Jannah Hausa Novel Complete

Yar wanke wanke

Jannah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

JANNAH

 

 

 

*E.W.F*

 

By

Mrs Bb

mom muhseen

 

wattpad name

Humaira3461

 

 

🅿️……2

 

 

Tun da muka iso asibitin tun karfe takwas, amman har anyi sallar isha’i babu wanda ya dubemu a wajen, saboda kuka jinake har ban gani innamu tun tana kukan harta hakura, yayanmu kam in kafafunsa basuyi ciwo ba Allah na sonshi, zaryar da yake tsakanin wajen nurses da metrori kadai ta isa ya sik’e, wannan rayuwar ace idan baka da galihu ko asibiti kaje babu mai kulaka, munata hauka bamusan baba ya sume a wajen ba, karar dana daddage na fasa itace ta janyo hankulan mutane da yawa akanmu, duk wanda yazo saiya dad’e hancinsa saboda warin da kafar baba keyi, mun dauka ya mutu muka hau koke koke da kururuwa saida wani likita yazo ya duba shi sannan ya kwatsan tsawa yana cewa,

 

“Dallah malama kiyi mana shiru, ubanwa yace daku mutuwa yai?”

 

Innamu na kuka tub’uran tace, “haba likita ku agaje mu mana, tun takwas muke nan ank’i saurarenmu, ya zamuyi da ranmu? Bawan Allah nan yana bukatar taimakon ku”

 

Tashi yayi yana kiran wasu nurses suka kawo wheelchair aka dora baban yace yayanmu kad’ai zai biyosa, godiya makai tayi ma Allah da taimakon da muka samu,shirun da mukaji yasa mukatai waje wurin wani famfo mukai alwallah muka dawo nan harabar mukai sallolin da bamuyi ba, muka d’uk’ufa rok’a ma baba sauki.

 

Yayanmu bai dawo ba sai wajen goma da rabi yana sharce gumi, yace “gwaje gwaje mukaje akai mashi, anci rabin kudin nan fa innamu gashi yanzu an shiga dashi wani daki an bani wannan takaddar zanje in nemo duk abunda suka rubuta”

 

“Babu komi sale kaje asai duk abunda ake buk’ata muga abunda Allah zaiyyi”

 

Haka ya juya yana tambaya ka nuna masa pharmacy,ya sai komida ake buk’ata sannan yaje yakai ya koma gefe yana jiran tsammani.

 

*bayan awa uku*

 

Likitan ne ya kira yayanmu suka wuce office d’insa bamu san me suka tattauna ba abunda muka gani kawai shine yayanmu ya fito yana kuka, tunda nake ban tab’a ganin kukansa ba jarumin mutum ne mai dakiyar zuciya, tun daga haka naji zuciyata ta buga naji jikina yana sacewa inajin kamar xan fad’i, saurin tarosa innamu da zainab sukai silalewa k’asa yai yana zaman dirshen yana cewa,

 

“Shikenan innamu zamu rasa baba! Domin baba yana cikin hadari”

 

A rikice innamu take dukta fita hayyacinta tace, “kai sale ka natsu ka gaya mana abunda yake samun malam, don Allah natsu karka saka in zare”

 

Ya kamo hannun innamu yana kuka sosai yace, “innamu likita yace ciwon daji ya samu baba, kuma yai masa mugun kamo wanda idan ba’ai gaggawar yimasa aiki ta hanyar yanke kafarsa ba ba tantama zamu rasashi, innamu kudin aikin kadai daya gaya mun yasa na sadakar baba mutuwa zai, innamu wai…….wai……mil…..miliyan biyu zamu kawo, innamu ina zamu sameta? Bamu tab’a ganin ko dubu dari ba sai yau da muka bada jinginar gidanmu, ta ina zamu nemo miliyan har biyu”

 

Innalillahi wa inna ilahir raju’un Allahumma ajirni fi musibati wa’aklif li khairan minha!!!

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Abunda na keta fad’a ina nanatawa kenan yayinda na silale k’asa dab’as ko ciwo banji ba, hawaye ne suka k’afe mun miyan bakina ya dauke, kukan innamu da zainab kurin kakeji yana tashi yayin da halin da nake ciki bai misaltuwa.

 

Bamu san iyakar lokacin da muka kwashe anan ba saida mukaji ana korar mu wai ba’a zama anan, farfajiya muka fito mukai cirko cirko cikin shakakkar murya innamu tace,

 

“Yanzu a wane hali yake ciki?”

 

Jikinsa ya mugun saki yace, “yana dakin gaggawa ana bashi treatment, yace zasu kula dashi na kwana uku idan bamu kawo kudi ba zasu koremu tare dashi”

 

Na sharce hayawane nace, “innamu miye amfanin gonakin ku keda baba, asaida mana muga idan zasukai yawan da ake buk’ata”

 

Girgiza kai tayi tace, “tunanin da bake yanzu kenan, duk da nasan ba zasukai ba ko rabi basuyi amman kila idan sukaga mun kawo wadannan din zasu tausaya mana su ansa”

 

“Yanzu ya zamuyi ina zamu kwanta, idan asuba tai zan sabko inje inga yadda za’ai d’in”

 

Innamu tace, “ga wasu bayin Allah can nasan suma jinya suke, zamu tambayesu ko zamu rab’a gefensu, saidai kai bansan ina zaka kwanta ba”

 

“Aa innamu naga masallaci waje zanje na kwana acan, kuyi amfani da tabarmar hannunku kuyi maleji zannuwan da kuka dauko saiku rufa dasu akwai sanyin sosai”

 

Hakan ce ta kasance kuwa basu hana mu ba muka shimfida yar madaidaiciyar tabarmar muka rufa da zannuwan, zuwa can saiga yayanmu ya dawo yace,

 

“Naga ba wanda yaci wani abu cikinku shiyasa naje na siyo mana abu da yan canjin da suka rage”

 

Nace”yayanmu kaida zaka koma gezawa gobe? Kana bukatar kudi”

 

Murmushin karfin hali yayi mani yace, “zasu isa kanwata”

 

Duk da bamuda natsuwa haka mukaci muka sha ruwa sai bacci ya sacemu, don akwai gajiya da rashin isassar natsuwa muka dunkule waje guda daka gan mu dole mu baka tausayi.

 

 

**********

 

Ana gama asuba yaya ya tafi gezawa mu kuma muka tafi ganin jikin baba, Allah yaso anbarmu mun shiga saida bamu dad’e ba akace mu fito, tabbas ana bashi kulawa ina kyautata zaton inhar akai aikin zai warke da iznin ubangiji, don babu cutar da bata da magani.

Ba wanda bai kuka ba ganin baba kwance an saka mashi abun shakar iska,kafar kuwa an zaizayeta duk ta koma wata iri alamun jiya an tsotse ruwan an fitar an masa gyara saboda ya samu sauki,ga drip nan an mak’ala mashi bacci yake sosai.

 

Fitowa mukai muka samu wajen hantsi muka zauna, da yake yayanmu ya bamu kud’in kalaci mutanen da muka kwana kusadasu naga yarinyar zata fita waje nace, “innamu bari na bita na siyo mana koda kunu da kosai ne”

 

“To ki kula dai”

 

“Kuma babanku ne baida lafiya ko?”

 

Inji yarinyar da bata wuce sa’ar zainab ba, murmushi nai mata nace”Ehy, kefa”

 

Sai naga zatai kuka tace, “muma babanmu ne muka kawo,ya samu lalurar shanyewar barin jiki saka makon faduwa dayai”

 

Cikin jimami nace, “Ayya Allah yabashi lafiya kibar kuka,duk zasu samu sauki kinjiko”

 

Ta d’aga kanta kurin mukaje muka siyo muka dawo, akan hanya ne take cemun.

 

“Kinsan me baiwar Allah, yayarmuce duk ta jawo wannan abun, saurayinta ta bari yai mata ciki taita b’oyewa ba asani ba daga karshe aka gane yanzu haka wannan watan take haihuwa, abunda ya jefa baba cikin wannan halin kenan……………

 

 

 

 

 

 

Mom muhseen✍🏻

[13/08, 9:40 am] +234 815 555 3884: *_💔JANNAH💔_*

 

_{A TRUE LIFE STORY}_

 

 

*E.W.F*

 

By

Mrs Bb

mom muhseen

 

wattpad name

Humaira3461

 

 

🅿️…..1

 

 

Duk’e nake na tusa mahaifina gaba ina kuka saboda banda kukan banda wani abunyi, haka mahaifiyata itama tana kusadani sai hawaye take sharewa, yayanmu Sule na tsaye gefe ya dora kanshi jikin tagar dakin Innamu sai kanwata zainab.

 

“Asabe wai nace daku mutuwa zanyi ne? Kun taru akaina sai kuka kuke mun bana son wannan koke koken,ba yau na fara wannan ciwon ba ya kamata ace kun saba dashi”

 

Baban ya fad’a cikin wahaltuwa muryar tasa kanta daker take fitowa, innamu na kukan take cewa, “malam ciwon ka ba shine yake samun kukan nan ba, rashin gata da galihun da muke ciki da zamu taimakeka mukai asibiti shine ya damemu, da kuma irin wahalar da kake sha aduk sadda ciwon ya tashi,kuka dole ne saboda ana cikin halin da ya zama wajibi ayisa”

 

“Ayi amfani da abunda ya samu mana asabe, ba naji sale ya zo da wasu kud’i ba”

 

Innamu na zubar da hawaye tace, “tun safe ya fita nema daker ya samu dubu uku, acikin dubu uku malam ko isa asibiti ba zata ishemu ba, tunda dole sai mun shiga cikin gari anan sun riga sun tabbatar mana bazasu iya mana komi akai ba”

 

Huci kurin baba keyi na zafin ciwo ina wajen kanshi ina shafa masa addua ina hawaye, cikin disashiyar murya nace “Baba sannu kaji,insha Allahu zaka warke zaka samu lafiya”

 

Ya sauke numfashin wahala yana mun murmushin karfin hali yace, “Allah yai maku albarka MURJANATU keda yan uwanki, ku cigaba da mun addua Allah ya kawo sassauci hakika ina cikin rad’ad’in ciwo, nikadai nasan me nakeji”

 

Kuka muka sake rushewa dashi nida zainab saboda yadda yake maganar kadai abun tashin hankali ne, yayanmu ya juyo idonsa jajur kamar an watsa masa yaji yace a dame,

 

“Innamu zanje na samu dillali anemo mai siyen gida mu bada gidan jingina abamu kudin da zamu kai baba asibitin cikin gari, wallahi tsoro nakeji mu sake kwana dashi a wannan halin da yake ciki, idan muka samu kudin ko nawane sa muje asibitin”

 

Innamu na sharce hawaye tace, “tun tuni ban kawo wannan shawarar ba sale, maza jeka hanzarta Allah ya taimakemu asamu maiyin wannan aikin ladar,”

 

Aguje yayanmu ya fita yana haki muka duk’ufa addua da neman rangwame wajen Allah, tun baba na iya magana har takai baya iya cewa komi saidai ido, tun azahar yayanmu ya fita amman har akai sallar la’asar babu alamun sa, ga jikin baban sake rikicewa kurin yake, wannan k’afa tashi mai wani irin rub’eb’b’en ciwo sai zubda ruwa mai wari take, kowa hankalinsa ya tashi kuka kau da hawaye na k’arewa da sun k’are saida ana gabda kiran mangaruba sannan sai ga yayanmu da mai siyen gida da dillali,gidan mu ba wani gida bane na azo agani gidane na k’asa duk ya zaizaye, abunda kawai zai saka yai d’an mutunci shine fad’in gidan duk wanda ya siya rushesa zai ya tada sabon gini, so zai samu isasshen fili dazai wadacesa, kasancewar cikin buk’atar kud’in muke da akai ciniki daker mutumin nan ya bada dubu dari da hamsin,ba yadda yayanmu baiba akan ya kara su cika dari biyu amman ya rufe idonsa yace idan bamu son hakan shizai fasa,

 

“Aa bata kai ga haka ba yallab’ai, mun siyar hakanma mungode Allah yai albarka”

 

Inji innamu shi kuma yayanmu ya anshi kud’i sanan akai rubutu saboda halin rayuwa, mu duka muka kwasa muka tafi saboda duk wanda aka bari hankalinsa bazai kwanta ba, daker aka samu motar daukar taki ta nan cikin kauyen namu muka shiga mu duka aka shimfid’e baba bisa tabarma,da yake harda yan kayanmu muka dauko don ba makawa sai an kwantar damu asibitin.

 

********

 

Sunan garinmu *GEZAWA* karamar hukumar kano state ce, haka na wayi gari na ganmu acikin wannan gari mai cike da mutane ma bambanta, masu kirki da marasa kirki rayuwar da ake a kauyen gezawa rayuwace dai ta kak’ani kaye, talakawa ne zuryan acikin wannan garin amman zan iya cewa ba wad’ada talauci yaima katutu irin gidanmu, tunda nai wayau haka ja tashi na samu baba baida lafiya sannan abinda zamuci yana mana wahala,duk da wannan ciwon nashi haka yake fita yana nemowa ko yayane aci duk da bakullin muke cin abinci ba, muna iya yini mu kwana bamu ci ba.

 

Har gona baba garesa innamu ma amman basu da halin noman saboda noma sai kana dashi kakeyi,basu ajeba basu ba wani ajiya ba.

 

A bakin innamu naji cewar su d’in yan gudun hijirane sukazo wannan garin, ankai ma garinsu hari aka kashe masu dangi da yan uwa dole suka gudo suka taho nan,tace acikin wannan gayyar suka had’u da babanmu sukai aure anan garin, su y’an Cameron ne innamu don ita d’in shuwa ce sadakar yalla shiyasa takeda mahaukacin kyau, takeda gashi indai akace maka shuwa to angama magana,babanmu kuwa su yan libiyane asalinsu tun kaka da kakanni amman shi daga wani gari dake cikin baushi sukayo gudun hijrar har suka had’u da innamu,shi fulanin bauchi ne shima babanmu badai kyau ba wannan had’in shine ya jawo mani ruwan kyan da nake dashi, duk gidanmu nafi kowa kyau a cikin gari saboda kyauna na tara makiya da dama,shiyasa banda qawa ni saboda sunajin haushina duk samarin su ni suke so, ni kam bana ma biyewa saboda yadda naga suna nuna mun.

 

A haka muka taso cikin gezawa nida zainab munyi primary da secondary amman ni na tsaya ne Jsce ban koma ba, duk da karatun kyautane hakan baisa na koma ba saboda halin rayuwa, kayan duk sun yage bana iya fita dasu a haka.

Zainan ce take aji biyu yanzu yayanmu ya samu ya kammala secondary dinsa kusan shekara biyarce tsakanin mu, sannan babu laifi munyi karatun allo littatafai duk mundan tab’a babu laifi don yanzu haka inda izu talatin da biyar akaina zainab ashirin yayanmu kau yai sauka, a shekarun mu kuwa yayanmu zaiyi shekara ashirin da bakwai ni kuma ashirin da d’aya zainab na bata shekara biyar itama yanzu tana cikin sha shidda kenan, wannan shine asalin mu.

 

 

 

 

Banyi alkawarin posting kullin ba, haka zalika duk abunda kukai ci karo dashi kuyi hkr haka labarin yazo dole a haka zai tafi ngd.

 

 

Mom muhseeN


‚Äč


Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na TelegramPowered by: www.mynovels.com.ng

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.