Ina So Hausa Novel
INA SO
*LITTATTAFAINA*
*FATIMA ZAHRA SA’EED*
*RANA DAYA TAK!!!*
*JARIRAI*
*SIDDABARU*
Da sunan Allah mai Rahama
mai jin kai.
Allah ka yi salati ga shugaban halitta Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wa’sallim.
*GODIYA*
Ta tabbata ga Allah buwayi da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi mai suna INA SO… Ina rokon Sa ya sa in fara lafiya in gama lafiya amin.
*YABAWA*
Ga yayata daya kwal a duk cikin tarin marubuta, wato Nana Aisha Hamisu Abdullahi, Allah ya dafa miki amin.
1/2
A gurguje Halima ta shiga bayi ta watsa ruwa ta fito ta shige ɗakinta, atampa ta zaɓo cikin kayanta ta sanya, ta ɗora zumbulelen hijabinta a sama sannan ta kawo niƙab ta yafa. Baƙin tabarau ɗinta dake ajiye a saman drawer ta ɗauko ta sakaye idanunta, sannan cikin sauri-sauri ta ɗauki agogo ta ɗaure tsintsiyar hannunta na hagu da shi.
Wayarta da ‘yar karamar jakarta ta hannu na yashe a saman katifarta ta sunkuya ta ɗauka sannan ta zura takalmanta marasa tudu da suka sha wanki da mai sai sheƙi suke yi.
Ta fito daga ɗakin a hanzarce, daidai lokacin Umma ita ta fito daga ɗakinta, tsayawa ta yi tana ƙare mata kallo.
“Da gaske dai wai Halima ba za ki tsaya ki karya a gida ba?”
Sake duba agogon hannunta ta yi, ƙarfe takwas har da mintuna uku, ta girgiza kai. “Umma lokaci ya ƙure sosa, takwas har ta wuce, gwara in tafi da breakfast ɗin na ci a can, in na ce zan tsaya ci lokaci zai ƙara ƙure min, na san kafin in je ma sai wajen takwas da rabi.”
Gyaɗa kai Umma ta yi cikin sallamawa ta ce. “Shikenan na sa Auta ma ta haɗa miki komai a cikin kula, bari in ɗauko miki.” Ta juya ta koma ɗakin, jim kaɗan ta fito riƙe da wata madaidaiciyar kula ta miƙa wa Halima.
Cikin girmamawa Halima ta karɓa tare da yi wa Umma sallama. “Na wuce Umma.”
“To Allah ya tsare ya ba da sa’a.”
“Amin Umma na gode.”
“Kar ki manta ki yi addu’a kafin ki fita.”
“In sha Allah Umma.”
Ta fice tana sauri.
Allah da ikonSa ba ta sha wahalar samun abin hawa ba, tana tsallaka titi mai adaidaita na tsayawa, matar da take ciki ta sauka ita kuma ta hau ta yi masa bayanin inda za ta sauka.
Duk gudun da mai adaidaita sahun yake yi sai take ganin kamar tafiyar kunkuru ake yi, ji take kamar ta yi fiffike ta tashi ta isa inda take son zuwa kafin ta ƙara makara sosai.
Tun kafin a ƙarasa gurin ta zaro adadin kuɗin da za ta biya mai adaidaita ta riƙe a hannunta, Allah ya taimake ta canji ne a hannunta don haka tana sauka ta miƙa masa ta gaggauta tsallakawa ta nufi katafaren gingimemen shahararren babban kantin da babu ce kawai ba a sayarwa a cikinshi.
PRINCE ALI HADI KARMA SHOPPING MALL shahararren kanti wanda kusan kaf faɗin jihar nan babu wani kanti da ya kai shi girma da kawo kaya na gani a faɗa, suna da manyan rassa a garuruwa daban-daban cikin faɗin jihar nan. Amma wannan shi ne babban shalkwatarsu.
Cikin saurin da ta kwaso tun daga gida ta isa cikin kantin bayan ta gaishe da securies. Tun daga ƙofar shiga ta fara shan jinin jikinta sakamakon abin da idanunta suka gane mata, gabanta ya ɗan faɗi kaɗan, ta shiga waige-waige da hange-hange daga nan inda take a tsaye.
Ba komai ne ya saka ta shiga wannan yanayin ba face ganin dukkan ma’aikatan kantin a tattare a waje ɗaya, gabansu kuma wani matashi ne zaune a kan kujera ya tasa su a gaba.
A ‘yar tsayuwar da ta yi ta ga ma’aikatan sun fara gabatar masa da sunayensu da kuma matsayin aikin da suke yi a kantin, duk wadda ko wanda ya faɗa sai ya ba shi umarnin ya wuce.
Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke sannan a hankali cikin ɗari-ɗari ta fara taku zuwa ciki. Kafin ta ƙarasa ta ƙara tsayawa gabanta na faɗuwa, ta soma addu’a a cikin ranta. Karaf ta ji muryar wata abokiyar aikinta ta yi mata magana da cewa.
“Ki ƙaraso mana Sadiya!”
Wannan magana ita ta saka ta zabura da sauri ta taka ta ƙarasa, shi kuma saurayin da sauri ya yi wani irin juyi don ya ga wadda aka yi wa maganar.
A hankali idanunshi suka sauka a kanta, mamaki ya kama shi nan take sakamakon yanayin shigar da ya gani a jikinta. Kafin kowa ya yi magana tuni ya buɗe nashi bakin da muryarshi mai karsashi ya ce.
“Ke kuma fa?”
Kasa yin magana Halima ta yi, sai wannan abokiyar aikin tata mai suna Ladidi ce ta yi saurin cewa “Ranka ya daɗe ita ma ma’aikaciya ce, ita ce sabuwar cashier.”
A zabure ya ƙara kai dubanshi gare ta, sama da ƙasa ya fara kallon ta, ya zare baƙin gilashin dake idanunshi tare da miƙewa tsaye, agogon hannunshi ya duba sannan ya ɗago ya sake tsare Halima da kallo da daskararrun idanunshi masu matuƙar sanya tsoro a zuciya.
“Sai yanzu kike zuwa aiki? Ƙarfe nawa agogonki ya ce?”
Da sauri ta duba agogon hannun nata, Tara saura mintuna uku. Ta yarfe hannaye. Duk da ba ta san kowaye shi ba da matsayin shi a kantin amma a abinda idanunta suka gani ya tabbatar mata lallai mai naira shi yake luntsuma hannu ya ɗauko alkakin ƙasan kwano, don haka ba ta san lokacin da ta fara zuba ba.
“I’m sorry Sir. Makara ba ɗabi’ata ba ce, yau ma matsala aka samu ne, ina roƙon a yi min afuwa…” Ta ƙare maganar da ajiye kular abincinta sannan ta haɗe tafukan hannayenta biyu ta ɗora su a saman haɓarta, alamun roƙo.
Kallon ta kawai yake yi har ta gama, ya ƙara ɗaure fuska tamau ya ce. “Tabbas na san irin ku masu wasa da aiki da ƙin bin dokokin aiki… Saboda irin ku dama na dawo ƙasar nan don in ga yadda kuke tafiyar min da dukiyar mahaifi, ga shi a karon farko na fara kama ki da laifi.”
Halima ta ƙara rikicewa ta shiga roƙon shi tana tabbatar mishi wallahi kowa zai ba da shaidar ba ta makara, sannan in an duba register duty ta kullum ma za a gani ba ta makara.
Matse kafaɗa ya yi cikin halin ko’inkula ya ce shi sam wannan bai dame shi ba, shi dai ya kama ta da laifi kuma kar ta kuskura ya sake kama ta a karo na biyu.
Cike da murnar ta kuɓuta ta juya da sauri da nufin isa mazaunin aikinta, kwatsam ta ji ya daka mata tsawa.
“Dawo ban sallame ki ba!”
Ta koma ta tsaya cikin matuƙar jin haushi, tun tafiya ba ta yi nisa ba ta fara jin haushin gayen nan, haka kawai tana aikinta lafiya-lafiya zai zo ya fara kawo mata tarnaƙi.
Sai da ya gama sallamar kowa saura ita kaɗai, jikinta sai ɓari yake don ba ta san me zai kuma ce mata ba.
Ya waiwayo gare ta sosai.
“Cire wannan glasses ɗin da wannan abin da kika saka a fuska.”
Gabanta ya faɗi sosai yadda har sai da ta ji zafi a ƙirjinta saitin zuciyarta. Nan da nan ta fara karanto Innalillahi da hasbunallahu tana maimaitawa.
Ganin har kamar mintuna biyu da ba ta umarnin da ya yi kuma ba ta cika ba ya sa ya ƙara ɗaga murya.
“Cewa fa na yi ki cire wannan glasses ɗin da wannan abin munafurcin da kuke rufe fuska da shi ku ba larabawa ku ba ‘yan tawaye ba!”
Hawaye ta soma ji na taruwa a idanunta, muryarta da rauni sosai ta yi ƙasa zuwa gwiwoyinta.
“Ka yi hakuri don girman Allah, ba zan iya cire glass da niƙab ɗin fuskata ba, a haka aka yarda aka ɗauke ni aiki a haka kuma nake aikin… Ina roƙon don son da kake yi wa mahifinka kar ka matsa min a kan sai na cire…”
Duk suka yi shiru, ita tana haɗiyar kukan da ke ta hanƙoron taso masa shi kuma mamakin furucin nata ne ya kashe shi.
Suna a wannan yanayi har tsawon wasu daƙiƙu, miƙewa ya yi daga kan kujerar da yake zaune ya taka ya isa gabanta.
“Kina iya tashi ki tafi.”
Tuni ta miƙe cikin sauri ta fara tafiya.
“Wannan ba naki ba ne?” Ya faɗa yana nuna kular da ruɗewa ta saka ta mantawa da ita. Ta dawo da sauri ta ɗauka ta bar gurin.
Ya ɗan jima a tsaye a nan yana aika mata kallo inda ta je ta zauna, gaba ɗaya jikinta ya gama yin sanyi ta kasa kataɓus ɗin komai sai kame-kame da danne-dannen computer take yi.
Kiran wani masinja ya yi ya sa shi ya janye kujerar da ya zauna shi kuma ya nufi escalator ya hau zuwa sama ofishin manaja.
Manajan ya tashi da sauri ya miƙa masa gaisuwa.
“Barka da shigowa ranka ya daɗe!”
“Yawwa Malam Jafar.”
“Bismilla ga guri ka zauna.”
Bayan ya zauna ya dubi manaja. “Akwai wata ma’aikaciya cikin ma’aikatan nan wadda take aiki da fuska a rufe?”
Gyaɗa kai Malam Jafar Manaja ya yi. “E ranka ya daɗe, akwai ta, Halimatu Sadiya Ibrahim. Tana da larura ne a fuskar tata, dalilin da ya saka ba ta iya buɗe fuskar kenan.”
“A hakan kuma kuka ɗauke ta aiki?”
“Ranka ya daɗe Alhaji ne da kanshi ya ba da umarnin a ɗauke ta, saboda duk cikin ma’aikatan da suka nemi aikin takardunta sun fi kyau, kuma mun jarraba ta tana da experience sosai.”
Ya yi shiru yana juya wasu zaren zantuka a zuciyarshi. Zuwa can ya miƙe ya karkaɗa kafaɗa sannan ya ce. “Shikenan.”
Ya juya ya fice, Malam Jafar Manaja ya bi shi da addu’ar Allah ya tsare.
A can ɓangaren Halima kuwa ta yi ƙoƙarin sanyawa ranta nutsuwa, ta tash ta nufi common room ta buɗe kular abincinta don ta karya kafin customers su fara yawa don an fara shigowa sayayya.
Wainar gero ce mai kyau da Umma ta soya musu, wainar ta tashi sosai ta yi tulu-tulu sai ƙamshi take, miyar gyaɗa ɗin da aka dafa don cin wainar tare ita ma sai zuba ƙamshi take.
Ladidi ta taso daga kujerarta ta nufi ɗakin ita ma. Fuska cike da murmushi ta karasa ga Halima.
“Haba Sad-baby, kin sani sarai yadda nake mugun son wainar Umma shi ne za ki taho ki ci ke kaɗai.”
Halima ta yi guntun murmushi ta ce. “Ni kuwa ina zan kai wannan uwar wainar ni kaɗai? Ita kanta Umma don ta san za ki ci ne ya sa ta zubo da yawa.”
Ladidi ta zauna suka fara cin wainar tare a gurguje. A sannan ne Ladidi ta fara tsegunta mata labarin Ali da wasu daga cikin halayen shi da ta ji ana labari.
Halima ta girgiza kai. “Sai da na ayyana a raina cewa duk yadda aka yi wannan gayen sunanshi Ali, na ga izzarshi da taƙamarshi sun yi yawa.”
“Ai kaɗan ma kika gani, yadda ake bayar da labarin shi wallahi an ce ba ƙaramin tantiri ba ne, ga gadara da taƙama da kuma shegiyar izza da girman kai… Ke dai ki shirya takun saƙar ku da shi tun da kun fara, don an ce ya dawo kenan, shi ne ma zai cigaba da kula da wannan gurin.”
“Sai yanzu na fahimci wani abu Ladidi, wato sunanshi ma aka sanyawa wannan kanti kenan.”
Cikin murmushi Ladidi ta ce. “E mana, sunanshi ne.”
“To a ina ya samo PRINCE ɗin da aka maƙala a sunan?”
Dariya Ladidi ta tuntsire da ita har da tuntsirawa kafin kuma ta ce. “Ki bari in ya fito sai ki tsayar da shi ki tambaye shi.”
Suka cigaba da hirarsu har suka cinye wainar, suka wawwanke hannu sannan kowacce ta koma bakin aiki saboda tuni mall ɗin ya fara cika da masu sayayya.
**
Koda Halima ta koma gida sai da ta labartawa Umma abin da ya faru da ita yau a gurin aiki, suna zaune a ɗaki da dare bayan kammala cin tuwon dare take ba ta labarin.
Ran Umma ya sosu sosai, a duniya in akwai abin da ta ƙi jini to bai wuce a wulaƙanta mata zuri’a ba, musamman babbar ‘yarta bango abin jinginarsu baki ɗaya. Don haka muryarta babu sauti sosai ta ce. “Irin yaran nan ne masu mugun hali masu amfani da ɗarfin ikonsu suna ƙuntatawa mutane.”
Halima ta kai hannu ta kaɗe wani mayataccen sauro da yake ta kawo mata farmaki ta ce. “Sosai kuwa, a yadda Ladidi ta ce ta samu labarin shi ma har shaye-shaye yake, riƙaƙƙen tantiri ne dai.”
“To Allah ya yi mana tsari da sharrin sa, ke kuma sai ki yi taka-tsan-tsan ki mayar da hankali a kan aikinki.” Umma ta ce cikin bayyanar damuwa a allon fuskarta.
“In sha Allah zan kiyaye duk sanadin da zai haɗa ni da shi ma.”
Suka cigaba da hirarsu mai daɗi har dare ya fara yi sosai suka kwakkwanta saboda su tashi da wuri gobe.
***
A ɓangaren shi Ali kuwa yana can tare da abokinshi Sadiq ya labarta masa abin da ya faru a ɗazu da ya je Mall dinsu.
Cike da mamaki Sadiq ya dube shi. “To kuma kai meye na damun kanka a kan batunta? Kawai ka share ta ka cigaba da sabgoginka kar ka ce ma za ka yi sakacin da ma’aikatanka za su raina ka.”
Girgiza kai Ali yake yi ya ce, “Inaaa ai wallahi dole ko ta halin yaya sai na ga fuskar yarinyar nan, sai na ga abin da take ɓoyewa a fuskar tata.”
Dafa shi Sadiq ya yi. “Ka rabu da batun nan my man, tun da ka ce Manaja ma da kanshi ya ce ba su taɓa ganin fuskar tata ba to a kan me kai zaka matsa dole sai ka gani? Ba ka tsoron ka je ka ganewa idonka abin da zai tayar maka da hankali?”
“Daga yanayin muryarta na fahimci lallai fuskarta dole za ta kasance tana da wani abu da zai fusgi hankali, shiyasa nake son ganin larurar da tauye mata fuskar ta tilasta mata sakaye ta a kodayaushe.”
“Mai yiwuwa ma gatsorin haƙora gare ta shi ne take ɓoyewa ko kuma irin matan nan ne da suka yi bilichin ya babbake musu fuska shi ne take wannan sinƙe-sinƙen!” Cikin sigar kashe gwiwa Sadiq ya yi furucin.
Kai tsaye shi ma Ali ya ce. “Ko kuma wataƙila Zabiya ce ma.” Sai kuma ya girgiza kai da sauri ya warware tunanin ya ce. “Kai ba za ta kasance zabiya ba don na ga fatar hannunta, ga alamu ma ba ta da hasken fata sosai.”
“To dai ka san babu yadda za a yi mace ta dinga ɓoye kyawunta, dole wani mummunan abu ne take sakayewa.”
“Shi ne dalilin da ya sa na ji ina matuƙar son ganin me take ɓoyewa ɗin.” Fuskarshi ta nuna furucin daga ƙasan zuciyarshi ya fito.
“Ni raini nake guje maka a wajen ƙananan ma’aikata, kai ba ka taɓa yin aiki da cuɗanya da mutane irin haka ba shi ya sa nake guje maka shiga sabgar ƙananan ma’aikata.”
“Kai ka san babu wata ‘ya mace da take da zarrar da za ta raina ni, da ƙarfin ikona kawai zan yi amfani in tilasta mata ta buɗe min fuskar tata in gani… Na rantse da buwayar ubangiji kwanaki uku ba za su zo su wuce ba ba tare da na ga fuskar yarinyar nan ba!”
Sadiq ya zaro idanu sosai cikin matuƙar ta’ajibi. “Me ya yi zafi haka har da saurin cin alwashi? Kar fa ka sa in fara wani tunani daban kan wannan al’amari!”
“Tunanin na kamu da son ta ko?” Ya saki malalacin murmushi. “Shirme ma kenan, kawai ƙarfin ikona zan nuna wa yarinyar… Haka kawai jikina ya ba ni yarinyar irin masu iyayi da kankanba ne da son nuna isar ba a isa ba, don haka sai na nuna mata irin nawa salon izzar, daga gobe za ta fara sanin wane ne Prince Alee Hayder!”
Gyaɗa kai Sadiq ya yi da alamun shakku a fuskarshi.
Ali ya yi murmushi. “Na san zuciyarka cike take da inkari a kan hakan, amma ka sani za a yi kuma za ka gani…”
08164243585
*share please👏🏼*
[28/08, 10:41 am] +234 802 201 4771: ❤️ *INA SO…* ❤️
💞💞💞💞💞💞💞💞
*______________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
*______________________________________*
*LITTATTAFAINA*
*FATIMA ZAHRA SA’EED*
*RANA DAYA TAK!!!*
*JARIRAI*
*SIDDABARU*
Da sunan Allah mai Rahama
mai jin kai.
Allah ka yi salati ga shugaban halitta Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wa’sallim.
*GODIYA*
Ta tabbata ga Allah buwayi da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi mai suna INA SO… Ina rokon Sa ya sa in fara lafiya in gama lafiya amin.
*YABAWA*
Ga yayata daya kwal a duk cikin tarin marubuta, wato Nana Aisha Hamisu Abdullahi, Allah ya dafa miki amin.
*Page 3/4*
*RANAR FARKO.*
Yana fakawa da gabjejiyar motarshi a gurin parking tana sauka daga adaidaita sahu. Da yake ta san yau ba ta makara ba don haka komai a nutse take yi babu gaggawa irin ta jiya.
Ta tsallaka titi a hankali ta nufi cikin Mall ɗin, suka gaisa da masu gadi kamar yadda ta saba sannan ta wuce ciki.
Ya fito daga cikin motar tashi, daga ɗaya ɓarin ma Sadiq ya fito. Nan da nan masu gadi da sauran ma’aikatan dake waje suka ƙarasa da sauri suka miƙa gaisuwa.
A gadarance yake amsa musu cikin izza sannan ya sa kai ya nufi cikin Mall ɗin yana karkaɗa ‘ya’yan mukulli, Sadiq na biye da shi. Yana shiga ma’aikata suka fara miƙewa tsaye suna miƙa gaisuwa ciki har da Halima, a daidai saitin gurinta ya tsaya ya yi ƙasa da murya ya ce. “Ki same ni a ofice!”
Da sauri a rikice ta ɗaga kai ta dube shi. Ta kwaso wata uwar in’ina. “Ran… ranka… ranka ya daɗe ina… Ina ne ofis ɗin?”
“Ki hau sama ki tambayi Manaja da kanshi zai kawo ki har ofis ina.” Cikin matukar ɗaure fuska ya faɗa, daga bisani ya juya ya dubi Sadiq.
“Let’s go!”
Ta sauke wani gwaggwaɓan numfashi tana ji babu daɗi a ranta, alamu sun nuna dai wannan mutumin zai zame mata ƙalubale a wannan gurin aikin nata.
Komawa ta yi ta zauna tana hangen Ladidi na ƙunshe dariya a baki ea hannayenta biyu, ta kawar da kai zuwa ga wata customer da ta kammala sayayya ta zo wajen biyan kudi, sai da ta sallame ta sannan ta dubi Najib maƙocinta ta roƙi alfarmar ya cigaba da aikin kafin ta dawo, dama duk aiki ɗaya suke yi.
A ofishin Manaja bayan ta gaishe da shi cike da girmamawa ta tambaye shi ofis ɗin Ali.
Da sauri ya ɗaga kai ya kalle ta cikin buɗe idanu. “Hala ba ki san wane ne shi da matsayinsa a nan ba ko?”
Ta rausayar da kai. “An faɗa min cewa yaron Alhaji ne ko?”
“Shi ne kuma kike faɗar sunanshi haka babu girmamawa, ko ba ki ga kowa yana ba shi girma ba ciki har da ni?”
Ta yi ƙasa da kai cikin jin yanayi mara daɗi a ranta.
Malam Jafar Manaja ya ƙara da cewa. “Kodayake ba ki jima sosai a nan ba shiyasa ba za ki san matsayinsa da irin makauniyar soyayyar da mahaifinsa yake yi masa ba, amma ba komai ai na san kin fahimci hatta guraren nan da sunanshi ake amfani ko?”
“Zan kiyaye gaba in sha Allah.” Ta faɗa murya cike da rauni.
Da kanshi ya jagorance ta har zuwa wani ɓangare daban wanda tun da ta fara aiki ba taɓa shiga ba.
A iyaka abin da idanunta suka gane mata ba karamin tsaruwa sashen ya yi ba, ta san ofis ɗin kuwa sai abin da ido ya gani.
Ƙwanƙwasa ƙofar ta fara yi, daga ciki ya ba da umarnin ta buɗe ta shiga. Da sallama ta shiga ofis ɗin cikin ɗari-ɗari. Wani sanyi mai mugun daɗi a jiki ta ji ya fara ratsa ta a hankali, yayin da kuma ƙamshin turaren ɗaki da ya gama gauraye ko ina ya fara shiga ƙofofin hancinta da sannu-sannu.
Ta dirice ta rasa abin da ya kamata ta yi a lokacin. Shi kuma gogan ya yi shiru ya kawar da kai yana sabgoginsa a waya tamkar ba shi ya kira ta ba. Sadiq ma hankalinsa na kan waya sai dai ya ɗaga kai lokaci-lokaci ya kalle sannan ya mayar ya cigaba da harkokinsa.
“Ranka ya ɗade ga ni.” Ta faɗa a gajiye da muryarta a can ƙasan maƙoshi.
Wani wulaƙantaccen kallo ya watso mata kana daga bisani ya cuna mata gefen da kujeru suke a ajiye da leɓen bakinsa ya ce. “Zauna ina zuwa.”
Tuni ta zauna tana ajiye numfashi, damuwa mai yawa ta fara ziyartar zuciyarta. Ta tabbata dai wannan bawan Allah so yake ya wulaƙanta ta hakan nan ba tare da ko kallon banza ta taɓa yi masa ba.
Sai da ya kwashe kusan mintuna goma tana nan a zaune ita bai ce mata ta tafi ba kuma bai ce mata komai ba, yana can yana shafe-shafen waya.
Ajiye wayar ya yi ya ɗaga kansa ya dube ta bayan ya kwashe ƙafafunsa ya zuba su a saman faffaɗan teburin dake girke a gabanshi ya ce.
“Meye ma sunanki?”
“Halimtu Sadiya.” Ta amsa.
Ya girgiɗa kai. “Kin san me nake so da ke?”
Ta jijjiga kai alamar a’a.
“Wannan abin na fuskarki nake so ki cire… Ina so in ga larurar da aka ce kina da ita da ta saka kike ɓoyon fuska.”
Jikinta ya soma rawa, ta fara jin tsoron kar wannan mutumin ya keta mata haddinta, tana tsoron kar ya yi amfani da ƙarfin ikonsa ya tilasta mata buɗe fuskarta ba tare da ta shirya.
Girgiza kai ta soma yi, muryarta cike da rauni ta ce. “Ka yi hakuri, ba zan iya buɗe fuskata ba, akwai babbar matsala yin hakan.”
Ranshi ya fara ɓaci, fuskarshi ta nuna haka.
“Wai uban meye a fuskar taki da ba za ki buɗe ba?”
Ta soma kuka duk da babu wanda yake ganin idanunta.
“Ka yi wa girman Allah ka rufa rayuwata asiri kar ka matsa min a kan sai na buɗe fuskata…”
“Idan kin ga kin fita daga gurin nan to ki tabbatar kin buɗe min fuskarki na gani… Amma kafin sannan bari in faɗa miki wani abu da baki sani ba…”
Ya ajiye ƙafafunsa a ƙasa ya miƙe ya fara taku ya nufo ta, sai da ya zo daidai saitin ta ya tsaya ya rankwafo kanta yadda har tana iya jin hucin numfashinshi ya ce. “Rashin narasa ba ta daga cikin ƙaddarata, ban taɓa sanyawa a raina ina son wani abu na rasa ba… Saboda haka ina so ki tabbatar wa da kanki tun da na ji INA SO in ga fuskarki to babu makawa sai na gani, a yanzu a take!”
Ta tsorata sosai da yanayinsa, hakan ne ya saka ta zabura ta miƙe da sauri tana ja da baya.
Ta fara yi masa magiya da roƙo a kan ya ƙyale ta saboda son da yake yi wa iyayenshi amma tamkar busar sarewa take yi masa a kunne, idanunshi sun rufe ya fara ƙoƙarin saka ƙarfi ya fizge niƙabin fuskar tata.
Ba ta san lokacin da ta saka hannaye bibiyu ta riƙe masa nasa hannuwan ba da duk ƙarfinta. Abin da ba ta taɓa yi ba a rayuwarta yau ya sa ta yi, wato ta riƙe hannun wani namiji wanda ba muharraminta ba. Kuka take yi sosai tana cigaba da roƙon shi da roƙon Sadiq a kan ya saka baki ya ƙyale ta, amma Sadiq ya yi fumfurus ya ƙi yin ko ƙwaƙƙwaran motsi.
Saura ƙiris ya yi nasarar fizge mata niƙab ɗin saboda yadda ƙarfinshi ya nunnunka nata, hannayenshi na riƙe gam cikin nata tana kuka tana girgiza masa kai tana faɗin “A’a! A’a!! A’a!!! Ba na so! Ba na so!!! A’aaaaa”.
Ji suka yi an fara ƙwanƙwasa ƙofar ofis ɗin daga waje. Hakan ne ya tilasta masa sauke hannayenshi cikin matukar ɓacin rai.
Idanunshi kawai ya kai ga ƙofar bai iya bayar da umarnin a buɗe a shigo ba, can kuma sai ya ga an murɗa ƙofar an shigo. Alhaji Hadi Karma ne ya shigo, wato mahaifinshi.
Da ƙarfi Halima ta yi ajiyar zuciya tare da godewa Allah da ya kawo mata mafita a lokacin da ƙarfinta ya riga ya gama ƙarewa.
Fuskar Alhaji cike da murmushi ya dubi Ali.
“Kana tare da Malama Halima kenan? Tana cikin sabbin ma’aikatan da muka ɗauka ai.”
“To amma Daddy me ya sa aka ɗauke ta aiki bayan an ce ba ta taɓa buɗe fuskarta an gani ba? Ba a tunanin hakan zai zama matsala ga security gare mu.”
“Babu wata matsala my son, laurara ce ta sanya faruwa hakan, kuma bincike ya tabbatar da babu wata matsala.”
Wannan dama da Halima ta samu da ita ta yi amfani ta sulale ta bar ofis ɗin ta koma gurin aikinta zuciyarta a jagule.
Aikin wunin ranar gaba ɗaya ta yi shi ne cikin wani irin yanayi mara daɗi, taimakon da Allah ya yi mata ma shi ne har lokacin tashin ta daga aiki ya yi ba ta ara jefa Ali a idanunta ba saboda zuwan mahaifin nashi sun yiyyi wasu ayyuka ne da lissafe-lissafe a kan cigaban gurin.
Koda ta koma gida ta so ta ƙara labartawa Umma abin da ya faru yau sai kuma ta ji tsoron sakamakon abin da hakan zai haifar, musamman in ta tuna yadda Umma ta shiga damuwa a jiya balle kuma abin da ya faru a yau ya ninninka na jiya.
Ta sani sarai ba ƙaramin aikin Umma ba ne ta ce kar ta ƙara zuwa gurin aikin muddin haka za ta cigaba da faruwa. Ita kuma tana tsoron rasa wannan babbar dama da ta samu da za ta tallafawa mahaifiyar tata da ƙannenta biyu don su huta da wahalar duniya.
Hakan ne ya sa ta yi ƙaryar cewa kanta na ciwo, don haka tana cin abinci ta nemi guri ta kwanta dayake ita din ba ma’abociyar ƙaunar shan magani ba ce, babu yadda Umma ba ta yi ba a kan ta sha paracetamol ɗin da ta aika Auta ta sayo, amma ƙememe ta ƙi sha ta ce in ta samu bacci ma shikenan ciwon kan zai tafi.
*******
A nashi ɓangaren kuma tun fitar Halima daga ofis ɗin nashi bai wani mayar da hankali a kan abin da ya kawo Daddyn nashi su yi ba. Gaba ɗaya hankalinshi na ga Halima da tunanin yau ta yi nasara a kanshi, karon farko kenan da aka taɓa cin nasara a kanshi.
In ya tuna hakan ba ƙaramin ƙuna ranshi yake yi mishi ba, abin da yake ƙara ba shi haushi shi ne yadda tunda suka taho a hanya Sadiq ke yi masa dariya da shegantaka a kan diramar tasu da kuma yadda yau aka ci shi da yaƙi.
Bai biyewa Sadiq ba don kar zafin zuciya ya sa ya kai masa mummunan naushi, ba ƙaramin aikinsa ba ne hakan. Ya san cewa akwai gobe, in yau ta kuɓuce masa ai gobe na nan, dama kuma kwana uku ya ba wa kanshi, don haka gobe ya shirya ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai ya buɗe mata fuskar ya gani, ba ma zai tsaya yi mata wata magana ba kawai hannu zai saka ya cire niƙab ɗin kai tsaye ya cillar gefe.
In ya tarar da cewa ita ɗin mummuna ce da take sakaye munin nata a cikin niƙab da tabarau ya ci alwashin tozarta ta a gaban sauran ma’aikata, in kuma irin bilichin ɗin nan ta yi ya babbake mata fuska nan ma za ta sha ƙasƙanci. Kai duk wani tazgaro da ya tarar a fuskar tata to tabbas sai ya muzanta ta da kyau yadda ba za ta ƙara marmarin yin jayayya da shi ba a gaba! Wannan shi ne tunaninsa.
Gidansu Sadiq ya fara biyawa ya sauke shi, daga nan ya wuce zuwa wani jangul da ‘yan shaye-shaye suke cin dabdalarsu.
Daga nesa kaɗan ya faka motar tashi ya ɗan sauke gilashin motar.
Goga wanda shi ne ja-gaba a jangul ɗin ya tashi da sauri ya nufi motar. Da ya isa sai da ya tsaya ya yi masa kirari irin na neman fada. Duk da ɓacin ran da yake ciki haka ya saki fuska kaɗan ya nuna godiyar shi ga goga sannan ya buaci a kawo masa BABBAR HAJA (Littafi na gaba).
“Ka daɗe ka yi karko na wajen Alaji!” Goga ya faɗa yana ƙara sara masa sannnan da sassarfa ya tafi zuwa inda suke ɓoye kayan aikin nasu ƙarƙashin wani rusheshen dutse, ya ture dutsen ya zaro ƙunshin wata baƙar leda, ya warware ta ya fara fita da sinƙi-sinƙin ƙulli na tabar wiwi. Ƙulli biyar wanda lissafinsu ya kama Naira dubu biyar ya tattara su ya naɗe a wata takarda sannan ya koma da sauri gurin Ali.
Naira dubu goma Ali ya duntso ya miƙa wa Goga sannan ya kunna motarshi ya wuce. Sai da ya tsaya a hanya ya kwashi kayan fruits sannan ya wuce gida.
Lokacin da ya isa magriba ta yi, maimakon ya wuce kai tsaye ya yo alwala ya yi sallah a’a, ai watsa ruwa kawai ya yi ya fito ya fara murza dular tabar wiwi ɗinsa.
Da ya gama tsaf sai ya cinna mata wuta ya fara zuƙar hayaƙi yana ambular da shi waje ta ƙofofin hanci cike da gwanancewa.
Nan da nan farin hallitar gilashin idonshi suka fara sauya launi zuwa ja-ja-ja baƙi-baƙi.
Ya cigaba da busar tabarshi yana cigaba da saƙa zaren tunanin yadda zai yi da Halima a gobe, tasirin hayaƙin taba da kuma ƙarfin sharrin zuciya suka cigaba da ingiza shi wajen ƙara jin haushin ta da cin mummunan alwashi a kanshi.
Jin ana ƙwanƙwasa masa ƙofa daga waje ne ya sa shi zabura da sauri ya murje guntun dular tabar wiwi ɗin a cikin wani ɗan karamin tray, ya ɗauki tray din ya tura ƙasan makeken gadonshi sannan ya yi hanzarin ɗauko room freshener ya fara feshe ɗakin.
Sai da ya tabbatar ƙamshin freshener ya gauraye ɗakin sannan ya nufi ƙofar ya buɗe.
“Mom!” Ya faɗa ƙasa-ƙasa.
Tsayawa ta yi tana ƙare masa kallo kafin ta saka kai zuwa cikin ɗakin tana cewa da shi.
“Na ga shigowar ka fa, amma sai na ji ka shiru ba ka fito ba…” Maganar tata ta maƙale sakamakon ƙamshin freshener da kuma warin wiwi da suka haɗu suka bayar da wani irin yanayi na daban a hancinta. Ta dinga buɗe ƙofofin hancinta tana shaƙar abin tana fesarwa kafin ta kyaɓe fuska ta dube shi.
“Mene ne wannan ka saka a ɗakin nan?”
“Freshener ce Mom!”
Ta yi saurin kallon shi. “Wace irin freshener ce haka mara daɗin ƙamshi? Anya ba wannan matsiyaciyar tabar taka ka sha ba shi ne za ka yi basaja da room freshener? Ni dai na san ba haka ƙamshin freshener ɗin nan yake ba.” Cikin tsattsare shi da idanu ta yi furucin.
Ya soma sosa ƙeya. “No Mom, ban sha komai ba.”
“Ƙarya kake wallahi, ga idanunka nan sun nuna.”
Ya shiru cikin ɓacin rai.
Ta ɓata fuska ita ma. “Son ba na so ka je jefa rayuwarka cikin matsala ta hanyar wannan zuƙe-zuƙen, Ka sani sarai yadda shan tabar nan yake da babbar illa ga rayuwa musamman ma matashi, me ya sa ba za ka raba kanka da sha ba?”
“Addu’a za ki cigaba da yi min Allah ya sa na daina.”
“Addu’a kullum ina yi maka Allah ya shirya ka.”
Ya amsa. “Amin.”
Ta ce. “Ka shirya ka fito mu yi dinner!”
Gyaɗa kai kawai ya yi, ta juya ta fice. Tana fita ya zaro tray ɗin nan ya sake murza wata dular tabar ya banka mata wuta don sam bai ji kanshi ya yi masa yadda yake so ba, ga shi ita ma Momsy ta zo za ta ƙara masa pressure don haka sai ya babbaka kanshi sosai da hayaƙi sannan zai fita ya je gurin nasu.
Wannan kenan!
*RANAR TA BIYU.*
Kamar dai Halima baki ta yi wa kanta don kuwa da wani irin matsanancin ciwon kai ta tashi tare da zazzafan zazzaɓi. Tana kwance rufe da bargo amma haƙwaranta sai karo suke da juna yayin da gangar jikinta ke ta rawa.
Hankalin Umma ya tashi sosai duk ta rikice.
“Tun jiya na matsa miki ki sha magani kika ƙi, da kin daure kin sha watakila da ciwon bai tsananta miki kamar haka ba.”
“Ina wayata Umma?” Ta faɗa da ƙyar.
“Me za ki yi da wayar kuma?”
“Manaja zan kira in bayar da uzurin rashin zuwa gurin aiki yau.”
Da sauri Umma ta dubi Maryam ta ce ta ɗauko wayar yayar tasu. Maryam ta kawo wayar. Cikin sassarfar harshe Halima ta ce wa Maryam ɗin ta lalubo lambar da aka rubuta Baba Manaja ta kira. Bayan kiran ya shiga an ɗaga ta hau katifar da yayar tasu take kwance ta kara mata wayar a kunne.
Da ƙyar Halima ke magana ta gaishe da Manaja sannan ta ƙara da cewa. “Na tashi da zazzafan zazzabɗɓi da ciwon kai mai tsanani, ina roƙon a yi min uzuri, wallahi ko tashi ba ina iya yi.”
Cike da alhini da tausayawa ya amsa. “Ayya! Subahallahi Allah ya sauƙaƙa miki ya ba ki lafiya, babu matsala duk lokacin da kika samu sauƙi kya dawo bakin aiki.”
“Yawwa na gode Baba.”
Ya katse kiran, ta ce ta lalubo lambar Ladidi ma, ita ma ta sanar mata da zazzaɓin da ta tashi da shi don haka yau ba za ta samu fitowa aiki ba. Daga nan aka kashe wayar aka ajiye.
Umma ta yi iyakar bakin ƙoƙarinta a kan Halima ta tashi ta sha magani amma ta ƙi, ta kuma ƙi cin komai hatta da ruwan koko da Umma ta dama musamman saboda ita ta samu ta saka abu mai ruwa-ruwa a cikinta amma ɗememe Halima ta yi wa bakinta mukulli ta ƙi.
Umma ta dubi Maryam. “Maryama ko Atine mai kyamis za ki je ki kira ta zo ta yi mata allura?”
Wata irin zabura Halima ta yi cike da shagwaɓa ta ce. “Allura kuma Umma?”
Umma ta ɗaure fuska. “E mana, tun da kin ƙi shan magani kuma kin ƙi ci da shan komai ai sai a zo a yi miki allura mana.”
“Umma kin san fa ba na son allura.”
“Hakan nan za ki daure.”
Ta juya ga Maryam. “Ke yi maza ki je ki faɗa mata kafin ta fita.”
Maryam ta amsa da to ta fice.
*Share please👏🏼**
08164243585
[28/08, 10:41 am] +234 802 201 4771: ❤️ *INA SO…* ❤️
💞💞💞💞💞💞💞💞
*______________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
*______________________________________*
*LITTATTAFAINA*
*FATIMA ZAHRA SA’EED*
*RANA DAYA TAK!!!*
*JARIRAI*
*SIDDABARU*
*JINJINA*
Ga kanwata Aisha Muhammad Sani Zeeshatulkhair (Xayyesherthou)
*page 5/6*
Ya shigo Mall ɗin ransa fal da muguntar da ya ƙunso ya tsara zai yi mata. Idanunshi a wurin zamanta ya fara ajiye su, ga mamakinshi Najib ne a zaune a wajen yana gudanar da aiki a maimakon ita.
Ya ƙarasa gurin ya tsare Najib da idanu.
“Kai ina yarinyar da take aiki a gurin nan?”
Jikinshi yana rawa ya hau in’ina. “Ba ta samu zuwa ba saboda ta tashi ba ta jin daɗi.”
“Ba ta jin daɗi?”
“E haka ta ba da uzuri ranka ya daɗe.”
Dogon tsaki ya ja ya bar gurin yana jin matuƙar rashin daɗi a ranshi, wato yarinyar nan da gaske dai sai ta yi nasara a kanshi shiyasa ta zaɓi ƙin zuwa a yau ta fake da rashin lafiya, ya ji a jikinshi babu wata rashin lafiya kawai ta yi hakan ne don ta kuɓuta daga tarkon da ya ɗana mata a yau. To ko dai ta san shirin da yake yi a kanta ne?
Ya girgiza kai ya hau escalator zuwa sama ya nufi ofishin Manaja.
Malam Jafar Manaja ya tashi da sauri ya miƙa gaisuwa. Ali ya amsa cike da izzarshi sannan ya ɗora da tambayar.
“Ban ga wannan yarinyar ta zo aiko ba yau?”
“Halima ko? Ta kira ta sanar da uzurin rashin lafiya ranka ya daɗe.”
“Ƙarya take babu wani rashin lafiya, ta ƙi zuwa ne saboda wani dalili kuma tabbas sai na hukunta ta…” Ya miƙe daga zaman da ya yi.
“A cire ranar yau cikin kuɗin albashin da za a ba ta.!”
Wani irin kallo Malam Jafar ya bi shi da shi, sai dai ba shi da ikon musawa duk da cewa a dokar aikin wajen ana yin alfarmar rashin lafiya, da a ce babu wani sahihin uzuri ne shi ne za a datsewa mutum albashi amma ban da larura. Kawai dai ya fuskanci akwai wani takun saƙa ne tsakanin shi da wannan baiwar Allah wanda ya yi imanin kawai tsabar zaluncin shi ne ya sa.
Gaba ɗaya bai ji daɗi zaman ofis ɗin na yau ba saboda bai samu ya aikata mugun ƙullin da ya niyyar yi ba, don haka babu abin da ya dinga yi face bankawa sigari wuta yana turara kanshi da hayaƙi. Nan da nan idanunshi suka yi jajir kuma suka yi mitsi-mitsi da su.
Inda Allah ya taimake shi ma yau Sadiq ya tafi wata sabga don haka bai san wainar da za su toya ba, da yana nan dai kam da babu abin da zai ƙara masa face pressure da tsokanar shi a kan rashin nasarar da yau ma ya yi.
Yana cigaba da jan isakar sigari yana cigaba da ayyana yadda zai yi da ita a gobe final, tabbas ba zai bari gobe ta wuce masa ba ba tare da ya aikata abin da yake so ba. Muddin yarinyar ta ƙi zuwa a gobe ya yi alƙawarin sai ya binciko address ɗinta ya je har gida ya ci mata mutunci.
Kira ya shigo wayarshi, da ya duba sunan Jessica ne, duk cikin ɓacin ran da yake ba zai iya ganin kiran Jessi ɗinsa ya turbuɗa a kwandon shara ba. Hannu ya sa ya ɗaga kiran ya kara wayar a kunnenshi bayan ya yi iyakar ƙoƙarin saita muryarshi.
“Hello.” Ta fara magana cikin shagwaba cikin harshenta na nasara. Nan ya biye mata suka yi ta zuba soyayya cikin harshen turanci inda ta dinga faɗa mishi yadda ta yi missing ɗinshi, tana matuƙar son ya koma su cigaba daga inda suka tsaya.
Da ƙyar ya shawo kanta da ƙarairayi sannan suka rabu, ya koma ya cigaba da zuƙe-zuƙen shi.
*
Can gidansu Halima kuwa an kira Atine mai kyamis ta zo ta yi wa Halima allura. Da ƙyar da daddanewa aka samu aka yi allurar. Kuka sosai Halima ta dinga bayan an yi allurar.
Atine ta rubuta magungunan da ya kamata a siya. Umma ta duba asusun da suke ajiyar kuɗi ta iske akwai ragowar canji, su ta ɗauko ta ba wa Atine aka yi lissafin kuɗin maganin sannan ta wuce Auta ta bi ta don karɓo maganin.
Wajen Shan maganin ma sai da aka yi tataɓurza da ita sannan ta haɗiɗiyi ƙwayoyin magungunan tana jin kamar za ta amayo kayan cikinta.
Zuwa yamma ta ware tas zazzaɓin ya tafi, har ta taya Umma aikin tuwon dare. Da dare suka ci tuwon suna shan hira kamar yadda suka saba.
RANA TA UKU.
Washegari ta tashi garas, har ta ɗan faɗa. Yadda ta ji daɗin jikinta ya sa ta yi tunanin ta fita aiki.
Umma ta so hana ta amma ta nuna babu matsala za ta iya fita, don haka ta shirya a gurguje ta nufi gurin aiki.
Sun yi mamaki da suka ga ta zo yau, don sun yi tsammanin za ta iya ɗaukar kamar kwana uku ko sati kafin ta dawo. Baba Manaja da sauran ma’aikata suka yi mata sannu da jiki.
Ta zauna gurin zamanta ta cigaba da gudanar da aikinta.
Tana jin fargaba sama-sama na sukar zuciyarta tana ƙoƙarin kore hakan da addu’a da neman tsari a kan sharrin Ali. Allah ya kuɓutar da ita ya shiga tsakanin su.
Wajajen ƙarfe sha dayan safe sai ga shi ya dira a Mall ɗin kamar wanda aka jefo. A guje ya shigo kamar yadda ya saba, ya faka motarshi sannan ya fito ya shiga. Daidai gurin zamanta ya fara cilla idanunshi, tana nan!
Har wani farin ciki ya ji a ranshi, yana zuwa ya ce ta same shi a ofis. Gabanta ya yi mummunan faɗuwa, abin da ya faru shekaranjiya ta tuna, tana tsoron kar hakan ya kuma faruwa yau, ba ta san waye yau kuma zai cece ta ba in har ya kuma zuwa mata da makamancin abin da ya zo da shi a baya. Hakan ya sa ta fara canki-canka a zuciyarta na ta je ko kar ta je? Wane sashe na ingiza ta a kan kar ta je inyaso duk abin da zai faru ya faru!
Wane sashen kuma nusar da ita yake yi kuskuren da za ta yi in ta aikata hakan. Gwara ta tashi ta je ta miƙa lamuranta ga Allah zai kare ta da duk kariyarsa, addu’ar Ummanta kuma za ta yi tasiri a kanta, babu abin da zai faru da ita kamar yadda a wancan karon Allah ya kawo mata ɗaukin zuwan Alhaji Hadi yau ma in ya so zai iya kawo mata wata mafitar.
Da ƙarfin gwiwa ta tashi ta nufi ofishin nashi. Bayan ta nemi izini ya ba ta dama ta tura ƙofar ta shiga. Ga mamakinta abin da ta fara yin arba da shi shi ne tulin kuɗi bandir-bandir a barbaje a kan faffaɗan teburin dake gabanshi, hakan ne ya sa gabanta ya yanke ya faɗi.
Cikin jin matuƙar izza ya miƙe yana murmushin mugunta. “Ki ɗibi ko nawa kike buƙata a matsayin farashin fuskar taki… Tun farko wannan hanyar ta kamata in bi don na san babu abin da kaji suka fi buƙata face hatsi, da tuni kin buɗe matsiyaciyar fuskar taki da kike kunshewa a niƙab!”
Addu’a ta soma yi tana roƙon Allah ya tsare ta daga sharrin shi.
Tsawa ya daka mata. “Ba ki ji abin da na ce miki ba? Ko kina ganin sun yi miki kaɗan ne in ƙara miki?”
Ta soma girgiza kai. “Ka yi hakuri, ban ce ina buƙatar kuɗi don in buɗe fuskata ba, fuskata ba haja ce da na kasa a kasuwa ba balle in yi mata farashi, saboda haka Ka bar kuɗinka kuma ka cire ran zan buɗe maka matsiyaciyar fuskata ka gani.”
Ta yi furucin amma zuciyarta kamar ta tsinko ta fito waje saboda yadda take hanƙoro a ƙirjinta, tsananin tsoro na kewaye dukkan gaɓɓanta, nan da nan sai ga jikinta na rawar ɗan mazari.
Shi kuwa a nashi ɓangaren mutuwar tsaye ya yi, kalamanta sun kashe shi matuƙa! A ina yarinyar nan ta samu zarrar datsa masa magnganu haka? Kenan fito-na-fito ta shirya yi da shi?
Ranshi in ya yi dubu kowane ɗaya ya baci. Ya fara taku a hankali yana matsowa inda take. “Ke ‘yar matsiyata! Ba yau na fara cin karo da irin ku masu masifar jiji da kai alhalin ba ku da ko sisi ba, ba ku ajiye ba ba ku ajiye mai ajiye muku ba! Kar ki ce za ki yi wani burga da ƙi-faɗi… Kuɗi babu abin da ba sa saya ciki har da abin da ya fi komai daraja wato lu’u lu’u bare wannan ƙazama mummunar fuskar taki da duhun talauci ya baibaye ya sa kike ɓoye ta saboda ƙurajen pimples ko kyasbi ko na bilicin, shashasha sakarya… Ki sani ko ki ɗauki kuɗi ko kar ki ɗauka yau wallahi sai na ga fuskar nan ta ki…”
Ya tunkaro ta gadan-gadan, hakan ya sa ta kwasa a guje ta fice daga ofis din, shi ma da gudun ya biyo ta idon shi a rufe yana cigaba da faɗa mata maganganun wulaƙanci da ƙasƙanci.
Ya cimmata a ƙasa bayan sun sauka daga escalator. Nan da nan kallo ya koma kansu, da ma’aikatan da customers masu sayayya kowa ya tsaya yana kallon ikon Allah.
Cikin nuna ƙarfi Ali ya sa hannu ya riƙo gefen hijabin Halima ya janyo ta da ƙarfi ta faɗa jikinshi. Zuciyarta ta yi wani irin soyewar da ba ta taɓa ji ba, tsoron da take ji duk ya kwaranye idanunta suka rufe, a karon farko a rayuwarta ta cire yatsunta biyar ta sharara masa mari kuncin gefen hagu.
Amma da yake shi shegen kanshi ne ya shanye zafin marin ya cigaba da kokawar cire mata hijabin jikinta gaba ɗaya.
Tuni harabar Mall ɗin ta rikice, wasu suka fara ƙoƙarin tunkarar su don su ƙwaci Halima daga hannunshi yayin da wasu suka kira waya suka sanar da Baba Manaja da kuma securities dake waje.
Kafin a kai ga kai mata ɗauki tuni ya yi nasarar cizge mata baƙin tabarau ɗin da take sakaye idanunta ya yi cilli da shi a ƙasa. Take tabarau ɗin ya tararratse ya zama fisis. Niƙab ɗin ma ya samu nasarar yage shi da ƙarfin tsiya cillar da rabi, rabi na riƙe a hannunshi.
Take fuskarta ta bayyana kowa ya gani!
Innalillahi wa’inna Ilaihir raji’un! Hasbunallahu wa’ni’imal wakil!
Abin da mutane suka dinga maimaitawa kenan sakamakon abin da idanunsu suka gane musu a fuskar Halima.
Ashe gaba ɗaya tabin fuskarta gefen dama daga sama har ƙasa a ƙone yake. Saboda tsabar lalacewa da ɓarin fuskar tata ya yi fatar gurin har wani baƙiƙƙirin ta yi ta tattare ta cure babu kyan gani. Yayin da ɗaya barin gefen hagu yake lafiya sumul.
Shikenan mai afkuwa ta afku, kasa kuka ma Halima ta yi face juyawa a guje ta fice daga cikin Mall ɗin zuciyarta na wani irin zafi da raɗiɗin baƙin ciki, mutane suka dinga bin ta da kallon tausayawa matuƙa, masu raunin zuciya kuwa har da zubar da hawaye. Shi kanshi gogan abin ya daki rashin sosai, yana nan tsaye hannunshi riƙe da guntun tsumman niƙabin nata Baba Manaja ya karaso.
“Lafiya me yake faruwa ranka ya daɗe?”
Girgiza kai ya yi. “Ba komai.!”
Ya juya ga sauran ma’aikata ya ce. “Kowa ya koma ya cigaba da aikinshi, case closed! Abin da nake so in gani na gani!”
Ya kaɗe jikinshi ya cillar da guntun niƙab ɗin ya juya ya hau escalator ya koma office.
Allah ya kaɗai ya san iyaka adadin mutanen da suka zage shi a zuciya da masu tsine masa a kan halin shi na rashin imani.
Ladidi kuwa jikinta bai daina rawa ba saboda yadda lamarin ya doke ta, tun da Halima ta fara aiki babu wanda suka shaƙu sosai sama da ita, to ko ita ba ta taɓa matsa mata a kan lallai sai ta ga fuskarta ba tun da ta fahimci akwai dalili mai ƙarfi da ya sanya ta yin hakan. Baiwar Allah ashe ƙonanniyar fuska gare ta take ɓoyewa? Allah Sarki!
A fili ta dinga jerawa Ali Allah ya isa a madadin Halima, ba ta taɓa tsammanin rashin imanin shi har ya kai haka ba!
*** ***
*Yawwa na ce ba🤨 ya kamata a fara biya tun yanzu don free pages ba su da yawa sosai.*
*Za a iya biya ta wannan account din.*
*0731666403*
*Muntasir Shehu*
*Access Bank*
*Sai a turo shedar biya ta wannan lambar 08164243585*
*Masu turo kati ma za su iya turo MTN ta wannan lambar*
*Masu karatu a arewabook kuma za su dinga samun duk chapter a kan Naira 20 kacal*
*Ku bi wannan link din don yin register ku fara karanta wannan littafi na INA SO wanda ya zo da wani sabon salo na musamman.*
*A sha karatu lafiya*
*Idan an karanta a taya ni sharing don Allah.*
Leave a Comment