Hausa Novels

Jarirai Page 1-200

 

*JARIRAI*

Lamarin ya fara ne a wata ranar Laraba da safe ina ta sauri dan fita aiki, kasancewar yau ranar ina da wasu manyan ayyuka da zan gabatar.

Ina Toilet ina murza wanka da injin Bature mai tunkuɗo ruwa, (Shawa), kamar almara kunnuwana suka fara jiyo min sautin kukan *JARIRAI* daga wajen ɗakin, nan da nan na dakata da murza soson wankan da na ke yi a jikina nayi tsai! Ina sauraro dan tabbatar da saƙon da kunnuwan nawa suke aikewa da ƙwaƙwalwata.

Da gaske dai kukan *JARIRAI* ne na ke ji, Ras! Ƙirjina ya buga da ƙarfi, ba komai ne kuma ya saka ni cikin wannan yanayin ba face sanin da nayi cewar Matata ko ɓatan wata bata taɓa yi ba tsawon shekaru bakwai da yin aurenmu balle in saka ran ita ce cikinta ya tsufa ta haife shi yanzu-yanzu.

Kukan Jariran ya cigaba da ratsa dodon kunnena ya na ƙara hauhawar min da farashin faɗuwar gaba.

Nan da nan nayi jifa da soson wankam na shiga ɗauraye jikina babu shiri, dukda cewar ban gama wankan ba hakannan na janyo ƙaton Tawul na rufe jikina da shi nayi waje da sauri dan in ga zahirin abin da kunnuwana ke jiye min.

Matata Nuratu na ci karo da ita ta yi ɗai-ɗai a kan faffaɗan gadonmu hannunta riƙe da waya, ko ba a faɗa min ba na san abin da take aikatawa da wayar, chating ne wanda bata da aikin da ya wuce shi a kullum.

Da sauri na isa gabanta na tsaya ina maida numfashi tamkar wanda ya ci tseren gudun famfalaƙi.

“Nuratu a ina aka samu *JINJIRI* a gidan nan?”

Na watsa mata tambayar ina zare idanu tamkar maye ya ci yaji.

Wani irin kallo take watso min itama wanda ya fi kama da na wacce aka zo wa da maganar rainin hankali.

Bakinta a mele ta ce, “Jinjiri kuma? Ban gane wannan tambayar taka ba malam, ko ko dai abin naka ne ya motso maka ka zo ka sauke min kwandon rashin mutunci akan rashi haihuwa kamar yadda ka saba?”

Da sauri na girgiza kai, “Kinga Nuratu dan Allah ba wannan maganar ba ce ta kawo ni, babu ma muhallinta a yanzu. Wai ba ki ma lura da yanayin da na fito daga wankan ba ne? Wallahi kukan *JARIRAI* ne ya ishe ni shine na fito inga ko baƙuwa muka yi.”

Kallo na ta yi sama har ƙasa, “Hmmm! Maza kenan kun san takan bariki! In kuka so latsa matayenku kun fi kowa iya shan babbar kwana… To ai sai ka koma ka ƙarasa wankanka, *JARIRI* kuma wata kila in ka fito ka tarar na haife maka shi tunda har kukansa ke yi maka gizo a kunne.”

Na fuskanci dai Nuratu ba ta ɗauki maganar tawa da muhimmanci ba, dalili kenan da yasa na ƙara takawa na nufi falo dan dai in ƙara tabbatarwa ko ba baƙuwar mu ka yi ba, dan ni fisabilillahi na ji kukan jariri, kuka ba irin wanda na saba ji daga bakunan *JARIRAI* ba, wannan kukan na musamman ne, cike yake da ban tsoro da haifar da fargaba.

Na isa falon na shiga dube-dube tamkar ɓarawon da ya shigo yin sata, babu kowa kuma babu komai, falon yana nan yadda yake bai karu da komai ba bai kuma ragu da koda silin tsinke ba.

Har na yunkura da nufin sake komawa dakin namu dan in koma Toilet in ƙarasa wanke kumfar wankan da ta riga ta bushe a jikina sai na sake jin wata muryar Jaririn ta canyare da kuka…

Tamkar yadda idan Zakara ɗaya ya yi cara sauran Zakaru suke amshewa su yi ta yi, haka na ji muryoyin *JARIRAI* sun amshe da kukan su ma.

Ai sao na ji ina neman yanke jiki in faɗi, na daure dai na ƙwaci ƙarfin gwiwa na koma ɗakin da sassarfa, ashe abin da zan gani shine zai kusan yin ajalina ta hanyar tsoratani.

Babu Nuratu a kwance a gadon kamar yadda na fita na barta, maimakon hakan ma sai wani kyakkyawan *JARIRI* shimfide a kan gadon namu cikin shigar alfarmar sai faman tsandara ihu yake ga wani farin abu mai kama da ruwan nono na ɓuɓɓugowa daga babban ɗan yatsansa da ya ke cikin bakinsa.

Nayi yunƙurin juyawa cikin zafin nama dan na fita a guje amma sai na ji tamkar an riƙe min ƙafafuna da dabaibayi. Jikina ya shiga rawa kwatankwacin tsohon Baushen da ya ji kidan farauta, bakina da zuciyata suka kulle balle in samu damar halarto addu’ar neman tsari daga shaidanu.

Abin da ya ƙara gotar min da saitin ƙwaƙwalwata shine ganin yadda jinjirin ya taso cikin iska shuuu tamkar wanda aka sa hannu aka dauko shi, a daidai saitin kaina ya tsaya yadda zan iya ganin sa sosai.

A yanzu babu riga a jikinsa, cikinsa kuma a ɓule jini na ta ɓulɓula yaron yana cigaba da kukan da yake ƙara zare min ƙarfin gwiwata.

Baki sosai jinjirin ya buɗe ya soma magana cikin kukan da ya ke yi.

“Sunana *BABUL* ni ne ɗanka na farko! Dan me yasa za ka ji tsoro na? Shin ba ka so wannan ziyarar ta mu gare ka ba ne ko me? Ta ya ya *UBA* zai ji tsoron ‘ya’yansa?

Ka sani ya kai Babanmu, yanzu adadin mu mun kai mu ɗari Bakwai da Sittin da Biyu, kuma sannu a hankali kowa zai kawo maka ziyara ɗaya bayan ɗaya har zuwa kan Autarmu, kuma kowa da irin sigar da zai bayyana da ita gareka, musamman autarmu tafi kowa fitina, sai ka yi haƙuri da irin sigar da za ta zo maka…

Wannan zuwa na ne a matsayi na na jagoran tafiya, na zo maka da saƙon cewa ka shirya kyakkyawar tarba ga sauran ‘yan uwana da su ke tafe gareka, kafin daga bisani mu zo maka gaba ɗayan mu bayan kowa ya kawo maka tasa ziyarar shi kadai…”

Yana gama faɗin haka na neme shi sama ko ƙasa na rasa, sannan kuma kamar an yi ruwa an ɗauke haka na ji ɗif komai ya tsaya, kukan *JARIRAN* da na ke jiyowa sama-sama shima ya ɗauke ɗif.

Sannu a hankali kuma ganina ya koma dishi-dishi, sautin da kunnuwana ka iya ji shi ma ya dusashe, sai na ji komai na jikina ya saki tamkar an kwance Akuyar da ta shekara a ɗaure.

Na zame na zube ƙasa sharab bakina na ambaton sunan matata Nuratu! Nuratu!!!

Muntasir Shehu

*JARIRAI*

2

Komai ya wuce tamkar dama ba a duniyata ta zahiri duk abin da ya faru, ya faru ba.

Sai dai ƙwaƙwalwata da gangar jikina sun ƙi yarda da hakan, dan haka har zuwa lokacin da muke zaune gaban Teburin cin abinci ba a cikin saiti na ke ba.

Na kai dubana ga Nuratu, gaba ɗaya hankalinta na kan wayarta ta na aikin da ta saba, sam ta ƙi yarda ma ta ba wa halin da nake ciki muhimmanci.

Wayata da ke ajiye saman Teburin cin abincin tayi karar shigowar sako, karar ta yi daidai da bugawar zuciyata da karfi, na miƙa hannu da sauri na janyo wayar dan in duba sakon da ya shigo.

Shiru nayi na wasu dakikoki ina nazari, nazari na ke a kan yadda za a iya turo saƙo da lamba guda ɗaya jal! Lambar ma kuma ta mafarin ƙirga, wato (1).

Tun kafin na kai ga bude sakon ƙirjina ke dukan dubu-babu-iyaka. Da na bude sakon kuwa sai na tarar da abin da ya kusa tsinke ruhina daga gangar jikina.

“Hawayen *Baƙin ciki*, Hawayen *Jini*, Hawayen rabuwa da *Mahaifiya*, Hawayen rabuwa da *Duniya*.
Duniya mai cike da farin ciki, Duniya mai cike da ƙyale-ƙyale, Duniya mai samar da *Shagala* da rusa *Fanɗararru*.
Ya kai *Babanmu*, yau ba ma *Duniyarku*, ba ma tare da ku, sai dai *Duniyarmu* ta fi taku sau babu adadin lissafi, Allah ya fi son mu fiye da ku, dan haka muna gare shi, ku kuma ku yi ta zama a cikin taku duniyar mai cike da rikici da ruɗani, akwai lokacin da *Nadama* za ta zowa mai aikata ba daidai ba, mai burin raba gangar jiki da *Ruhi* mai burin raba *Ɗa* da *Mahaifiyarsa*…

Saƙo daga babban ɗa a wajenka.
*BABUL*”

Abin da ke kunshe cikin sakon kenan, wanda kuma ya yi tasirin tsuke kwanyata ta kasa aiwatar da komai koda kuwa yin gutun nazari a kan sakon.

Zafin da na ke ji a cikin kirjina ya sa ni zargin ko fargaba ta sanya zuciyata ta tsage ne, lokaci guda kuma na ji wata Atishawa mai karfi ta taso min ta yi fitar burtu daga hancina, abin tashin hankali gudaddajin *JINI* ne suka zubo.

Da sauri na sake kai dubana ga Nuratu, wani irin takaici ya turnuke ni, wato duk wannan halin tashin hakalin da nake ciki ita ba ta ma san ina yi ba, tana can tana cigaba da chatting dinta, wannan karon ma ta canza alkiblar da ta ke fuskanta.

Wayar tawa ta sake ruri, a wannan karon ba kukan shigowar sako ba ne, kira na a ke, dan haka na yi saurin duba fuskar wayar ina share uban gumin da ke ambaliya a jikina tamkar wanda ya hadiyi wuta.

HAJIYA ALTI.
Shine sunan da na gani a fuskar wayar, sai na ji sam ban ji dadin kiran na ta a wannan lokacin ba, dan haka ma ban daga kiran ba har ya katse, ko minti daya ba a yi ba wani kiran ya sake shigowa, na dai daure na daga na kara wayar a kunnena.

“Hello Baban aiki ga mu nan fa a kan hanya mun kusa karasowa.” abin da kunnuwana suka fara jiyo min kenan cikin wayar, na yi shiru kuma ban tanka ba.

“Hello Baban aiki ko ba ka ji na ne?” Ta sake tambaya.

“Ina jin ki” na amsa da kyar.

“Wallahi ka ga wata yar guntuwar *Gafiya* ce da ni tsautsayi yasa ta je ta ciyo *Mushe* shine nake so a cire mata *Mushen* a raba ta da shi.”

Na dan yi karamin tsaki, “Hajiya sai dai ki yi haƙuri dan ba zan samu fitowa ba yau, na tashi ba na jin dadin jikina sai dai zuwa gobe ko jibi.”

Daga haka na kashe wayar na yasar. Na dauki cokali na debi lomar abinci, na kusa kaiwa baki mu ka ji an buga mana kofa da karfi.
Aka cigaba da bugun ƙofar tamkar za a cizge ta daga muhallinta.

Ina ji Nuratu ta soma jero tagwayen tsaki, “Mtsw! Wace irin jaraba ce wannan za ta sa a dinga bugawa mutane gida da sanyin safiyar nan haka!”

Ta miƴe fuuu kamar iska tayi hanyar waje. Sai na ji tsoro ya dabaibaye ni tamkar zan sake yin arba da *JARIRIN* da ya tsorata ni dazu, dan haka ba shiri na mike na bita.

Ina zuwa na iske ta buɗe kofar, wata matashiyar *Mata* ta baygana wacce ni dai a ganin ido ban san ta ba, amma na yi mamakin yadda Nuratu ta washe baki tana duban matar tamkar ba ita ce me masifar an zo ana bubbuga musu gida da sanyin safiya ba.

Maganar Matar ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na fara shillawa.

“Nuratu dan Allah taimako za ki yi mana… kin ga Marwanatu ce ta haihu tun daren jiya kuma mun kasa yanke *Cibi* saboda tsananin taurin da cibiyar ke dashi tamkar *Rodi*, rezozi ashirin da biyar muka balla amma cibi ya ki yankuwa, kuma tun jiya *JARIRIN* ke kuka har yanzu bai yi shiru ba ko na sakon daya, ga uban *Jini* da ke fita ta hancinsa da bakinsa… wallahi abin ya matukar bamu tsoro, dan Allah ki taimaka mana kar mu rasa su shi da uwar…” a rikice ta ke maganar cikin sassarfar harshe.

Matar na dire maganarta Nuratu ta kwanto dankwalin kanta ta yafa ba tare da ta ko kalle ni ba tace da matar “Muje.”

Kallo na bi su dashi ina jin wani abu mai dumi na fita a kasan wandona, wato dai fitsari na ke, *fitsarin tsoro*.

Dole in yi fitsarin tsoro, baƙin abubuwan da su ka shigo rayuwata a yau tun daga safiya zuwa yanzu sun isa tashin hankalinsu ya raba ni da numfashina.

Na tuna da yadda lamarin fara, jin kukan *Jarirai*; yadda Nuratu ta juye ta koma *jinjiri*; jinjiri mai tashi cikin iska; mai ɓulallen ciki *JINI* na zuba har kuma ya ka iya bude baki ya yi wasu zantuka masu wuyar zama a kwakwalwa, ga sako ya shigo wayata mai dauke da wasu kalamai da ni dai ban fahimci alƙiblarsu ba.

Yanzu kuma ga wani sabon abin tayar da hankali, wai an haifi *Jariri* da cibiya mai tauri kamar rodi har aka balla reza guda ashirin da biyar gurin yankewa, ta yaya ma za a ce *Jariri* ya kwashi tsawon awanni akalla goma da cibi a jikinsa a raye?

Wane irin sabon lamari ne ya shigo rayuwata haka? Me zai sa a dinga tsorata ni da *Jarirai?*, anya ba sharrin Nuratu ba ne? Anya ba ita ta ke shirya wannan lamarin ba dan ta saka ni cikin rudani?

Kai gaskiya ina da shakka akan lamarin Nuratu, za ta iya aikata komai cikin hatsabibancinta.

Muntasir Shehu

Leave a Comment

error: Content is protected !!