JARIRAI*
3
Ina nan tsaye sai ga Nuratu ta dawo hannayenta sanye da safar asibiti (Hand gloves) wacce tayi face-face da *JINI*, Jinin har ɗiga yake.
Gabana ya fadi, na zuba mata idanu ina kallon ta tana ta faman jero tsaki.
Ta gefe na ta ratse ta wuce tana ta faman babatu.
“Allah wadaran naka ya lalace! Wai ace Mata su kasa yanke cibi, kuma duk ciki babu wacce ba tayi haihuwa sama da huɗu ba amma yanke cibi ya gagara.”
Ban san lokacin da nayi magana cikin rawar harshe ba.
“Yanzu dai kin yanke musu cibin?”
Tana min wani irin kallo ta amsa, “Tun yaushe! da *Farce* ma na gutsure ta dan su tabbatar da bamabancin da ke tsakanin ma’akaciyar lafiya da sauran mata gama-gari, kuma har na yi wa yaron wanka na gyara shi na gyara uwar, kuma ka san wani abu ma?”
Girgiza kai nayi.
“Matar nan ƙarya ta ke da ta ce *JINI* na fita ta hanci da bakin jaririn?”
“To ke ya aka yi jini ya zo hannunki?” Na jefa mata tambayar ba tare da na shirya ba.
“Hmm! Jinjirin ne yayi ta *aman jini*”
Nayi shiru na kasa magana, yanzu tsoron Nuratu ya gama dabaibaye min zuciyata, tabbas duk wannan abin da ke faruwa shirinta ne, to in ba haka ba ta ya ya daga fitar ta ko mintuna biyu cikakku ba ta yi ba amma ta ce min ta yankewa jariri cibiya kuma har ta yi wa yaron wanka ta gyara uwar? wannan fa wani aiki ne da akalla zai kwashi mintuna talatin ko fiye, to ta yaya za a yi haka cikin abin da bai gaza mintuna biyu ba?
Sannan kuma ta ya ya za a ace an yanke cibiyar jinjiri da farce?
Wannan sam ba abin da hankali zai dauka ba ne, dan haka da sauri na dubi Nuratu.
“Nuratu me na yi miki ne dan Allah da ki ke shirin zautar da ƙwaƙwalwata? Duk me ya kawo wannan shirin na tsoratar dani? Tun dazu ki ke tsotatar da ni, dan Allah ki fada min me na yi miki?”
Kallon mamaki ta yi min baki sake, kafin dagabisani ta kaɗa kai cikin gutun murmushin takaici.
“Fatuhu me na yi maka da za ka kawo wadannan maganganun? Yaushe na yi abin da ya tsorata ka? Maganar jin kukan *JARIRAI* da ka ce kana ji dazu kaga dai ashe makociyarmu ce ta haihu, to me ye abin tsoro a ciki?”
“Haba Nuratu kina nufin kice min ba ke bace dazu ki ka rikide ki ka zama *JARIRI mai magana* ba?”
Da sauri ta kalle ni lokacin da take zare safunan da ke hannunta, har yanzu jini bai daina ɗiga daga jikinsu ba.
“Wace irin magana ka ke haka Fatuhu mai kama da almara? A ina ka taba ganin mutum ba *Aljani* ba ya rikide ya canza zubin halittarsa?”
“Ni dai Nuratu dan Allah ki taimaka ki rufa min asiri mu bar batun nan, kin ga saboda wannan halin da na shiga yau ko fita ba zan iya yi ba. Dan Allah ki yi hakuri Nuratu indai maganar *Haihuwa* ce na daina yi miki ita insha Allah.”
Ta wuce ba tare da ta tanka min ba.
Wunin ranar haka na yi shi jikina a sake, tsananin tsoro ya sanya ko ƙofar gida na kasa fita, gani nake kamar idan na kaɗaice kaina zan sake ganin *Aljanin jaririn* da ya zo ya tsorata ni dazu, dan haka ina tare da Nuratu duk inda ta shiga sai na bi ta. Sallolin ranar ma gaba daya a gida na yi su.
Barci a daren ranar ma sai barawo ne ya zo ya sace ni.
Can cikin barcin na soma jin kukan *JARIRAI* kamar a mafarko kamar kuma a zahiri.
Kukan ya cigaba da ratsa dodon kunnena har sai da na tashi a gigice ina ta sharba uban gumi, sai dai me? A zahiri ma kukan jariran cigaba da tashi yake. Nayi sauri na lalubi makunnar fitila na kunna, haske ya gauraye dakin, na kai dubana wajen kwanciyar Nuratu.
Tana zaune ta kifa kan ta cikin tafin hannayenta ta juyo min bayanta.
Cikin rawar jiki na kai hannuna da ke karkarwa na taba ta, fitgigit! Tayi ta dago kai tamkar wacce aka watsawa ruwan sanyi.
Ta juyo da kanta mu ka yi ido biyu, Innalillahi.. kun san me na gani?
Kan Nuratu na gani ya juye ya koma kan *JARIRAI* sannan kuma bakinta cike da zakwa-zakwan hakora tana ta fitar da *Yawun jini* daga bakin.
Ta sanya wani irin kuka mai kama da na *MAGE*, ta soma tunkaro ni tana cigaba da yin kukan *Magen*
Muntasir Shehu
*JARIRAI*
4
Na yunƙura da dukkan zafin namana dan na tashi na gudu daga ɗakin amma sai na ji tamkar an ɗaure jikina da sarƙoƙi, Nuratu kuma ta cigaba da tunkaro ni ta na cigaba da yin kukan magen, sai da ta zo daf da fuskata sannan ta tsaya.
Ta fashe da wata mahaukaciyar dariya da ta dinga girgiza dakin da duk abin da ke cikinsa.
Jikina ya dinga ɓari tamkar tsohon Baushen da ya ji kidan farauta, baya ga wani zazzafan gumi da ke keto min ta kowace kafa ta jikina.
Bakina na rawa na shiga yi mata magiya a kan kar ta cutar da ni dan Allah.
Nan da nan ta dakata daga dariyar da ta ke babbakawa ta kuma turɓune fuska.
“Me yasa ka ke tunanin zan cutar da kai? Ni fa ‘yarka ce! Ta ‘ya za ta cutar da Mahaifinta?”
Girgiza kai na dinga yi ba tare da bakina ya iya kara furta wata kalma ba.
Mikewa Nuratu ta yi tare da juya min baya. “Ka yi hakuri da yanayin da na zo gare ka ya kai Babanmu, ni ma na kawo maka tawa ziyarar ne kamar yadda yayanmu BABUL ya zo maka, ni sunana SHASHAT, kuma da haka na ke maka sallamar bankwana, ka huta lafiya…”
Ta na gama fadin haka ta taka ta nufi Toilet, nan ni kuma na ji duk wani ɗauri da nake ji an yiwa jikina ya saki.
Na yunkura kuwa da karfi na sauka daga gadon kai tsaye kuma hanyar fita na nufa.
Ji na yi an kira sunana, na juya da sauri, Nuratu ce tsaye a bakin Toilet din fuskarta na digar da ruwa wanda hakan ke nuna wanke fuskar tata ta yi.
Ban san lokacin da na fara magana cikin zafin zuciya ba, “Nuratu ashe ke Matsafiya ce? Yaushe ki ka fara mu’alama da Aljanu? Wallahi yau sai kin faɗamin dalilinki na shiga kungiyar asiri har ki ke turo min Aljanu suna tsorata ni.”
Ganin ta fara taku ta na shirin nufo inda nake yasa ni ma na fara ja da baya ina daga mata hannu alamar ta dakata.
“Kar ki sake ki karaso nan Nuratu!”
Tsayawa ta yi tana cigaba da auno min kallon mamaki, ta dan jima a haka kafin ta yi magana.
“Fatuhu ni ce ka ke zargi da shiga kunyar Tsafi? Fatuhu ni ka ke cewa ina ta’ammali da Aljanu? Haba Fatuhu yanzu fa dare ne! Me yasa ba za ka bari zuwa gobe da safe ba sai mu yi magana idan ma tsorata ka ke yi.”
Da sauri na dakatar da ita, “In bari sai gobe ko? Wato kafin goben kin karasa kashe ni ko?”
“To yanzu ya ka ke so mu yi Fatuhu?”
“Fice min za ki yi daga gida, dan ba za ki kara kwanar min a gida ba Nuratu.”
Share ni ta yi ta juya ta haye gado ta ja bargo ta yi kwanciyarta ta bar ni nan tsaye cikin jin matukar tsoro da fargaba da kuma tarin takaicin ta, na ayyana a raina ba zan kwana a dakin ba gwara in fita ko a tsakar gidan ne in kwana yadda da na ji wani abu da zai tsorata ni zan ji dadin fecewa.
Amma sai dai me? Ina yunkurawa da nufin daga kafata in tafi sai na ji ta gam ta manne a ƙasa, na dage duk karfina na sake yunkurawa amma ina! Tamkar an saka gam an like kafartawa. Nan kuma na ji wani abu mai nauyi ya zo ya danne min kwakwalwa, take na ji duk kuzari na ya kare ban san lokacin da na zame na zube a nan gurin ba.
Washegari koda na tashi ban bi takan Nuratu ba, hasali ma ji na yi na kasa yi mata maganar komai duk da cewa abin na ta yi min yawo a zuciya amma na kasa ko yi mata kallon tuhuma, haka na shirya na fice gurin aiki.
A Asibitin da na ke aiki na cigaba da duba marasa lafiyar da su ke da bukatar gani na kasancewa ta Likita mai kula da abinda ya shafi mata da kananan yara.
Bayan na sallami wadanda ke cikin ofis din nawa a lokacin sai na basu umarnin su turo min wacce ta ke gaba.
Aka turo kofar aka shigo cikin rangaɗa doguwar sallama, haka kawai sai na ji gabana ya fadi da ganin baiwar Allahr nan, na zuba mata ido har ta samu guri ta zauna tana cigaba da jijjiga Jinjirin da ke hannunta wanda ya soma kuka.
Gaishe da ni ta yi cikin girmamawa kafin ta fara rattabo jawabanta.
“Likita ka ga yarona ne yau kwanan sa biyu da haihuwa amma cibinsa ba ta daina zubar da jini ba, wata makociyata ce ta zo ta yanke masa cibin kuma da Farce ta yanke, da ta yanke cibiyar kuma sai ta saka sauran cibiyar a leda ta tafi da ita…”
Matar na direwa kwakwalwata ta shiga tariyo min abubuwan da su ka faru a jiya, na tuna yadda Nuratu ta ce min ta yankewa Jinjiri cibiya da Farce, kenan wannan matar ce?
Kenan ta tabbata Nuratu Matsafiya ce tun da gashi wannan matar ta sanar min cewa bayan Nuratun ta yanke cibiyar ta kulle sauran a leda ta tafi da shi, to me za ta yi dashi kenan? a ina ta boye shi kuma?
Nan da nan gumi ya soma tsiyaya a jikina na mike cikin zafin nama bakina na ambaton sunan “Nuratu! Nuratu!!!”
Matar ta kalle ni da sauri tana kada kai, “Tabbas ita ce! Sunanta Nuratu, ashe ka san ta? Wallahi ita ce kuma ina zargin kodai Mayya ce ita ko kuma ‘yar Mafiya, kuma wallahi in har yarona bai samu lafiya ba sai na yi shari’a da ita.”
Tsawa na daka mata, “Ke! Tashi ki fice min daga ofis, wato ke ta turo kara dagula min lissafi ko? Wallahi idan ba ki fice ba sai na kira Police sun tafi da ke ta hanyar ce musu ke barauniyar JARIRAI ce!”
Tuni matar ta rikice, jikinta na bari ta rungume jinjirin hannunta ta mike ta yi wuf ta fice.
Da sauri na yunkura na bi ta dan inga inda za ta nufa, amma abin mamaki wayam babu ita babu dalilinta.
Wasu mata da ke zaune a kofar ofis na tambaya ko sunga wacce ta fita yanzu suka tabbatar min ba su ga kowa ba.
Na cigaba da tsayuwa a gurin ina cigaba da ayyana abubuwa da yawa a raina a game da Nuratu, tabbas zama na da Nuratu ya zo karshe, dole ne in sanar da iyayenta halin da ake ciki.
Da wannan tunanin na kulle ofis gaba daya duk da cewa lokacin tashi na bai yi haka na rufe ofis din na fice daga Asibitin.
Kai tsaye gurin da mu ke ajiye motoci na nufa cikin sauri jikina na cigaba da rawa.
Na bude motar tawa zan shiga, kamar an ce min in juya bayana, kwatsam! Na ga wata ‘yar mitsitsiyar yarinya da ba ta fi shekaru biyu ba a zaune rungume da JARIRI ta na shayar da shi…
Na runtse idanuna da sauri tare da kokarin karanto addu’o’i amma na kasa, na dai kokarta na shige motar tawa na tashe ta na falla a guje na hau titi.
Tuki na ke ba tare da ina tantance menene a gabana ba, burina kawai na ga na isa gidan Yaya Murtala yayan Nuratu dan in sanar masa da abinda ke faruwa, kamar daga sama na soma jiyo kukan Jarirai, kafin na ankara sai na ga dukkan motocin da ke gabana sun rikide su koma JARIRAI sabbin haihuwa da ko cibiya ba a yanke musu ba, su na kwakkwance a titin su na cigaba da tsanadara ihu mai shiga cikin kai ya haifar da tsananin tsoro da razani mai barazanar tafiyar da numfashi.
Ban san lokacin da na take burki da karfi ba, ji ka ke ‘kiiiiiiii!
Muntasir Shehu
Leave a Comment