Jiddatul Khair Hausa Novel Complete

Jiddatul Khair Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Jiddatul khair

Slowly yake driving din idonsa a kan titi yana sauraron abokinsa, amininsa, kuma d’an uwansa dake xaune kujera me xaman banxa cikin motar, can dai ya ja tsaki ya girgixa kai, speaking calmly yace “Ni fa da ma ka canxa labarin nan naka Ahmad, in anyway ban ga amfaninsa ba…” Dariya abokin nasa Ahmad yyi yace “Toh ai ni yana da amfani gareni sosai tunda ina sonta and i want to marry her, look Captain don Allah ka cire son xuciya ka gaya min meye aibun Maryam let me know” Wanda ya kira da captain ya shafa lallausan gashin kansa yace “Kasan mene?” Kallonsa kawai Ahmad yake yana jiran jin abinda xai ce,

Captain yace “Ina son ka sanar dani me yasa ku Hausawa baku da xancen da ya wuce na soyayya, ga dai abubuwan ilimi iri iri masu ma’ana da mutum xai karu da su duniya… Amma ku dai soyayya kadai ku ka sa a gaba, did u know that it’s just of recent ina wani karatu nayi discovering cewar Airplane water is riddled with bacteria, not even that, jiya jiyan nan na gano cewar….”

Ahmad dake masa wani kallo ya dakatar da shi ta hanyar cewa “Wannan kai da masu tunani irin naka ya shafa, what u are saying now will add no value to people like me gaskiya” Captain ya maida hankalinsa gaba daya kan tukin da yake, Ahmad yace “Duk sanda na kawo maka maganar Maryam you always have a way to get rid of the discussion ko me yasa?” Captain yace “Ohk you asked me of her flaws if i am not mistaken, right?” Ahmad yace “Yes so” Captain yace “To xaka ji ynxu…. first of all she is local, secondly she gat no qualities da xai sa ka makale mata dude, just imagine an undergraduate fa?? And worst of all she isn’t even beautiful enough, ga dai big babes a garin da ka baro Abuja, sannan….. her hygiene is nothing to write home about, i mean nothing….

Shine ma babban damuwata ma ni” Da mamaki Ahmad ke kallonsa, da farko kasa ce masa komai yyi, can kuma yace “Wani rashin tsaftar kaga tayi??” Captain ya saci kallonsa yace “Oho, wataran xaka gani” Ahmad ya girgixa kai yace “You are talking off hook, Maryam tana da qualities din da ni nake so, I think that’s all? Kuma dama kai idan baka son abu to fa baxa ka ta6a son abun ba, ka dingi discouraging mutum a kai kenan” Captain ya gyada masa kai yace “Ehh haka ne, plss close the chapter”

Ahmad xai yi magana ya hango inda ake tuyar awara a gefen titi, da sauri yace “Captain plss ka d’an tsaya, I want to get this, na mance yaushe rabon inci awara, tun kafin in tafi Uk fa…” Captain ya d’an kalli wajen da ake tuyar awaran ya kara ma motarsa gudu yace “Allah ya kiyaye, domin na je dauko ka a railway station doesn’t mean xa ka mayar da mu gantalallu a hayi….

Meye kuma awara?” Ahmad yace “Toh ka ajiye ni, ai bance sai ka xo ka daukeni a tasha ba dama, you offered to do so” Captain yyi kasa da murya yana rage gudunsa yace “Yanxu Ahmad kasan ta ynda suka yi processing abun nan da xaka ci? Hayi ne fa nan, ka bari kaje gida kasa ayi maka mana, ni Allah bana son locality din nan naka” Calmly Ahmad yace “Su ‘yan hayin ba mutane bane Abuturrab?” Captain yace “Aa ba haka nake nufi ba,

 

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

 

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

I mean… hygiene din, they don’t value it, ka gane ai” Ahmad yace “Kai komai sai kace hygiene, to sannu sarkin ‘yan tsafta, a haka kuma nake son in siya, ba ruwanka kuma” Captain bai kuma ce masa komai ba ganin wani waje da ake suyan yyi parking kafin ya karasa wajen yace “To sai ka sauka kaje ka siya, amma gaskiya you ain’t worth being a Dr wllh, very careless Dr that looks down on Hygiene” Ahmad na hararansa yace “Ae ba dankali nace maka xan ci ba malam,

Awara nace kuma nan dankali ake siyarwa” Captain ya kalli wajen masu tuyan yace “Toh ai ban san yanda Awaran yake ba, ba shi bane wnn din?” Ahmad yace “Ba shi bane” Captain ya ja motarsa yana tukin a nutse, can underneath his breath ya ja tsaki, Ahmad is just too local for his liking, Ahmad yace “I think ga wani wajen can” ta gefen wajen da ya nuna masa Captain ya gangara yyi parking yana kallon yarinyar dake tuyan awaran yana yamutsa fuska shi wnn ko yunwa xai kashesa xai iya cin abinda take yi kuwa, Ahmad ya bude motar ya sauka ya tafi gun ta, ita kadai ce xaune sai yara da almajirai dake tsaye suna jiran a siyar masu awara,

Ahmad yace “Me awara nawa nawa ne awaran naki?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Daya Ashirin” Ahmad ya buda ido ya rike waist dinsa yace “Ikon Allah, kamar dai muna fada da me awara irin wnn amsawan” Still bata kallesa ba ta ci gaba da sallaman yaran da ke gabanta, ta mota Captain ke kallonsu, shi dai Ahmad na tsaye bai sake ce mata komai ba ganin mood dinta, sai da ta sallami yaran gabanta ta daga kai ta kallesa tace “Na nawa xa’a sa maka?” Ya daga kafada yace “Na dari biyar kawai” Tace “Baxai kai ba, sai dai in xaka jira a soya wani” Yace “Toh ba damuwa xan jira a mota” Daga haka ya juya ya nufi motar ya bude ya shiga yana kallon Captain da ya kauda kai da sauri yana kallon daya side din.

Leda biyu tayi masa sannan ta hadasu gaba daya a wani ledan daban,
yajin ma ta xuba masa a wani ledan snn ta mike ta nufi motar ta mika masa ta glass dake bude, amsa yyi yana kallonta da murmushi fuskarsa yace “Kamar dai an 6ata ma me awara rai” Ita dai bata ce masa komai ba, dubu biyu ya ciro a aljihunsa ya mika mata yace “Toh gashi” ta daga kai tana kallon kudin tace “Na dari biyar kace” Yace “Ehh sai ki rike sauran canjin ai ko” Ta sauke idonta kasa tace “Aa ka dai bani dari biyar din dai kawai” Ya bude ido yace “Dama ana maida hannun kyauta baya” ta girgixa masa kai tace “Ban san wa xance ya bani ba a gida” Cikin sanyin murya ta karasa maganan, yayi murmushi yace “Sai ki boye kayan ki” Daga haka ya saki kudin nan kasa yace “To sai anjima me awara,

Allah ya kawo kasuwa” captain da ya ki kallonsu ya tada motar suka bar wajen. Sai da suka kusa fita titin hayi Ahmad yace “I imagine may be condition ne ya sa yarinyar tuyan awara a rana ko, the country is getting tougher and tougher for the less privileged everyday…..”

Captain dai bai ce masa komai ba, Ahmad yyi kasa da murya yace “On a serious note ina jin tausayin poor masses a kasar nan, yanxu banda situation me xai sa iyayenta su barta bakin titi tana wnn sana’a? Allah dai ya rufa ma kowa asiri” Still Captain bai ce masa komai ba har suka shigo Unguwan Sarki, yana kallon Ahmad yace “Mu je can gida ne kawai?” Ahmad ya gyara xama yace “Aa kai ni in ga Ummata tukun, da yamma xan shigo in sha Allah” Captain bai ce komai ba yyi driving har xuwa gidan kanwar Mum dinsa Hajiya Ramlah warce ita ce mahaifiyar Ahmad…

A kofar gida yyi parking Ahmad na kallonsa yace “Baxa ka shigo ba?” Captain yace “Aa ni fa ko jiya na xo gidan nan” Ahmad yace “Sai dai idan Ummi ce ta aiko ka ba dai xuwan kanka ba” Captain ya shafa kansa yana xare manyan idanuwansa ya kasa cewa komai, Ahmad ya ta6e baki ya bude motar ya sauka, da sauri Captain na nuna masa ledan awaransa yace “Heyy ga kullinka ka mance min a mota” Juyowa Ahmad yyi ya jefa masa wani kallo ya dau ledan awaran ya nufi cikin gidansu, Captain ya bi sa da kallo yana murmushi, can ya kashe motar ya sauka ya bi bayansa walking slowly…

 

Siyama ta sake yayanta da ta rungume ganin Captain da ya shigo parlon, tana murmushi tace “Yaya sannu da xuwa” Yace “How are you Siyama” tace “I’m fine” Yace “Ina su Maimuna?” Tace “Sun tafi islamiyya” Yace “Ke fa” Tace “Ka manta nace maka bani da lafiya jiya?” Yace “Ohhh ohk na tuna, Allah ya kara lafiya, Umma fa” Tace “She’s in her room” Tuni Ahmad ya nufi dakin Mahaifiyarsa,

Captain ya bi bayansa.

 

Sai bayan Magrib Captain ya bar gidan tare da Ahmad xuwa nasu gidan a Malali, Babban gida ne duplex me wadatattcen tsakar gida…. Captain yyi parking a daya daga parking lot biyu dake katon compound din, suka sauka motar tare da Ahmad suka shiga ciki Ahmad na cewa “Amma Abba baya gari ko?” Captain yace “Ehh baya nan”

Karanta littafin Gidan Uncle Complete

Zaune take a d’an karamin tsukakken tsakar gidan nasu da kwanon tuwonta a gaba sae dai ba ci take ba duk da kasancewar hannunta cikin kwanon, wata matashiya ce xaune cikin daya daga kananun dakuna uku dake D’an tsakar gidan hannunta rike da mafici tayi daurin kirji, xaune a tsakar gidan kan tabarma wani middle aged man ne da baxai wuce 58 ba, daga cikin dakin matar ke cewa “Munafuka algunguma kawai, sae ana magana tayi mukui ta ki cewa komai, a haka xaki kare cikin nukurci da bakin hali, banda haka uwar me ya ci min naira hamsin a kudina, ko da yake dama ae kin saba halin bera, sae dai na yau yayi min ciwooo tunda ko biyar ubanki bai kawo min yace gashi kiyi cefane ba, to a kan me??” Ita dai bata iya ta ce komai ba har lkcn hannunta na cikin kwanon tuwon ta kasa ci, mikewa matar tayi tana gyara daurin kirjin jikinta ta fito a fusace ta janye kwanon tuwon jin almajiri na bara tace “D’an malam shigo ka amsa” Malam Isuhu dake xaune saman tabarma yace “Ita kuma ta ci me Hansatu??” Wani kallo ta jefa masa tace “Sae ta ci wanda ka nemo aka girka yau” tana fadin haka ta juye ma almajiri ta ajiye kwanon tayi shigewarta daki, shi dai bai kuma cewa komai ba, a hankali ta mike ta dau kwanon ta kai wajen wanke wanke ta shiga hada kayan wanke wanken tsakar gidan, sae da ta gama gaba daya ta mike mahaifinta dake tsakar gidan har sannan ya fiddo hamsin a aljihunsa yace “Gashi ki je ko dankali soyayye ki siyo ki ci Jiddah” karasawa tayi ta amshi kudin da ladabi tace “Nagode Baba” bata rufe baki ba Hansatu ta fito da gudu ta warce kudin tana kallonsa da kyau tace “Saura dari hudu da hamsin kudin cefane na na yau” tana fadin haka ta kulle kudin bakin xaninta ta shige akurkin dakinta, Jiddah ta juya a hankali ta shiga dakinsu ba tare da ta yarda hawayen dake makale idonta ya xubo ba.

 

Washegari da safe wata dattijuwa da baxata haura 55 ba ta shigo wani babban daki ta kulle kofar tana kallon wanda ke kwance yyi rub da ciki saman gado, karasawa ciki tayi ta buga gadon, juyowa yyi da sauri ya mike xaune ganinta yace “Aunty ina kwana?” Tace “Jiya da daddare ina kaje har bayan isha baka shigo ba” yace “Aunty ina gidansu Ahmad fa, kuma tare ma muka dawo nan da shi na xata kin yi bacci shi yasa bamu shigo ba” Tace “Ohk, jiya Ahmad din ya dawo” Yace “Ehh” Tace “Ai na xata tadi kaje” D’an murmushi yyi yace “Tadi kuma Aunty…

 

Ai tana Abuja” Tace “Atoh na sani ko ka kyallara ido ka ga wata ka watsa min kasa a ido??” Bai kuma ce mata komai ba sai murmushi da yayi, ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita ta kulle kofar, mikewa tsaye yyi yana kallon agogo dake nuna karfe tara ya shiga bathroom. Kasancewar ranan asabar ce sai kusan karfe sha daya Abuturrab ya fito daga dakinsa sanye cikin kananun kayan da suka matukar amsar sa, lkci daya kamshin turarensa ya gauraye parlon gaba daya, kanninsa mata ne xaune Main parlor din gidan, duk kallo daya suka yi masa suka dauke kai, bangaren Mahaifiyarsa ya nufa, Ramlah ta bi sa da kallo tace “Ummi ta fita fa” Ya juyo ya wuce side din Stepmum dinsa…

 

A parlonta ya sameta tana yi ma autarta Aisha tsifa, yace “Xan je gidansu Ahmad Aunty” Tace “Breakfast din fa?” Yace “Ni nayi breakfast da asuba fa” tace “Oh ka dawo breakfast din asuban kenan” Yace “Ehh” tace “Kawata xata tafi Lagos ranan Monday daga kano shine nace kilan ma you will be piloting the plane….” Yace “In dai flight din safe ne” Tace “Na safen ne ma ina ji” Yace “Allah ya kai mu” Daga haka ya juya yace “Sai na dawo” yana fita parlon, Hajiya Amina da suke kira da Aunty ta kalli autarta tace “Me yasa baki gaida sa ba?” Aisha ta buda hannu tace “Wllh Aunty ranan ce mana yyi mu daina gaishesa a gidan nan idan yana nan, and he was serious about it” Aunty tace “Me ku ka yi masa?” Aisha tace “Babu komai, ranan Thursday da ya dawo duk muna parlor da su Aunty Safiyya muka gaishesa bai ce komai ba, muka sake gaishesa, har ya tafi ya dawo on a serious note yace mana kar mu sake gaishesa baya so, and since then no one is greeting him again and he is very comfortable with that” Aunty ta ta6e baki tace “Toh ai shkkn” A daki Abuturrab ya tadda Ahmad bayan ya isa gidansu, Abuturrab ya nufi window din dakin ya dage curtains din ya bude windon yace “Allow natural ventilation mana” Ahmad yyi dariya yace “Gaskiya ne bature, to kashe Ac din ko?” Abuturrab ya xauna yace “Aa bar shi, how are you?” Ahmad yace “Fine, ya su Ummi” Abuturrab yace “Cool” Ahmad yace “Are you flying on Thursday?”

Abuturrab ya d’an yi shiru trying to recall his piloting schedules, kafin yace “Yea, Kano to Lagos, Then Lagos to Abuja, on Friday kuma Abuja to port harcourt” Ahmad yace “Ohk dama Maryam will be going back to schl Thursday I tot kana nan mu kai ta tare” Abuturrab ya ta6e baki yace “Ahmadu Bello?” Ahmad yace “Ehh” Abuturrab yace “Ka kai ta tasha ka sa ta a mota mana, kawai yarinya karama tayi ta juyaka” Hararansa Ahmad yyi, Abuturrab ya fiddo wayarsa dake ring yana duba me kiransa. Bude kofar dakin aka yi Maimuna ta shigo da tray dauke da warmer din danwake da tamarind drink a jug, ajiyewa tayi ta gaida Abuturrab da murmushi fuskarta yace “Ya kike Moon?” Tace “Alhmdllh, Yaya xan je Abuja fa” Yace “To sae ki xo in makala ki a jirgi ko?” Dariya tayi sosai tace “To ai shi sa na gaya maka” yyi murmushi bai ce mata komai ba, ta mike ta fita, bude warmer din Ahmad yyi, Abuturrab dake ta kallon danwaken warmer din yace “Ya ma abin nan da ka siya jiya a hayin Rigasa? Kamar shi nake gani a nan” Ahmad ya wara ido ido yyi dariya yace “Ohh wannan danwake ne, wancan kuma awara, kamar kuwa kasan yau ma xan je in siya, kaji dadin awaran nan kuwa? Gaskiya sun iya sosai, har Umma sai da ta ci, ni uku kawai naci su suka cinye sauran” Abuturrab ya dinga kallonsa da mamaki, can yace “Har komawa xaka yi kenan ka sake siya” Ahmad yace “Yes, I had intention dama” Abuturrab ya gyada kai bai sake ce masa komai ba. Har yamma Abuturrab na tare da cousin din nasa kuma abokinsa…. Su yi fada su shirya, duk bayan sati uku Ahmad ke shigowa kd yyi weekend daga Abuja don a can yake aiki as a medical Doctor, throughout weekend din kuma tare suke spending dinsa da Abuturrab idan shi ma yana garin, karfe biyar saura Ahmad ya mike yace “Captain mu je ka rakani mana pls” Captain ya kallesa yace “In raka ka ina?” Ahmad yace “Hayin Rigasa” Abuturrab yace “Aa sae dai Hayin banki, kaga malam mu fita tare kawai kayi hanyarka inyi nawa, don gida xan wuce yanxu in sha Allah” Ahmad yace “Ae ko baka isa ba, wllh sae ka rakani” Abuturrab ya dau wayarsa xae dau makullin motarsa Ahmad ya dauke yace “Sae ka tafi da kafa ai” kallonsa Abuturrab yyi, lkci daya ya wani hade rai, Ahmad ya fita dakin yana murmushi. Driving Ahmad yake yi, ya kalli Abuturrab dake xaune gefensa yace “Wai Aneesah fa?” Abuturrab ya gyara xama yace “She’s good, baka ji muna waya daxu ba” Ahmad ya girgixa kai yace “Kai ynxu da gaske mace da idanuwanta suke a bude da sunan wayewa kake so Captain….” Abuturrab yace “Look at you, kai baka san wayayyun sun fi tsafta ba, ni fa I don’t care…. As far as xata yi tsafta 100%, wllh ko haduwa da mace kazama ban son yi a rayuwata, sae inji gaba daya hankali na ya tashi, u know how sensitive I am….” Dariya Ahmad yyi yace “Ita Aneesar tana da irin tsaftar da kake so kenan” Abuturrab yace “Kai ma kasan da ba don haka ba da tuni ae na rabu da ita, kawai sae kaga mace ta ci kwalliya iya kwalliya ta fito amma just check inside, ni in dai mace na da tsafta ko kyanta bai fi 80% ba i will manage her…” Girgixa kai Ahmad yyi yana kallon titin gabansa, Abuturrab yace “Ba ga wajen danwaken can mun wuce ba” Ahmad bai san lkcn da yyi dariya ba yace “Aa D’an gyero ne ba danwake ba” Abuturrab dai bai ce masa komai ba da ya lura u turn yake son yi, dai dai gun awaran Ahmad yyi parking, wata yarinya ce da baxata wuce shekara sha daya ba xaune a wajen tana juya awaran cikin kasko, Ahmad na kallonta yace “Ina me awaran?” Yarinyar tace “Ta je dauko canji a gida shine tace in tsare mata, ae sunanta Aunty Jiddah, a gidansu Bibalo take…” Ahmad ya koma jikin motarsa yace “Gidan ba nisa?” Yarinya ta nuna masa wani rubabben layi dake gefensu tace “Can karshen layi ne, gidansu daya da Bibalo” Shi dai Abuturrab na xaune kujera me xaman banxa yana kallonsu, Yarinyar tace “Lah ga ta can xuwa” Duk suka kalli direction din da ta nuna, Tafe take fuskarta daure hannunta rike da yar karamin bokiti dake a rufe, wanda ke dauke da dafaffen awara, sanye take da hijab ruwan kasa da iyakarsa gwiwa duk man awaran da take tuya yayi staining Hijab din, Abuturrab ya d’an yi tsaki ya hade girar sama da ta kasa yana kallon titin gabansa, tana isowa yarinyar ta tashi tace “Aunty Jiddah gashi xa a siya a awara, da motarsu ma suka xo” Ahmad ya wara ido yace “Aunty Jiddah a bamu kalan na jiya” Ta daga kai ta kallesa tace “Na nawa?” Yyi murmushi yace “Yanda kika sa jiya” Bata ce komai ba ta durkusa ta sa masa awaran sannan ta mika masa ledan, dubu daya ya ciro ya mika mata, tana kallon kudin tace “Yanxu na kai kudi gida na amso canji, ka d’an yi hakuri sai in koma in dauko…” Ya juya ya kalli Abuturrab yace “Ko a siya maka kai ma Captain?” Kallon Abuturrab din tayi ita ma suka hada ido, yyi saurin dauke idonsa yaki cewa komai, Ahmad ya kalleta yace “Toh kinsan abinda xai faru me awara? ki ajiye canjin….” Da sauri tace “Aa ka jira in tafi in dawo ynxu” yace “To tsaya ki saurareni mana, ajiyewa xa ki yi gobe idan Allah ya kai mu na xo sai a bani awara na canjin” tace “Toh” murmushi yyi ya nufi mota rike da ledan awaran, sae da ya shiga motar ta ga ledan yajinsa bata sa masa ba ta mike da sauri tace “Kayi mantuwa” motar ta nufa tana mika ma Abuturrab ledan yajin, da mamaki yake kallonta kamar dai mugun abu take mika masa, yace “Kai!! kinga na siya abu a wajen ki ne?” wani kallon cikin ido tayi masa snn ta xaga ta mika ma Ahmad ta koma gun xamanta tana juya awaran kan wuta, Ahmad ya tada motar suka bar wajen yana hararan Abuturrab da ko a jikinsa. Jiddah na xaune a d’an dakalin kofar gidansu bayan isha, dawowarta kenan daga bakin titi ta gama tuyan dankali da take yi, ta ta takure waje daya cikin hijab din jikinta, wani matashi ne da baxae wuce shekara ashirin da tara ba xaune d’an nesa da ita, yace “Kin yi shiru Jiddah” Ta d’an kallesa tace “Nace babu wata matsala” yace “Kin tabbatar?” Ta gyada masa kai, yace “To ki ci gaba da hakuri kin ji…. In sha Allah idan…..” Kamar daga sama suka ji muryar Hansai, ta rike kugu tana kallonsa da kyau tace “Ta ci gaba da hakurin gyatuminka?” Ya kalleta ya duka har kasa yace “Ina yini Baaba” Ta wani sha kunu tace “Da ban yini ba xaka gan ni algungumi?? Ta ci gaba da hakuri a saboda ana cutarta ko? Sannan ban rabaka da kofar gidan nan ba? Dama tun da naga yara sun shigo da kayan tallanta ita bata shigo ba nasan da walakin goro a miya, shine nace bari dai in leko in ga ikon Allah” shi dai bai ce komai ba ya sunkuyar da kansa, tuni Jiddah ta mike ta makale da bango gabanta na faduwa, Hansai ta cire takalmin kafarta ta jefa mata a mugun fusace tace “Wuce ciki munafuka kawai, dama ban rabaki da wnn yaron mara tarbiya ba, ni xa ki ja ma abun kunya a unguwar nan?” Da sauri Jiddah ta shige ciki Hansai ta kai mata dundu da karfi, sannan ta maida dubanta kansa tana huci tace “Wllh na sake ganin ka tare da yarinyata gidan gayun garin nan yyi mana kadan da ni da kai, idan kuma karya ne mu xuba da kai” Tana kai wa nan ta shige ciki ya mike a hankali ya bi ta da ido….

 

2..

 

Abuturrab na kwance saman gadon dakinsa yana rike da wayarsa, kunnensa sakale da earpiece, video call yake da wani matashin da baxai wuce sa ba, matashin na xaune cikin wani ubansun parlor yana cin apple, Abuturrab ya girgixa kai yana kallonsa yace “Look… I don’t want to say anything about that…. idan Mummy na kusa ka bata mu gaisa” Matashin na taunar apple yace “It’s already late, tayi bacci…” Abuturrab yace “It’s late tunda baka son fita, so when are u coming to kd?” El-Basheer yace “Xa mu shigo kano tare da Mai martaba next week in sha Allah, probably ni xan karaso, amma sai kana nan” Abuturrab yace “In dai Friday ne ina nan in sha Allah” El-Basheer ya daga kafada yace “Ohk then” Abuturrab yace “Let me pick a call, sai da safe” El-Basheer ya gyara xamansa yana murmushi yace “The lady u don’t want to talk about?” Katse call din Abuturrab yyi ya dau daya wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne hade da cewa “How u babe?”

Abuturrab ne xaune parlonsa a gidansa dake Abuja shigowarsa gidan kenan ko awa daya bai yi ba, kasancewar weather babu kyau yasa suka yi landing flight da suka yi piloting daga Lagos a Abuja a maimakon kano…. Grapes ne gabansa yana ci a hankali yana kallon wani action movie da ake yi a tv, bude kofar parlon aka yi, lkci daya ya daga kai, he was expecting no one other than Ahmad da ya sanar ma yana Abuja… Tsayinta matsakaici ne…. ita ba siririya ba ita ba mai jiki ba, ta karasa shigowa parlon ta kulle kofan tana kallonsa ta cire Nikab din fuskarta, fara ce sosai, kallonta shi ma yake, she looks so orderly from head to toe, tuni kamshinta ya baxa parlon, shi dai kallonta kawai yake ta nufesa da damuwa ta xauna gefensa tace “Why ain’t you picking my call Captain?” Ya gyara xamansa yace “It wasn’t long da muka sauka ai, na sa wayar a caji a can daki, how are you doing?” A hankali tace “I’m fine, ya gajiya?” Yace “Alhmdllh, where are u coming from?” Ta buda manyan idanuwanta tace “Home… kace min xaka sauka Abuja shi sa na samu na fito” ya shafa beard dinsa yace “Ahmad na hanya, bana son ya xo ya sameki nan, u know how he thinks” Ta langwabar da kai tace “Ohk, amma nace maka ina son muyi magana, ina ta bin ka yau kusan sati biyu kenan sai kace min you will be piloting today, u will be piloting tomorrow….” Da damuwa ta kare maganar, Ya kalli agogo yace “To ina jin ki yanxu, I’m sorry i forgot about that” Shiru tayi, ya kafeta da idanuwansa, sai kuma yyi murmushi ya kamo hannunta yace “Ina jin ki Aneesah” Tayi kasa da murya tace “Aliyu a gidanmu an takurani in fito da miji, kwanaki kuma na gaya maka baka ce komai ba, idan har da gaske kake kana sona what is hindering you pls?” Ya dauke idonsa daga kallonta, bayan few seconds yace “To a jira ki gama karatun mana ko? Ina ce saura kadan” Ta girgixa kai tace “Aa last week Abbana ya kara min magana, and he is very serious about it this time, don’t u love me ne Aliyu?” Abuturrab ya xaro ido yace “Not at all Aneesah, kema kinsan ina sonki…. kar ki damu xa mu yi magana, yanxu ki tashi ki tafi kafin Ahmad ya xo…” Ta gyada masa kai sannan ta mike, mikewa yyi shi ma ya wuce daki ya dauko kudi ya mika mata kafin yace komai tace “Aa ni da motana na fito don’t worry” Bai ce komai ba ya rakata har balcony snn ya amshi jakarta ya sa mata kudin yace “I know da mota kika xo, Chocolate din da ban kai maki ba last week sai ki siya, ba kudi ne me wani yawa ba” Murmushinta me kyau tayi, tayi kasa da muryarta tace “Thank you my Captain” ya kashe mata ido yace “C’mon babe…. Nikab din kuma na meye yau kika sa?” Tace “I just felt like” ya daga kafada yace “Alright sai mun yi waya” ta gyada masa kai ta nufi gate ya juya ya koma parlor, her neatness melt his heart always nd make him fall for her deeply. Wata dattijuwa ce xaune dakinta tare da yan mata biyu, aka bude kofar dakin duk suka daga kai, Dattijuwar na murmushi tace “Aa Abuturrab sannu da xuwa” ya karasa ciki yana murmushi shi ma, ya xauna sannan ya gaisheta da ladabi, tace “Ka dawo weekend kenan” yace “Ehh daxu muka sauka, ya karfin jikin Umma?” Tace “Alhmdllh na ji sauki yanxu” yace “Allah ya kara lfya” tace “Ameen” ledan hannunsa ya ajiye yace “Ahmad yace in taho maki da wannan” Tace “Kun hadu a Abujan kenan” Yace “Ehh kwana na biyu a can, weather babu kyau sai yau na samu muka bar Abujan xuwa kano, daga kano na biyo private jet” Umma tace “Toh Allah ubangiji ya tsare mana ku dai, Allah ya rabaka da sharrin kayan bature, haka kai kuma Allah yayi hanyar cin abincin ka” Amira tayi ‘yar dariya tace “Kabu kabun jirgi Ya Abuturrab yake fa” Ta gefen ido ya kalleta bai ce komai ba, amma ya hade rai sosai, Umma tace “Ni dai Allah ya tsare min shi” a hankali yana kallon kanwar mahaifiyar tasa yace “Ameen Umma” Tace “Mun yi waya da Ahmad daxu nace masa wani awara da yake kawo min nake son ci wllh, gaba daya bani da appetite, yace kuma a hayi ake yi ko” Abuturrab ya d’an buda ido, sae kuma da sauri yace “Allah sarki, baxa a iya maki a gida ba Umma? Ae kamar yafi tsafta ayi a gida kawai” Tace “Aa da wahala, beside babu ma waken suyan a kasa, Hurairan da xata yi ma ta tafi garinsu daxu, kanninka kuma babu abinda suka iya gasu nan dai xaune, gwara kawai a siya a wajen ya fi, naga me kyau ne sosai ran da ya siyo ae” Abuturrab dai bai sake cewa komai ba, tace “Kuma yace ka san wajen, tare ma ku ke xuwa” Da sauri Abuturrab ya kalleta, lkci daya ya kirkiri murmushi yace “Anya xan gane kuwa Umma, a wani layi ne can cikin hayi fah, the place is very complicated” tace “Aa Aliyu na fa sanka sarai, ko baka sob xuwa ne, idan ma da gaske ne baka gane wajen ba ai kiran Ahmad din xaka yi ya sake maka kwatance” Bai ce komai ba amma lkci daya mood dinsa ya canxa har hakan ya kasa boyuwa a fuskarsa, sai dai bai bari ta lura ba, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe biyar da few minutes, Umma tace “Ko kana da inda xaka je ne?” Ya d’an shafa kansa a hankali yace “Aa, bari in je in dawo” tace “To Allah yyi maka albarka” da kyar ya amsa da “Ameeen” snn ya mike ya fita, sosai ya hade rai bayan ya shiga motarsa, why will Ahmad tell her ya san wajen, ynxu kawai sai ya fara driving xuwa hayi wai yaje siyan awara why??? wani tsaki yyi ya tada motarsa ya bar compound din. Driving kawai Abuturrab ke yi har ya shigo hayi, he was very observant kar ya wuce inda ake suyan awaran, haka nan yake jin ransa na baci, wani ma ya gansa ya xata shi xai ci, U turn yyi ya samu waje yyi parking yana kallon yarinyar da ta mike xata shiga karamin layin nasu bayan ta sauke kaskon awaran kasa, almajirai uku ne tsaye gun da wasu yan mata biyu, Abuturrab ya dake yace “Kee” bata juyo ba don tafiyarta kawai take kuma da alama ma bata ji ba, Daya daga yan matan wajen tace “Bata ji ba, yanxu xata dawo, xata amso canji ne” Bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujeran motar, bayan kusan minti biyar sai ga ta tana dawowa, kallonta yake har ta iso bakin titi, ta kalli motar sannan ta durkusa gun sana’arta, Yarinyar daxu tace “Ke jiddah jiranki ake xa a siyi awara” Sai snn ta daga kai suka hada ido da Abuturrab, ya hade giran sama da ta kasa yace “Nawa kike siyar da kayan siyarwar taki?” Tace “Wanda ya rage a nan bashi da yawa, amma ynxu xa a kawo daga gida….” Bai ce komai ba ya dauke kai, ta sallami mutanen dake tsaye a wajen, bata son komawa gida dauko danyen awaran Gwaggo Hansai ta sake koranta tace bata gama ba, kuma ta bar mata dukiyarta a titi almajirai su sace, Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallon agogon wrist dinsa, wata yar tsohuwa ce ta xo wucewa da kullin icce a kanta, hannunta daya rike da yar leda, ta rike ha6a tana kallon jiddah tace “Har yanxu kaddararren awaran nan bai kare ba har na je inda xa ni na dawo? Ke dai kin yaye islamiyya ko, Amma Hansai dai daga d’an iska sai ita, ko da yake ba ruwana, ba dangin iya balle na Baba ace na fiye sa ido, amma banda haka kullum ke kenan bakin titi kina tuyan awara babu arabi ba boko ubanki kuma ba bakin magana ya xama mijin ta ce, to ba dai ruwana da abinda bai shafeni ba….” daga haka tayi wucewarta, Jiddah ta bi ta da ido hade da daure fuska, Abuturrab ya bi tsohuwar da ido har ta isa wani d’an kuturun gate ta bude ta shiga, ya sake kallon Jiddah dake gyara wutan murhun kusa da ita, Bibalo ce ta iso wajen rike da bokitin awara ta ajiye nan kasa tana fari da ido, fuskarta kamar warce ta shafa boju tace “Hansai dai tace na dubu da dari uku da tamanin ne kafin anjima da daddare kice na dubu da dari uku da hamsin kika gani tunda dama kin saba….” Ko kallonta Jiddah bata yi ba tayi wucewarta tana taunar cingam… Jiddah na fara xuba awaran a mai Abuturrab ya sauke glass din motarsa gaba daya yace “Ke malama jiranki nake fa, kina bata min lkci, kinsan minti nawa nayi a nan yanxu” Sai a sannan ta kallesa tace “Toh ai sai an soya ko baka ganin danye ne? Idan kuma danyen kake so ai magana xaka yi” Dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya rungume hannu daga xaunen da yake cikin mota yana kallonta da mamaki yana sake apprehending abinda ta fada masa, sai bayan minti goma ta kallesa bayan ta kwashe awaran da ya soyu tace “To na nawa kake so?” Ya mata wani kallo yace “Me kika ce min daxu? Sake fada in ji” Ta rufe awaran da ta kwashe a takaice tace “Toh baxan siyar ba, ka tafi gaba can akwai wata me awaran a gaba” muryar Hansai taji a bayanta tana cewa “Bai soyu bane Jiddah, ko ba awaran me motar xai siya ba? Baxa kiyi da jini ba kin xauna kamar wata rubabbiya ni Hansai” da sauri Hansai ta karaso tana kallon Abuturrab tace “Alhaji yi hakuri a kwashe maka yanxu, ta nawa kake so?” Abuturrab na tada motarsa yace “Ae tace ba na siyarwa bane, in tafi akwai a gaba” Da sauri Hansai ta bude roban awaran taga soyayyen awara da ta kwashe a jibge, ga wasu ta xuba a mai, wani lafiyayyen mari ta wanke ta da shi tace “Ubanki ne xai siya wannan da kika kunshe min a gwagwa? Yo ina ma yaga arxikin siyewa tukun, muguwa, axxaluma yar bakin ciki, to Allah ya isa cutata da kike….” Wani marin ta sake wanka mata a mugun fusace ta hankadata, Abuturrab ya xaro ido yana kallon ikon Allah, Hansai ta juya garesa da sauri tana dukawa tace “Don Allah kayi hakuri Alhaji, kayi hakuri Alhaji…. wllh akwai na nawa kake so?” Kasa ce mata komai yyi, ya kalli Jiddah da ta mike tsaye tana shessheka ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta, Yace “Toh har ya kai ki mareta haka??” Hansai ta kara hankade Jiddah da karfi tace “Toh idan ban mareta ba me xan mata, wannn da kake gani makira ce me mugun hali, kuma babu abinda na rageta da shi wllh tllh” cikin tsawa tace “Baxa ki bace min daga nan ba sai na watsa maki man kaskon nan a jiki gaba daya?” Matsawa tayi daga wajen tana kuka sosai, Hansai ta kara turata tace “Muguwa bar min awarata xan karasa suyan, ki je wannan tulin wankin na tsakar gida ban son in xo in ga ko hankici a kasa, duk in samesu kan igiya da lema” Tafiya kawai Jiddah take bata ce komai ba tana kuka, Abuturrab dai dauke kansa yyi, Hansai ta marairaice murya tace “Kayi hakuri Alhaji nasan ta 6ata maka rai sosai, na nawa kake son awaran?” Yace “Dubu daya” da sauri ta shiga saka masa har ta gama sannan ta mike ta kai masa ya bata kudin ta risina ta amsa tana murmushi hade da godiya, bai ko kalleta ba ya ja motarsa ya bar wajen. Washegari Saturday Abuturrab da yamma ya shirya ya fito daga dakinsa, Umminsa ce xaune parlor da Stepmum dinsa, duk ‘yan matan gidan sun tafi makaranta, Ummi ce ke magana Aunty na ta kallonta absentmindedly lkci lkci tana duba wayar hannunta, Ummi tace “Ai mu ma ba sonmu Allah ya fi yi a kansu ba, toh meye a ciki don ta shigo nan ta xauna?” Aunty tace “Haka dai kike ga babu komai a ciki, amma kina da labarin kudin cixo na makalewa jikin kaya kuwa?” Ummi tace “Gashi ai naji a bakin ki yau” Aunty na kallon Abuturrab tace “Kai ka ji fa Aliyu…. Musa me gyaran fulawa ne ya xo da matarsa da yara uku wai sun xo gaishemu daga kauye ina laifin parlan can na boys quarter da har sai sun xo nan don Allah, baka gansu ba wllh abun ba acewa komai, ni yanda kake da kyankyami ma nasan da kyar idan baka yi throw up ba, sai fa da nasa turaren wuta a parlorn ynxu….” Abuturrab ya d’an yi shiru, can kasan xuciyarsa yace for peace to reign…. Sai kuma ya dago kai a bayyana yace “To ai can din ya kamata suje dama ba nan ba Aunty” Wani kallo Ummi ta jefa masa, yayi murmushi yace “That’s the fact mum, ita Aunty tsoron bedbugs take….” Aunty tace “Toh ita cewa tayi wai ba a kyauta ba, haka kawai a bada mana kudin cixo a parlor a cuce mu?” Ummi tace “Toh Allah ya baku sa’a, idan walakanta d’an Adam abun yi ne, ku ci gaba” Abuturrab ya shafa kansa ya nufi kofa, Aunty tace “Ina xa ka Captain?” Yace “Xanje wajen wani abokina he just arrived from New york….” Har ya fita parlon Ummi bata ce masa komai ba, yyi murmushi bayan ya shiga motarsa, ko ina ruwansa da ‘yan kauye da suka xo da Aunty xata yi involving dinsa at d first place, girgixa kai yyi ya tada motar ya bar gidan, tafiyar kusan minti talatin yyi tunani iri iri na yawo a ransa, ba kasafai yake kwana da abu a ransa ba, infact it’s very rare hakan ya same sa, amma jiya ya kwana da yarinya me awara a ransa, dalili kuwa he lead to her been maltreated, she was slapped severally because of him, he felt guilty shi ne ma yasa ya kasa samun nutsuwa a ransa, yana isa dai dai gun da take awaran ya tarar bbu kowa, alamar ba ayi awaran yau ba, yyi ta bin dirty unkept layin da kallo wanda ko mota ba lallai ya iya bi ba sbda gutters dake kwance ta ko ina, ji yyi kamar yyi amai, hankalinsa ya tashi sosai Bibalo ce ta xo wucewa fuskarta yau ma dai kamar warce tayi dambe da powder ga bakinta ya sha jan janbaki, lkci daya ya ganeta, ya sauka motarsa da sauri yana yamutse fuska yana kallonta yace “Yau babu abinda ku ke siyarwa ne?” Tayi fari da ido tana kallonsa tace “Ehh wllh, mijin kanwar babaarmu ne ya rasu yau da safe, tana can gidan mutuwar tace yau baxa ayi awaran ba” Yace “Ohk, ita warce take soyawan tana ina??” Ta wani yatsine fuska tace “Ohh wai Jiddah, tana can gida xata daura sanwan tuwon dawa, nima yanxu gidan mutuwar xa ni Baabarmu tace inje” yace “Ohkk, sai anjima” Tana murmushi tace “Toh sunana Bibalo kai fa?” Wayarsa ya ciro ya kara kunne snn ya koma cikin motarsa ya kulle, ta bi sa da ido sai bayan da yaga ta wuce snn ya bude motar ya tsirtar da yawu yana yamutsa fuska, ita kanta tsami take yi ga uwa uba warin gutter din anguwar, yaji gaba daya cikinsa ya fara hautsinewa, ya fi minti biyar xaune motar bayan ya cika Ac, har yaji ya dawo dai dai, wani yaro ya hango yana tafiya ya sauke glass ya kirasa, yaron ya xo, yana kallonsa yace “Wani gida ne ake awara a layin nan?” Yaron yace “Gidansu Bibalo ne” Ya sauko motar ya kulle sannan yace “Toh kai ni gidan” Nose mask ya sa a hanci bayan glass dake idonsa yana biye da yaron har suka isa kofar wani kuturun gida wanda shi dai ko dabbobi yake kiwo baxai sa su gidan nan ba don kilan Allah sai yayi ma dabbobin sakayya a kan ajiyesu da yyi a nan, gaba daya tsigar jikinsa tashi yake ga cikinsa da ya fara hautsinewa again, he have never been uncomfortable all his life kamar wannan moment din, yana kallon yaron da kyar yace “Shiga ka kira min me awaran” Ba musu yaron ya shiga, can sai gashi ya fito yace tana xuwa, ba a dau lkci ba sai gata ta fito, Hijab ne ta saka iya cinya sai xanin jikinta, gefen farin fuskarta duk bakin gawayi don wuta take rurawa, kallonsa kawai take alamar bata ganesa ba, ya sauke nose mask dinsa, ya cire glasses din idonsa, lkci daya gabanta ya fadi sosai bayan ta ganesa, hakan kuma bai hanata hade rai tana kallonsa ba duk da a tsorace take, shi ma dai cike da karfin hali yace “A xaton ki an mareki jiya sbda ni?” Kauda kai tayi, ya hade rai yace “Ki juyo ki kalleni ina maki magana” Ba tare da ta juyo ba tace “Ni dai ka rufa min asiri bance an mareni sbda kai ba, me ya sake kawo ka nan, in dai awara ne yau babu bamu yi ba” kallon yanda take maganan yake wanda komai ta fada sai dimples dinta ya lotsa, ta kallesa jin bai ce komai ba tace “Nace maka babu awara yau” Yace “Ohk dama sai kuna awara kenan kike wanka ki xauna bakin titi?” Ta wani xare ido tace “Ni nace maka banyi wanka ba??” Tana fadin haka ta kalli Hijab din jikinta wanda shima duk bakin gawayi ne hade da xaninta, slippers din kafarta ma duk ya tsufa, haka kawai ta ji kunya ya rufeta, ta 6ata rai tace “Ni sai kace nace ma banyi wanka ba, bayan girki nake yanxu” Bai tankata ba ya mayar da nose mask dinsa da glasses dinsa ya juya ya bar wajen ta bi sa da ido kamar me shirin kuka har ya kusa bakin titi snn ta juya a hankali ta koma cikin gidan nasu.

 

 

 

💖💖 *Jiddatul~ Khair*💖💖

 

 

 

_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻

 

 

 

 

3…..

 

Karfe taran dare Jiddah ta fito tsakar gida ta xauna kan tabarman dake bakin kofar dakinsu, muryar Hansai ne ya kaurade d’an tsakar gidan tana ma mai gidanta isuhu masifan ita ta gaji da ciyar da shi, shi dai yana xaune baya cewa komai hakan yasa tayi ta daga murya wanda da kyar ba a jin ta a kofar gida, a hankali Jiddah ta mike ta sa takalminta ta fita gidan, wani karamin gida can karshen layinsu ta tafi, tana waige waige ta shiga zauren gidan sannan ta karasa ciki, Wata yar dattijuwa ce tsakar gidan xaune tana ma yara uku dake kwance kan tabarma fifita, Datijuwar tace “An gama tuyar kenan…” Jiddah ta kwance ha6ar xaninta ta ciro dubu biyu tace “Aa yau ai bamu yi ba Baabarmu taje gidan gaisuwa, Iyah ki ajiye min wannan Usman ne ya bani daxu mun hadu bakin titi naje auno waken suya, ki dau dari biyar, sai ki ajiye min dari biyar sai ki sa dubu dayan a asusun da nayi ma Abbana” Iyah tace “Kai Allah dai yyi ma yaron nan albarka, kwana biyu ma bai shigo ya gaisheni ba, ni da a shirye yake ai da ya fito kawai ko Allah xai yanke maki wnn shegen wahalan, kai ko da akwati daya yayi maki indai xai rabaki da Hansai yafi maki wllh, ba yace min a can cikin gari yake da iyayensa ba, nan kuma wajen kanwar babarsa yake xuwa?” Jiddah ta gyada mata kai ta mike ta nufi kofa tace “Sai da safe Iyah kar baabarmu ta nemeni” Tana fadin haka ta fita da sauri kafin a lura bbu ita a can gida, Iyah ta girgixa kai tace “Allah sarki, tsakaninsa da Allah yake sonta wllh, tsorona daya makirar bakar matar can kada ta shiga ta fita ta raba su, tunda ga bibalo babu mashinshini har yanxu sai yawon unguwa unguwa take a hayi, kuma duk sa’annin juna ne, to dai bbu ruwana tunda babu dangin iya balle na baba”

 

Ahmad ya gama sa cover shoe dinsa yana kallon Abuturrab dake kwance kan 3 seater hannunsa rike da remote yace “Ya naga kamar duk ka damu in tafi ne Captain?” Abuturrab ya kike xaune yace “Ohh toh ka yi xamanka mana ina ruwana, dama don kace kana night duty ne yasa nake ta reminding dinka, naga it’s almost 6, an kusa kiran magrib” Ahmad ya ta6e baki ya mike yace “Yaushe xa ku wuce kanon ne?” Abuturrab yace “Am off for someday kawai i just decided to be in Abuja for a while, may be on friday xan bi train in sha Allah” Ahmad yace “Ohh that’s great nima friday nake son xuwa kadunan, rabona da kaduna ai an kwana biyu” Daga haka ya nufi kofa ya fita, yana fita gidan ko minti goma ba ayi ba Aneesah ta shigo, Abuturrab na kallonta yace “Sorry i kept u waiting kinsan Ahmad….” Ta karaso parlon tace “Yeah i understand…” Xaunawa tayi ta ajiye jakarta, ya dawo kusa da ita yace “Kwana uku xan yi a Abuja….” Ta wara ido tace “Har uku?” yace “Yea, ko baxa ki tayani xama ba?” Ta juya ido tace “Aa kaga Dad dinmu yana gari, sai dai in dinga xuwa Ina tafiya…” Ya jingina da kujera yace “No need inyi kwana uku kenan, gobe inyi tafiyata kaduna dama sbda ke na sauka Abuja” Ta marairaice masa tace “Haba dear, to kar ka damu i will try and be with u” Mikewa tayi tace “Me xan girka maka nasan har yanxu baka ci abinci ba” Yace “Just a cup of tea now, mun sha fruits tare da Ahmad” bude kofar aka yi duk suka juya lkci daya, Ahmad ne ya shigo parlon, kallo daya yyi masu ya nufi gun da ya mance wayarsa ya dauka, yana kallon Abuturrab yace “Shi yasa ka damu in tafi kenan” Aneesah dai daure fuska tayi, kamar baxata ce komai ba sai da ya nufi kofa tace “Ina yini?” Banxa yyi mata ya fita ya kulle kofar, Abuturrab ya shafa kansa, a hankali tace “But am afraid Captain…” Yace “You are afraid of what?” Komawa tayi ta xauna da damuwa tace “I think this is the 5th time da Ahmad ke ganina a gidanka, ina tsoron kada ya sa iyayenku su ki amincewa da aurenmu” Abuturrab yace “Ni xan xauna da ke ko wani, don kina xuwa gidana does that mean anything?” Ta girgixa kai bata dai ce komai ba, ya mike ya isa kusa da ita ya kamo hannunta yace “Cheer up dear, beside Ahmad will never do that, i know who he is” kallonsa tayi da manyan idanuwanta ya sakar mata lallausan murmushi ya kai hannu dogon hancinta yace “Basu san samun me tsafta irin ki yanxu sai mutum ya dage ba?” Murmushi kawai tayi yyi pecking cheeks dinta yace “Babu wanda xai raba mu in sha Allah” hanyar kitchen ta nufa ya bi ta da kallo. Suna fitowa train station suka nufi motar dake tsaye yana jiransu, Ahmad ya bude back seat yana kallon saurayin dake xaune driver seat yace “Sorry for keeping u waiting salem, mun hadu da wani abokinmu ne muka tsaya gaisawa” Salem na murmushi yace “Ina yini ya Ahmad” Ahmad yace “Lafiya lau, ya su Aunty” Salem yace “Lafiya kalau” Abuturrab ya xaga ya shiga front seat bayan ya gama wayar da yake yana kallon stepbrother din nasa yace “How are you” Salem yace “Fine, how was the journey?” Abuturrab yace “Cool” Driving din motar salem yyi suka fara tafiya, tunda suka hau saman titin hayi idon Abuturrab ke gefen hanya, Ta madubi ya kalli Ahmad dake danna wayarsa, da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Yau baxa ka siyi awara ba kenan” Sai a sannan Ahmad ya dago kai ya kalli inda suke, ganin sun kusa wajen da yake siyan awaran yace “I had no intention but let me get it for Umma and my siblings” Abuturrab ya ta6e baki bai ce komai ba, Ahmad na kallon Salem yace “Kana wuce layin nan ka tsaya a layin gaba” Salem yyi parking dai dai inda Ahmad yace, Ido hudu Jiddah tayi da Abuturrab da sauri ta sunkuyar da kanta tana gyara hijab din jikinta, Ahmad ya bude motar ya sauka yana kallonta smiling broadly ya rungume hannunsa yace “Sannu me awara” Bata yarda ta kallesa ba tace “Ina yini” yace “Lafiya lau ya kasuwa?” Tace “Na nawa xa a sa maka?” Yace “Ki sa na dari biyar ko?” Satan kallon Abuturrab tayi suka sake hada ido ya dauke nasa idon yana kallon gefen hanya, ta gama sa awaran ta mike ta mika ma Ahmad, ya amsa yana kallonta, sae kuma ya juya ya kalli Abuturrab yace “Bani 1k wajenka I’m not with cash” Abuturrab bai ce komai ba, ita dai tana tsaye, can ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika ma Ahmad, Ahmad ya amso ya mika mata ta amsa ta koma ta durkusa xata dauko canji yace “Aa ki bari idan na xo sake siya, shkkn ba sai na sake bada kudi ba koh?” shiru tayi, lkci daya ta mike tace “Toh ai akwai canjinka dari biyar a wajena da ka siya ranan nan, ka tuna?” tana fadin haka ta mika masa dubu dayan, yace “Aa ni na manta…” Daga haka ya shiga mota yace ma Salem su tafi, da ido ta bi motar sannan ta koma ta xauna gun kaskon awaranta. Hansai ta rike ha6a tace “Yau naga ikon Allah, baxa ki fito ana jiranki ba Jiddah???” Sai kuma tana murmushi ta kalli Iliya dake xaune kan tabarma tace “Da yake bata yi la’asar ba kilan sllh ta fara, bari in shiga ciki dai” daga haka ta mike daga kan kujeran tsugunno da take ta shiga dakin, can taga Jiddah xaune kusa da ghana must go din kayansu tana kuka a hankali, Bude baki Hansai tayi tana kallonta, can ta karasa a mugun fusace ta fincikota ta bugata da bango murya can kasa tace “Don ubanki kina ji na kika kyaleni bawan Allah ya xo tun daxu yana jiranki? Saukansa fa kenan daga legas yace kuma anjima da daddare xa su bi tirelan kaya su koma” Cikin rawan murya hawaye na sauka idonta tace “Wllh Baabarmu bana sonsa, shaye shaye fa yake….” Bata rufe baki ba Hansai ta buge mata bakin da karfi ta rankwasheta ta hankadata bakin kofa tace “Fita kar in sumar da ke, yar bakin ciki kawai muguwa” Goge hawayenta tayi ta fita da sauri tana hadiye kukan dake son subce mata, Can nesa da tabarman ta xauna ta hade rai taki cewa komai, Iliya na murmushi da jajayen idonsa yace “Hauwa kuluwa kwandon kilishi…” Sosai ta kara hade rai, yace “To d’an kalleni mana farin cikin xuciyataa” wani harara ta xabga masa, yayi wani murmushin da lebensa da ya dafe saboda shaye shaye ga idanuwansa kamar garwashi, yace “Mun sauke wani kayan ne yau, amma mun yi lodi xa mu koma xuwa nan da bayan magariba” Ita dai ko kallonsa bata sake yi ba, ya ciro rafan ‘yan ashirin ashirin guda biyu sababbi ya ajiye kusa da ita yace “Hansai tace Babanki ya bukaci in turo magabatana, to in sha Allahu ranan laraba xamu yo lodi daga lagos, ina dawowa kuma xan turo tsohona da yayansa, a nan take ma xa a bada sadaki a saka mana rana, don ni a shirye nake” Wasu hawaye suka kawo idon jiddah, ya mike yace “Kice ma Hansai na tafi sai Allah yayi mana dawowa” daga haka ya fita ta bi sa da kallo da dafaffen farin shaddan jikinsa, yana fita Hansai dake la6e tana sauraron duk abinda yace ta fito, dauke kudin tayi tace “Allah yayi masa albarka, ai iliya ba dai xuciya ba, ga masara can ya kawo mana rabin buhu, da wake xai yi kwano biyar wllh, Allah yayi masa albarka” tana gama fadin haka ta dau gyale ta fita gidan….. Jiddah ta hade kai tana kuka sosai, mikewa tayi ita ma ta fita gidan, ta shiga gidan iyah, Iyah ta dinga salati tana kallonta ganin yanda take kuka, duk lallashin duniyan nan tayi mata amma taki sauraronta balle tayi shiru, Iyah tace “Atoh bari in je in ci gaba da tankade gari na kawai” daga haka ta mike ta koma gun da take tankadenta ta xauna ta ci gaba, Da kyar Jiddah ta dago kanta bayan wani lkci tana share sauran hawayen idonta cikin rawar murya ta shiga gaya ma Iyah abinda ya faru, Iyah ta ajiye matankadin hannunta tace “To ubanki ya xama sususu shashasha kenan, banda haka meye mutum xai maida kansa kamar gunki, ko min wani irin asiri tayi masa ai bai ci ya xama kamar gunki haka ba, mutum kawai bai da amfani Allah na tuba, Hansai dai wllh baxata gama da duniya lafiya ba, me yasa bata ba ma Bibalo iliyasun ba, waye bai san iliya ba a garin nan, kawai don axxaluma ce ita ta dage sai ta hadaki da d’an gwangwan d’an shaye shaye? Ranan babu inda labari bai kai ba kan cewar Iliya ya mari mahaifinsa, ba ga uwarsa can a kana radd ba tana 6ara, kanninsa mata kuwa duk karuwanci suke kowa yasani ba wani boyayyen abu bane, ohh na shiga uku ni iyantama, kaiii Hansai da kyar taga annabin rahama, da tasan abun arxiki ne iliya wllh baxa ta so ki da shi ba sai dai Bibalo amma da yake tasan waye shi sai cusa maki shi take alallai adole….” Jiddah dai kuka kawai take, Iyah tace “To dai ba ruwana nawa ido tunda ‘ya yana sun hanani shiga maganan da bai shafeni ba, barin ma na gidan Hansai matar da bata gaji mutunci ba” tana fadin haka ta tafi ta ci gaba da abinda take, a hankali Jiddah ta mike tana share idonta ta fita gidan kada Hansai ta koma taga bata nan.

 

Abuturrab na xaune parlon Umma tare da Ahmad suna cin abinci a tare, Umma dake xaune tana kallo tace “Toh ba dole ku yi shiru ba dama” murmushi kawai Abuturrab yyi, Ahmad yace “Ni xan kawo maki ita ai ta gaisheki Umma….” Umma ta katse sa tace “Ka kawo min wa?” Bai kuma cewa komai, Abuturrab yace “Warce xai aura wai Umma” Umma tace “Akwai wata da xai aura bayan Ramlah ban sani ba?” A tare suka kalleta, Ahmad dai ya ci gaba da cin abincin gabansa bai ce komai ba, Umma tace “Ban da dai ku yaran yanxu abinda ku ke hange daban gida bai koshi ba ai ba a kai waje ba, is there anything wrong with Ramlah da baxaka iya aure ba?” Still Ahmad bai ce komai ba, Umma tace “Ni baxan yi abinda xai cutar da kai ba, meye da Ramlan da baka sonta ka gaya min” Jin bashi da abun ce mata ta mike ta fita daga parlon, Abuturrab dai sai kallon Ahmad yake, bayan few seconds Ahmad ya dago ya kallesa, d’an murmushi kawai yyi ya ci gaba da cin abincinsa, calmly Abuturrab yace “I dont want to believe kayi ma Umma shiru ne saboda Ramlah kanwata ce” Ahmad ya d’an kallesa sai dai he was mute, Abuturrab ya girgixa kai yace “Don’t be quiet because of me, coz if i were in ur shoes i wont keep quiet, baka son Ramlah ga warce kake so to meye na yin shiru? Abinda ake tunanin shi xai karfafa xumunci shi ke 6ata shi, meet Umma…. Pour out ur mind to her, tell her who u intend marrying” Murmushi kawai Ahmad yyi ya maida dubansa kan TV, mikewa Abuturrab yyi yace “Xan amsan ma Ummi drugs a pharmacy so i will be on my way now” Ahmad yace “Alright, anjima da daddare xan shigo in sha Allah” Abuturrab yace “Ok then” daga haka ya fita parlon, amma sai da ya fara shiga main parlor yyi ma kanwar Mahaifiyarsa sallama sannan ya fita gidan. Abuturrab na bedroom dinsa bayan magrib Ahmad ya shigo, Ramlah ce biye a bayansa hannunta rike da cup din shayi da xata kai ma yayanta kamar yanda ya sa ta, Ahmad ya xauna gefen gado, Abuturrab na kallon Ramlah bayan ta ajiye shayin yace “Aunty ta dawo?” Ta girgixa kai tace “Aa bata dawo ba” Yace “Ohk” Ta kalli Ahmad dake danna wayarsa tace “Ya Ahmad su Umma fa?” Ya kalleta yace “She is fine, ya school?” tace “Lafiya lau, ya su Siyama” Yace “Alhmdlh” tace “Kai ma in hado maka shayin?” Yace “Aa sai kace nine Abuturrab” Dariya tayi, Abuturrab dai bai ce masu komai ba, ta nufi kofa, bayan ta fita Abuturrab yace “Mun yi waya da El-Basheer daxu yana gaisheka” Ahmad yace “Oh Yarima, kwana biyu bamu yi magana da shi ba ma” Abuturrab yace “Xai shigo Kadunan amma may be kana Abuja lkcn” Ahmad yace “Allah sarki, Allah ya kawosa lfya” Abuturrab yace “Did u talk to Umma?” Ahmad yace “About what?” Abuturrab yace “Ohh har ka manta” Ahmad yyi murmushi yace “No i dont need to, tunda ga abinda Umma take so, in sha Allah hakan xa ayi” Abuturrab ya mike a fusace yace “What nonsense, why will u say so bayan kai ba son hakan kake ba” Ahmad yace “Tunda Umma tana so nima dole in so” Abuturrab yyi masa kallo yace “Why just speak like an illiterate now?” Ahmad yace “Wait Captain, is there anything wrong with Umma’s choice?” Abuturrab yace “Yes tunda ba son choice din kake ba” Dariya Ahmad yyi yace “Mun ta6a magana da kai nace bana son Ramlah? Asali ma duk cikin cousins dina babu wanda muke shiri da irin Ramlah, Ramlah was kinda brought up in our home since she was 2, tunda takwaran Umma ce kuma rainonta ce ita shi yasa take son ta hadamu, fine if Ramlah is okay with that ni bani da damuwa” Tsaki Abuturrab yyi ya koma ya xauna, Can yace “Ita kuma Maryam din dama yaudaranta kake kenan?” Ahmad yace “Idan wani xai min wnn kallon banda kai Abuturrab, it’s just that my Umma’s choice is my choice” Abuturrab ya jawo wayarsa dake ring ganin Aneesah ke kiransa ya katse ya shiga kiranta, Ahmad ya mike yace “Bari in gaida Ummi” daga haka ya fita dakin….

4……

 

Jiddah ce xaune kusa da Abbanta dake kwance tsakar gida saman tabarma da wani pillow da ya yakune, hawan jininsa ne ya tashi tun daren jiya, magunguna ne ajiye daga gefensa wanda da kudin da take tarawa wajen Iyah ta samu ta siyo masa magungunan, ko bi ta kan inda ta samo maganin Hansai dake ta yankan dafaffen awaranta bata yi ba, Sosai Abban nata ke jin jiki shi yasa duk hankalinta ya tashi, Hansai dai sai ta6e baki take, lkci lkci kuma tayi tsaki har ta gama abinda take yi ta mike tace “Yau ai sai ki xuba ruwa kasa ki sha tunda baxaki siyar min da awara ba kin wani makale kusa dashi wai bai da lafiya, to a duniyar nan yanxu wake da lafiya? Kowa ba lallaba kansa kawai yake yi ba, idan ka xauna ka fake da ciwo ai sai yunwa ta kar ka, ko da yake shi kwanciyar tasa ma da rashinta duk daya ai, Atoh duk daya mana tunda mace ce ke rike da gidan” Daga haka ta daura roban fentin dafaffen awaranta a kai da jarkan man gyada tace “Idan kinga dama in Bibalo ta dawo kice ta sameni bakin titi, tun safe ni ko ganin gilmawarta ban yi ba ko ina taje oho” kofa ta nufa da xaninta da yyi dukundukun xata fita, Jiddah ta goge hawayen dake makale idonta tana kallon Abbanta a hankali tace “Sannu Abba….” Bai iya yace mata komai ba, Hansai ta saka kai xata fita suka kusa cin karo da Iyah, Hansai ta koma baya tana washe baki tace “Sannu da xuwa Iyah” Iyah tace “Yauwa Hansatu, ya me jiki naji ance Isuhu bai ji dadi ba” Hansatu tace “Wllh da sauki kuwa, ga magungunan da na siya masa can ma, to ko kwayan hatsi bamu da shi a gidan shine nace Jiddah ta xauna tare da shi in fita in siyar da awaran nan, ba wata me yawa bace ta dubu uku ce kawai don dai a samu na cin abincin yau da gobe, kinga ai ba a xauna dukka ana jinya ba” Iyah tace “Gaskiya ne, Allah dai ya rufa asiri, yi maxa yamman ma tayi, Allah ya bada sa’a” Hansai tace “Ameen” Daga haka ta fita gidan, Iyah ta karasa ta dau kujeran tsugunno ta xauna tace “Sannu Isuhu” Da kyar ya gyada mata kai, Iyah ta rike ha6a tace “Farin mutum bafillatani duk ya kode kamar bai ta6a haske a rayuwarsa ba, Allah dai ya baka lafiya ya rabaka da cutan nan” Nan ma dai ya gyada mata kai, Iyah ta kalli Jiddah tace “Ya sha magungunan kuwa?” Jiddah ta gyada mata kai, Iyah tace “Toh Allah ya yaye masa” A hankali Jiddah tace “Ameen” Iyah ta bi d’an kuturun tsakar gidan wanda hansai ta mayar kamar na mahaukata da tarkacenta da kallo snn ta ta6e baki ta maida dubanta kansa tace “Amma kana ji na Isuhu” shi dai kallonta kawai yake yana numfashi da kyar, tace “Don muhammadurrasulillahi S.A.W…. ba a dai san gawan fari ba amma ka dubi Allah ka gaya ma wnn yarinya Jiddah inda dangin uwarta suke taje ta nemo su a fadin duniyar nan” Ya sauke numfashi da kyar muryarsa baya fita sosai yace “Iyah Mahaifiyar Hauwa ‘yar Nijar ce….” Iyah tace “Kullum xancen ka kenan Mahaifiyarta yar Nijar ce, to a Nijar din bata da dangi ne Isuhu?” Ya sauke wani numfashin yace “Ni dai kowa yasan ni maraya ne ina almajiranci Uban gidana Alhaji Auwal ya daukeni ya rike kamar d’an sa sbda duk safiya xan wanke masa mota in share masa tsakar gida har ma in je masa aike, ni ban san garinsu Amina mahaifiyar Jiddah ba a Nijar din, ni dai tace min su ‘yan Nijar ne, rana daya uwarta ta daukota suka dawo Nigeria wanda babu tantama kurciya aka mata, ko da suka dawo Nigeria basu walakanta ba don wata Hajiya ta amshe su hannu bibbiyu kakar Jiddah na masu aiki….” Iyah tace “To kai duk a ina kasan wannan labarin da ka kunshe ma cikin ka isuhu?” Yace “Mahaifiyar Jiddah ta bani labarin” Iyah tace “Toh ina ji” a hankali yace “A haka har Allah yayi haduwata da Mahaifiyar jiddah ranan naje kasuwa mai dakin uban gidana ta aikeni, ita kuma Jiddah Mahaifiyar ta aiketa, ban wani sha wahalan samun Mahaifiyar Jiddah ba sbda uban gidana ne ya tsaya min kan komai, a gidan da muka xauna wanda uban gidana ya kama mana haya a lkcn, muka hadu da Hansatu tana xuwa gun kanwar Mahaifiyarta, suka shaku sosai da Amina Mahaifiyar Jiddah duk da ko a lokacin Hansatu xata yi Shekara kusan talatin da wani abu amma bata ta6a aure ba, a lkcn kuma aurenmu ko shekara bai yi ba da Aminatu, ni dai nasan watarana na dawo daga kasuwa Amina ta sani gaba ai sai na auri Hansatu sun xauna tare yau Hansatu ta 6ata labarinta da irin tsananin da ake mata a gida duk don bata samu mijin aure ba kuma taji tausayinta sosai, wllh wllh Auren Hansatu kaddara ce daga Allah amma Amina ce sila, ta takurani, hatta iyayen gidana basu amince da auren ba a sannan, amma sbda son da nake ma Aminatu bana kuma son bacin ranta na lallabasu sai dai sun nuna min babu ruwansu a batun auren kuma babu biyar dinsu a auren, yawanci xannuwan da nayi ma Hansatu na lefe ma xannuwan Aminatu ce ta bani, kinji dalilin auren Hansatu, ni baxan ce sun yi xaman tashin hankali ba gaskiya don ko hakan ya faru Amina bata ta6a nuna min ba don har yau ban ga mace me hakurin Amina a duniya ba duk da xaman mu bai yi nisa ba don ta haifi Jiddah da shekara daya ta rasu, a lkcn Hansatu na da cikin Bibalo kin ji yanda rikon Jiddah ya koma gun Hansatu tun ba a yayeta ba, Uban gidana ya so Jiddah ta dawo wajensu bayan rasuwar Mahaifiyarta amma Hansatu ta saka mana kuka xa a rabata da jiddah, ita a bar mata ita xata raineta kamar yanda xata raini Habiba su taso tare, hatta Mahaifiyar Amina ta so amsan Jiddah bayan rasuwar ‘yar ta, Amma Hansatu ta bi ta da dadin baki taki bata, ashe ita ma ba mai tsawon rai bace, don bayan rasuwan Amina da shekara uku ita ma ta rasu….” Jiddah dai kallon Abban nata kawai take don bai ta6a bata labarin nan ba sai yau, ta dai sha jin mutane na cewa Hansatu ba baabarta bace amma bata yrda sbda ita ta taso ta gani, Iyah sai girgixa kai take tana cewa “Allah me girma, ashe dai Hansatu baxata wanye lafiya da duniya ba… wuhuhu, Allahu akbar, To su iyayen gidan naka suna ina suka bar ka ka walakanta ka gantale haka, ai ko ba komai nasan sun ci moriyarka dai ba adadi” lkci daya Hawaye ya kawo idonsa yace “Hansatu ce dae ta rabamu, Alhaji Auwal ya bani kudi miliyan 2 in kai masa banki ban samu xuwa bankin a ranan ba sbda ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya ina tsoron bin hanya da kudi haka, sae na dawo gida da kudin, Hansatu ta xare dubu dari biyu a ciki, kudi ko sama ko kasa, sbda Alhaji Auwal din yace bai yrda ba bayan na sanar masa 6atan kudin da naga bani da mafita, shine matar nan taje har gida ta ci masu mutunci ba na wasa ba, basu yi mata komai ba amma shine har yau, kudi kuma yace ya yafe min ya dai amshi sauran kudinsa, to kinji abinda ya faru… Wnn gidan ma da muke ciki ai shi ya siya min wllh, yau shekara bakwai kenan da ya bar kaduna suna Abuja da iyalansa” Iyah tayi tagumi tace “Yau naga tsinanniyar mata, dama ance ita ta talauta ka da ba haka kake ba, ilai ga magana ta fito….” Yace “Duk ta bi ta siyar min da filayena biyu da gonata daya, da wnn gidan kadai na tsira….” jiddah ta goge hawayen dake makale idonta duk jikinta yyi sanyi, Iyah tace “In sha Allahu xa mu ga karshenta kuwa, abinda Allah baya bacci, ynxu damuwata inda wnn yarinya jiddah xata samo danginta, to gidan da kakarta tayi aikatau a ina yake?” Yace “Wnn ai sun fi shekara sha biyar da barin kaduna, idan ko ba barin kaduna suka yi ba to sun sauya wani gidan ne don xuwana biyu duk akan haka amma aka sanar min sun tashi” Iyah tace “Abu ya lalace kuwa, banda haka ai baxata rasa basu labarin kanta da garinsu ba, kaga da ko su sai suyi ma jiddah hanyar xuwa dangin uwarta ita ma ta dawo mutum, amma ina mutum a nan ba dangi” girgixa kai kawai yyi, Iyah tace “Toh Allah ya rufa asiri, xaka ci tuwon masara da miyar kubewa in tafi in yi maka yanxu?” Jiddah tace “Xai ci iyah, tun safe bai ci komai ba sae kunu da ya sha” Mikewa Iyah tayi tace “Toh bari in je in hura gawayi yanxu ina da komai a gida, yanxun nan xan gama, to ae mayyar ba wani damuwa da rayuwarsa tayi ba, ehh Hansatu ba” Daga haka ta nufi kofa ya bi ta ta ido har ta fita, murya can kasa yace “Kiyi ta hakuri kin ji Jiddah, wataran sai labari, nasan ban ta6a cutan wani tsawon rayuwata ba, ina fatan Allah ya dubi hakan, albarkacin hakan kada ya bari ki walakanta, Allah ya yanke maki wnn wahala da kike sha cikin gaggawa yayi maki abinda yafi alkhairi a rayuwarki, ina maki addu’an Allah ya baki hakuri da juriya da kauda kai irin na Mahaifiyarki Amina, kar ki kaga ana maki abubuwa ina shiru Jiddah, har gobe bani da kamar ki a duniya jiddah tun bayan rasuwar mahaifiyarki, Ban yi shiru a kan batun aurenki da wannan takadirin yaron da take ba, don har yanxu ban furta komai ba hakan ba yana nufin na aminta da auren bane, idan anyi duniya domin manzon Allah xaki auri mijin da xai kula dake yayi maki abubuwan da mu muka kasa maki, xaki auri wanda xai rike ki bisa gaskiya, wanda xai yanke maki wannan wahala da kike ciki in sha Allah” Hawaye ya shiga sakko mata ta kasa ce ma Abban nata komai, amma taji hankalinta ya kwanta sosai, da kyar ya ci gaba “In sha Allahu wannan takadirin ba mijin ki bane Jiddah…” ta gyada masa kai tana gyara masa kwanciyar kansa, ya lumshe ido yace “Tashi ki je kiyi wanke wanken da ta sa ki kar ta dawo kin ji” Ta goge idonta cikin sanyin murya tace “To Abbana Allah ya baka lafiya” Yace “Ameen Jiddah” Mikewa tayi ta tafi gun uban kwanukan da Hansai ta tula bakin kwararo k’uda sai fareti suke a kai, sbda yawan kwanukan sai kusan la’asar ta gama ta mike ta dau buta ta xuba ruwa jin ana kiran sllh ta ajiye inda Abbanta ke alwala ta koma kusa da shi ta durkusa tace “Abba ka daure ka tashi kayi alwala” Jin yyi shiru ta kai hannu jikinsa tace “Abba la’asar yyi….” hannunsa taga ya xamo kasa daga jikinsa, ta kamo hannun tace “Abba….” Shiru bai amsa ba, komin bacci ko rashin lafiya shi din ba me nauyin bacci bane, hakan yasa ta sake kiransa nan ma shiru, jijjigasa tayi taga dayan hannun ma ya xame, bata san lkcn da ta kwala wani ihu da karfi ba kan kace me mutane suka shigo gidan da sauri jikinta na rawa tace “Ku taimakeni Abbana yaki tashi” Wani makocinsu wanda har da shi ya shigo ya kai hannu jikinsa lkci daya ya saki salati yace “Isuhu ai rai yyi halinsa” Daga wnn Jiddah bata sake jin komai ba ta dai bude ido ta ganta kwance saman tabarma dare yyi ga mutane cike tsakar gidan. Bayan kwana uku, Jiddah na xaune tsakar gida da idonta da yyi bulu bulu ga wani rama da tayi don har sannan bata iya cin komai, Hansai sai faman yankan awara take tana cewa “Ke kadai aka ma mutuwa idan ba munafurci ba, Ita Bibalo ba ubanta ne ya rasu ba halan, munafuka kawai me neman suna, kin taso kin fita da kayan awara bakin titi ko sai na taso na nakada maki shegen duka, idan bamu yi awara ba yau ubanki xa mu kwakulo a kabari mu ci?” Hawaye kawai Jiddah take ta mike ta dau kaskon awara da coal pot da wasu kananun kayan ta fita xuwa bakin titi, Hansai tace “Ni wllh idan ba binsa kabarin kika yi ba bansan kina yi ba, bayan mutuwan da yyi ya bar ni da wahalan yi maki kayan aure duk da dai katifa da robobin kitchen kadai Allah xai hore min inyi maki, to ince me wnn wahalan da ya bar ni da shi, ina ta sintirin xuwa gidan Saude xaman makoki miji ya rasu ashe nima nawa na kan hanya xai tafi ya bar ni da wahala, to banda dai dama ya gaji da duniyar daga tashin hawan jini sai mutuwa Allah na tuba, shi dai yaji da munafurcinsa kawai dama ya gaji da duniyar ne, to ba dai ya mutun ba dai ai shkkn, yanxu ga aurenki dake ta karatowa ya gudu ya bar ni da wahala” A haka jiddah ta dawo ta sameta tana ta kumfar baki ta dau robon awaran ta fita, har sannan jiddah taki dawowa dai dai, gani take kamar mafarki take xata farka taga Abbanta bai rasu ba, har yau da aka yi uku abincin kirki ta kasa ci, don ma Iyah na tsareta sai ta sha kunu, banda tsine ma Hansai babu abinda yan anguwan ke yi ganin Jiddah bakin titi tana tuyan awara, daga mutuwar miji da kwana uku har ta ci gaba da awaranta wnn wani irin xuciya gareta, yawanci duk Jiddah ake tausayi don shkkn ta xama marainiya gaba da baya yanxu…. Abuturrab na kallon Ramlah dake yankan ma Umma Fruits yace “Umma ta ci abinci kuwa?” Ramlah tace “Aa bata wani ci ba, Amma Aunty Zainab taje gida xata yi mata tuwo yanxu” Ummi dake xaune kan farin kujera a ward din tace “Ga farfesun hanta ma da nayi mata bata ci ba” Abuturrab ya kalli Umma dake kwance da drip a hannunta yace “Umma ko a siyo maki awara?” Ta d’an yi shiru kafin a hankali tace “Toh Allah ya sa in iya ci, bana jin dadin komai a bakina” Ummi tace “Toh wannan ai dole ne Ramlah… Kawai daurewa xaki yi kici ko kadan sai kiji jikin ya maki kwari” Abuturrab yace “Toh bari in je in siyo maki yanxu” Daga haka ya fita, Slowly yake driving din har ya karasa hayi, dai dai u turn din wajen ya juya ya nemi waje yyi parking yana kallonta ta glass din motar, kanta a kasa tana juya awaran cikin man kaskon a hankali, ya sauke glass din motar yace “Ki bani awaran dari biyar” Dago kai tayi tana kallonsa, kallon idanuwanta da suka kumbura yyi, bata ce komai ba ta saka masa awaran yanda yace snn ta mike ta isa gun motar tana mika masa ledan, bai amsa ba yace “Kukan me kika yi haka??” Ta sauke idonta kasa, lkci daya xuciyarta yayi mata rauni wasu sabbin hawayen suka cika idonta, da mamaki yake kallonta, bata san lkcn da ta fashe da kuka sosai ba tace “Abbana ne ya rasu” Daga nan kuma kamar warce aka tunxura ta jingina da motar ta dinga rera masa kuka, a hankali underneath his breathe yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Kuka kawai take so painfully, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya bude motar ya sakko ya xagayo yace “Yaushe ya rasu?” Cikin kuka sosai tace “Yau aka yi uku” Da mamaki yace “Shine kika fito suyan wannan abun” Cikin rauni tace “Baabarmu ce tace sai na fito” Dauke kansa yyi, can yace “Awaran na nawa ne gaba daya?” Ta juya ta kalli roban awaran cikin shessheka tace, wai na dubu biyar tace min” Ya girgixa kai bai ce komai ba, can ya juya ya bude motarsa, kudin da ya ciro xa ayi masa delivering eye glasses da yyi ordering online ya dauko a motar, kamar wanda ya tuna wani abu ya fasa fito da kudin a haka sai da ya saka a wani ledan turare snn ya juyo yana kallonta, har sannan kuka take sosai, ya mika mata ledan kudin yace “Gashi ki kai mata kice ance kada ki sake fitowa sai an kwana biyu” Kallon ledan ta dinga yi da yyi mata dishi dishi sbda hawayen idonta ya kamo hannunta ya mika mata ledan ya amshi ledan awaran ya saka a mota yace “Allah ya gafarta masa” daga haka ya xaga ya shiga motarsa ya tada ya bar wajen, share hawayen idonta tayi ta leka ledan taga dari biyar sababbi dal a rafe, sosai gabanta ya fadi, ta kasa kwakkwaran motsi, wani almajiri ne yace “Awaran ki na konewa” Da sauri ta juya ta sauke awaran, ta xauna xuciyarta na bugawa da karfi, muryar Hansai taji a bayanta, Hansai ta ajiye bokitin wani awaran tana cewa “Ta dari biyar ce wnn, gaba daya ya kama dubu biyar da dari biyar….” ganin awara ya kone a mai tayi tsit tana xare ido, lkci daya ta saki salati da karfi tace “Na shiga uku awaran kika kona min Jiddah???” A mugun tsorace Jiddah ta mika mata ledan kudin tace “Baabarmu wllh wani ne ya xo ya kawo min wnn wai in kai maki kar mu sake fitowa sai bayan kwana biyu….” Hansai ta karbi ledan tana duba ciki da sauri, xaro ido tayi tana kallon tulin kudin cikin ledan, lkci daya ta dinga bin anguwan da kallo, murya can kasa tace “Daga ina yake?” Jiddah ta buda hannu har sannan jikinta na rawa tace “Wllh ban sani ba” Hansai tace “Dauko jarkar man da roban awaran mu wuce gida ai ya kare ma” A haka Jiddah ta kwashi kayan awaran ta bi bayan Hansai dake tafiya da sauri da sauri, A bakin kofar dakin Hansai Jiddah ta makale tana kallonta tana ta faman kirgan kudi duk ta hada xufa, har ta gama kirgen tana xaro ido tace “Dubu dari a wannan marran ni Hansatu, Allah yyi ma bawan Allahn nan albarka, yanda ya taimaki marayu Allah ya taimakesa haka shi ma, kaiii a duniyar nan ma dai xaman wasu toshe hanyar alkhairi kawai yake, banda haka daga rasuwan Isuhu kamar daga sama Allah ya jefo bawan Allah ya bamu dubu dari cif cif, yaushe rabon inga dubu ashirin da idona ni Hansatu” Jiddah dai ta sunkuyar da kanta xuciyarta na mata xafi bata ce komai ba, Hansai tace “Maxa ki sa ruwa kiyi wanka kema ko kya ji dadin jikin ki, kinga dai mutuwar nan alkhairi ne garemu sai kiga Allah yyi ta bude mana hanyoyi iri iri, aa ni dai wllh gwara da ya bamu hanya mu san me muke ciki a duniyar, to da ya baki kudin sai yace maki me?” Cikin sanyin murya tace “Yace kar in sake fitowa sae bayan kwana biyu” Hansai ta fashe da kuka tace “To dama banda talauci me xai sa mijina ya mutu in fara awara a ranan da aka yi sadakan uku, ai sai dai talaucin dama” Ta kara rushewa da kuka tana matsar kwalla da bakin xaninta, juyawa jiddah tayi a hankali ta bar bakin kofar tana dada jin mutuwar mahaifinta kamar a mafarki wanda hakan yasa hawaye kawowa idonta.

 

 

*Still on free pages kar labari ya dauko maku dadi ku ga an datse don free pages din ba yawa ehee, u can proceed with payment sbda kawai a ci gaba ba sai an tsaya ba after free pages din, that is idan kunyi payment kenan fahh….*👌🏻

Tunda dai littafin me sunana ne wannan kunsan baxan gantalar da littafin ba, don haka kar kuyi fargaban komai ku ma baxan gantalar da xuciyoyin ku ba a gaskiya😹😹

 

Ping 07087865788 for payment details.

 

 

 

 

💖💖 Jiddatul Khair💖💖

 

 

 

 

_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻

 

 

 

 

 

5…..

 

 

Alhaji Usman ne xaune parlonsa tare da Hajiya Hauwa, ya ajiye wayar hannunsa yace “Toh ke ya kika ga Madam?” Ummi tace “Aa in dai tana so babu wani matsala daga gareni sai yanda kace” Ya jinjina kai yace “Toh shi Ahmad din ne yace yana sonta?” Ummi tayi murmushi tace “Toh wannan kuma gaskiya i can’t say Alhaji” Abba yace “Toh sai na fara magana da shi Ahmad din da Ramlah, don ke da kanwar nan taki na lura kanku kadai ku ka sani” Yana murmushi ya kare maganar, tayi ‘yar dariya tace “Aa ai baxa ayi masu dole ba dama” Yace “Toh Allah yayi xabi mafi alkhairi dai” Ta amsa da Ameen. Bayan sati daya aka saka ranan bikin Ahmad da Ramlah wanda xa ayi bayan wata uku. Abuturrab na gidansa na Abuja tare da Ahmad da shigowarsa gidan kenan, banda kamshi bbu abinda ke tashi a gidan, ko ina so very neat and tidy kai kace da mace a gidan, Ahmad ya fito daga kitchen rike da cup din coffee yana juyawa da spoon yace “Matar gidan bata iso ba har yanxu kenan” Wani kallo Abuturrab ya jefa masa, Ahmad yyi wani dariya yace “Ka gama yaudaran yar mutane daga karshe ka samu yar sweet sixteen ka aura abun ka” Abuturrab yace “Sai ince na auri me? Ashe xaka sha mamaki kenan idan kaga na auri Aneesah” Ahmad yace “Gaskiya don ban ta6a sawa a rai cewar xaka auri Aneesan nan ba, ku dai gama holewan ku tayi auren ta kayi naka” Abuturrab bai kuma ce masa komai ba ya maida hankalinsa kan TV dake aiki, Ahmad ya nemi kujera ya xauna yace “To in har da gaske sonta kake da aure kayi magana mana a saka mana rana daya gaba daya” Abuturrab that is already getting pissed up yace “You dont have to tell me what to do with my life dude…” Dariya Ahmad yyi yace “Of course, especially in a case like this” Tsaki Abuturrab yayi ya mike ya dau wayarsa ya wuce daki ya bar masa parlon… Ahmad na gama shan coffee din ya mike ya bisa xuwa dakin, xaune ya samesa da wayarsa yana magana alamar video call yake, Abuturrab ya kallesa sannan yace “Toh gashi nan ya shigo sai ku gaisa” Ahmad yace “Waye?” Abuturrab ya mika masa wayar, amsa yayi yana kallon screen din, suna hada ido ya buda baki yace “Mutanen Egypt ne dama” Bai rufe baki ba tace “Waye wannan???” Dariya yayi yana kallon uban glass da ta saka a ido fuskarta duk ya cika screen din wayar yace “To glass din kuma da kika maka haka wa ya ara maki?” Ji yayi tana cewa “Farida xo ki mayar min da fuskar Aliyu don Allah, kamar ya shiga wani kiran fuskar wani nake gani” Wata yar budurwa ce ta leko wayar ta xaro ido tace “Lahh Hajja ai Yaya Ahmad ne” Warce ta kira da Hajja tace “Kaji wani xance to ni ina ruwana da shi xa a sako min fuskarsa, ki mayar min da fuskar Aliyu nace, idan kuma baxai yiwu ba ki kashe kawai, waye kuma wani Ahmad, ni na san shi” Ahmad dake ta dariya yace “Nima ae ba saninki nayi ba kawai miko min wayar aka yi” Hajja ta sake wayar ya fadi tace “Ni dai na shiga uku, A gaskiya wannan ai walakanci ne da cin fuska, ya xan dinga magana da Aliyu fuskar wani kato ya fito, wayar taki ce ta lalace ko wa’adin da aka debar mana na magana da Aliyun ne ya kare aka sako min fuskar wani can” Farida ta ma rasa abun cewa sai dariya take, Ahmad ya katse wayar ya jefa gefen Abuturrab shi ma yana dariya, Abuturrab yyi murmushi yace “Yanxu fa take tambayar ka shine ka shigo na baka fa….”

 

Iyah ce tsaye kan jiddah dake ta kuka kamar an aikota, A fusace tace “Toh meye amfanin wnn shegen kukan da kike ne wai, nace ki hado tsummokaranki in sa ki mota tunda da kudin ki a hannuna ki tafi legas wajen Salame kawai” Jiddah na kuka tace “Toh Iyah idan iliyan ya hadu da ni a legas din fa? Shi ma fa a can yake aiki ai” Iyah tace “Legas din bai fi Najeriya girma ba aka ce maki, ta ina xai ganki a gari me girma haka” Shiru Jiddah tayi tana kallonta wasu hawayen na sauka fuskarta, Iyah tace “Ni dai ba ruwana ina kokarin ganin na rufa maki asiri kar a aura maki takadiri kina min gardama, hakkin makotaka fa nake son in fita, banda haka me na hada dake Jiddah?? Sannan ni ce mutum ta karshe da Allah ya ba iko nayi hirar karshe da mahaifinki kafin ya mutu, to sai in xuba ido ki tagayyara ya kullace ni duk inda yake?” Jiddah ta sauke idonta dake xuban hawaye xuciyarta yyi rauni, Iyah tace “Atoh babu ruwana wllh, ba dai gobe xata tafi kasuwar tasha siyo kayan sana’arta ba, sai ki shirya tana fita in kai ki tasha kawai, ko da tirela ne sai ki bi xuwa legas din, amma idan ba haka ba shkkn rayuwarki ta lalace idan aka aura maki Iliyasu” Iyah na kai wa nan ta tafi gun tuwonta dake kan murhu tana cewa “Na fita hakkin ki duk da ba dangin iya ba na baba, amma hakkin makotaka fa??” Jiddah dai gaba daya jikinta yyi sanyi, she is too young to even think straight for her age, hakan yasa taji gwara kawai ta gudun don gashi har an xo an sa mata rana wata daya dai dai da Iliyasu a yau.

 

Aunty na kallon Nafisa, cike da fada tace “Tashi ki fita ki ban waje” Ba musu Nafisar ta mike ta fita kamar xata yi kuka, Aunty ta dubi Abuturrab dake dakin yana kallonta tace “Wllh baka gansa ba Captain, ni dai ban ta6a ganin haka ba, banda yarinta da dolanci me xata yi da shi don Allah??” Abuturrab na cin Apple din hannunsa yace “Meye da shi wai Aunty?” Cike da takaici Aunty tace “Don dai sai da yamma ka dawo jiya da ka gane ma idonka….” Yace “Aa ni a garin nan ma nayi sllhn juma’ah, private jet muka biyo daga kano, sha biyu da rabi ina kaduna…” tace “To a ina ka tsaya sai bayan la’asar ka dawo gida?” Yace “Muna tare da wasu abokanmu” Aunty tace “Shi yasa, ai da ka gansa wllh… Muna xaune fa jiya da safe kamar abun arxiki tace mana wai Salis yace xai xo bayan an sakko juma’ah mu gaisa, na xata abun arxiki ne har da sa masu aiki su tayata yi masa snacks iri iri wai ashe gantalalle xata kawo mana…” Abuturrab dake ta kallonta yace “Toh meye da shi baki fada min ba har yanxu” Tace “Toh kaga Captain tun daga bakin titi da kafa ya tako har nan, ashe ko motar ma bashi da, sai kaga wani yakunannen yadin da ya sa bbu gugan arxiki, kana ganinsa dai kaga ‘ya yan ya ku bayi, ni ko a raina nace ko ina wannan yarinyar ta samo mutumin nan haka, ni wllh a bakin stairs na tsaya amsa gaisuwarsa ban yarda na karaso parlon ba” Abuturrab yyi murmushi ya kai Apple dinsa baki yace “Wani sana’a yake yi?” Wani kallo ta jefa masa tace “Sana’a, wa ke ta wani sana’arsa banda abun ka, ko ka mance da wannan saying din that goes thus… The way u dress will be the way u will be addressed??” Abuturrab ya gyada kai kawai bai ce komai ba, tace “Wllh na sake ganinta tare da shi Allah sai na ji mata ciwo kowa ma ya huta, ita kuma Ummi da taya bera 6ari sai wani nan nan take da shi, tarba dai yanda kasan mutumin arxiki haka tayi ma yaron, ni ko kunya kamar in nutse wllh, Salem kuma inda ya burgeni ko kallonsa bai yi ba da ya shigo parlon kawai yyi wucewarsa daki…” Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya yace “Toh Allah ya kyauta….” Tace “Ameen sai ka kirata and talk sense into her head… Ba ni xata kwaso ma abun kunya ba” Mikewa yayi, tayi saurin cewa “Captain ban kai ka kaje kaga filin da na siya ba ae” Yace “Xuwa gobe in sha Allah” tace “Lahadin xaka koma aikin?” Yace “Idan Allah ya yarda” Tace “Wancan satin kasa nayi maka tamarind drink baka dawo ba…” Ya shafa kansa yace “Wlh daya daga pilot din da xai yi piloting jirgi daga lagos xuwa port Harcourt bai ji dadi ba shine ni nayi, wnn satin ma ban yi niyyar dawowa ba coz i was so stressed out during the week” Tace “Gashi ko ka xo kadunan ba wani hutawa kake ba tunda ba xama kake gida ba” yyi murmushi kawai, tace “Sai kaji an sa ranan Ahmad da Ramlatu” Yace “So Abba told me” Tace “Atoh bai fi mata ba, yar uwarta ta tsaya kula ya ku bayin garin nan, Ahmad ai d’an gayu ne d’an boko ga hankali da nutsuwa duk da dai ni ba wani shiri muke da shi ba, though auren xumunci ne ma ai amma gwara hakan, Nafisa ma tace min ai tasan tsohuwar Budurwarsa Maryam islamiyyar su daya kafin ta canxa islamiyyan” Abuturrab ya nufi kofa yace “To Allah ya kyauta” Tace “Bayan an gama da na Ramlah sae a dawo naka da Aneesah ko?” Murmushi yyi yace “Allah ya kai mu lokaci” Daga haka yyi mata sallama ya fita yana duba agogon wrist dinsa, kira ne ya shigo wayarsa, ya duba ganin Aneesah ya daga ya kai kunne yace “Don’t tell me har kin sauka?” Tace “God!!! Nima Don’t tell me baka fito ba Captain” Ya wara manyan idanuwansa yace “Ban dade da shigowa gida ba… But in few mins time xan karaso I’m sorry” Bai jira me xata ce ba ya katse wayar ya fita ya hau motarsa…. Tafiyar minti ashirin ya kai sa train station, murmushi yyi ganin yanda ta hade rai tana tsaye daga nisa, abaya ne baki jikinta da yyi matukar amsan farin fatarta, ja da bakin lallen dake hannunta ya kara contributing wajen haduwarta a lkcn, she looks so sweet, mutane dai daya ne ke wucewa wajen basu kalleta sun sake kallonta ba, ya karasa inda take smiling, cikin soft voice dinsa yace “Sorry Baby, kinsan dole in je in gaida su Ummi da Aunty beside dole ma sai na koma gidan na dauko mota tunda ban dade da sauka ba nima….” Cike da shagwaba tace “Kasan mutane nawa suka tambayeni numbata tsayuwar da nayi nan yanxu” Yace “Sai kika basu kenan” Ta juya masa fararen idonta ta ki cewa komai, murmushi yyi ya amshi trolley din hannunta ya fara tafiya xuwa gun motarsa tana biye da shi tana kallonsa don komai yyi burgeta yake. A hankali yake driving din Aneesah dake gefensa tace “I learnt about Ahmad’s engagement with Ramlah” idonsa na kan titi yace “So i heard also” Tayi kasa da murya tace “To mu kuma namu fa?” Still bai kalleta ba yace “Xa ayi” Tace “Yaushe??” yace “Am trying to put things in order first, i don’t get why u are in a rush Aneesah, ba dai ni nace xan aure ki ba, meye kike damun kanki haka? Do i look like a liar or do my words sounds deceptive?” Ta kai hannunta kan nasa cikin sanyin murya tace “I just can’t imagine loosing u My Captain, i just can’t….” Yace “Keep ur mind at rest Neesah, i am all urs and urs alone” Yana fadin haka ya sakar mata murmushinsa dake kara narkar da xuciyarta, dai dai nan kuma ya kai layinsu Jiddah, yau bata awara a bakin titin don babu alamar ma ta fito, sai dai mutane ne cike fal a d’an layin nasu, a hankali yake driving din yana kallon cikin layin, Aneesah dake kallon direction din ita ma tace “What’s happening there, ko anyi rasuwa ne?” kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Ko in sauke journalist taje ta gano mana???” Dariya tayi tace “Oops a wnn local area din xanyi journalism dina Captain? Haba this is so disgusting…” Tana magana tana yamutse fuska, shi dai bai ce komai ba yana ci gaba da driving dinsa, can gidan Kanwar babanta ya ajiyeta a unguwar sarki, bayan ya yi mata few shopping na kayan ciye ciye, ta sauka motar bayan yyi parking tana kallonsa, shi ma ya sauko ya fiddo mata da trolley dinta ya kai bakin gate din ya ajiye, ta dau ledan shopping din da yyi mata tana kallonsa bayan ya dawo cikin sanyin muryarta tace “Thank you My Captain, plss ka daure ka xo anjima da daddare mu yi hira…” Ya kashe mata ido yace “Ohk babe….” Daga haka ya shiga motarsa yyi reverse ta bi sa da kallo har ya fita layin tana sake jin wutan sonsa na ruruwa a xuciyarta. Abuturrab na komawa gida yyi parking nan kofar gidansu ya shiga ciki yyi alwala snn ya fito ya shiga masallaci don ana ta kiran magrib, bayan an idar ya fito masallacin ya shiga motarsa ya xauna yana danna wayarsa, ajiye wayan yyi yana kallon flowers dake xagaye kofar gidan nasu trying to imagine the meaning of the crowd they saw earlier a layin yarinyar nan me awara, did someone die again, tunanin hakan ya sa ya tada motarsa ya bar layin, yana isa yyi parking bakin titi ya dau nose mask dinsa a motar ya saka snn ya bude motar ya sauka, ashe da daddare sana’a ake yi sosai bakin titin layin, just like sauran layukan anguwan gaba daya, daga me soya wancan sai me soya wannan, masu siyar da gyada, rake, abubuwan ci na gargajiya dai yawa… A hankali yake tafiya cikin layin yana yatsine fuska, he is even afraid kada allergy ya je ya kamasa cos he is so sensitive to anything Filth,… har dai ya kai dai dai kofar gidan da yaron nan ya ta6a kai sa a matsayin gidansu yarinyar, tsaye yyi yana bin duk wajen da kallo, ginin block ne sai dai ko plaster babu, sannan gidan karami ne sosai, duk gidajen layin haka suke, banda gida daya da ya d’an darasu girma shi ma da kadan wato gidan Iyah, wata yarinya ce ke tafe ko takalmi bbu a kafarta, ya bi ta da kallo yace “Baby….” Juyowa tayi tana kallonsa yace “Xo in aike ki cikin gidan nan” Yarinyar da baxata wuce shekara shidda ba ta dawo tace “Gidansu Bibalo?” Yace “Ehh, shiga kice ana kiran me awara a ciki” Da gudu yarinyar ta shiga, babu kowa tsakar gidan don Hansai ko minti biyar ba ayi da fitarta ba, ta shiga makota, Bibalo kuma tun la’asar rabonta da gidan, yarinyar ta kutsa kai cikin dakin su Bibalo tana kallon Jiddah dake kwance ta takure waje daya kan yakunannen katifarsu da Bibalo, tace “Wai ana sallama a waje” Da sauri Jiddah ta mike xaune da idanuwanta da suka yi jajir, duk da tasan Hansai ta fita gidan don sai da ta bar mata sallahun bakar magana ma kafin ta fita amma hakan bai hana xuciyarta dinga bugawa ba jin abinda yarinyar tace, A tunaninta saurayinta ne Usman ya xo, kilan ya ji abinda ke faruwa ne, da kyar dai ta lallaba ta mike ta cire Hijab din jikinta ta dau wankakke dake a linke ta saka, sanyi take ji sosai don xaxxabi ne jikinta, ta fito dakin ta sa takalminta tana tafiya kamar iska xai kadeta ta fito kofar gidan, babu haske sosai wajen hakan yasa ta dinga kallon mutumin dake tsaye da fararen kaya ya juya baya, gani tayi ba Usman bane don wnn yafi Usman tsayi, ta bi layin da kallo tana kara tsoron kada Hansai ta dawo ta tarda ita a waje bayan an yi mata iyaka da wajen daga daxu da yamma, da kyar tace “Wa kake nema?” Sai a snn ya juyo ya sauke mask din fuskarsa yana kallonta, ta xaro ido tsoronta ya tsananta, haka xaxxabinta ma taji yana neman fin na da, don sanyi sosai ya dinga shigarta, kallonta ya shiga yi daga sama har kasa, rasa abin cewa tayi daga karshe ta jingina da bangon gidan, still looking at her yace “Baki da lafiya ne?” Ta gyada masa kai, lkci daya hawaye ya kawo idonta, bin layin ya sake yi da kallo, can yace “Baki sha magani ba?” Hawayen dake makale idonta ya silalo kasa ta girgixa masa kai tace “Babu maganin” yace “Ke da waye a cikin gidan?” Tace “Ni kadai ce, Baabarmu ta fita yanxu” Shiru yyi kamar me naxari sai kuma ya kalli inda motarsa yake yace “Akwai asibiti a nan anguwar?” Ta gyada masa kai tana nuna masa tace “A layin can gaba” Yace “Mu je” Da mamaki take kallonsa tace “Ina?” Ya wani hade rai yace “Mu tafi can din nace” ta marairaice cikin rawar murya tace “Baabarmu tace idan na sake fitowa ko nan bakin kofa sai ta kasheni wllh” Shiru yyi na few seconds kafin yace “Saboda me?” Tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace “An sa min rana” Daga sama har kasa ya sake kallonta snn yace “Da wa?” Ta fashe da kuka tace “Da iliya” tana fadin haka kamar an tunxurata ta dinga rera kuka, yace “Ohk, amma bai san baki da lafiya bane bai kawo maki magani ba” Bata basa amsa ba sai kukan da take yi sosai, yace “Mu je” ganin ta ki motsawa ya daure fuska sosai yace “Ke kinsan daga inda nake?” Ta shiga goge idonta bata ce komai ba, yace “Mu tafi nace” A hankali ta fara goge idonta, ganin ya fara tafiya ta bi bayansa gabanta na faduwa tana waige waige har suka kusa bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta don duk maxaunin bakin titin nan babu wanda bai santa ba, ya bude mata back seat, xuciyarta ya dinga bugawa da karfi ta tsaya tana kallonsa, ya sauke nose mask dinsa yace “Kina 6ata min lkci” A hankali tace “Baabarmu xata…..” Wani kallo yyi mata yace “Nace ki shiga malama” shiga motar tayi a tsorace, ya rufe sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da ya hau saman titi yace “Ina asibitin yake?” Layi uku dake gaba da nasu ta nuna masa ya shiga layin suna isa yaga irin asibitin yyi parking yana kare ma wajen kallo, kafin yace “Nan din ne asibitin?” Kai kawai ta gyada masa, ya ja tsaki ya tada motarsa yayi reverse ya bar wajen, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, wani asibiti a cikin gari ya kai ta, yana parking haraban asibitin ba tare da ya juya gareta ba yace “Sauka” kalle kallen motar ta dinga yi alamar bata ma san ta ina xata bude ba, ya sauka ya xagayo ya bude motar, sauka tayi ya rufe motarsa, ganin yanda ta tsaya ya dake yace “Mu je” he sounds so pissed off, Ba musu ta bi bayansa har cikin asibitin, nan take ya yankar mata kati, ba a dau lkci ba nurse din ta sanar masa xa su iya shiga gun likita, yana daga xaune ya nuna mata office din likitan yace ta shiga ta gaya masa duk abinda ke damunta, Jiddah ta mike gabanta na faduwa tana kallonsa a hankali tace “Ai tsoro nake ji” ya hade rai a d’an tsawace yace “Tsoron likitan sbda xai cinye ki?” Sunkuyar da kanta tayi, yace “Juya ki shiga” a hankali ta juya ta nufi office din likitan da ya nuna mata, kamar me tsoron kofar ta murda ta shiga, sai a sannan ya mike ya bi bayanta xuwa cikin office din, tana xaune ta takure waje daya likitan na cewa ta kwantar da hankalinta ta nutsu, ganin ya shigo sai taji hankalinta ya kwanta, ya ja kujera ya xauna suka gaisa da likitan, likitan na kallonta yace “Me ke damun ki?” Cikin sanyin murya tace “Kai na ke min ciwo, ina jin xaxxabi, kuma ina ganin jiri….” Mikewa yayi ya dawo kusa da ita yana duba idonta da wani d’an abu kamar fitila a hannunsa, Abuturrab dai na xaune yana dubansu har likitan ya gama gwaje gwajensa snn ya koma ya xauna yana kallon Abuturrab yace “Xa ayi mata test, though symptoms din na malaria ne, but it’s good ayi test din sannan kuma …. Is she ur sister?” Abuturrab ya d’an kalleta sannan a hankali yace “Yea” Likitan yace “Me ke damunta haka, yar yarinya da ita na ga Bp dinta ya hau” sake kallonta Abuturrab yyi, likitan na kallonta yace “Kina da damuwa ne ‘yan mata, idan ma baxa ki gaya ma d’an uwanki ba ni ki gaya min” Sunkuyar da kanta tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, Abuturrab yace “Dont worry Dr i will talk to her about that, ynxu dai idan ba damuwa kawai a hada mata drugs if there is need for injection ayi mata ba sai an yi mata test din ba cos i guess it will take up to 40mins kafin result din ya fito mu kuma a kan hanya muke” Likitan yace “Toh shkkn babu damuwa” daga haka ya fara rubuce rubuce yana gamawa ya mika ma Abuturrab ya amsa snn ya mike yyi masa godiya, ganin har sannan bata mike ba yace “Mu je” Mikewa tayi yana gaba tana biye da shi har suka fita office din, wajen bada allura Abuturrab ya ga abinda bai ta6a gani ba, don kememe taki yarda ta dinga rusa masu kuka a asibitin tana rokansu, hakan yasa ya koma office din likitan yasa ya rubuta magunguna kawai gaba daya ya biya bill din sannan suka fita asibitin, har sannan shesshekan kuka take, ya bude front seat ya hade rai yana kallonta a hankali ta shiga ya kulle sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, sai da suka fita asibitin yace “Kin ci abinci?” Girgixa masa kai tayi tace “Baabarmu ta ba almajiri nawa” Ya dinga nanata sunan da ta kira a ransa, wai Baabarta, girgixa kai yyi cikin ransa still yace ba dai baabarki ba, gidan wani cin abinci ya tsaya ya siya mata abinci sai malt guda biyu da bottle water, yana shigowa motar ya ajiye mata, kallon ledan ta dinga yi, can ta bude ta ciro malts din ta ajiye gefe tace “Ban iya sha ba” Yace “Sai me?” Tayi shiru bata ce komai ba, yace “Tambayarki nake” a hankali tace “Ban iya shan lemo ba ni” Bai kuma ce mata komai ba, sai da suka shigo titin hayi yace “Taron me naga aka yi a layinku daxu da yamma?” Shiru tayi sai kuma ta kallesa a hankali tace “Baabarmu ce take dukana” Da mamaki yace “Saboda me?” Ta share hawayen da ya kawo idonta tace “Dama Iyah ce tace xata sa ni a motar tirela in gudu legas don kar a min aure da Iliya, shine sai na gaya ma wata kawata da muke xuwa makarantar dare tare da ita da, don gobe Iyah tace xata kai ni tasha, sai kawata taje ta gaya ma baabarta shine baabarta ta xo ta gaya ma Baabarmu, shine Baabarmu ta dinga dukana wai xata kasheni, duk aka taru a layin….” Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Shi dai sauraronta kawai yake yi, bayan few seconds yace “Wacece Ita warce tace xata sa ki mota ki tafi lagos?” Cikin rawar murya tace “Wata tsohuwa ce a layinmu ana ce mata Iyah….” Ya kalleta yace “Har yanxu xa ki tafi lagos din kenan don kar a maki auren?” Ta girgixa masa kai hawaye na sauka idonta tace “Aa baxan je ba amma xan kashe kai na” Bai ta6a expecting jin hakan daga bakinta ba, yyi parking yana kallonta da mamaki yace “Xa ki kashe kanki?” Ta gyada masa kai, yace “Da me xaki kashe kan naki?” Cikin rawar murya tace “Piya piya xan siya in sha” Bai san lkcn da ya bude baki ba yana kallonta ganin she is so damn serious, da wani expression yake kallonta ganin she is truly depressed and frustrated, tana goge hawayen dake xuba idonta tace “Dama ae Abbana ma ya tafi ya bar ni, ba sai in bi sa ba” ya kwantar da murya yace “Amma kina xuwa islamiyya kuwa?” Ta girgixa masa kai a hankali tace “Na daina tun da dadewa, tun sanda muka fara sana’a” Yace “Toh saboda xa a maki aure kike son kashe kanki?” Ta gyada masa kai, sai kuma ta hade kanta da gwiwa ta fashe da matsanancin kuka tace “Shaye shaye fa iliya ke yi, kuma har kwaya yana sha shine Babarmu take son in auresa….” Kallonta kawai yake, can yace “To wa kika ta6a ganin ya kashe kansa sbda xa ayi masa aure da wanda baya so?” Tana shessheka tace “Akwai wata ma ai ta kashe kanta a nan hayi” yace “Shine ke ma xaki kashe kanki?” Ta gyada masa kai, yace “Toh duk sanda kika shirya ki min magana ni da kaina xan kawo maki piya piyan, kin ji ni?” Ta dago tana kallonsa tace “Toh ai ni na shirya” yace “Yaushe?” Da kyar tace “Yau da daddare nake son in sha” yace “Aa kinga ni sai yau na sani, ki bari ko xuwa jibi xan kawo maki” tana shessheka sae kuma ta sakar masa kuka tace “Yayi min nisa” Yace “Ya sunanki?” Tana kallonsa da hawaye idanuwanta tace “Jiddah” Ya d’an yi shiru, bayan few seconds yace “Jiddah…. shekaranki nawa??” Cikin sanyin murya tace “Babaarmu tace sha bakwai” yace “Toh ki jira sai na kawo maki da kaina, kar ki kuskura ki siya da kanki, kin ji me nace maki?” Ta gyada masa kai kawai, yace “Ki yi min alkawari xa ki jirani” Tace “Nayi” yace “Kina komawa gida ynxu ki ci abinci ki sha maganin ki ai nurse din ta nuna maki ynda xa ki sha” Ta gyada masa kai, tada motar yyi ya ci gaba da driving dinsa gaba daya yana kara naxarin xancenta.

 

 

‚Äč

 

 

Name: [JIDDATUL KHAIR HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


37 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published.