Jariri Hausa Novel Complete

JARIRI HAUSA NOVEL COMPLETE

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Jariri Hausa Novel Complete

JARIRI

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

 

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

 

GARGAÆŠI

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

 

1&2

 

Fuskar Halifa É—auke da damuwa yace, “Inno gaskiya zuwa gidan Nusaiba da matsala saboda ko kaÉ—an banasan tayi nesa dani, na shaÆ™u da matata banasan ko nan da cen taje kawai kuyi haÆ™uri ku barta a nan” Inno ido ta zura masa tana ganin rashin kunyar Æ´aÆ´an zamani ido biyu, kafin tayi magana Goggo ta karÉ“e zancen da, “Ka ji mun yaro da sabuwar salawaitun fitsara ido biyu, mu zaku gwadawa fitsara da rashin kunya? Munga tantabaru ma wajen soyayya yaran yanzu da komai sai sun nuna rashin kunya a ciki, mun Æ™i mu bar maka ita sakarai kawai” Inno ta ce, “A’a barshi Hansai ya nuna mana ya kusa haÉ—a kafaÉ—a da mu, tunda ya kusa ajje É—a kinga mun haihu shima ya haihu ai mun zama É—aya da shi, fitsararre mai idanun marasa É—a’a dubi yadda yake fiÆ™i-fiÆ™i saboda É—iban albarka” Nusaiba da ke gefe ta zumÉ“uri baki gaba ta ce, “Ni dai gaskiya Inno ku Æ™yaleni a nan inyaso wani a cikinku yazo ya zauna mun”

 

Nusaiba na rufe baki Goggo ta ce, “La’ilaha’illallahu Muhammada É—an Abdullahi, Inno kinji É—ibar albarka da yarinyar nan zatayi mana irin ta yaran zamani, kinji Nusaiba ta zaÉ“i miji akan gidan ubanta, ke dan Ubanki ni zaki nunawa rashin kunya ido biyu, idan ban kwashe miki albarka ba kice bani bace?” Halifa ya ce, “Goggo abun fa bai kai haka ba, saboda Allah zuwa gidan nan yayin haihuwa ba fa dole bane ku barmun matata a gida mana, ina jin É—umunsu ita da abinda zata haifa amma kunzo sai kwashe mana albarka kuke, a haka zan barta taje wanka gida kuna kwashe mata albarka? Haba ina dalili.”

Fataucin Mata Hausa Novel Complete Documents

Wannan karan Inno ce ta kuma rafka salati ta ce, “Tir da wannan halin naka na rashin É—a’a amma dai Halifa na sai na kwashe maka albarka, wato jarabar taka ido biyu har agabanmu dan rashin É—a’a? Wato mu bar maka yarinya inyaso ko arba’in bazatayi ba ka nuna rashin É—a’a mujita da wani cikin ko?” Halifa hannu biyu yasa ya rafka tagumi saboda tsofaffun ba Æ™aramin caja masa kai suke yi ba, cikin damuwa ya ce, “Inno wai dan Allah me yasa kunfiya matsala ne? Ni fa shiyasa wani lokacin ko ziyararku banaso saboda ba’a kwashewa ta daÉ—i da ku”

See also  Hotunan yadda ake saduwa da amarya

 

Inno daÆ™uwa ta watsa masa ta ce, “Ubanka Salisu shine me matsala, kuma wallahi kamar a kunnensa zan kira uban naka a waya naji ko shi ya baka lasisin da zaka É—ebe mun albarka” tashi yayi ya fice daga falon dan yasan indai ya cigaba da biye musu to tabbas zai hau sama da su.

 

Nusaiba da sauri ta tashi tabi bayan mijinta bisa tsautsayi ta harɗe ta faɗi, nan take ta fara naƙuda ba shiri suka fara ƙwala masa kira, hankali a tashe ya dawo suka kamata suka sakata a mota suka wuce asibiti.

 

Zuwan su asibiti da awa guda Allah ya sauki Nusaiba lafiya ta haifo ɗanta namiji kyakkyawa da shi, Nurse ɗin data karɓi haihuwarce ta fara goge jaririn amma wani abu daya ɗaure mata kai, yadda jaririn ya ƙura mata idanu ba kiftawa har hannu tasa ta rufe masa ido amma ƙir idanunsa a kanta, idan ba musu idanunta suke yi mata ba kamar ma harararta ta ga jaririn yana yi. A haka ta samu ta gama gyarashi da gurin aka sa masa kaya Nusaiba ta rungume abinta suka koma bacci, kafin wani lokaci tuni ƴan uwa sun cika asibitin kowa xai zo hannunsa ɗauke da kullar abinci yake shigowa, gudun hayaniyarsu yasa nurses suka hanasu shiga ɗakin da Nusaiba take saboda karsu hanata bacci.

 

Bayan wani lokaci, Nusaiba ce ta tashi gabaÉ—aya yunwa takeji cikinta kamar anmata yasa, batasan da kawo abincin da akayi tana bacci ba dan haka ta Æ™walawa Nurse kira, tana zuwa tace ta kira mata su Inno da sauri ta fita ta sanar musu da saÆ™on Nusaiba, su Inno tare da sauron Æ´an uwa ne suka shigo É—akin fuskarsu É—auke da farinciki, wasu daga ciki ne suka É—au jaririn, Nusaiba a shagwaÉ“e ta ce, “Inno yunwa fa nake ji ku haÉ—a mun ruwan tea” Inno ita da goggo da Æ™arfinsu suka nufi wajen kullar amma tunkafin su buÉ—e sukaci karo da tsottsatssen Æ™ashi da wanda aka taune akan murfin kular, suna buÉ—e Æ™atuwar kular abinci yace É—aukeni inda kuka ajiye.

 

Ledar Æ™aton buredin ma cen Æ™arÆ™ashin gado suka hangota, da alama anciye biredin iskar fanka ce ta tura shi cen Æ™asan gadon, mamaki ne ya kamasu amma babu wanda ya magantu a cikinsu, Inno ce ta É—akko flask É—in shayi shima ta jishi shafal ba komai a ciki, a hassale ta fara magana. “Yau naga rashin É—a’a ido biyu ni za’a gwadawa É—iban albarka. Waye ya cinye abincin da shayin gurin nan?” Goggo ta ce, “Gane mun hanya yarinya ta haihu madadin taci ta Æ™oshi gashi wasu Æ™arti sun cinye”

See also  Wani Haske Complete Hausa Novel Page 105

 

Da mamaki Mahaifiyar Nusaiba ta ce, “Inno duka abincin kulolin aka cinye? To Nusaiba ko kinci abinci É—azu?” Nusaiba ta girgiza kai, Inno ta ce, “Banda rashin É—a’a Nusaiba duk cinta ai bazata iya cinye cooler uku ta abinci ba, maza kiramun masu fararen kayan cen gabaÉ—aya sai na kwashe musu albarka banda su babu me aikata wannan rashin É—a’ar, yara sai rashin É—a’a da É—iban albarka kamar Æ´aÆ´an mayunwata.” Mami mahaifiyar Nusaiba ta nufi mazaunin Nurses É—in ta kira suka taho tare dan su a tunaninsu wani abun ne ya samu Nusaiba, suna zuwa Inno ta kalle su É—aya bayan É—aya ta ce, “Ina kuka kai abincin gurin nan saboda É—iban albarka yarinyar nan ko loma É—aya batayi ba, idan sha’awa ya baku basai ku tambaya a baku ba amma zaku nuna mana halin rashin É—a’a wato sai kunci na Allah ya isa ko?” kallan juna suka farayi kamar haÉ—in baki suka ce, “Wane irin abinci ana zaune Æ™alau kamar wasu mayunwata” Goggo kulolin ta janyo tana cewa, “Gasu naga É—azu ke kika taya ni shigo da wata” É—an zaro Ido sukayi suka ce, “Duka abincin cikin kular aka cinye” Inno ta ce, “Kiji mun shakiyyan yara marasa É—a’a tambayarmu ma kuke yi, wallahi ko ku fito dashi ko na É—ebe muku albarka ku bi duniya”

 

ÆŠayar nurse É—in ce ta É—an fara É—aukan zafi ta ce, “Iya wai me kuka É—auke mu ne saboda kuma muna ma’aikatan jinya duk wata Æ™ura aka É—ebo sai a watsa mana…” Inno a hassale ta katseta. “Amma kedai wannan yarinyar anyi maras É—a’a wallahi idan baki rufen baki ba zan kwashe miki albarka ki É“alÉ“alce ” ganin abun na nema zama faÉ—a Mami ta sasanta tare da yin waya gida akan a Æ™ara kawo musu wani abincin.

 

A yammacin ranar aka sallami Nusaiba ita da Jaririnta, tun a asibiti ake taÆ™addama akan zaman Nusaiba a gidan ita Mami ma shiru tayi saboda yadda su Goggo suke ja’ina da Halifa amma fir yaÆ™i yarda. A hassale Goggo ta ce, “Rakiya wai dole sai mun bi ta yaron nan ne? Shi da ita duk jikokinmu ne me zamu zauna muna bi ta tasu, ni idan ya bari idanma bai bari ba zan É—auke ta na wuce gurina da ita.” Inno sheÆ™eÆ™e ta ce, “Hansai au ke zaki tafi da Nusaiba? Wallahi bazan yarda da wannan É—iban albarkar ba nice na haifi Uban Halifa ni nake da iko da wannan maganar” Goggo ta ce, “Rakiya wallahi baki isa ba nina haifi Uban Nusaiba dan haka nina fi dacewa da tafiya da ita” Inno ta ce, “Ahayye Allah na dawo inji kishiyar me yaji, wallahi baki isa kizo mun da wannan rashin É—a’ar ba, ninan gurina zan wuce da ita.” Halifa ne ya shigo yaji yadda suka fara hawa sama a tsakaninsu dukda sun kasance Æ´an uwa kuma aminan juna, Halifa ya fahimci sarai inda maganarsu ta dosa yace,”Nifa gaskiya babu wanda zai É—aukarmun mata wai magana É—aya ayita yinta har a asibiti ina dalili, idan fa kuka takura zau É—auke matata na kaita wani gidan nawa inyaso na samu wacce zata dinga kularmun da ita ” Inno ta ce, “Oh La’ilaha’illallahu muhammad rasulillahi sallallahu’alaihi wasallam, oh ni É—iyar mutum huÉ—u ba ko É—aya naga abinda ya tsirewa kakata Laure ido, yanzu É—ibar albarkar da zaka mun kenan Halifa wani bari ubanka ya zo ya shata mun layi da kai, kai anya ma wannan ba’a sauyawa Salisu kai a asibiti ba?” Mami ce ta ce, “Inno dan Allah kuyi haÆ™uri ku bar masa matarsa tunda har yace bayasan taje gida wanka, shawara É—aya zan bayar gabaÉ—aya kuje ki zauna mata ai ina ga hakan yayi?” gabaÉ—aya sun aminta da shawarar Mami, Inno ta ce. “Hansai kinga gwara da akayi hakan dan kinsan ni yanzu bana iya aiki a bakin wuta, na dinga kula da aikin cikin gidan kina É—ora garwan wankan mejego da jaririnta idan ba haka ba kar naxo na aikata rashin É—a’a” Goggo ta ce, “Eh kuma fa hakane Rakiya kinga zamanmu bibbiyunma zaifi.”

See also  Juhud Hausa Novels Complete

 

Da wannan shawarar suka tarkata zuwa gida tare da Æ´an uwa da abokan arziki.

 

A daren ranar da suka koma da daddare kimanin karfe biyun dare Inno ce ta fito fitsari ahanyarta ta dawowa, ta hango Æ™aÆ™anin abu na tafiya idan yayi gaba sai ya dawo baya ya rangwaÉ—a kai gefe. A É—an tsoroce Inno ta ce, “Toooo yau wacce irin É—iban albarka nake gani da tsohon daren nan” ta Æ™arasa magana tana haskashi da Æ´ar fitilarta.

 

A zabure ta ja baya ganin jaririn Nusaiba ne tumÉ“ur ko wando babu, washe mata baki yayi ya dafe Æ™eya yana wani irin layi kamar wanda yasha ya maku, cikin wata irin murya ya cafe irin maganar Inno yace, “Tooo yau wacce irin É—iban albarka nake gani da tsohon daren nan” tana faÉ—a yana wani irin tsalle kamar zai faÉ—o kan Inno, wurgar da butar tayi saboda tsoro ta fara gudu. Tsalle yayi ya caÉ“e zanin Inno har ya taÉ—e ta ta faÉ—i da rarrafe ta dingan rarrafawa tana Æ™wala ihu, lokacin da ta Æ™arasa É—akinsu tuni ta daÉ—e da wurgar da zani daga ita sai É—an fatarinta.

 

0 thoughts on “Jariri Hausa Novel Complete”

  1. Pingback: FATAUCIN MATA HAUSA NOVEL COMPLETE DOCUMENTS - Hausa Novels

  2. Pingback: DOWNLOAD BABU SO HAUSA NOVEL COMPLETE - Hausa Novels - Gyaran Jiki - Sirrin Rike Miji - Kalaman Soyayya

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top