Hausa Novels

Jiki da Jini Hausa Novel Part 1

Jiki da Jini Hausa Novel Part 1

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*JIKI DA JINI*

 

*@HADIZA D AUTA*

 

 

Durƙushe take a bayin cikin mummunan yanayin da ita kaɗai ta san me take ji a cikin shi, tayi jiɓi sharkaf! sai uban nishi take zubawa iya ƙarfinta, tare da faɗar sunayen ALLAH a bakinta da kuma zucinta, wanda a lokacin ta riga da ta sare da rayuwa kuma ta sa a ranta ce wa ba ta da kowa sai ALLAH, don shi kaɗai ne zai iya magance mata matsalolin da ta shiga a baya, da kuma wanda take ciki a yanzu da take durƙushe tana jin tsananin azabar ciyon naƙuda, har ma da waɗanda za su biyo baya ma idan ta haihun.

 

A cikin wata siririyar murya take faɗin,. “Ya ALLAH ka fi kowa sanin halin da nake ciki, idan mutuwata ita ce maslaha ga rayuwata da ta abin da ke cikina, to Ubangiji ka yi gaggawar karɓar raina da abin da ke cikina ko da za mu huta da baƙinciki da takaici tare da ƙalubalen da zamu fuskanta a rayuwa, ALLAH kai ne gatana ba ni da kowa sai kai ALLAH, ina tawassuli da sunayenka tsarkaka a kan ka kawo mini sassauci dangane da abin da duk ya fi mani sauƙi cikin lamarina, ya hayyu ya ƙayyumu birahmatika astagisu ya ALLAH, Ya Rahamanu Arrahimu, ya mujibuddu’a’i ya malikul ƙuddusu, Assamadu, al’ahadu ya zuljalali wal’ikram……… ”

 

Cikin hikima ta Ubangiji ta ji wani ƙarfi ya zo mata tayi ƙwaƙƙwaran nishi sai ga jinjira ta ratso cikin jikinta ta faɗo ƙasa tare da mabiyarta duka, sai canyara kuka mai sauti take yi ba ƙaƙƙautawa, ta ci gaba da zuba wani kukan iya karfinta alamun shedar ce wa ga ta fa ta zo duniya.

 

Cikin magagin dawowa daga duniyar azabar ciyon ne, A’isha ta kai kallonta ga yarinyar sai ga wasu hawaye masu zafi shaa! Suna sauko mata a kan fuska, cikin shaƙaƙƙiyar muryar da ta sha wahala ta ce,.

 

“Alhmdulillah ala kulli halin”

 

Ta ja jikinta ta raɓa jikin bangon bayin tana maida numfashin wahala tare da ƙurawa yarinyar kallo, wadda har lokacin ba ta daina kukan da take yi ba, wanda sanadin kukan jinjirar ne ma ya jawo hankalin Hajiya Mariya da ke aikace aikacenta a tsakar gida, cike da kokwanto ta kasa kunne tana so ta gano ta ina kukan yake fitowa, aikuwa kunnuwanta sun tabbatar mata da ce wa tabbas daga ɗakin A’isha ne kukan jinjirar yake fita.

 

Gabanta ba shiri ya ƙire ya faɗi cikin tsananin firgici tare da ruɗewa ta jefar da bokitin da ke hannunta ta yi ɗakin A’ishar a sukwane, in da kai tsaye ta nufi ƙuryar ɗakinta tana wara idon neman ta ina zata hango jinjirar da har lokacin ba ta daina kukan ba, ganin ba ta ɗakin ya sa ta yi toilet ɗinta kai tsaye, sai ga ta idanuwanta sun hango mata abin da ya sakata jiri wanda saura ƙiris ta faɗi saboda tuntuɓen da ta yi da dakalin ƙofar bayin, don kuwa ta taradda A’ishar raɓe tana kuka gwanin ban tausayi, ga kuma ‘yar jaririyarta da ta haifo a gefe ɗaya tana ta kukan neman agaji ita ma.

 

Ta dafe ƙirji tare da zaro ido waje ta ce da ita;

 

“Aishahhhh! Me nake shirin gani ne haka?? Wayyo ALLAH ni Mariya yau naga rayuwa ganin idona,,, aure wata shida a ce har an haihu? Wannan wace irin muguwar ƙaddara ce aka haiho muna cikin gida ni Mariya???”

 

Ganin A’isha ta kasa cewa uffan saboda uban kukan da ya ci ƙarfinta ya sa ta fita da sauri, sai ga ta ta dawo da sabuwar reza ta yanke cibiyar yarinyar sannan ta ɗauko zane ta dunƙule ta a ciki ta kaita kan gadon A’ishar ta kwantar, cikin sauri ta je ta ɗora ruwan zafi cike da wata ƙatuwar tukunya.

 

Sannan ta koma ɗaki cikin tsananin tashin hankali ta ɗauko waya ta kira mijin A’ishar waton Dan’hajiya, kira ɗaya biyu ya ɗaga cikin shagwaɓar da ya saba yi mata ya ce

 

“Haba Hajiyata ga ni kan hanyar gidan fa yanzu zan zo ki bata haƙuri na siyo mata kifin da ta ce”

 

Hajiya Mariya ta yi ƙarfin faɗin;

 

“To ka yi sauri ka ƙaraso kai nake jira yanzu Ɗan Hajiya”

 

Sannan ta kashe wayar cikin sanyin jiki, da ruwan suka yi zafi ta cika ƙaton bokiti ta koma toilet ɗin in da har lokacin A’ishar take zaune tana ta cisgar kuka na fitar hankali, Hajiya Mariya ta taimaka mata ta kimtsa jikinta, saboda tsananin tausayinta da take ji har cikin ranta.

 

Amman jinjirar kam tun da ta ajiye ta kan gado bata sake bi ta kanta ba, suna zaune zugum-zugum daga ita har A’ishar Ɗan’hajiya ya shigo ɗakin cikin fara’a yana faɗin

 

“To ga ni na dawo Hajiyata a daina damuna da kira, ke kuma ga kifin na siyo miki sai a sakar mini mara hakanan na huta”

 

A’isha kukan da take yi a zuci ne ya fito fili ba shiri ta fashe da wani sabon kuka mai sauti tare da rufe bakinta, saboda tsananin takaicin halin da zai shiga idan har ya ji ta haihu saboda ta sani sarai ba ƙaramin so yake yi mata ba, yayi sororo yana kallonta baki a buɗe zuciyarshi cike da mamakin abin da take yiwa kukan, cikin sauri ya kai gwiwowinsa ƙasa ya yi durƙuso gabanta tare da ɗora hannunshi ɗaya a cinyarta ya saka ɗaya yana share mata hawaye yana faɗin

 

“A’isha me nayi miki kike kuka kums? wa ya taɓa ki bayan fitata ne? Nasan dai ba Hajiyata ba ce ko?”

 

A’isha ta kasa ba shi amsa sai ma sautin kukanta da ta ƙara rerawa, Hajiya ta miƙe tsaye cikin jajayen idonta da suka rine saboda tashin hankali, ta yi jarumtar dafa kafaɗarshi ta ce

 

“Ka yi haƙuri Ɗan’hajiya yanzu A’isha ba matarka ba ce saboda haka ka ɗauki dangana kuma ka rungumi ƙaddararka”

 

Cikin firgici ya yi saurin miƙewa tsaye yana ce wa,. “Saboda mi kika ce haka Hajiyata??”

 

Hajiya ta share hawayen da take maƙalewa sannan tace,.

 

“Saboda yau A’isha watanta biyar da sati uku a gidan nan har ma babu cikon kwana biyu, amman ta haiho yarinya yanzun nan don haka ko kaɗan ba matarka ba ce don ko da aka yi auren ka da ita tana ɗauke da juna biyu ba mu sani ba, domin wannan yarinyar da ta haifa ko a kallo ɗaya za’a gano cewa ‘yar wata tara ce ba wata shida ba”

 

Ɗan’hajiya ya zaro ido cikin faɗuwar gaba cike da ƙaraji ya ce,. “Ina yarinyar take!?”

 

Firgigit yarinyar ta farka tare da canyara wani sabon kuka mai sauti, saboda ƙarajin da yayi ya janyo ta zabura daga baccin da ya fisge ta, ta fara wutsil-wutsil da ƙafafuwa tana saka hannu a baki tana neman abincinta.

 

Ɗan’hajiya ya ƙarasa gaban gadon yana ƙarewa yarinyar kallo jikin shi sai rawa yake yi saboda tsabar firgicin da ya shiga, ya dinga nunata da hannu bakin shi yana rawa yana kallon A’ishar hawaye suna zuba akan fuskar shi, muryarshi a sarƙe ya ce da ita;

 

“Ƴar waye kika kawo cikin gidanmu Aisha!?”

 

Aisha ta sake fashewa da kuka cikin tsananin fushi ya isa wurinta ya shaƙo wuyanta yana ce wa; “Zaki faɗa ko sai na kashe ki? Ɗiyar waye na ce!? wa ya yi miki cikinta faɗa mini na cei Uban waye ya haife ta?”

 

Shaƙar da ya yi mata ce ta sa ta yi saurin faɗin “Wallahi ALLAH shine shaida ta ban taɓa aikata zina ba a rayuwata, kai ma idan zaka yi mini adalci za ka shaidi ce wa ba na bin maza tun da unguwarmu ɗaya da kai ka san komai…..”

 

Marin da ya falla mata ne ya sa ta yi shiru ba shiri, cikin zafin nama ya dinga kai mata duka ta ko’ina da ƙyar Hajiya ta ƙwaceta a hannun shi, saboda ganin zai illata ‘yar mutane ga ta ɗanyen jego a jikinta, cikin tsananin ɓacin rai yake faɗin

 

“Hajiya ki barni na daki shegiya ko da zan cire baƙin cikin da ta shuka mini a zuciya, ki duba ki ga yanzu duk adalcin da muka yi wa wannan yarinyar wai mu za ta cuta, haka kawai ta je ta kwaso cikin shegenta a waje ta kawo muna cikin gida ko tsoron Allah ba ta ji ba, ALLAH ya isa ban yafe miki kuɗina da na kashe na auroki ba A’isha, haka ma ƙwandalata da kika ci a gidan nan ban yafe miki ba, don nasan ko na ce a biya ni ba abin da zan samu a wajen baƙin dattijon ubanki, don haka kije na barki da ALLAH baƙar munafuka sumui-sumui da ke kamar ta ALLAH ashe ke riƙaƙƙiyar karuwa ce mai lasisi”

 

Ya yi kanta zai sake kai mata duka Hajiya ta yi saurin rantsewa a kan ce wa ba ta yafe ba matuƙar ya sake dukanta, ƙarshe ma janyo hannun shi ta yi suka nufi ɗakinta.

 

A’isha kam saboda tsabar baƙinciki durƙushewa ta yi tana wani uban kuka cikin tashin hankali tare da jin zuciyarta kamar ta tarwatse saboda tiririn zafin da take ji yana fitowa a cikinta, ta ɗauki lokaci tana kukan sannan wani tunani ya zo mata, ta miƙe cikin sauri duk da rashin ƙarfin jikinta hakan ta miƙe tana layi jiri yana kwasar ta, ta yi jarumtar share hawayenta da suke zubowa wasu bayan wasu, ta kai kallonta ga yarinyar da har lokacin bata daina kukan ba, ta nufi wajenta ta ɗauko ta tana ƙare mata kallo tun daga fuskarta har zuwa tafin ƙafafuwanta, saboda komai na yarinyar sak! Irin nata ne kamar an tsaga kara, hakan yasa ta rungume yarinyar jikinta ta sake fashewa da wani sabon kuka mai tsuma zucita tana ce wa;

 

“ALLAH kaine gatana bani da kowa sai kai ALLAH, kafi kowa sanin ni baiwarka ce mai tsananin biyayya agareka, mai kiyaye dokokinka mai tsantseni da rayuwar duniya, mai tsantsar tawakkali da duk halin da na tsinci kaina, Ubangiji ka ba ni ikon rungumar ƙaddarata, ALLAH ka jiɓincin lamarina da ƴar jinjirata don bamu da wani gata sai naka ALLAH”

 

Ta buɗe zanen da Hajiya Mariya ta rufe yarinyar da shi, wanda har jinin da ke jikinta ya bushe ya fara kama zanen, ta yi dubarar rabata da zanen sannan ta yi jarumtar ɗorata a bayanta ta goye ram!, ta nufi wardrobe ta janyo jakarta da take ajiyar kuɗinta na cinikin manjan da Ɗan’hajiyar ya siyo mata tana siyarwa ta tara ribar a ciki, ta cire ɗankwalinta ta ƙullesu gefe jabau!, sannan ta mayar da ɗankwalinta ta ɗaura a kai, ta ɗauko ƙaton hijabinta ta saka ta lulluɓe ‘yar shif-shif ta fito ɗakin ta nufi hanyar fita, sai dai abin da ta ji ya sa ba shiri ta ja ta tsaya, saboda maganar da ta ji Ɗan Hajiya da Hajiyar suna yi a kan ta,

 

“Yanzu zan kwasheta in kai ta gidansu daga ita har shegiyar ɗiyarta don A’isha ba za ta sake kwanar mana a gida ba, saboda ba zan taɓa lamuntar ajiyar ‘yar shegiya a cikin gidan nan ba” cewar Hajiya Mariya
Littafan Hausa Guda 1000 Download
 

Ɗan Hajiya cikin magiya ya ce da ita, “Don girman ALLAH Hajiya ki bar mini A’isha ina sonta, idan ma aure ki ke so na ƙara zan yi ni dai kawai abar A’isha ta ci gaba da zama tare da mu, kin san Baba Delu ba ƙaramar azaba take bata ba musamman yanzu idan ta koma da wannan abin kunyar”

 

Hajiya ta yi saurin rantsewa da ALLAH tans ce wa, “Na rantse da girman ALLAH ba zaka sake zama da A’isha a cikin gidan nan ba, ko bayan raina ban yafe maka ba muddin ka sake aurenta Ɗan Hajiya”

 

Hawayen baƙiciki suka sirnano wa A’isha a kan fuskarta, ba shiri ta saka hannu ta goge cikin sanyin jiki da rashin kuzari ta ja ƙafafuwanta ta fice gidan, tafe take tana sharar ƙwalla har ta ƙarasa gidansu, saboda babu tazara mai nisa a tsakanin gidansu da na Ɗan Hajiya, asali ma bai wuce gida huɗu zuwa biyar ba a tsakaninsu.

 

 

 

D AUTA CE✍🏼

Leave a Comment

error: Content is protected !!