Jaruma Hannatu Usman ta sha mari daga hannun Lawan Izzar So

Jaruma Hannatu Usman ta sha mari daga hannun Lawan Izzar So

Ana  zargin ɓacin rai ne ya sanya Lawan Ahmad ya ɗaga hannu ya kwashe jaruma Hannatu Usman da mari a lokeshin ɗin ɗaukar diramar nan mai dogon zango ta ‘Bugun Zuciyar Masoya’.

Wannan abu ya faru ne a Kano a lokacin da ake shirye-shiryen ɗaukar kashi na 37 na shirin, inda jarumar ke fitowa da sunan Nafisa.

Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa ran Hannatu ya ɓaci ne bayan an faɗa mata cewa labarin ba ya buƙatar ta a wannan lokaci kuma za a canza ta da wata sakamakon haɗari da ta yi a fim ɗin.

Majiyar, wadda ta buƙaci mu sakaya sunan ta, ta ba mu tabbacin cewa an samu matsalar, kuma ta ƙara da cewa, ”Kowane fim ana yin sa ne don riba kuma da man shirin fim mai dogon zango ya gaji haka, a cire ka lokacin da aka ga dama ko kuma ana ganin labarin ba ya yi da kai, sai a cire ka a sa wanda aka ga ya dace.”

Karanta kuma  Tallafin Ramadan: ‘Yan fim sun yaba wa Rarara.

A yayin da majiyar ke bayyana yadda marin ya auku, ta ce, “Kowa ya san Lawan Ahmad ya na da zafi kuma ita jarumar gani ta ke kamar ba za a iya yin fim ɗin ba in ba ta. To bayan an bijiro mata da wannan batun, nan fa ta fara maganganu marasa daɗi wanda har ya kai ga samun matsala da darakta Nura Mustapha Waye inda kuma Lawan Ahmad ya tsoma baki tare da zagin jarumar har ta kai ga ya mare ta.”

See also  Yanda zaki gyara Fuskar Ki tayi kyau Sosai

Cikin fushi, Hannatu Usman ta yi wani gajeren bidiyo a Instagram inda ta bayyana cewa, ”Ni ba cire ni aka yi a cikin ‘Bugun Zuciyar Masoya’ ba, ni ce nan na cire kai na sakamakon wani abu da ya faru mara daɗi. Duk wani ɗan’adam ba zai jure wulaƙanci ba duk da ana jurewa a yi haƙuri domin gaba in ka na nema a yi maka, amma duk mutumin da zai yi maka abu kan ya maka sai ya wulaƙanta ka ko cin mutunci, haƙura da abin shi ne mafi alkairi.”

Mujallar Fim ta so jin ta bakin jarumar kan wannan batu amma abin ya ci tura saboda ba mu same ta a waya ba.

Sai dai mun samu wanda ake zargi da marin jarumar, wato Lawan Ahmad, don jin haƙiƙanin abin da faru tsakanin su.

Nan take Lawan ya musanta labarin, ya ce shi bai ma san da zancen ba.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top