JARUMAN MATAN KANNYWOOD 10 DA SUKA FI TASHE DA KYAU
Abune Wanda kowa ya sani musamman masu bibiyar mu a wannan shafi na ArewaGuru.com cewa muna tsakuro labarai da rahotanni daga masana’antar shirya fina-finai Hausa ta kannywood.
Jaruman kannywood mata
To a yau ma insha Allahu muna tafe da Sharhi akan goma 10 daga cikin Yan wasan da sukafi kyau da Kuma tarin masoya musamman sabbin fuskokin jaruman Amman Koda zaku ga kadan daga cikin Wandan da tsofaffine Babu wani abu munyi hakan ne sakamakon Suma suna da yawan masoya a ko’ina a fadin duniya shi yasa muka Sanya su cikin jeren.
(1) UMMI RAHAB
Ummi Rahab jarumar kannywood
Sarauniyar kyauce Kuma ‘Yar autar kannywood domin ahalin yanzu babu Wata mace da ta kaita kankanta a masana’antar kannywood din, jarumar ta shigo harkar fim da kafar dama duba da yadda ake Sanyata acikin manyan Fina-finai Kuma daraktoci suna Kiranta ayyuka,
Ummi tana amfani da dandalin sada zumunta kamar haka Instagram, TikTok, wadannan sune kadai inda zaka iya samun hakikanin shafin jarumar,
Tana da masoya da yawan gaske a ko’ina sassa na duniya daban daban shi yasa ta zamto daya daga cikin jeren.
(2) Rahama Sadau
Rahama Sadau
Babu bukatar na tsaya ina yi muku bayani akan wacce Rahama domin Ina tsammani duk Wanda yake bibiyar Al’amuran da suka shafi masana’antar kannywood to zai yi mutukar wahala bai San taba sabo da yadda ta shahara sosai .
Jarumar kyakkyawa ce sosai Kuma tayi nasarar samun masoya fiye da 2.3m followers a Instagram account dinta don haka muka Yanke shawarar saka ta cikin jeren .
(3) Hafsat Idris
Hafsat Idris
Yadda jarumar take yawan fitowa a Fina finan hausa ya ka mata ace itama Kun Santa Amman bari mu danyi muku bayani a game da ita,
Shahararriyar yar wasan hausace Kuma tana daya daga cikin kyawawan Yan mata a masana’antar shirya fina-finai Hausa ta kannywood anfi sanin ta da suna Barauniya dalilin kiranta da hakan shine farkon fim din Mai suna BARAUNIYA shi yasa sunan ya bita ta yadda wasu daga cikin mutane basu ganewa sai an ambaceta da suna haka.
(4) Aisha Aliyu tsamiya
Aisha Aliyu tsamiya
Tsohuwar jarumace Kuma kyakkyawar gaske shi yasa tayi sama da fadi da masoya milyan 1 da dubu Dari 3 a shafin ta na Instagram Kuma ta kasance yar kasuwa a halin yanzu,
Kadan daga cikin fina finan da jarumar da dauki nauyin su sun hada da
(1) Kalan dangi
(2) Kayi nayi cigaban kalan dangi
(5) Fati washa
Fati washa
Ya zama dole Idan ana lissafa kyawawan Yan mata a masana’antar kannywood fati washa ta shiga ciki domin ta kasance Mai kyau kwarai da gaske shi yasa muka San yata acikin wannan jerin.
Sunanta na gaskiya Fatima Abdullahi Yar wasan ta samu nasarar washarere da mabiya sama da milyan 1 da dubu Dari biyar 1.5m a shafin ta na Instagram, sannan tana amfani da dandalin sada zumunta kamar haka, Instagram, TikTok,
(6) Maryam yahaya
Maryam yahaya
Itama zan iya cewa shahararriyar jarumace kamar yadda kowa zai iya fahimtar haka Idan mukayi la’akari da yawan Fina finan da ta fito aciki.
Hakazalika jarumar ta taso da farin jini sosai domin a cikin kankanan lokaci ta shahara kowa ya Santa sakamakon ta shigo masana’antar ne ta hanyar sarki Ali Nuhu An fara ganin fuskar tane a wani fim Mai suna Mansor wanda ta fito a matsayin Mai jagorantar Shirin.
(7) Maryam Musa waziri
Maryam Musa waziri
Ko shakka babu rashin sanin maye kyau ko kyakkyawar mace shi zai sa mutum yaki Sanya wannan jarumar acikin jerin kyawawan matan kannywood domin ta zarce sauran mata da yawa,
‘Yar wasan ta dade tana fim Amman bata bayyana kowa ya San taba sai da aka fara haska wani shiri Mai suna Labarina Wanda Malam Aminu saira ya bada umarnin sa.
(8) Hadiza Aliyu gabon
Hadiza Aliyu gabon
Shahararriyar yar fim ce itama Kuma kyakkyawar jaruma domin an dade ana damawa da ita kuna har yanzu akan ganta acikin manyan Fina-finai masu dogon zango Wanda ake haskawa a tashoshin talabijin da Kuma YouTube .
(9) Momee gombe
Momee gombe
Sabuwar jarumace Kuma ta shigo masana’antar shirya fina-finan Hausa da kafar dama domin cikin lokaci kadan mutane suka Santa bayan ta shafe lokaci tana rawa da waka.
(10) Aisha najamu
Aisha najamu
Nasan dukkanin masu bibiyar Shirin nan Mai farin jini wato IZZAR SO zasu San wacece Hajiya Nafisa to assalin sunanta Aisha najamu Kuma ta jima tana rawa da waka kafin tsundumarta cikin harkar fina finan hausa a masana’antar kannywood.
Kada ku manta kuci gaba da kasancewa tare damu a wannan shafi namu Mai suna mynovels.com.ng muna godiya da ziyarar ku.
[…] JARUMAN MATAN KANNYWOOD 10 DA SUKA FI TASHE DA KYAU […]
Slm
Masha allah
An hay fini a Zangan gabars
Masha allah