Inada Hujja Hausa Novels
Ayshat Ɗansabo lemu
ASALIN LABARI
Zaune take ta tasa cup ɗin shayi ruwan bunu a gaban ta,wanda ko arziƙin sukari babu a cikin sa.Tsuran ruwan lipton ɗin ne kawai ta ke juya shi da cokali,ba tare da cewa akwai mahaɗin da xata haɗa dashi ta sha ba,hawaye ne masu tsananin xafi ke sauka bisa kuncinta ba tare da ta damu da ta tsaida su ba,daga gefen ta ƙanin ta Aliyu ne ke zaune yana faman shan ruwan lipton ɗin tamkar ya samu wani zuma.Sam bai damu da rashin mahaɗi ko rashin sukarin da babu a cikin sa ba,burin sa kawai dama ya ji wani abu na ratsa cikinsa don rabon su da saka wani abu a ciki tun jiya da rana.Yanzu ɗin ma Khairiyyah ce ta tuno tayi ajiyan lipton ɗin cikin kayan ta,shine har ta samu ta haɗa musu suna sha,kafin su ga dawowan Yayan su Ahmad da yace su jira shi ya fita ya dawo.Kanta ta ɗaga takai duban ta can ma’ajiyan kayan makarantan ta inda ta ke ajewa,wasu hawayen suka zubo mata tana jin yadda zuciyanta ke sake ɗaukan tsananin zafi na tausayin kansu da halin da suke ciki.Rabon ta da karatu shekara ɗaya kenan tuni qawayen ta sun jima da shiga SS1 na sakandiri.Amma ita tunda ta samu ta gama JS 3 shiga SS1 ɗin ya gagare ta.Gashi Allah ya ɗaura mata burin son karatu,tana matuƙan son ta ga ta zurfafa karatu har zuwa matakin gaba da sakandiri,amma babu halin hakan wanda zai tallafe ta ta cinma gaci,babu tai masa katutu ƙarfin sa ya gaza.A shekarun ta na goma sha biyar ya ci a ce ta shiga matakin Senior Secondary school.Kaman yadda qawanyen ta suka wuce,sai dai ita a lokacin da sakamakon jarabawan JSCE ɗinsu ya fito alokacin ne iftila’i ya faɗawa Malam,masu garkuwa da mutane sukai nasaran tafiya da shi, akan hanyan sa ta dawowa daga Zangon Aya,ya je aikin ɗaukan Siminti da aka sauke sun kammala aikin ne za su dawo gida aka tare motan da su ke ciki akai garkuwa da su.Hakan ya zamo silan sake jefa rayuwansu Khairy cikin garari,har zuwa lokacin da Allah ya kuɓutar da shi da ƙarfin ikon sa ya dawo gida.Bayan sun gama cire rai da sake saduwa da shi,don koda wasa sun san in dai sai an biya kuɗin fansa ne xai dawo gare su to sai dai ya rasa rayuwan sa a hannun masu garkuwa da mutanan.Cikin ikon Allah su na xaune da maraicen wata ranan Laraba sai gashi ya shigo gidan wurjanjan.Bayan ya shafe sati bakwai a hannun su,tunda ya shigo gida a tsananin galabaice ya shigo.Wanda kallo ɗaya zakai masa ka san ikon Allah ne kawai ya kawo sa gidan,nan tsakar gida ya faɗi faɗuwan daya zamo silan samuwan laluran sa da har yau yake fama don saura kiris ya rage ya rasa sashin jikin sa na dama,hawan jini yai masa mummunan kamu Allah ne ya taƙaita abun bai nakasa sosai ba,tunda a yanzu an samu yakan dogara sanda ya fita zuwa masallaci amma baya ga masallaci baya nisa da gida sam,yana zaune a gida ne kawai yau ciwo gobe lafiya,sabida rashin samun shan magungunan sa yadda ya dace.Ga kuma tunanin halin da su ke ciki na ƙunci da talauci,wanda hakan ke sake taka rawa wajen taɓarɓarewan lafiyan sa,ba su da wani gata sai Allah sai kuma ɗan sana’an wankau da su ke yi idan sun samu,sai ko kitso da Khairiyyah ke yi da shine su ke samu su ci su sha,har su yi ɗan ƙananun buƙatu na yau da gobe,randa ba su samu ba su kwana da yinwa.Arziƙin su kenan gidan da suke xaune na su ne da wani abokin arziƙin Malam ɗin ya mallaka masa,wanda a halin yanzu ya rasu su ma iyalin sa sun tattara sun bar Zaria sun koma mahaifan mijin na su can Bauchi.Hakan yasa rayuwa ya sake tsananta ga Malam Lawal da iyalin sa dama Alhaji Harunan ne yake taimaka musu to shima gashi sun rasa shi.Khairiyyah ta sake juya cokali a cikin kofin shayin tunanin ta na katsewa a lokacin da ta jiyo muryan Aliyu yana faɗin”Yah Khairiyyah Inna na kiran ki.”
Wacce ya kira da Khairiyyah ta sauke manyan idanun ta a kan sa,sam ita bata ji kiran da Innan ke jero mata ba.Ta miƙe cikin sauri tana aje cokalin hannun ta da take ta faman juya shayin da tunani ya gagara barin ta ta sha,haka ta fice zuwa ɗakin Inna tana amsa kiran da take mata da faɗin.
“Na’am! Inna gani nan zuwa.”
Da sallama ta shiga ɗakin bayan an bata izinin shiga,ta isa kusa da Inna Salamatu wacce take zaune a gaban Malam Lawal tana juye masa kokon da Yayan su Khairiyyah Ahmad ya shigo musu da shi a cikin kofi.Ahmad na zaune daga gefe guda shima yana shan kokon cikin kofi,Khairiyyah ta dube sa tana faɗin “Yah Ahmad sannu da shigowa.”
“Yauwa sannu Khairy, Ba dai xaki daina yawan koke-koken nan bako?”
Ahmad ɗin ya faɗi tausayin su na sake mamaye zuciyan sa,yana sake jin cewa ya zama dole yayi anfani da lafiyan sa wajen dagewa da nema musu koda na abinci ne.Tuni ya jingine maganan Karatun sa shi ma,tunda ya samu ya kammala secondary da ƙyar ya aje batun karatun a gefe sabida rashin madafa,yanzu haka gareji yake zuwa yana kanikanci ɗan abinda yake samowa ne ake samu aci abinci,har a sai maganin daya samu wanda Malam ke sha.
Tunanin sa ya katsene da jiyo muryan Malam dake ma Khairiyyah magana yana faɗin “Taho nan kusa dani Mamana kinji,don Allah Ummul-Khairy na ki cire duk wata damuwa,ki zama me juriya akan duk halin da xaki tsinci kanki a rayuwanki.Sam bana jin daɗin wannan yawan kukan da kike akan irin jarabtan da muke ciki,karki manta Allah baya taɓa ɗaura ma duk wani rai abinda bazai iya ɗauka ba.Ubangijin mu yana sane da mu yana sane da halin da muke ciki Khairy,zai kuma kawo mana ɗauki da izinin sa.Na sani rashin karatun ku yana damun ki to amma kiyi haƙury ina ji a jikina zakiyi karatu ko ba yanzu ba zaki cika burin ki na zurfafa karatu Ummu.Don haka karki cire rai da rahaman ubangiji ku cigaba da addu’a kawai Allah zai kawo mana mafita.Maza ɗakko wani kofin a zuba muku kokon ku ma ku sha ke da Aliyu kinji Mamana.”
Khariyyah ta share hawayen dake zuba mata tana me gyaɗa kai ta miƙe ta fice don ɗakko cup ɗin.Malam Lawal ya maida duban sa ga Ahmad yana faɗin “Amadu kana dai ganin yadda rayuwa take gara mana ko?Nasiha ta a gareka a kullum shine ka sake dagewa da mai da hankali akan aikin garejin nan.Ka nemi sana’a ta halak kayi don ka rufa mana asiri da ƴan ƙanninka da kai karan kanka.Ban yadda da yawon maula ko bin gidajen mawadatan mu ba,kunfi kowa sanin irin yadda kuka taso kuka ganni ina gudanar da rayuwata,ni me yawan zafin nema ne don kawai in tallafe ku in inganta rayuwanku tare da kare mutuncin kaina.Ina da ƴan uwa mawadata kun sani amma baku taɓa ganin na je gare su da sunan naje maula ko bara akan ataimake ni ba,sai in su ne su ka ga dama su ka bani ɗan abinda su kai niyya,ba kuma komi yasa hakan ba sai gudun wulaƙanci.Allah ya gani nayi iyakan yina har kawo yanzu da ƙarfi na ya gaza lafiya ya kuɓuce min,duk da hakan kuma baka taɓa ji ko ganin na ɗauki sandata ina bin gidajen masu hannu da shuni da sunan naje maula ba.Don haka duk wani ɗa na da zai zama ɗan maula bazan taɓa yin alfahari da shi ba,ku tashi ku nemi halak ɗinku,kaine babba kaine kuma namiji don haka ka zama me kishin mu da sauran ƴan uwanka.Duk abinda zaka samu ka tuna dasu ka tallafe su musamman Mamana da take mace,ka kuma ji tsoran Allah a duk inda kake ka xama me riƙe amana da gaskiya,domin sune matakin nasara Allah yai maka albarka ya dafa maka a dukkan lamuran da xaka sanya gaba.”
“Ameen Malam insha Allah zaka sameni me aiki da dukkanin nasihohin ka,bari in tashi inyi shirin fita garejin zamu tafi da Aliyu shima.Abin da na samu sai na aiko shi da ɗan abinda xa’a ci da rana.”
“To shikenan tashi kaje Allah yayi albarka.”
Inna ta amsa da “Ameen ” ita kuma Khairiyyah da ta shigo riƙe da cup ɗin ta isa gaban Malam ɗin ta aje,ya dube ta da murmushi akan fuskan sa yana zuba mata kokon tare da tsare ta ta shanye a gaban sa,ana haka Aliyu ya shigo shi ma aka zuba masa ya sha,kafin Inna Salamatu ta sanar da shi zasu fita tare da Yayan sa Ahmad zuwa gareji.
Khairiyyah ne ta miƙe tana haɗa kufunan da suka gama shan kokon da su ta fice,don zuwa ta wanke ta maida su ma’ajiyan su.Ko da ta fito daga kitchen ɗin ɗakin da aka bar mata a matsayin mallakin ta ne,wanda yake falle ɗaya ne ɗan madaidaici me ɗauke da katifa sai drawern kayan sawan ta da sauran tarkacen ta,tsaf ɗakin yake cikin tsafta komi a kintse yake a kuma inda ya dace,wanka tayo ta dawo ɗakin don shiryawa ni dai kallon ta kawai na ke sabida yadda komi na ta ke birge ni,kyakykyawace na nunawa sa’a da alamu idan ta gama xama cikakkar budurwa za’ai kallon diri da kyawu.Color ɗinta me tsananin kyau ne sam ba fara bace sai dai akirata me hasken fata sosai ba mai duhu ba wanda turawa ke kira da (Brown skin) tana da hanci wanda ya tafi a miƙe zar tana da manyan idanu farare tas masu ɗauke da lashe’s gazar-gazar,ɗan ƙaramin bakin ta yafi komi ɗaukan hankali na,giran ta me cike da baƙin gashi cinkis tamkar anzana shi,shine abinda ya sake fiddo kyawun ta.Kaman yadda yalwataccen gashin ta da jelan kitson dake kanta ke reto bisa kafaɗun ta ya ɗauki hankali na.Doguwace amma tsayin ba irin can ɗinnan ba,tana da murjajjan jiki me ɗauke da lafiyayyan fata,kai kace a gidan hutu da jin daɗi take rayuwa.Cikin sauri-sauri take sanya kayan ta tana gamawa ta miƙe ta fice zuwa ɗakin Inna don tambayan Mallam zuwa gidan su Maryam Waziri da take son yi ta duba jikin ta,don kwana biyu kenan bata zo Islamiya ba.
So take tayi sauri taje ta dawo don kada azo yin kitso ko su samu wankau ya zam bata nan,ko da ta tambayesa ta sanar dashi inda zata ya bata izinin zuwa,tare da sanar mata cewa da ta je ta dubo jikin Maryam ɗin tayi sauri ta dawo gida kada ta yadda ta zauna,daga haka taima Inna sai ta dawo ta fito ta sake komawa ɗakin ta,Hijab ɗinta wankakke tas ta ciro daga drawern kayan ta ta sanya,ta fito fes da ita ta sanya takalmin ta ta fice daga gidan.Bayan tayi addu’an fita gida kaman yadda ta saba,duk wadda ya ganta ya ga natsatstsiyan matashiyan budurwan yarinya da ta samu tarbiya me nagarta.
******Lokacin da Khairiyyah ta dawo tun daga ƙofar shiga gidan na su ta ja ta tsaya,tana sauke manyan idanunta akan ƙatuwar motan da ta gani fake a ƙofar gidan su.Tsananin mamaki take yi tare da jin bugun zuciyan ta na sauyawa,tsora da fargaba na mamaye zuciyanta,ta shiga jan ƙafafun ta da taji sun mata nauyi tana takawa zuwa cikin gidan,zuciyan ta na ayyana mata wasu irin baƙi ne su kai da su ka zo a cikin irin wannan ƙatuwar mota haka?
Tana sanya kanta cikin zauren ta fara jiyo maganganu ƙasa-ƙasa na baƙin muryoyin da bata sani ba,hakan ya sa ta ɗaga ƙafa ta shiga cikin gidan bakinta ɗauke da sallama,idanunta suka sauka akan dattijon mutumin tare da wata mace a gefensa wacce itama da alama shekaru sun fara tura mata,Inna ce ta amsa sallaman da tayi yayin da mutanan duk su ka waiwayo su na sauke ganin su akan Khairiyyah,wacce tayi saurin risinawa tana gaida su cike da ladabi.Suka amsa da tsananin sakin fuska bata sake jiran komi ba ta nufi ɗakin Inna ta shiga,da Aliyu ta fara yin tozali kwance bisa ɗaya daga cikin kuzajjiyar doguwan kujeran da suka mallaka a ɗakin,kansa naɗe da bandeji fuskan sa ya haye yayi suntum da kumburi.Wani faɗuwan gaba ta ji ya sameta ta isa kusa da shi da sauri tana faɗi a fili “Subhanallah! Aliyu me ya sa me ka haka?”
“Tsautsayi ne ya same sa Khairy,waɗannan mutanan da kika gani ne suka kaɗe sa abakin titi akan hanyansa ta dawowa gida,Allah ma yasa mutanan ƙwarai ne da har su ka tsaya su ka dubi raunin da yaji har su ka kai shi asibiti.”
Inna ce me wannan maganan tana isa kusa da inda Aliyu ke kwance tana sake duba shi,Khairiyyah cike da alhini da tausayin ƙanin na su ta dubi Inna Salamatu tana faɗin “Allah sarki Aliyu Allah ya baka lafiya,kaman na san ba lafiya ba ina ganin mota a waje naji gabana ya faɗi.”
Sallaman Malam Lawal da shigowan sa cikin ɗakin dogare da sandar da yake doddogarawa ne ya hana Inna sake magana,ya dubi Khairiyyah yana faɗin “Mamana kinga tsautsayin daya sami qanin ki ko?Allah ma ya taƙaita da iya rauni ne kawai yaji babu karaya,kuma Allah yasa mutanan kirki ne suka kaɗeshi,da wasu ne yadda zasu gansa mara galihu sai suyi tafiyan su ba tareda sun tsaya ba.Amma wannan dattijon arziƙi ne da alama daga shi har me ɗakin sa sun san darajan ɗan adam.”
“Hakane Malam nima mutanan sun birgeni,dubi yadda su ke ta faman bamu haƙury,Allah dai ya saka musu da alkhairy ya kiyaye gaba.”
A tare Khairiyyah da Malam su ka amsa da “Ameen.” Malam ɗin na sanya hannun sa cikin aljihu ya zaro kuɗi masu yawa yana faɗin “Kinga abinda Dattijon ya bayar Salamatu yace a sake siya masa magani.Haƙiƙa Allah me rahama ne ga bayin sa ta hanyoyin da ba su yi zato ba,tabbas wani tsautsayin sai ya janyo maka alkhairy,ungu Mamana irga ki ga nawa ne kuɗin?”
Yaƙare maganan da miƙawa Khairiyyah kuɗin wacce tuni ta cire Hijab ɗin jikinta tana zaune a ƙasa kusa da kan Aliyu,ta amshi kuɗin fuskan ta na bayyana farin cikin ta itama da samun waɗannan kuɗi.
“Laaah! Malam wallahi har naira dubu goma ne kuɗin.”
Khairy tayi maganan cike da tsananin mamakin yawan kuɗin,murmushin farin ciki na sake bayyana akan kyakykyawan fuskan ta,suma dukkanin su da alama sunyi mamakin yawan kuɗin,Malam ya amsa yana me zama a bisa ɗaya kujeran one seater dake ɗakin yana duban Inna yake faɗin “Masha Allah,Allah mun gode maka da wannan ni’ima daka kawo mana,abinda za’ai yanzu Salamatu zaki tashi kuje nan kasuwan tudun wada ke da Mamana ku gwado mana kayan abinci dai-dai misali da duk wani ɗan abin da mu ke da buƙata.”
Inna ta gyaɗa kai cike da ƙaunar mijin ta,daya kasance ba shi da wani buri irin ya gansu cikin wadata da walwala,shi yasa har gobe ba ta nadaman kasancewansa miji kuma uban ƴaƴan ta duk da babun sa,domin tayi imani talaucin da suke ciki jarabawan su ne ita da shi domin da zafin nema yanasa a fita daga ƙangin talauci tabbas da tuni sunyi hannun riga da ba-bu tunda daɗewa,domin Malam mutum ne shi me zafin zuciyan neman na kansa da yin duk wani aikin ƙarfi don yaga ya rufa musu asiri sunfi ƙarfin ci da sha da sutura zuwa karatun yaran sa bakin gwargwado,amma da yake haka Allah yaso ya gan su babu yadda su ka iya.Ta sauke a jiyan zuciya tana faɗin “To shikenan Malam bari mu hanzarta da ma gashi rana ta fara yi ba tare da mun san abinda za mu ci ba,amma ka ɗauki koda naira dubu biyu ne ko dan siyan maganin ka.”
Yadda tai maganan cike da narke murya alamun magiya yasa Malam Lawal sakin ƙayataccen murmushi,ƙaunar matansa na sake huda jinin jikin sa,tabbas ya sani samun mace haƙurarriya me ɗinbin tawakkali da haƙuri da ba-bu irin Inna Salamatu sai an tona cikin wannan xamanin,bata taɓa nuna masa gajiyawa da halin da su ke ciki ko tai masa gorin talauci ba,sai ma yadda take aiki da jikin ta da lafiyan ta don a taru a rufawa juna asiri.Ya dube ta cike da ƙauna yana faɗin “Karki damu Innan su ku je da kuɗin duka ba sai na ɗauki komi ciki ba,sai dai Khairy ta ɗauki kwalin maganin can sai ku siya mun kwali biyu,sauran kuɗin ku siyo duk abinda ya dace,zaman mu babu abinci ba ƙaramin ɗaga min hankali yake ba,ina baƙin cikin mu wayi gari ba mu da abinda za mu ci,amma bakomi Allah na sane damu kuma ina da yaƙinin zai kawo mana mafita cikin rahaman sa da tausayinsa ga bayin sa,kuyi maxa ku je ku dawo ɗin.”
Kusan a tare Inna da Khairiyyah su ka miƙe don cika umurnin sa,su kai masa sai sun dawo su ka fito sanye da Hijaban su a jiki,tafiya su ke su na tattauna matsalolin su da yadda rayuwa ke gara mu su,Inna na sake kwantar ma Khairiyyah da hankali tana nuna mata muhammancin haƙury akan duk halin da bawa zai tsinci kansa a ciki watarana zai wuce,ya zama tarihi har su ka tari a dai-daita sahu su ka shiga kafin su kame bakin su bayan sun sanar da ɗan sahun inda xasu sauka.
Bakin gwargwado sun siyo kayan abincin da zasu ci,wanda a ƙallah zai mu su kaman kwanaki huɗu zuwa biyar,cike da farin ciki su ka dawo gidan su ka ajiye komi a inda ya dace bayan sun zube kayan Malam ya gani ya sama siyayyan albarka,tare da yin addu’an fatan alkhairy ga wanda ya basu kuɗin.
Koda Aliyu ya tashi daga bacci Inna ce tai masa wanka ta gasa masa jikinsa,Jallof ɗin taliya da suka dafa ta kawo gaban sa ta aje bayan ta sanya masa kaya,da kanta ta ciyar da shi Khairiyyah dake gefe riƙe da magungunan sa da ta ɓallo ta miƙa masa tana masa sannu,bayan ya shanye maganin sai Inna tace ya ɗan zauna har abincin yabi jikin sa sai ya sake kwanciya.
Ƙarfe huɗu Khariyyah ta fito cikin shirin tafiya islamiyyah,tana sanye da Maroon ɗin Hijab wanda shi ne matsayin uniform na islamiyan,sosai kalan yake mata kyau matuƙa,kafaɗan ta rataye da jakan littafan ta,taima su Inna sallama ta fice su na mata fatan dawowa lafiya, a ƙasa suke takawa xuwa islamiyan kasancewan basu da nisa can ƙasan layin su ne,tafe take tana jin nishaɗi a cikin zuciyanta,tana tsananin son karatu(Both) boko da islamiya kuma Allah ya bata ƙwaƙwalwan ɗaukan karatun,tana da masifan ƙoƙary a hadda da islamiyan na su,shiyasa malaman ke alfahary da ita,lokacin da suka fuskanci matsalan school fees(kuɗin makaranta) na son kawo ma karatun Khairiyyah matsala sai suka yafe mata biyan kuɗin makarantan baki ɗaya,hakan ba ƙaramin faranta ran Khairiyyah da iyayen ta yayi ba,Malam da kansa ya je har makarantan yai ma malaman godia.Yanxu matsalan dake damun Khairiyyah yana cin xuciyanta bai wuce matsalan rashin cigaban karatunta na boko ba,gashi har an dosa shekara guda,wannan tunanin da tayi ne ya rage walwalan ta,haka dai ta ke takawa sannu a hankali har ta karya kwanan da zata ɗauki hanyan makarantan direct,idanunta ta sauke akan ƙaton gidan da aka gina cikin watanni uku kacal,gini ne na gani na faɗa wanda kaf anguwan dama sauran layukan dake gaban su babu gida kwatankwacin sa,tun da ake ginin duk wanda ya zo wucewa sai ya tsaya ya kalla bare kuma yanxu da aka kammala komi tarewa acikin sa kawai ya rage wa ma su shi,gini ne da ta sha ji mutane na faɗin irin na ƴan Abuja ne,idan tace gidan baya birgeta to tabbas ta yi ƙarya shi ya sa duk sanda zasu wuce ta gaban gidan ita qawarta abokiyan jerawanta zuwa islamiya Ruky Sulaiman sai sun tsaya sun morewa kallon sa,tana tasbihi ga Allah daya yo ma su arxiƙi da marasa shi,tana cikin ƙarewa gidan kallo ne taji an dafa kaɗunta ta baya,cikin sauri tayi saurin waiwayowa idanunta na sauka akan Ruƙayyah Sulaiman.Wacce ta kasance Qawa a gun ta kuma maƙotan juna da suke suna abin arziƙi sosai,kuma aji ɗaya suke a Hadda da Islamiyya baki ɗaya.Ganin Ruky ce hakan yasa Khairiyyah sakin bayyanannen murmushi cikin muryan ta da yake a narke cike da ƴar shagwaɓa ta ke faɗin “Kai Ruky Sulaiman kinfa so tsorata ni.Ina nan ina kallon aljannan duniya sam bana gajiya da ƙarewa gidan nan kallo,da alamu mamallakin gidannan ba ƙaramin dukiya ya tara ba.”
Ruky ta dubi Khairiyyah itama tana sakin murmushi,tare da kallon gidan tana faɗin “Tabbas kam yana da kuɗi sosai a yadda naji su Yah Kamal na labari,sun ce ma wai nan da sati biyu masu gidan zasu tare anan za su yi azumi har zuwa sallah shi da iyalin sa.”
Khairiyyah ta jinjina kai tana faɗin “Masha Allah to Allah sa su zame mana maƙwabta na gari,don ni lamarin masu kuɗin yanzu yana bani tsoro yadda sam babu tausayin talaka da sanin darajan sa a zukatan su inba za su bautar da shi bane.”
Yadda Khairiyyah tayi maganan cikin tsananin raunin murya,yasa Ruky sake jin tausayin su ya kamata.Ta sani duk da suma talakawan ne amma sau dubu sunfi su Khairiyyah wadata tunda su dangin mahaifinsu suna taimakon su akai-akai,ba kaman su Khairy bane da basu da kowa a garin sai Allah sai wanda ya dubi Allah ya tallafa musu.Har su ka jera su ka isa islamiyan na su ba su daina tattaunawa akan halin masu kuɗin yanxu ba waɗanda da yawan su basa son taimakon talakawa.
Ƙarfe Six na yamma aka tashe su still tare da Ruƙayyah suka jero zuwa gida,gida uku ya raba tsakanin gidan su Ruky da na su Khairiyyah,sun zo daf da ƙofar gidan su Ruky su ka tsaya su na sallama da juna,Ruƙayyah ta dubi Khairiyyah tana faɗin “My Khairiyyah idan an taso skull gobe zan zo ki ɗan kwashe min kaina,daga nan kawai sai mu wuce Islamiyyah tare zan taho da shiri na.”
Khairiyyah ta zabgawa Ruƙayyah harara tana faɗin “Ai tun da na ji yadda kika karya murya wajen kiran sunana na san zancen kitso ne,to shikenan Allah ya kaimu goben lafiya ki gaida Guggo.”
“Zata ji Khairy ke ma ki gaida min Inna.”
Cewan Ruky tana shigewa gida ita kuma Khairy ta kamo hanyan zuwa gida,zuciyanta cikeda kewan karatunta na boko data rasa,wasu hawaye taji na son taruwa mata tayi saurin maida su tana tuna nasihan Malam a gare ta ” _Khairy ki miƙa lamuranki ga Allah tare da godema ni’iman sa gare ki,ki sani kinfi wasu gara ke kin kai matakin aji a uku a sakandiri ɗin sannan kika tsaya.Kin iya rubutu da karatu hatta ɗan turancin nan kina ji kin kuma iya shi bakin gwargwado,wasu na nan cikin duhun jahilci na babu Arabi ba Bokon,ke kuma duka Allah yai miki ni’ima da samun su bakin gwargwado,don haka ki gode masa idan da rabon zaki cigaba sai ki ga Allah ya kawo wani hanyan._ ”
Tunanin ta ya katse ne a lokacin da ta iso ƙofar gidan su,ta sauke ajiyan zuciya tana jin zuciyan ta na yin sanyi a duk sanda take tuna irin rarrashi da nasihan Malam a gare su,tana sake jin ƙaunar sa na sake ratsa zuciyan ta.
Da Yah Ahmad suka kusa gwabza karo zai fita,tayi saurin ja da baya tana faɗin “Sorry Yah Ahmad.”
Ya balla mata harara yana faɗin “Allah ya shirya ki Khairy mutum yai ta tafiya baya kallon gaban sa.”
Tasaki dariya tana raɓa shi ta wuce zuwa cikin gida
Shatu Ɗansabo ce 👌🏻