana goge hawayen da suka mata caɓa-caɓa a fuska ta fara magana;

“Eh, tabbas!, tabbas kai ƙaddararta ne, irin ƙaddarar da kowane bawa yake rokon ubangiji ya kareshi daga gareta, irin ƙaddarar da idan ta gaba to ka take hanaka bacci, ka zame mini ƙarfen ƙafa Ameer!, wlh zuciyata gab take da bugawa idan har ka cigaba da furta irin waɗannan kalaman masu muni a gareni, kanada ilimi, sanin ya kamata, nutsuwa ta zuci data zahiri amma shaiɗan ya rinjayi zuciyarka, ka kasa gane abun da yake daidai da kuma wanda yake ba daidai ba.” Durƙusawa ƙasa tayi ta haɗe hannayenta waje ɗaya alamar roƙo tana kuka ta cigaba da faɗin;

See also  A Jininsa Yake Hausa Novel Complete

“Dan girman Allah, dan darajar Annabi, dan alfarmar iyayenka ka manta dani cikin rayuwarka, ka cire wannan tunanin daga cikin ranka, wlh babu kyau ko kaɗan nifa matar Maheer ce, sirika nake a gurinka. Ka taimaka Ameer! Ka taimaka min. Ta zube a ƙasa tana sake rushewa da wani sabon kukan kamar ranta zai fita, tun da ta fara magana Ameer ke kallonta a hankali kuma yake lumshe idanunsa, gefen gadon ya zauna ya dafe saitin zuciyarsa jin yanda take bugawa da ƙarfi. Above 5mins babu wanda ya ce wani abu a cikinsu, a hankali kuma ta fara rage sound ɗin kukan nata sai ajiyar zuciya da take ta saukewa, miƙewa tsaye ya yi ya fara takawa cikin tafiyarsa ta isa ya ƙaraso gabanta. Sunkuyawa ya yi yana kallonta for some seconds sai kuma ya sakar mata kyakkyawan murmushi, saurin ɗauke idanunta tayi tana runtse su saboda yanda taga ya yi mata wani irin kwarjini. Ya ɗauki mintuna akanta kafin ya tashi ya fice daga ɗakin ba tare da ta sani ba.

 

Washegari.

Tana ƙoƙarin sanya takalmin ta ya shigo ɗakin, fuskarsa a ɗaure babu alamar fara’a, kallo ɗaya Imara tayi masa ta cigaba da abin da take. Saida ta kammala sanya takalmin wanda yake canvas white colour sannan ta tashi tsaye, hang bag ɗinta ta ɗauka ta ratsa ta gefensa zata fita taji ya janyota, gabansa ya dawo da ita fuskarsa dab da tata, kallonta ya shiga yi frm head to toe sai kuma ya wani yatsine fuska bai ce komai ba ya kama hannunta suka fita daga ɗakin.

 

***Gaba ɗaya jama’ar gidan sun hallara wajen cin abinci, babu abin da ke tashi sai ƙarar spoons da knives, “Ayn Jūdā? (Ina Joda?),” Immi ta faɗa tana sake ɗaga kanta, murmushi Dameer ya yi ya ce” Maybe akwai mutanen da bata son gani yasa bata fito ba.”, duk suka ɗago suka kalleshi, Shamma ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba ta ture plate ɗin hannunta ta tashi ta bar wajen.

“Dameer!”

Cikeda ladabi ya kalli Ameer ya ce” Na’am Ameer”

” La tuḥāwilu abadan mā faʿaltahu al-ān (Karka sake irin haka)” cewar Ameer yana tashi tsaye, cikeda ladabi Dameer ya ce ” in sha Allah”. Bai sake kallon kowa ba ya bar wajen. Miƙewa Immi tayi tana kallonsa ta ce”ka sameni a ɗaki” okay ya ce sannan y tashi yabi bayanta. Tsaye ya sameta tana kai kawo cikin ƙaton parlon dake cikin part ɗinta, da idanu ya bita ganin kamar hankalinta ba a kwance yake ba yasa ya ce “what’s going on Immi?” dafe kanta tayi ta ce”Dameer abubuwa na gab da lalacewa, UDAID na gab da barin hannun mu, sirrin da na daɗe ina ɓoyewa nason fitowa fili.” Ɗan murmushi ya yi yana girgiza kansa ya kamo hannunta ya riƙe cikin nasa cikin son kwantar mata da hankali ya fara magana

“Haba Immi, wannan ba abu bane mai yiwuwa, nayi miki alƙawarin yin duk wani abin da ya kamata wajen ganin na cika burinki, saboda haka ki kwantar da hankalinki”. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta gyaɗa masa kai ba tareda ta ce komai ba.

 

*SHAMMA*.

“Ƴaƴana?, Ƴaƴana?, ku ba Yarana bane!, wlh dana riƙe ku matsayin ya’ya gara na mutu na bar duniyar, koda wasa bana ƙaunarku, tunda har kun zaɓeta matsayin uwa to nima na haƙura na sallama mata ku, ta raine ku, ta baku kulawa, amma har abada babu ni babu ku!”

 

“Shamma dan Allah kar kiyi haka, ke uwace nasan kina son mu, karki bari a rabamu dake, ki jiƙanmu a matsayin mu na yayanki, dan Allah Shamma, karki ji mata ciwo ki taimaka Shamma!” A fusace ta riƙo hannun ƙaramar yarinyar da bazata shige 4-5yrs ba ta hankaɗata, wata razananniyar ƙara yarinyar ta saki dalilin tafasasshen ruwan heatern data zubo a jikinta, da gudu yaron ya saki hannunta ya ƙarasa wajen yarinyar ya shiga jijjigata saidai duk inda ya cire hannunsa sai fatarta ta biyo hannunsa ganin haka yasa ya saki wata irin ƙara, nan take idanunsa suka kaɗa suka yi jajur tamkar gauta, jijiyoyin kansa suka firfito. Tamkar wanda aka zabura haka ya miƙe tsaye naman jikinsa na wani irin rawa wacce ke nuni da ɓacin ran da yake ciki, hannunsa ɗaya ya sanya ya tattare gashin da ya rufe fuskarsa ya maƙaleshi gefen kunnensa, ya kafeta da manyan idanunsa bakinsa na rawa.

 

“Shamma! Shamma!”, girgiza kai Maha tayi ta ƙaraso gabanta ta dafata, a firgice Shamma ta ɗago kanta tana kallonta, sai kuma ta ɗauke idanunta tana ƙoƙarin ɓoye hawayen dake cikin idanun. Zama Maha tayi gefenta cikeda damuwa ta ce “Shamma something went wrong with you but you couldn’t tell anyone why?” Kyakkyawar fuskarta ta larabawa Shamma ta kalla sai kuma tayi murmushi ta ce cikin harshen larabci ” karki damu baby, ina lafiya” girgiza kai Maha tayi ta ce”shikenan Allah yasa haka ne” “Ameen ya rabbi” Shamma ta faɗa tana kaƙalo murmushi. Tashi Maha tayi ta ce”daman fita zanyi shine nazo na faɗa miki saina dawo bye” hannu kawai Shamma ta ɗaga mata dan batajin zata iya cewa wani abu ta fice daga ɗakin. Tana fita Shamma ta ɗora kanta gefen pillow ta fashe da wani sabon kukan mai cin rai tana nadamar abubuwan da suka faru a baya.

*Education City, Doha, Qatar*
_DOHA INSTITUTE OF GRADUATE STUDIES (DI)_

 

3:30pm.

Zaune suke cikin capteria kowa na duba abinda zai yi order, ganin hankalinta gaba ɗaya baya wajen yasa Rania ta taɓa ta, a ɗan firgice ta kalleta sai kuma ta sakar mata murmushi tana murza idanunta wanda yayi jajur dashi, ajiye Menu book ɗin Rania tayi ta juyo tana fuskantar ta ta ce cikin harshen larabci “Katalina meke damunki?, tunanin me kike?, me yake hanaki bacci naga idanunki sun koma haka?” Rania ta jero mata tambayar tana kafeta da manyan idanunta, kasa cewa komai Imara tayi kawai sai ta faɗa jikinta ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Dafa kanta Rania tayi bata ce komai ba, saida ta barta tayi kukan mai isarta sannan ta fara sakin ajiyar zuciya a hankali tana shassheƙar kuka, ɗago fuskarta Rania tayi tana kallonta ta ce”now tell me what wrong with you?” Ɗan murmushi Imara tayi tana goge hawayen idanunta ta ce”babu komai fa, kawai na tuna wani abu ne shikenan.” Baki buɗe Rania take kallonta sai kuma ta girgiza kai

“Me kika tuna da yake sanya ki kuka?, ko shikenan Allah yasa hakane abinda kika faɗa”
Jinjina mata kai Imara tayi ta ce”hakane ma” ta faɗa tana lumshe idanunta. Shiru suka ɗauka na wasu sakkani kafin Imara ta sake kallonta ta ce”can I ask you friend?” “Why not?” Rania ta bata amsa tana kallonta with full attention. Numfasawa Imara ta yi sai kuma ta ce cikin harshen larabci” inada wata friend so tana cikin matsala nikuma na kasa bata shawara shine nake neman taimakon ki ki bani shawara ” jinjina kai Rania ta yi, Imara ta cigaba da faɗin”zan baki ɗan labarin abin da ke damunta sai ki bani shawara Please”.

 

Tunda Imara ta fara magana Rania ke bin ta da kallo irin na mamaki, da daɗe bataji abin da ya gigita mata lissafi ba irin wannan, wane irin son zuciya ne wannan?, wace irin duniya muke ciki ne? Inna’lil lahi wa ina ilayhi raji’uun, shine kawai abin da take iya furtawa gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Ganin yanda tayi yasa Imara tayi murmushi tana taɓa ta ta ce ” karki damu kanki fa, kawai shawara nakeson ki bata” numfasawa Rania tayi tana kallonta ta ce

“Imara na daɗe ban ji abin da ya bani tsoro ba irin wannan, kuma da gaske nufi yake ta rabu da ɗansa?” Jinjina mata kai Imara ta yi ta cigaba da faɗin;

“Shawara anan shine kawai ta cigaba da addu’a even through nasan tanayi but ta ƙara, na biyu kuma tana iya using wannan opportunity ɗin wajen ganin ta samu amsar tambayar da take nema, I mean ta tambaye shi wasu abubuwa game da mijinta da kuma matar da yake magana akai, ta nan ne zata gane abin da mijin ke ɓoye mata da kuma wanda ya faru a baya. Idan tayi haka zata iya gano bakin zaren daga nan sai ta yankewa rayuwarta hukunci dan wannan ba ƙaramin al-amari bane!”

 

Murmushi Imara tayi ta ce”yawwa Friend Nagode sosai in sha Allah nima zan sanar da ita Allah yasa a dace” Ameen ya rabbi Rania ta ce sannan suka cigaba da duba abincin.

 

 

 

***Zaune yake gefen gadonsa idanunsa maƙale akan wani Enlargement na hoto ya zuba mata idanu, fuskar dake jikin hoton sak Imara babu abin da ya raba su. Yanayin shigar dake jikinta ne kawai ya bambanta domin ita wannan ƙananun kaya ne a jikinta gashin kanta kuma a buɗe babu veil.

Da gudu ya ƙarasa sauka daga saman yana tafe yana ture mutane, can ya hango su suna tsaye kana ganinsu kaga ɗalibai, ajiyar zuciya ya sauke sanda ya hangeta fuskanta a sake sai murmushi take, tana ganinsa ta saki murmushi da gudu ta tawo ta shige jikinsa, murmushin shima yake ya riƙeta gam, sun jima a haka kafin ta sake shi tana kallonsa ta ce cikin cool voice ɗinta “you kept me waiting” ta faɗa tana tura baki gaba, hannunta ya kama ya riƙe cikin nasa yana dariya ya ce “I’m sorry na tsaya duba patient ne” langwaɓar da kai tayi ta ce” shikenan kaje sai mun haɗu anjima”

“Really?”

Jinjina masa kai tayi ya bata peck a goshi sannan ya juya zai bar wajen.

“Maheer!”

Juyowa ya yi jin tayi kiran sunansa abin da ya daɗe bai ji ba a rayuwarsa, ɗaga mata gira ya yi ya ce”what?” Murmushi tayi har saida beauty point ɗinta ya loma ta ce” don’t forget with me, I love you” yanda tayi maganar jiki a sanyaye ya sanya yayi murmushi ya gyaɗa mata kai

“Har abada Peanut”, murmushi ta saki ta ɗaga masa hannu alamar bye shima ya mayar mata sannan ya juya ya shige motarsa.

 

“PEANUTTTTT…”

Ya faɗa a fili yana shafa hoton, ɗumin da yaji a fuskarsa ya tabbatar masa da cewa kuka yake kuma daman ya cancanci ya yi kukan, he missed her, ƙaunar da yakewa Katalina daban take a cikin zuciyarsa amma ta tafi, she left him without even say goodbye to him, why? Why???.

 

“Saboda baka yi deserving rayuwa da ita ba, kanada son kanka, kana fifita buƙatarka akan ta wani, kana iya salwantar da wani abu matuƙar kai zaka samu biyan buƙata, you are too selfish Maheer!”

 

# *Bestnovel
# *Nanameera
# *Imara
# *2025.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top