Kannywood News

Izzar So: Daraktan Shirin Izzar So Nura Mustapha Waye ya rasu

Izzar So: Daraktan Shirin Izzar So Nura Mustapha Waye ya rasu

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Nura Mustapha Waye

Innalillahi wainnailaihirrajiun Allah Ya Karbi Rayuwar Nura Mustapha Waye Director IZZAR SO Za Ayi Zanaidarshi Karfe 11 Insha Allah, Allah Ya Yafe Masa Kurakuransa Amin, Allah Yasa Idan Tamu Tazo Mu Cika Da Imani Amin.

Izzar so

YA SAMU SHAIDA MAI KYAU

 

Mun wayi gari da samun labarin rasuwan Daraktan shirin Izzar-So Malam Nura Mustapha (Waye)

 

Kasancewar ni ba ma’abocin kallon fina-finan Hausa bane, Wallahi ban sanshi ba, amma naga ya samu shaida mai kyau

 

Matana ta kirani a waya take bani labarin wannan bawan Allah, mutumin kirki ne, tace min ya tsarkake shirin film dinsa, yana bawa addinin Allah kariya a fim dinsa, babu batsa balle ruguza tarbiyya

 

Matata tace min duk karshen fim dinsa sai ya yabi shugaban Halitta Annabi Muhammad (SAW) saboda tsananin kaunar da yake yiwa Annabi (SAW)

 

Nura Mustapha yayi mutuwar bazata, Ali Nuhu yace ko jiya ma suna tare a gabansa yayi posting a Instagram, bai sani ba ashe saura awanni ya koma ga Mahaliccin mu

 

Muna rokon Allah Ya jikansa, Allah Ya kyautata namu karshen, Allah Ya kara mana kaunar Ma’aiki (SAW)

Nura Mustapha Waye…

Yana daga cikin Daraktocin da suka so juya Duniyar kanywood zuwa makaranta ta musamman yafito da abubuwa da yawa wanda wani abun kafin kazo karatun za’a kwana biyu musamman yanda matasan mu suka watsar da zuwa makarantu islamiyya, yadda yake kawo abubuwan da suke isar da sako da nuna tarbiyya da koyi da magabata uwa uba fito da koyi da nuna soyayyar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) da Ahlil baiti.

.

Film ɗin Izar So yana daga cikin Film ɗin daya samu karɓuwa sosai inda yara, manya, iyaye da ƴaƴa suke haɗuwa su kalla batare da fargabar furuci ko nuna wani abu daya saɓa da al‘ada ba.

Nayi matukar jinjina wa Mustapha Waye sosai wajen fito da karatu sosai musamman wani scane ɗin a yake jan hankali mutanen da suke zuwa su tarar ana Sallah su tawo da gudu batare da sunyi kabbarar Harama ba, kuma mutane dayawa sukan hakan.

.

Film ɗin Izar So shine film ɗin da yayi daraktin duniya ta sanshi idan ya ankarar ma matasa yanda ake tsarki, Sallah, hakuri, mu’amala tsayawa akan gaskiya da kuma soyayyar Annabi da ahlinsa kuma fito da ayoyi da hadisai, Nura Mustapha Waye ba iya daraktan Film ɗin Hausa yake ba har wakokin yabo yana Daraktin.

.

Inalillahi wainna ilahi rajiun

A yau ne aka tashi da rasuwar Mustapha inda aka tabbatar da lafiya kalau ya tashi rashin lafiya lokaci kaɗan ce tayi ajalinsa, tuni dai yanzu haka anyi jana’izarsa a gidansa dake Goran dutse inda aka binne shi a makabarta dandolo dake goran dutse, muna addu’ar Allah yajikansa yayi masa rahama Allah yasa Annabi ya tarbeshi Amin.

Hassan Naseer Musa Gwammaja

3/7/2022

3 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!