Tunatarwa

Ina zinar yaya mata ta samo asali

INA ZINAR YA’YA MAZA TAKE SAMO ASALI?

 

 

 

 

 

 

Nayi alkawarin yin magana akan tarbiyya, musamman ta bangaren tarbiyyar yara maza. Duk da dai bani da lokaci amma zan danyi magana kadan a kan wani bangare dana lura iyaye da yawa suna dauke kansu daga kai. Wannan bangaren shine sexuality na boys;

Idan iyaye, musamman uwa mace tana da ya mace, da zarar yarinyar nan ta fara tasawa za’a fara yi mata magana akan kamun kai, rufe tsiraici, kiyaye mu’amala da yara maza da sauransu. Wadansu iyayen ma idan yar su mace ta fara menstruation sukan tsoratar da ita da cewa idan ta kama hannun namiji zata yi ciki amma ban taba jin inda aka gaya wa yaro namiji cewa in ya kama hannun mace zaiyi mata ciki ba.

 

Me yasa muke ignoring adolescent na maza muke bawa na mata muhimmanci? Shin dan muna gudun kar yayan mu mata su dauko mana abin kunya in sunyi zina? Shin mun manta su mazan suma in suka yi tamkar wani bashi ne suka dauka wanda duk daren dadewa sai sun biya a cikin zuriar mu? Shin bama ganin ignoring sexuality na yara maza yana daya daga cikin dalilan da yasa a halin yanzu mafi yawan marital issues suke kasancewa cheating ne ta bangaren mijin?

Wannan zai cigaba har sai iyaye, musamman iyaye maza sun fara bude baki suna magana da yayan su maza. Yara maza suna fara samun erection ne da zarar adolescent ya zo musu, basu san menene ba sai dai kawai su gansu.

Siffofi Guda Goma Da Mata Ke So Agurin Namiji

 

sannan sai su fara exploring da kansu. Wannan yana zama da hatsari musamman idan yaro yana boarding school inda suke da seniors, anan zasu iya dora shi akan hanya wadda ba dai dai ba kuma in Allah bai kare ba sai ya hau kai tunda ku iyayensa baku nuna masa hanya mai kyau din ba. Zaiyi ta exploring jikinsa yana fahimtar menene yake triggering erection din, menene kuma zaiyi dashi?

Lokaci daya sai kuga yaron da da kyar ake saka shi ya jima a toilet yana wanka ya koma sai da kyar ake fito dashi daga toilet…..amma still babu wanda yake paying attention to that change.

 

Suddenly gashi zai fara fito masa a jikinsa, muryarsa zata bude amma still babu wanda zai zaunar dashi yayi masa bayani yayi guiding dinsa saboda ana ganin ai shi namiji ne. Daga nan zai fara yammata, tun ana yin na wasa ana ganin yarinta ce amma shi a zuciyarsa dole akwai abinda ya saka ya zabi that particular girl, still babu wanda zai tambaye shi

dalili ballantana ya bashi shawara.

At the SS class, care is not taken, anan suke fara masturbating, yes, let’s face reality, masturbation is real musamman a gurin teenage boys sai wanda Allah ya kare, sai kuma munsa ido sosai mun kuma dage da addu’a. Ana shiga jami’a kuma sai a fara real yammata, tun daga nan ake fara ta’asa. Ku iyaye kuna ganin tunda danku namiji ne ai babu wani abu dan ya kwana a wani gurin ba gida ba, ba ruwanku dan ya kwana yana waya da yammata, wata uwar ma ba zata sani ba in ya kwana yana wayar, ba ruwanku da social media activities dinsa saboda shi namiji ne ai bashi da abin kunya. Da yawa daga nan suke farawa. Yanzu kuma idan yaron ya zama babba, ya gama karatu ya

zama miji sannan ya zama uba, anan ne problem din zai fara,

a lokacin da matarsa ta fahimci vana aikata zina Apan ne

a lokacın da matarsa ta fahnımcı yana aikata zina. Anan ne asiri zai tonu, anan ne kuma drama zata fara. At this point, maza da yawa suna iyakacin kokarin su suga sun daina musamman in suna son matan nasu amma sai su kasa, kun san dalili? Saboda sex is an addiction…

Kamar yan shaye shaye ne, in dai an riga an saba to da wahala a daina, in za’a daina ma to sai ansha wahala, kafin nan the harm has already been done. Ya riga ya rusa rayuwar sa, ya rusa ta iyalinsa, ya rusa ta zuri’arsa. Eh, mu cigaba da koyar da yayan mu mata about menstruation, adolescent, kula da miji, ciki da haihuwa amma mu manta da yayan mu maza mu barsu su koya da kansu.

Wannan yana daga cikin manyan mistakes din da iyayen mu

sukayi, kar mu maimaita saboda future din al’ummar mu. Idan ke uwa ba zaki iya ba, ki roki mijinki yake zama da yaron ku suna maganar “boys things” Kamar yadda mu iyaye mata muke maganar “girls things”. Allah ya gyara mana zuriyar mu badan halin mu ba, Allah yayi mana jagora ya kare mu da yayan mu daga sharrin shaidan, AMIN THUMMAH AMIN Yaa hayyu Yaa Qayyum.

Leave a Comment

error: Content is protected !!