JERIN JAMI’O’I 3 MAFI INGANCI WAJEN KARATU A NAJERIYA

JERIN JAMI’O’I 3 MAFI INGANCI

 

 

 

 

 

 

Alkaluman cibiyar AD sun nunar da jami’o’in Najeriya uku ne suka yi zarra a Afirka da kuma duniya Cibiyar ta ce ta yi la’akari da kwarewar jami’o’in wajen janyo masana kimiyyar.

Jami’ar Cape Town da ke Afirka ta Kudu ce ta yi zarra a Afirka. Jami’ar Ibadan (UI), da Jami’ar Najeriya, Nsukka (UNN), da Jami’ar Ilorin (UNILORIN) sun zama kan gaba dangane da masana kimiyya mafi inganci a Najeriya.

JERIN JAMI’O’I 3 MAFI INGANCI 

Cibiyar AD Scientific Index, wacce take kan gaba ta fuskar fitar da alkaluman kwazon jami’o’i a duniya wanda ke da mazauni a Turkiyya, a kwanakin baya ne ya fitar da jerin sunayen kwararrun masana kimiya da jami’o’i na duniya da suka yi zarra na shekarar 2021.

Kamar yadda jerin ya nunar Jami’ar UI ta kasance ta 19 a nahiyar Afirka kuma ta 1,350 a duniya yayin da Jami’ar UNN ta kasance ta 25 a cikin nahiyar kuma ta 1,522 a duniya.

Fashin baki kan cutar corona

Jami’ar UNILORIN kuma ta kasance ta 41 a Afirka sannan ta 1,941 a duniya. Jami’ar Fasaha ta Tarayya, da ke Akure (FUTA) ita ce ta zo ta hudu yayin da Jami’ar Calabar (UNICAL) ta zama ta biyar mafi inganci a Najeriya a kan matsayin.

Jerin jamio’i 3 mafi inganci a fagen masana ilimin kimiyya a Najeriya

Cibiyar AD Scientific Index ta ce matsayin “ya nuna kwarewar jami’o’in wajen jawo hankalin masana kimiyyar da kuma karfin cibiyoyi ta fuskar karfafa ci gaba da rike masana kimiyyar.”

Jami’ar Harvard ita ce kan gaba a duniya kamar yadda jerin ya nunar yayin da Jami’ar Cape Town da ke kasar Afirka ta Kudu ta kasance jagaba a Afirka.

See also  Koyon Turanci: Fassarar wasu kalmomin Hausa zuwa Turanci

A nan kasa, jerin jami’o’in Najeriya ne bisa ingancin ilimin kimiyyar a kamar yadda alkaluman shekarar 2021.

Ga Jerin Jami’o’in

1. Jami’ar Ibadan (UI)

2. Jamiar Nigeria, Nsukka (UNN)

3. Jami’ar Ilorin (UNILORIN)

4. Jami’ar Fasaha, Akure (FUTA)

5. Jami’ar Calabar (UNICAL)

6. Jami’ar Ahmadu Bello Zaria
7. Jami’ar Benin (UNIBEN)

8. Jami’ar Port Harcourt (UNIPORT)

9. Jami’ar Lagos (UNILAG)

10. Jami’ar Obafemi Awolowo

11. Jami’ar Ladoke Akintola LAUTECH

12. Jami’ar Fasaha, Owerri

13. Jami’ar Jihar Legas

14. Jami’ar Usman Danfodiyo

15. Jami’ar ilmin Likitanci na Legas

16. Jami’ar Redeemer’s

17. Jami’ar Kimiya da Fasaha ta Africa Abuja

18. Jami’ar Skyline

19. Jami’ar Covenant

20. Jami’arNnamdi Azikiwe

21. Jami’ar Fasaha ta Minna FUT

22. Jami’ar Uyo

23. Jami’ar jihar Delta

24. Jami’ar Bayero Kano

25. Jami’ar jihar Ekiti

26. Jami’ar Landmark

27. Jami’ar Maidugri

28. Jami’ar Abuja

29. Jami’ar Jos

30. Jami’ar Oye Ekiti

31. Jami’ar Ndufu Alike Ikwo (FUNAI)

32. Jami’ar Olabisi Onabanjo

33. Olabisi Onabanjo jihar Osun

34. Olabisi Onabanjo Abubakar Tafawa Balewa

35. Jami’ar jihar Akwa Ibom

36. Jami’ar jihar Kwara

37. Jami’ar fasahar Modibbo Adama Yola

38. Jami’ar tarayya Dutsin Ma

39. Jami’ar Adekunle Ajasin

40 Jami’ar jihar Edo Iyamho

41. Jami’ar Amurka a Najeriya

42. Jami’ar Neja Delta

43. Jami’ar tarayya dake Wukari, Taraba

44. Jami’ar jihar Ebonyi

45. Jami’ar jihar Nasarawa

46. Jami’ar Elizade Ilara Mokin

47. Jami’ar Bowen

48.Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu

49. Jami’ar tarayya dake Dutse Jigawa

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top