Jan Kunne Hausa Novel Complete

Angela Bassett

Jan Kunne Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

[01/10, 7:37 pm] +234 703 966 0069: 🧏🏾‍♀️ *JAN KUNNE 🧏🏾‍♀️*

 

_True life Story_

 

 

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*

 

 

this book is written

by

*Sadiya Nasir Dan*

 

 

*BISMILLAHI RAHMAN ALRAHIM*

 

Dukkan godiya ta tabbata ga ALLAHU subuhanahu wata’ala, tsira da aminci sutabbata wajen fiyayyen halitta ANNABIN rahma ( S.A.W ).

 

 

Page 1

 

Ina Tafiya ina Sakawa da War-warewa cikin Zuciyata! Tunanina ina Abba ya tsaya haka! Har ya Mance Dani A Makaranta? Cike da Damuwa na Karasa Gidan mu, Ganin Motar Abba A Kofar Gida yasa na Sauke Ajiyar Zuciya na Fada Cikin Gidan ko Sallama Banyi ba! Sanin Bana Magana da Suwaiba Matar Abba.

 

Ina shiga Na jiyo Muryar Gwaggo Habiba tana Magana cikin Daga Murya! A hankali na Karasa ta Window baya! Na dakin Aunty Suwaiba na Kasa Kunne “Gaskiya Nafara Gajiya da Irin Bakaken Maganganun da Ake Fadamin A Kanka! Haba Auwalu Sai Kace Akanka Aka Fara Haihuwar Yarinya Uwarta ta Mutu? Ka dauki Soyayyar Duniya ka daura Mata? Gaskiya wannan ba Tarbiya bace, Na Rantse da Allah kaGidan i Matakin Gyara.

 

Suwaiba Yarinyar kirki ce! Duk Cikin Matanka daka Aura kana Sakewa Babu wacce take da Hakurin ta, to Wallahi na Fada Maka karka bari Suwaiba ta Kubuce Maka! Na Tabbata babu Wanda zai sake Baka Aure! Indai A Garin Bauchi ne”

 

“Amma Yaya Habiba Kinsan dai…

 

“Ya isa Auwalu! bana Bukatar jin Ko Kalma Daya daga Gareka! Ni dai na fada Maka, Kaji Tsoron Allah, Suwaiba Don Allah Kiyi Hakuri, Yanzu Ina Hajaran take Auwalu?”A take Gabana ya Fadi! Jin Yaya Habiba Ta Ambato Sunana! A hankali na koma da Baya nabar Gidan Gaba daya.

 

Gidan su Waleeda na Nufa da Sauri! Dankar Yaya Habiba ta Ganni A Hanya! Bare harta Fada min Maganar da zata Tabamin Zuciya! Sallama nayi na Fada Cikin Gidan, Kasancewar Rana tayi! Ga zafi! Yasa Babu kowa A Harabar Gidan, Dakin Maman Waleeda na Nufa! Jin Hayaniyar Yara A wajen.

 

Sallama nayi na daga Labulen dakin, Amir ne ya taso da Gudu ya Rungumeni “Aunty Hajara Oyoyo” daukarsa nayi Cak muka Shiga “Auta ina Waleeda?”

 

“Barin kirata tana Ciki” to nace na saukesa yayi dakin Maman su, Maida Hankalina nayi Jikin Kallon da Yara suke A TV, Sai jin Hanun Waleeda nayi A Jikina, dan Murmushi Nayi “Baki Karasa Gida bane? Na ganki da Uniform?”

 

“Humm ke dai Bari Kawai Waleeda, Ina shiga Gida naji Muryar Gwaggo Habiba! Tasa Abba nah A Gaba tana Kan tsigaleshi Akan Aunty Suwaiba, Ni A tunanina zan dawo in samu Abba ya Saki Aunty Suwaiba, Ashe An samu Munafukin da yaje ya Fada wa Gwaggo Habiba? Shine na samu Na fito ba tasan na shiga Gidan ba, bare ta sani A gaba ta zageni Tsaff”.

 

Kama Baki Waleeda tayi “Iko Sai Rabbi! Hajara ni Banga Mai Matar nan ta tsare miki ba! Amma kin dauki tsanar Duniya kin daura Mata? Haba Hajara! Kar kiyi Anfani da Son da Abba yake Miki kina Hana shi zaman Aure! Don Allah?”

 

“Huhmm ke Ai kullum baki Gane meye Ake nufi! Matar nan shiga Hakkin mu take! Ba hali ta Ganmu tare zata Fara Wani shan Kamshi! Tana Kumbura, shiyasa kawai nace Ya saketa, Mutum da Mahaifinsa Amma bayi da Ikon sakewa dashi?”

 

“Huhmm! Amma kiyi Tunani! Kar Ace Abba ya fiye Aure Sake, yanzu Aunty Suwaiba ko Shekara ba tayi ba! Kuma kike so ya saketa?”

 

“Ni ya isheni Malama! Mubar zancen! Ina Mama?”

 

“Na dawo Islamiya na samu Bata Nan! Yanzu nake Shirin shiga Kitchen na daura Taliya Muci Kafin ta dawo”

 

“Shikenan Muje in tayaki” Hijab Dina na Cire na Rataya A Jikin Kofa na Ajiye Jakar Makaranta na muka Nufi Kitchen, Muna Aiki muna Hira! A haka har Muka Kammala, Taliyar ta zuba Mana muka dawo Harabar Gidan inda Akwai Inuwa muka zauna! Saka-makon zafin Ranar da Ake kodawa.

 

Ina sa Hanu A Taliya Yaro yana shigowa bakinsa dauke da Sallama! Dago idanu nayi na Kallesa gamida Amsawa “Wani ne ya Aikoni wai Hajara tazo Nan Gidan?” Murmushi nayi domin Nasan Abba ne “Kace Gani Zuwa! tsame Hanuna nayi na dubi Waleeda, Wallahi Abba ne! Barinzo” Zaro Idanu Waleeda tayi, zaki sha Fada kenan? Bai San kinzo Nanba?”

 

“Kibari Kawai ina zuwa! Nasan meye zance dashi” Dakin Maman Waleeda na shiga na dauko Hijab Dina na Fice, A jikin Motarsa na Hangosa ya Harde Hannaye! Kana Ganin Fuskarsa kasan yana cikin Damuwa, Take naji Raina ya sosu, Jiki A sanyaye na Karasa “Sannu da zuwa Abba nah?”

 

Dago idanu yayi ya Kalleni “yanzu kin Kyauta kenan Hajar? Babu inda ban dubaba Amma Bakinan? Me yasa kika kasa Jirata kika Zo nan?” Dan Turo Baki nayi na dubesa “Abba Naga An watse yasa na tafi Gida, ina shiga Naji Muryar Gwaggo Habiba tana Magana Akan Aunty Suwaiba shine kawai na fito nabar Mata Gidan, Amma kayi Hakuri”

 

“Shikenan ya wuce Amma karki Sake, Suwaiba tana Neman Mu Sami Matsala Babba Hajar, Sabida Wulakanci Harta taka Kafarta babu Izini taje Gidan Yaya Habiba takai Karata? Kuma Akanki? Bayan tasan Duk Duniya Babu wanda zai Kawo Kushe A Kanki Ya sha A Hanuna?”

 

Sake Turo Baki Nayi Abba “Wallahi Na tsani Matar nan, Ka Sallameta Kawai! Ni Mu Zauna Kawai Nida Kai Abba nah! Bana So ka sake Wani Aure” Kwafa kawai Abba yayi ya bude Motor ya shiga, Karasawa nayi Na bude daya Gefen nima na shiga, Sai da Muka Shiga Layin Gidan mu Kafin ya Dubeni, Hajar “Kin san Meye Yaya Habiba Tace?” Da Sauri Nace “Aa Abba?”

 

“Humm wai zata daukeki ki Koma Gidanta duk Ranar da Suwaiba ta sake Kai Mata Kara Akanki” Dafa Kirji nayi na Dubesa “Abba Nikan Mutuwa zanyi Wallahi idan na koma Gidan Gwaggo Habiba, Wallahi bata So na” Cak ya tsaya da Motar har sai da Na tsoratani, Rai A bace ya dubeni “Hajar baki da Hankali ne? Meya kawo Zancen Mutuwa Kuma?

 

Kin Mance Yaya Habiba Ita kadaice Nake Gani Naji Sanyi A Zuciyata? Don Allah kar kice zaki Kullaceta, Awannan Gabar bazan Zuba Idanuba, Ki taimakeni Don Allah? Rashin Mahaifiyarki yasa Na Susuce da Soyayyarki! Yau idan Kika bar Duniya ya kike Ganin Rayuwata zata Kasance? Kar kisake Fadin Haka idan Har Kina Sona Kinji?”

 

Ajiyar Zuciya na sauke “Insha Allah Abba nah Muna tare Ba yanzu Zamu Mutu ba”

 

“Yauwa Hajar! Zuciyar Abban ta” Dariya nayi, Hira ya Rinka Jata dashi Har Mika iso Kofar Gidan.

 

“Don Allah Duk Abinda Suwaiba zata Miki Karki Kulata, kinji Dai Abinda Yaya Habiba tace?” Turo baki nayi “shikenan Abba Naji” Bude Murfin Motar nayi na Fice, Sai da Yaga Shigata cikin Gidan kafin ya tada Motar.

 

A zaune na sameta A tsakar Gida tana Gyara Alayyahu! Wani Irin Kololon Bakin Ciki naji A zuciyata na Ganinta da nayi, Ba tace dani Uffan ba Na wuce, Nima Bata isheta Kallo ba Na Ratse ta Gefenta Na wuce dakina.

 

Wayata na Ciro Keypad da Abba ya siyamin idan Ina da Bukatar wani Abu, Dialling Number Abba Nayi, Ringin daya Ya dauka, Cike da Shagwaba nace “Abba meye kace Aunty Suwaiba ta dafa ne?” Daga bangarensa Yace “Tuwo Miyar Taushe tace za tayi” Dan daga Murya nayi Yanda za taji “Abba ba zanci Tuwo ba, Kawai Zan dafa Mana Cus-cus da Kai! Idan ka dawo Muci, Shuru Yayi Baice Komaiba, Abba Kayi Shuru kuma?”

 

“Shikenan ki dafa Hajar idan Har kina so” Cike da Murna na kashe Wayar na cire Uniform Dina Nasa Kayan Zaman Gida, Alola nayi Na daura Sallar Azahar! Ina Idarwa na fito nayi Kitchen, Aunty Suwaiba tana ciki tana Hada Miyar Tuwo, Tabe baki nayi Na shiga Store din Gidan na Dauko Cus-Cus guda Daya, Kayan Miya nagani A Markade Cikin Blender! Na dauko na Zuba cikin Tukunya “Kutumar Uba……. Kalmar data Fito daga Bakin Aunty Suwaiba kenan….

 

 

*SADIYA NASIR DAN ✍🏽*

 

Ga Masu Bukatar Tallata Musu Hajarsu! Zasu Iya tuntubata A Wannan Lambar 07051244211, Watsp Kawai……

[01/10, 7:37 pm] +234 703 966 0069: 🧏🏾‍♀️ *JAN KUNNE 🧏🏾‍♀️*

 

_True life Story_

 

 

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*

 

 

this book is written

by

*Sadiya Nasir Dan*

 

 

*BISMILLAHI RAHMAN ALRAHIM*

 

Dukkan godiya ta tabbata ga ALLAHU subuhanahu wata’ala, tsira da aminci sutabbata wajen fiyayyen halitta ANNABIN rahma ( S.A.W ).

 

 

Page 2

 

“Hajara Kina da Hankali Kuwa? Kiga Na Ajiye Kayan Miya Zanyi Anfani dashi ki dauka? Uwar miye za kiyi da Kayan miya Bayan Gashi Ina Girki? Kawai Neman Magana don Kar A Zauna Lafiya?. Tabe Baki Nayi Na cigaba da Neman Kayan Hadin Girki na, Magana nake Miki Fa? Amma kinyi Banza Dani? Kuma Kina cigaba da Abinda Kikeyi?”

 

“Kuyi Ta Kanku! Nima Nayi Ta Kaina Dariya Ba…. Bakina Naji Yamin Nauyi! Take Naji Wani Irin Zafi yana Tsara Kwanyar Kaina, Hanu Nasa na Shafa Bakin, A Razane na Kalli Hanuna, Nashiga Uku Ta kasheni! Wayyo Allah Bakina”

 

“Na Rantse da Allah! Muddin ki kace Raini zai Shiga Tsakanina dake wahala za kisha, Dubeni da Kyau! Da nayi Auren Wuri Dana Haifeki Hajara, Akan me? Don Ubanki yana Biye Miki sai Ki nemi Ki Takani? To Mu zuba mu Gani Tsakani dake, Duk Abinda Za kiyi ki Tsaya Iya Kan Auwalu? Amma ki kace Gonata zaki Shiga Akwai Matsala Wallahi”

 

Kallonta Nayi Ido Jazur “Kika Fasa min Baki? Ni Hajara Suwaiba kika Fasa wa baki?”

 

“Ahayyeee! Na fasa miki Baki Hajara! Don Allah idan Uban naki yazo kice ya Sallameni! Ko Anfada miki Dan Autan Maza ne? Yana Sallamata zan Sami Miji Gangariya, Amma bazan dauki Raini Agun Yar Shekara Goma sha Hudu ba, da Allah bani Kayan miyata”

 

Bangajeni tayi har Sai da na fadi Kasa ta dauki Tukunyarta, Kuka Nasa da Sauri nayi Dakina da Gudu na dauki Wayata, Number Abba na Kira, Ringing daya Ya dauka, A Rude nace “Abba! Aunty Suwaiba sabida Nace Bazanci Tuwo ba! Naje Dafa Cus-Cus! Kawai ta Kamani ta Rinka Duka Kamar Jakarta, Gashi ta Fasa min Baki! ta kuma Taka min Wuya, wayyo Abba zan Mutu”

 

“Innalillahi wa’inna Ilaihi Raju’um, Kalmar data fito A bakinsa kenan, Ina zuwa Hajar ki Kwantar da Hankalinki. To nace na Katse Kiran na kwanta A gadona na cigaba da Risgar Kuka.

 

Suwaiba? Suwaiba? A hasale Abba yake Magana, Ajiyar Zuciya na sauke na fito Tsakar Gida, yana Ganina ya Nufo Gareni ya Kama Hanuna Jikinsa harna Rawa, Maida Kallonsa yayi Kan Fuskata, Nashiga Uku! Haka bakin naki yayi, ke Suwaiba? Wallahi idan Baki Fito ba zan Saba Miki?”

 

A Gadarance ta Fito Dankwalinta A Saman Goshi “Lafiya kake Kwalamin Kira Haka? Kamar wacce nayi Sata Auwalu?”

 

“Auwalu? Abba ya Mai-Maita, Lalle Suwaiba Kina Neman Tashin Hankali! Meye Hajara ta Miki da zaki Kamata Ki Mata Irin wannan Dukar Sai kace Yarki? Ni Ubanta ban taba Daukar Hanu na Bugeta Haka ba?”

 

“Naji Niba Uwarta bace! Amma Na bugeta! Kuma wallahi duk Ranar data Sakemin Makamancin Abinda Tamin Yau Na Rantse da Allah Saina Fasa Mata Baki! Akaro na Biyu! Akan meye? Kawai don Ina Auren Ubanta? In Ajiye Kayan Miya zanyi Anfani dashi ta dauka ta Juye? Inyi Mata Magana ta Fara min Waka? Kai A Matsayinka na Uba! Idan Uwarta tayi wa Haka zata Barta?”

 

“Eh Lalle Suwaiba! Wato Zuwan da Yaya Habiba Tayi Gidan Nan! Dama ta baki kimin Rashin Arziki kenan? Zanje na Sami Yaya Habiba Ni bazan iya zama da Matar da Baza taga Mutuncina ba! Duk Cikin Matan Dana Aura Babu wacce takai Hanu Jikin Hajar sai ke? To Wallahi bazan daukaba! Ya zama dole Ki gyara”

 

“Meye saika wani Sami Yaya Habiba? Ai Igiyar Auren Kai keda iko da Ita? Don Haka in har Hajara za tayi Abinda bai dace ba na Hukuntata kazo kana Kumfar Baki Akai! Toka Sallameni Bakomai! Nayi Iya Kokarina Akanku Amma Baku Gani! Don Haka Ba’a dole”

 

“Suwaiba ni kike Fada wa haka?”

 

“Eh Auwalu na Gaji ne! Nima A Wuya nake” Kwafa Yayi ya Dubeni “Sa Mayafi kizo Muje Gidan Yaya Habiba! A Yau zan Kawo Karshen Wulakancin da Suwaiba take miki, kiyi Hakuri Kinji Hajar?”

 

 

“Mtsww! Ta Jima ba tayi Hakuri ba! Aikin banza kawai” Daki ta Koma Abinta Tabarmu A tsaye. Turo baki nayi “Abba Tace ba’a zama dole! Don Allah ka Sauwake Mata! Ni Wallahi in har tana Gidan Nan to Ka nema min wani Gida na zauna! Kar Watarana ta Kasheni?”

 

“Kiyi Hakuri da Kalmar Kisar Nan? Jawo Kunnena yayi Yanda Aunty Suwaiba ba zata jiyo me Nake Fada ba! Hajar idan na Sauwake Mata Yaya Habiba daukarki za tayi, ko Kin Mance da Maganar dazu ne? Ke dai Fito kawai? A sannu zan Tusa Mata Bakin cikin da yafi Wanda Ta tusa miki”

 

“Shikenan Abba nah, Hararan Dakinta Nayi na wuce dakina na dauko Mayafi Na fito, Mutafi Abba?”. Chemist muka Wuce Direct Aka Wanke min Baki, Ganin Abba A wajen yasa Nayita Narkewa Kamar Mangyada ina Shagwabewa.

 

Ina Kallon idon Mai Chemist din Sai Kallon banza yake min, Abu ne da Za’ayi shi A 2Minute, Amma Sai Gashi Muna Neman 30Minute, Ana Gamawa Abba ya wuce Damu Gidan Abinci Mafi Tsada A Garin mu, Anan Muka cika Cikin Mu Tam Nida Abba nah.

 

Ganin Karfe Uku da Rabi yasa Muka dawo Gida, Aunty Suwaiba tana dakinta Muka shigo, Abba ne ya dubeni “Je kisa Uniform barin zo” to Nace na wuce Abuna, Ina ganin Abba ya shiga Dakin Aunty Suwaiba naji Raina yayi Matukar Baci, Wato duk Abinda tayi Min Abba zai iya Kulata? Kasa Nutsuwa nayi, A hankali na Fito na zaga ta window Baya! Na kasa Kunne! Na Fara jiyo Abinda Suke Fada.

 

“Bazan iyaba Auwalu! Ka Riga kaba Hajara dama ta gama Rainani, duk Irin Abinda nake Muku Baku Gani! Wallahi Auwalu Na Gaji! Kai Kanka Kasan na Shanye Abubuwa da Dama! Ban taba Fada ma wani ba! Yaya Habiba ma bakomai na Zaiyana Mata ba, kai Kasan wallahi da Baka isa kasha ba”

 

“Matsalata dake Suwaiba Zuciya! Ke Kanji Kinsan Halin Yara! Duka Bashi daga Cikin Tarbiya! Nasan kina Kokari! Amma harga Allah naji Zafin Dukar Hajar da kikayi! Duk da Na fahimci Laifin Natane! Amma kinyi Saurin Yanke Hukunci.

 

Don Allah Nan Gaba duk Abinda zata Miki ki Fadamin! Ni Zan Hukuntata da Kaina, Bana So Mu cigaba da Samun Matsala A tsakaninmu Akan Hajar! Haba Suwaiba! Shikenan Nidake Raha tana Neman Kauce Mana? Ko Tarairayar da kike min yanzu bani Samu? Haba Suwy Tawa”

 

Dan Shewarta naji! Take naji Raina ya Dada Sosuwa “Ai ba’ace wa Yaro Yada Garma Yaya Auwalu? Kuma wallahi Da Abinda na shirya Maka! Kaida Kara Kusantata Ba Nan Kusa ba! Sabida Na Sanka Akan wannan Hidimar baka da wasa”

 

“Haba Suwy Kogin Madara! Ai kinsan bazan Iyaba, dole Zuwa Dare zanyi Biko! Irin wannan Duniyar da kike Aikani? Ai dole in Susu ce Suwy Maliya, Danzo Mana Mugaisa! Dazu sai wani Turosu Kikeyi sabida kinsan bani Ganinsu na Kyale”

 

“Yaya Auwalu kenan! Ai nakane Gasu Taba”

 

“Yauwa Ko kefa, Wayyo Dadi! kinga Somin tabi kenan? Barin Kai Hajar Makarnata na dawo! Yau Akwai Aiki! A shirya Kafin na dawo! Don Wallahi Sakon naki Ta Amsu Suwy Maliya”. A hankali na Bar wajen na dawo daki! Zuciyata kamar zata Fashe! Kenan Abba yafi son Aunty Suwaiba Akaina? Lalle kuwa Akwai Sake.

 

“Hajar kin shirya?. Ina jin Haka na kwanta A Gadona na Fara Rawar Dari, Jin Shuru Ban Amsaba ya shigo, Subhanallah Hajar Jikin ne? A hankali nace “Zazzabi na keji bazan iya zuwa Makaranta ba Abba”

 

“Innalillahi sannu Hajar Allah ya Baki lafiya, ko zamuje Asibiti?”

 

“Aa Abba idan nayi Barci zanji dai-dai”

 

“Toshikenan Allah ya Baki lafiya ina zuwa” da Sauri ya Fita! Bayan 2Minute sai gashi da Aunty Suwaiba! Tasa Wasu Tsinannun Riga da Skatt, duk Rabin Nonon ta A waje, Kallo daya Nayi Mata na kauda Kai “Sannu Hajara Ashe Zazzabine? Allah ya baki Lafiya! Kina Kiyayewa Don Allah! Sabida Lafiyarki” idan Gawa na Magana to Nayi, Sanin Halina yasa bata sake cewa Komaiba ta Fice.

 

Maida Kallona nayi Gun Abba! Naga Gaba daya Hankalinsa na wajen Aunty Suwaiba, Da Karfi nace “Innalillahi wayyo Kaina” A Rikice ya Hayo Gadon ya Tallafi Kaina ya daura A Cinyarsa “Sannu Hajar Allah ya baki lafiya”

 

“Ameen Abba, Amma jikin naki babu Zafi Ai?”

 

“Eh Abba cikin Jikina kemin Zafin”

 

“Subhanallah Sannu ko? Kiyi Barcin Barin Watsa Ruwa! Idan Kin Farka Baki daina jiba dole za muje Asibiti Hajar” Hawayene ya zubo A Fuskata “Abba Don Allah ka zauna Anan! Kayi Wankan A dakina! Idan ka tafi inaga Mutuwa Zanyi………….

 

 

*SADIYA NASIR DAN*

 

 

 

Ga Masu Bukatar Tallata Musu Hajarsu! Zasu Iya tuntubata A Wannan Lambar 07051244211, Watsp Kawai……

[01/10, 7:37 pm] +234 703 966 0069: 🧏🏾‍♀️ *JAN KUNNE 🧏🏾‍♀️*

 

_True life Story_

 

 

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*

 

 

this book is written

by

*Sadiya Nasir Dan*

 

 

*BISMILLAHI RAHMAN ALRAHIM*

 

Dukkan godiya ta tabbata ga ALLAHU subuhanahu wata’ala, tsira da aminci sutabbata wajen fiyayyen halitta ANNABIN rahma ( S.A.W ).

 

 

Page 3

 

Ajiyar zuciya ya sauke “Kiyi hakuri ko Hajar? Suwaiba ta riga ta surka ruwan A dakinta, Kinga idan na dawo nan za taji haushi! ko kin manta lallabata mukeyi ne? Kallon Abba nayi! naga Gaba daya Magana yake Amma hankalinsa baya kaina, hawayen takaicine suka zubo Akan fuskata, kuka kuma Hajar?”

 

“Abba ni….

 

“Yaya Auwalu?” Muka jiyo muryar Aunty Suwaiba tana kwala mai Kira “Kiyi hakuri ki daina Kuka ina zuwa ko? Barin watsa ruwan?” Shuru nayi, ganin bani da niyyar cewa komai yasa ya Mike jiki na tsuma yabar dakin.

 

Tashi nayi na zauna A bakin gado na saki kuka mai tsuma zuciya, kenan Akwai ranar da Abba zai fifita Matarsa Akaina? Shikenan zata kwace matsayi na? Innalillahi wa’inna Ilaihi raju’um! na Ambata A hankali tare da dafa kuncina, nan nacigaba da tunanin rayuwa, ganin zaman da nake bashi da Anfani yasa na mike ta fito Waje.

 

Kama baki nayi cike da mamaki ganin dakin Aunty Suwaiba A ture, Kwafa nayi na koma daki na zauna Zuciyata tamkar zata fita, in dai hasashena ya bani gaskiya to Abba Iskanci suke da Aunty Suwaiba? Tunda naji maganar da suke ta bayan window, shine zai cemin wanka zaiyi ?

 

Kasa tsayawa nayi, Tuni zuciyata ta fara raya min na shiga dakin, A hankali na tura Kofar, na shiga na tsaya A tsakiyar Palon, daga cikin dakin na jiyo muryar Abba tamkar wanda ya shekara Dari yana jinya “Suwy bazan iya rabuwa dake ba? Suwy kin zama rayuwata!wayyo Suwy Karki Rabu Dani Kinji?”

 

Banda Umm babu Abinda Aunty Suwaiba take fadi, Kama kaina nayi take hawaye masu zafi suka fara sauka kan fuskata, tamkar An dauramin dutse A Kafa haka na lallaba na fito A dakin, duk wannan Abin basusan na shigo ba.

 

Dakina na koma nasa Uniform Dina da sauri nabar gidan, jin zuciyata nake tamkar zata fita don bakin ciki, A haka na Samu na isa Makaranta.

 

Nana Monitor na hango A kofar Aji! sai taunar cingam take, Hanunta Rike da hausa novel tana karantawa, tana ganina ta gimtse Fuska, tuno bulalar da Abba yasa Akayi mata saka-makon fasa min jiki da tayi, Ratsewa nayi ta gefenta na wuce Cikin Aji.

 

Ganin dalibai sun cika kujerun Ajin Saura nasu Nana Monitor yasa na tsaya ina hasashen ina zan zauna, ganin babu mafita yasa na zauna A Kasa cike da bakin ciki, Bitan karatu muka soma! A haka har Malam Bala ya shigo, yana ganina A kasa yace “Aa lafiya Hajara kika zauna A kasa bayan ga kujera? Kallonsa nayi bance komaiba, maza tashi ki zauna A can?” Nan ya nunamin bencin su Nana Monitor, jiki A sanyaye na shiga na zauna, Malam Bala yana Ffita Fatima ta Kalli Nana Monitor.

 

“Kinsan Allah Jiya da kyar nayi Barci? Wannan littafi Akwai Abubuwa, Har mafarki nayi gani da Saurayina A gado irin na Littafi” Dariya Nana tayi “Ai shiyasa bani rabo da karantawa, Ina son Inyi Aure Wallahi Fatee! Rayuwar Akwai dadi, yanzu haka Wannan littafin jiya na karbo Haya, ko Rabi banyi ba! Amma kinga yanda Matar Littafin take Rikita mijin? Gaba daya ya susuce Akanta, ke Harya fi Sonta Akanta Yaransa”

 

“Ke haba dai? Kice Akwai cakwakiya?”

 

“Kwarai kuwa! Meye soyayya bai Bari ba? Ai duk Abinda yake ba laifinsa bane, yanda take biyar dashi ne”

 

“Gaskiya Nana zaki bani in Karanta idan na gama na Hanuna”

 

“Badamuwa, zuwa gobe zan gama! Cikin dare zan farka na karanta, kin san Akwai Munafukai! Suna gani zasu fada wa Umma”

 

“Hakane! Nima A islamiya nake samu na karanta, A gida bazai yuyu ba, tunda kinga A dakin Umma nake kwana, kuma makarantar boko Akwai tsauri, babu ta yanda zan karanta” cewar Fatee kenan, Tabe baki Nana tayi “Nikan bani da wannan Matsalar! Da zaran Aunty na tayi Barci shikenan zan farka na kunna torchlight din wayarta nasha Karatu”

 

“Ikon Allah” Maida hankalinsu sukayi kan Littafansu, kura wa Littafin hanun Nana idanu nayi! Gaba daya na kwadaita da son jin labarin Matar da Nana take tadi, shin Wacce irin Soyayya ce haka take mishi harya mance Yaransa? Tabdijam na Anbata A Raina.

 

Amma kasar zuciyata sai bani Shawara take Akan nabi Nana ta bani littafin ko Nawa ne zan biyata, da wannan tunanin A Raina Aka tashi A makaranta, Muna fitowa kofar Aji na taba Kafadar Nana, A Hasale ta juyo “Lafiya Hajara Auwal?”

 

Dan murmushi nayi “Nana don Allah kiyi hakuri dukan da Abba yasa Aka miki, kiyafeni kinji? Bani so Inga kina bata Rai idan kika ganni?” Tabe baki Nana tayi “Au Ashe kin gane ba’a kyauta minba kenan? Sati guda nayi ina jinya! Kuma Allah ya isa”

 

“Kiyi hakuri Nana baza’a sake ba”

 

“Shikenan ya wuce”

 

“Yauwa Nana nagode”

 

“Bakomai! ni zan tafi sai gobe”

 

“Allah ya kaimu, Amma Nana don Allah littafin da kike karantawa nake so na karanta? Ko nawa ne zan baki kudin haya?” Zaro Ido nana tayi “in baki kije Abbanki ya gani yazo makarantar Nan A kasheni da duka? Lalle Hajara baki da hankali?”

 

“Haba Nana wallahi ba zai ganiba dakina daban, da zaran na shiga Barci rufe kofa nakeyi”

 

“To yanzu dai kinga ina Karantawa, amma gobe idan munzo zan baki”

 

“Yauwa toshikenan Nawa zanzo dashi?”

 

“Karki damu Nan gaba idan zaki karba sai ki biya kudi”

 

“To nagode Nana” cike da Farin ciki na fito daga cikin Makaranta, Abba na hango yana Magana da wani Malamin Hadda, Wani sanyi naji A Raina, da sauri na karasa wajensa na Rike Hanunsa “Abba Kazo?” Dafa bayana yayi “Nazo Hajar! Baku gaisa da Abokina ba?” Kara shigewa Jikinsa nayi Tamkar Mage “Anyini lafiya”

 

Kallona yayi “Lafiya kalau Hajara ya Karatu?” Alhmdullah na Amsa. Kallon Abba Malam din yayi “Malam Auwalu Hajara ta Girmafa? Bai kamata kana barinta tana Shigewa Jikinka Haka ba? A rika kiyayewa Sai Allah ya tsaremu” Dan Bata Fuska Abba yayi “Okey bakomai Nagode da Shawara! Hajar shiga mu tafi” Mika mishi Hanu Malam yayi sukayi Sallama ya shige.

 

Abba yana shigowa Motor ya dubeni “Hajar kika tafi Makaranta babu izinina? Bayan kince baki da lafiya? Ina fitowa kawai naga baki nan? Na duba uniform dinki babu? Ashe kin taho?” Fuska ba yabo ba fallasa nace “Eh Abba jikin naji da sauki shine na fito, nayi Magana Akofar Aunty suwaiba Baku Amsa ba”

 

“Yanzu dai wannan ba! Hajar kiga Malamin Ku? Ina ganinsa da Mutunci zaisa na kullacesa! Idan ban jaki A jiki ba wa zanja? Kai Mutane suna da Sa idanu wallahi” Shuru nayi bance Komaiba domin bani da Amsar Maganar, ganin Haka yasa ya tada Motar muka tafi Gida.

 

A kofar Gida ya saukeni ya wuce, ko Sallama banyiba na fada cikin Gidan, Aunty Suwaiba ne zauna ita da wata Makociyarmu Maman Sauban, ko Kallansu banyiba na shige dakina, Ina zama A bakin gado na jiyo Muryar Maman Sauban “Lalle Suwaiba kina da Aiki? Yaushe Zan zauna yarinya karama tana nuna min ta isa A Gida?

 

Ki duba yanda ta shigo? ko kallo bamu isheta ba? Na rantse da Allah samun dama tayi, Kibar shegiya da Yunwa! Dan Ubanta tana fitowa da safe tana wanke kwanoni da daura Abincin kari! Tuni zata shiga taitayinya, yaushe Aka haifi Y’ar Mijin da zata min wannan iya shegen?”

 

“Kibar kawai Maman Sauban, Hajara ta wuce duk yanda kike tunani! Kuma ta samu goyon bayane A wajen Auwalu, da Ace ina barin Hajara da Har Kashi za taci Akaina, ni babu Ruwana da Gabar da takeyi Dani! Don haka ki kyaleta kawai, duniya ce tana jiran Wanda bai zoba”

 

Take Raina naji ya baci, Lalle Matar nan bata sanni bane, wallahi Abba zai dawo, ta daina shigowa Gidan Nan kenan.

 

Haka na rika jinsu suna zageni tsaf, daga bisani suka dawo hiran Maganin Mata da suke sha.

 

Sai bayan isha’i Abba ya dawo, dakina ya Fara shigowa, ina zaune A gefen gado ina jin Gidan Radio A wayata “Hajar din Abba?” Dan turo baki nayi “Abba ya kaji ma baka dawo ba? Da zan bika Ai?”

 

“Haba Hajar ina Magidanci? Ai zama ba tawa bace, ya jikin naki?”

 

“Abba Akwai sauki”

 

“To Alhmdullah, kinci Abinci?”

 

“Eh naci Tuwo”

 

“To Naji dadin hakan, barinje wajen Auntyn ki”

 

“Yauwa Abba kasan Miye? Aa yace da Sauri, zauna kaji Abba, da Sauri ya zauna A gefena, Abba kaga Maman Sauban Makociyar mu? Matar nan munafukace, na dawo Makaranta na sameta, ina shiga daki ta cigaba da zageni tsaf ita da Aunty Suwaiba, har tana cewa Aunty Suwaiba ta barni ne, Abba hadda ce Mata ta samin shinkafar bera ta samin na Mutu idan na Isheta, wai Yarinya Guda daya ta Addabi Mutane! Banda Kashe Aure Babu Abinda Nakeyi…….

 

 

 

*SADIYA NASIR DAN*

 

 

Ga Masu Bukatar Tallata Musu Hajarsu! Zasu iya Tuntubata A wannan Number 07051244211

[01/10, 7:37 pm] +234 703 966 0069: 🧏🏾‍♀️ *JAN KUNNE 🧏🏾‍♀️*

 

_True life Story_

 

 

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*

 

 

this book is written

by

*Sadiya Nasir Dan*

 

 

*BISMILLAHI RAHMAN ALRAHIM*

 

Dukkan godiya ta tabbata ga ALLAHU subuhanahu wata’ala, tsira da aminci sutabbata wajen fiyayyen halitta ANNABIN rahma ( S.A.W ).

 

 

Page 4

 

Zaro ido Abba Yayi “Tace wa Suwaiba tasa miki shinkafar bera ki mutu? Hajar kin tabbata anyi haka? Kar naje na dauki hukunci Akan karya?” Matso Kwallar Karya nayi “Abba da gaske na keyi, Ai idan Aunty Suwaiba zata fadi gaskiya tasan anyi haka”

 

“Shikenan ina zuwa, da Sauri ya fice A dakin, ni kuwa mikewa nayi na Saki tsallen Murna, na tabbata Maman Sauban ba zata sake shigowa gidan nan ba, Dan Hayaniya na fara ji yana tashi A hankali, fita nayi A dakina na matsa gab da dakin Aunty Suwaiba! Yanda zan rika jiyo meye suke fada.

 

“Suwaiba Abinda bazan dauka ba kenan, duk Matar da zata shigo gidan nan! Don ta gurbatamin Tarbiyar gida to ta zauna A inda Allah ya Ajiyeta, bana so A fara jina da makota Akanki”

 

“Haba Auwalu, tunda ka shigo dakina! Banda fada babu Abinda kakeyi? Hakan shine tarbiyar da kake ikirari za’a bata maka? Yarinya ta zauna ta fada maka karya da gaskiya ka zauna Akai? baka da Adalcin yin bincike? gaskiya bazan iyaba Auwalu, Wallahi duk yanda na kai da in zauna lafiya A gidan nan bazai yuyuba”

 

“Meye kike nufi da hakan Suwaiba?”

 

“Ai kai ba yaro bane! Kafini sanin meye nake nufi, wallahi Auwalu idan kaje ka sami Baban Sauban Akan zancen karya! Second idan na Kara A gidanka! To kasani ni ba ‘yar Halas bace”

 

“Au ta inda kika bullo kenan Suwaiba? Lalle kuwa, to ina so ki sani, Duk Abinda za kiyi A Gidan Nan zan dauka sabida ina sonki, Amma banda zancen kisan Kai, don haka ya zama wajibi da safe in sami Mijinta yaja mata kunne, kar in sake ganin Kafarta A gidana, wanann shine hukuncina Suwaiba”

 

“Ni kuwa kana zuwa kana samun Mijin Maman Sauban Akan maganar karya, toka sani zamata A gidanka ya kare, shine kawai ni bazan iya ba, da Igiyar Aurenka wallahi gwara zawarci”

 

“Haka ki kace? shikenan”

 

“Na fada na sake fada Auwalu, da tashin hankalin da nake fuskanta A gidanka gwara nayita zama A bazawara”

 

“Anzo wajen” na Anbata gami da Sakin Tsalle, jin Alamar Mutum! Yasa nabar wajen da Sauri na koma daki na, zama nayi A kan Gadona! Ina jin zuciyata Namin dadi, shikenan za’a kori Aunty Suwaiba cikin Sauki.

 

“Hajar?” Naji Muryar Abba yana kwala min Kira, da Sauri na Amsa na fito, kallona yayi “ya jikin naki dai?”

 

“Da Sauki Abba?”

 

“To Alhmdullah, kiyi Hakuri zuwa safiya zanje na sami Makocina yaja wa Matarsa kunne Akan Abinda kika fadamin, zuwa Gidan Nan ba Zata sake ba, maza kiyi hakuri kije kiyi Barci”

 

“Shikenan Abba Saida safe” Karar kofar Aunty Suwaiba mu kaji Alamar tasa Kuba A dakin, Kwafa Abba yayi ya dubeni “Suwaiba tana neman Masifa, amma Allah ya tsayar Mata Akanta, nizan kwana A dakina karta bude dakin, maza Je kiyi Barci”

 

“Abba meye zai hana in kwana A dakin ka? Ni ina tsoron Abinda zai biyo baya! Kaga tana cikin Fushi, Kai kana dakin ka, kar tamin wani Abu” shafo gashin kaina yayi “Haba Hajar? Da Key A dakinki fa! Ki fada min ta yanda zata iya budewa?” Shuru nayi na share Kwallar karya “shikenan Abba na tafi, juyawa nayi da Sauri nayi daki.

 

“Hajar ?” na sake jin Muryar Abba “Na’am na Amsa na sake juyowa “kizo mu kwana bakomai” dan Murmushi nayi nace “To Abba nah” Dakina na shiga! hula kawai na dauka Nasa A kaina na fito na jawo kofar dakin, Sallama nayi na fada dakin, zaune yake A bakin gado ya zuba tagumi, nasan Tunani yake Akan Furucin da Matarsa tayi.

 

“Abba lafiya?” Kallona yayi “Lafiya Hajar kwanta Abinki” OK nace na zaga na kwanta nesa dashi, A hankali Barci ya daukeni mai dadi, Cikin dare Fitsari ya tasheni! ina bude idanu nayi tozali da Abba A zaune A yanda na barshi, har yanzu tunani yake, Mamakine ya baiyana Akan Fuskata “Abba na?” Na Ambata A hankali, ido Jazur ya juyo ya dubeni “Lafiya Hajar kika Farka?”

 

“Abba meye ya sameka kake Kuka?”

 

“Haba Hajar kuka kamar Karamin Yaro? Kawai barci na keji shiyasa idanuna suka sauya”

 

“To Abba shine ba zaka kwanta ba?”

 

“Karki damu Hajar bana jin Barci ne” Gyara zama nayi “toshikenan Abba nima barin zauna Mukwana haka, ba zan iya Barci in barka idanunka biyu ba” murmushi yayi “shikenan koma ki kwanta zanyi yanzu” Mikewa nayi “barinyi Fitsari Abba”

 

Ina fitowa na samu ya kwanta ya rufe idanunsa, Dadi naji A Raina na zaga na kashe Mana Wutar dakin na kwanta A gefensa, ina jin Sautin Ajiyar Zuciyarsa.

 

“Hajar tashi kiyi Sallah mun makara” bude idanu nayi dakyar! Bakina dauke da Salati “Abba Barci nake ji”

 

“Hajar kinsan karfe nawa kuwa? Duba ki gani karfe 07 na safe? Ba kyau A Makara Sallar Asuba” OK nace nayi Mika na sauko Akan Gadon, Toilet dinsa na shiga na dauro Alola na fito, A Sallaya na sameshi yana lazimi, Bude kofar dakin nayi na fito, Aunty Suwaiba tana zaune Akan dakalin Kofar dakinta, ko Kallonta banyiba nayi Kofar dakina nasa Key zan bude.

 

“Laaaa Nashiga Uku! Meye zan gani A Gidan Auwalu? Hajar A dakin Abbanki kika Kwana?” Tamke Fuska nayi na juyo na dubeta “Eh A dakin na kwana Lafiya?”

 

“Innalillahi wa’inna Ilaihi Raju’um! Yanzu lalacewar Auwalu har takai haka? Wannan shine Tarbiya? Lalle Andauko Hanyar Halaka” Jin Maganar da Aunty Suwaiba takeyi yasa ya fito “Farar Safiyar ma ba za’a Zauna Lafiya ba? Haba Suwaiba?”

 

“Huhmm Lalle Auwalu ka kuremin hadda, Har Kwana kake daki daya da Balagaggiyar Yarinya? Wannan shine So? Nashiga Uku ni Suwaiba, lalle idan kana Raye babu Abinda ba zaka gani ba, Innalillahi wa’inna Ilaihi Raju’um, wallahi kaji tsoron Allah ! Wai”

 

“Ke Hajar wuce kiyi Abinda za kiyi, ke kuma karki Fasa” Dakinsa ya shiga Rai A bace, haka na bude daki nayi Sallah! Ina jin Irin bakaken Maganganun da Aunty Suwaiba take jifarmu dashi nida Abba, da Sauri nasa Uniform na dauki Jakata na fito, dakin Abba na shiga, yana zaune ya zuba tagumi, zama nayi A gefensa “Abba Antashi lafiya?” Dan Sake Fuska yayi ya dubeni “Lafiya Kalau Hajar, Anshirya kenan?”

 

“Eh Abba zan tafi Karna Makara”

 

“Shikenan! duba cikin waccan Rigar, Akwai kudi ki dauka kisaya Abin Kari ki hau Napep, kinga yanda muka tashi A Gidan yau”

 

“Hakane Abba shiyasa nace Maka ka Sallami Aunty Suwaiba bata da Anfani” Kama hanuna yayi “Tana da Anfani Mana, ke dai kiyi Hakuri, zaman da kika ga nayi Aban! tunanin mafita nake”

 

“Huhmm Abba, duk Matar da zata quntata maka bata da Anfani, ni Wallahi na tsaneta ka Sallameta kawai”

 

“Hajar nasani Amma Anfanin Girma Hankali, ke dai jeki Makaranta idan nazo daukarki za muyi Magana”

 

“Shikenan Abba saina dawo”.

 

Cike da damuwa na isa Makaranta, Sam bani son ganin Abba cikin irin wannan yanayi, na tabbata jiya baiyi Barcin Arziki ba, A shago na tsaya na saya Coke da Biscuit na shige Aji, Ina Shiga Aji mu kayi ido biyu da Nana, tuni na saki Murmushi na karasa Kujeransu “Antashi Lafiya monitor?”

 

Murmushi tayi “Lafiya kalau Hajara Auwal, zauna Mana? Cike dajin dadi na zauna, Littafin ta dauramin Akan Cinya, gashi Kwana biyu na baki, ki tabbatar kin Kammala, Matar bata da kirki ne” Rungume Nana Monitor nayi “Kai Amma nagode sosai insha Allah ina komawa Gida zan Fara, cike dajin dadi Nasa Littafin A cikin Jakata.

 

Coke da Biscuit din na dauka na Ajiye A saman Kujera Monitor muna kwarya?”

 

“Karki damu Hajara! Wallahi A koshe nake”

 

“Duk da haka wannan Ai Abun Mar-marine” duk yanda nayi da taci Sam taki, haka na hakura na zauna na cike cikina, burina A tashi A makaranta na isa Gida na fara karanta littafin Nan………

 

 

*SADIYA NASIR DAN*

 

 

Ga Masu Bukatar Tallata Musu Hajarsu! Zasu iya Tuntubata A wannan Number 07051244211

[01/10, 7:37 pm] +234 703 966 0069: 🧏🏾‍♀️ *JAN KUNNE 🧏🏾‍♀️*

 

_True life Story_

 

 

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*

 

 

this book is written

by

*Sadiya Nasir Dan*

 

 

*BISMILLAHI RAHMAN ALRAHIM*

 

Dukkan godiya ta tabbata ga ALLAHU subuhanahu wata’ala, tsira da aminci sutabbata wajen fiyayyen halitta ANNABIN rahma ( S.A.W ).

 

 

Page 5

 

Hira muka cigaba dayi jefi-jefi, A haka Fatee tazo ta samemu, tunda Fatee ta zauna! Banda tadin Soyayyar da Akeyi A littafi babu Abinda sukeyi ita da Nana Monitor, gaba daya sun samin shaukin Karantawa, burina kawai in ganni A kwance A Gadona ina Karanta Littafi.

 

Zan iya cewa babu Abinda na fahimta ! Dan gane da karatun Wannan Lokacin, domin hankalina yana kan Littafin Hausa, wani Abin takaici! gaba daya lokacin ma bai tafiya, Ina jin Karar Belt naji wani Sanyi A zuciyata, da Sauri na dauki Jakarta na fito daga cikin Makaranta.

 

Motar Abba na hango, Tuni Farin ciki ya lullubeni, ina shiga naga Fuskarsa da Alamar damuwa “Abba lafiya kuwa? Kallona yayi baice Dani Uffan ba ya tada Motor, Abin duniya duk yabi ya isheni, Abba kayi shuru kuma?” Kallona yayi! Yaga Alamar damuwa Karara A fuskata, A hankali ya tsayar da motar A gefen Hanya.

 

“Hajar kin yadda cewa ni Mahaifinki ne? Kuma kinyarda cewa ban can-canci Karya A gareki ba?” Kallonsa nayi “Eh Abba na yarda”

 

“Alhmdullah! Don Allah mai yasa kika min karya Akan Maganar jiya? Mai yasa kika fadi Abinda ba haka ba? Kina so rashin yadda ya shiga tsakanina dake ne Hajar? Kamar yanda kika fadamin Magana kuma nace miki da safe zan sami Makocina Akai, tabbas na same shi, Amma Hajar daga karshe nine naji Kunya.

 

Domin Maman Sauban Rantsuwa tayi wa Mijinta na Musulunci! har tana ikirarin dafa Qur’ani, Kinga duk Wanda ya kusanci haka, to wallahi yana da gaskiya, gashi yanzu kinsa Suwaiba ta Kama hanya ta tafi ni bansan ina taje ba, nakira wayarta yafi sau A kirga taki dagawa, daga karshema kashe Wayar tayi, kinga Anan idan Yaya Habiba taji Hajar baki da yanda za kiyi, dole Yaya Habiba zata rabamu, don na tabbata zaman gidanta ya zame miki dole”

 

Ajiyar Zuciya na sauke “Abba tabbas Maman Sauban ta shigo gidan mu! kuma ta bini da munanan kalamai, kuma na rantse da Allah taba Aunty Suwaiba mugun shawara Akaina, idan Karya nayi Allah ya jefani A wuta, Sannan Maganar Aunty Suwaiba Abba ka kyaleta ta tafi, duk Abinda ta keyi maka zan rika yi maka, ni wallahi ba ita bama! Abba Aure da kowa ma ban so.

 

Gidan Gwaggo Habiba kuwa wallahi bazan jeba, Abba Matar nan ta tsaneni wallahi, Kwanaki daka turani Gidan kullum cikin sani Aiki take, ga zagi data kemin wai ban iya komaiba, ni Abba bazan jeba”

 

“Huhmm Hajar Ai kamar yanda kika fada haka Maman Sauban ta fada, tabbas taba Suwaiba shawara Akan irin zaman da kikeyi da ita, kin shigo Gidan babu wacce kika kallah cikin su, Amma Hajar ba tace Suwaiba ta baki shinkafar bera ba, Sannan Maganar Yaya Habiba! Kullum ina fada miki ki daina tunanin Yaya Habiba bata Sonki, Na rantse da Allah bayan ni! Duk duniya baki da Gatan data wuceta”

 

“Huhmm Abba..

 

“Ya isa Hajar Allah yana bayan mai gaskiya, Jan motar sa yayi da Sauri muka karisa gida, ki shiga Gida, ni zan tafi Neman Suwaiba, ki dafa Abinda zaki iya ci”

 

“To Abba kai ba zaka ci bane?”

 

“Karki damu bana jin Yunwa sai na dawo” ok nace na fita A motar nayi cikin Gida, harara nabi dakin Aunty Suwaiba dashi “Insha Allah kin tafi kenan Makirar Mata kawai” tsaki nayi na wuce dakina na bude na shiga, Jakata kawai na Ajiye na dauki littafin da Nana ta bani na kwanta A gado na na fara karantawa.

 

Tun daga farkon littafin na Fara Arba da kalaman soyayya masu gigita kwa-kwalwa. Haka na dukufa karatu har Akayi kiran Sallar Azahar Amma na kasa tashi, gashi idanuna sai Zafi suke min sabida rashin sabo, Gaba daya littafin ya tafi da imanina.

 

Sai wajen karfe Uku naji tsayuwar Motar Abba, da Sauri na boye littafin na kwanta A gado, A hankali nace “Lalle dole Aunty Suwaiba ta gama da Abban mu, Ashe Iskancin da sukeyi ne yasa ba zai iya Rabuwa da ita ba? Huhmm”

 

“Hajar? naji Muryar Abba yana kirata, A hankali na Sauko na fito, ji nayi cikina tace Kuluulu, gaba daya Yunwa tagama Addabar cikina, kallona yayi meye kikaci?” Hamma nayi “Abba banci komaiba”

 

“Mai yasa Hajar? Ba nace ki dafa Abinda zaki iya Ciba?”

 

“Kayi hakuri Abba! Kaina ya soma ciwo shine kawai nayi Barci”

 

“Sannu Allah ya Kara sauki, ga Nono ki juye ki kawo Mana” karba nayi na wuce Kitchen nayi Abinda ya sani, A Cup daya na hada Mana na fito na dawo dakinsa, Ajiyewa nayi A gabansa na zauna na dauki Ludayi, Sai da mukayi nisa da Fara sha na dubeshi “Abba ya batun Aunty Suwaiban?”

 

“Huhmm Suwaiba gidansu taje Hajar, naje na sami Babanta na Bashi hakuri iya iko Akan ta dawo, Amma sai yace min naje na sameta mu sasanta, domin Suwaiba Yarinyar Kirkice, tunda har tazo Gida! to tabbas Ankaita bango ne, kin san wani Abin Mamaki Hajar? Suwaiba haka ta kekeshe tace Sam ba zata dawo ba, na kai Hour guda ina Abu daya Amma taki.

 

Shine na hakura na dawo, zan sake bata kwana biyu, idan taki dole yaya Habiba ta sani” Zaro idanu nayi “Abba Gwaggo Habiba fa kace? Ka mance meye tace ne? Ni wallahi da Saketa kayi da yanzu An wuce wajen, duk cikin Matan ka babu wacce take gasani irinta, Amma Abba na rasa mai yasa ka kasa Rabuwa da ita”

 

“Hajar kenan, Yaranta ke damunki shiyasa ba zaki gane illar rashin zaman na Miji magidanci ba Mata ba, Sannan Mutuncin kine na nema miki Uwa Hajar, Duk Soyayyar da nake miki dole watarana za kiyi Aure Hajar, kinga Suwaiba tana da Anfani, Sannan Ina son Suwaiba Hajar, duk cikin Matan Dana Aura banda Mahaifiyarki babu wacce nake jin zan iya Rayuwa da ita na har Abada irin Suwaiba”

 

“Tabbas nasan Suwaiba tana da hakuri! Sannan tana da Kawaici, Amma na rasa mai yasa take kishi dake, duk Abinda zanyi Mata zata hakura Amma banda Bangarenki, wallahi shine Abinda yake tsananin damuna Hajar. Wani irin bakin ciki ne ya ziyarci Zuciyata, jin furucin Abba wai ba zai iya Rabuwa da Suwaiba ba, tashi nayi A wajen na koma gefe na Rakube.

 

Cike da Mamaki Abba ya kalleni, Hajar Fushi kikeyi Dani? Toki fadamin meye nayi miki? Kin sani bani son ganinki cikin damuwa?” Hawayene suka zubo Akan fuskata “Abba yanzu Ashe Akwai matar da zaka hada soyayyarta data Mahaifiyata, bayan duk duniya kace babu wacce za kaso A Rayuwarka irinta? Kenan Aunty Suwaiba tayi tasirin da ba zaka iya fadan Aibuntaba Abba sai tawa?

 

Shikenan ya tabbata Nan gaba zata Rabani da Mahaifina?” kuka na fashe dashi sosai, Ajiye Ludayin yayi ya dawo gefena ya dafa Kaina “Hajar Sarkin Rikici, Hajar Zuciyar Auwalu, tashi kiji wani Abu, dago idanuna nayi na kallesa, Hajar ko kinsan mai yasa nake Kaunarki? Nake jinki A Raina fiye da komai?”

 

“Aa” nace Murya A sanyaye “to kisani Soyayyar Mahaifiyarki ce ta shafeki, Sabida Tsaban Sonda nake wa Fatsuma yasa nake jin ‘Yarta tamkar ita, Aduk sanda naga fuskarki to tamkar Fatsuma nake gani, shiyasa bani iya controlling Kaina Akanki Hajar, Ina sonki Hajar fiye da komai A Rayuwata, Hajar Akanki babu wanda bazan iya Rabuwa dashi ba! Matukar zai taba miki zuciya.

 

Amma Hajar ina so kisani Matsayinki daban data Suwaiba, kuma ko wacce da muhallinta A zuciyata, kinga Suwaiba?

Ita Matata ce, duk Sonki dana keyi Hajar Akwai Abinda dole Suwaiba ce za tamin, Suwaiba Katanga ce ga Rayuwata! A Matsayina na Magidanci Mai Lafiya Hajar.

 

Abinda nake so dake Hajar, ki tayani da Addu’a Allah ya shawomin Kanta, idan ta dawo zan zauna daku naji Matsalar kowa”

 

Cike da takaici nace “Shikenan Abba, Mikewa nayi na dauki dankwalina na daura, ni zan tafi daki nayi shirin Makaranta”

 

“Allah ya taimaka Zuciyar Auwalu” dariya nayi na fice A dakin na koma dakina, zama nayi A bakin gado ina tuna Maganganun da mukayi da Abba yanzu, tuni zuciyata tafara sakamin Abubuwa da dama, Ajiyar zuciya na sauke, ya zama dole nasan meye Aunty Suwaiba takeyi wa Abba da yake cewa ta zame mishi Katanga ga Rayuwarsa A matsayinsa na Magidanci mai lafiya.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
A shirye nake! Dana San komai, kuma na Aikata, komin Wahalar Abin, da Rashin dadin sa, na shirya Akan haka, Abinda ya ragemin na samo Amsar Tambayata, Tabbas idan har zaiyi sanadiyyar da Aunty Suwaiba zata bar Gidan! Da kuma rayuwarsa gaba daya, mu zauna mu biyu! Muyi rayuwarmu……

 

 

 

*SADIYA NASIR DAN*

 

 

Ga Masu Bukatar Tallata Musu Hajarsu! Zasu iya Tuntubata A wannan Number 07051244211

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.