
Hausa Novels Littafan Hausa Guda 1000 Masu Dadi
Hausa Novels Littafan Hausa Guda 1000 Masu Dadi
Zaku iya samun dukkan littafan hausa da kuke nema anan akwai littafan hausa novel maras adadi anan zaku iya saukewa tare da karantawa a kyauta anan. Akwai manhajar android ta hausa novel kyauta wadda zaku iya saukewa itama kuna iya karanta dukkan littafin da kuke so a kyauta.
Ga wani littafi mai suna Dan iskan namiji.
DAN ISKAN NAMIJI
*NA*
*FAREEDA ABDULLAHI*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
*NA SADAUKAR DA WANNAN BOOK DIN GA MAHAIFINA ALLAH KAJIKANSA KAI MASA RAHMA KASA ALJANANA*
*WANNA LABARIN KAGAGGENE BANYI DAN WATA KO WANIBA NAYI SHINE DAN FADAKARWA KAWAI ALLAH YASA MU AMFANA DA ABUNDA KE CIKINSA KOFA ABUDE TAKE GA WANDA ZE MUN GYARA KO BADA SHAWARA*
*Assalaamu alaikum masoyana wannan shine sabon novel dina kuyi hakuri cigaban arnan daji yana nan zakujini kar kuyi fushi*
*Kuyi hakuri ba kullum Zan dinga typing ba yanzu saboda uzurirrika nagode*
1-2
Mahaukacin tuki yake ko gabansa baya gani saboda tsabar buguwar dayayi tuki yake yana zuga uban gudu a bakin wani tankamemen get ya tsaya yafara danna horn ba kakkautawa a guje me gadi ya taso cike da magagi ya bude tangamemen gate a guje ya Danna hancin motar
Yai wani irin parking a karkace ya bar Motar a kunne ga security akai wani irin ihu motar take da har makota saida ta tasa a furgice suka firfito parlour nafeesat ce matar gidan da kanwarta maryam suka tsaya cirko cirko ganinsa ya shigo a bige ihu nafeesat tasaka wani ihu waye wannan maryam dubamun dakyau nagani ta karasa wajensa ta kalle shi ihu tasaki wallahi shine
Ta karaso itama wazata gani mijinta ne arfan ta fada day karfi meke damunka ka shigo a galabaice haka uwarr….ki nace nida gidana Zak……..i tambayeni meye haka gaba dayansu sun firgita amma ita maryam tabbas tasan cewa wannan warin giya ne amma bazata iya fada ba tana jin tsoro anty ki kama shi mukai shi daki inaga beda lafiya
Maryam karar nan ta dameni jeki kashe dan Allah motar sace da hanzari tafice ta tarar get din makotansu su biyu Har sun leko suna bala i megadi ya hanasu shiga yauwa kigayawa mijinki cewar dayan mun gaji da daukan hakkin mu dayake sati biyu mun huta da ya aureki amma yanzu abun ya dawo haka yake damun mu dakarar motarsa kullum bama iya rintsiwa muda iyalanmu kuma security ne a motar ko anzo ba a iya kashewa wallahi mun gaji da wannan iskancin kema kwadayine yasa Kika auri dan iskan namiji kokema hakan kike
Kuka maryam take kawai tana tausayin yayarta me hakuri ashe lumbu lumbu yai musu Dan iskane basu saniba mashayin giya baki fara kuka ba sai kin fara ganin mata na safara a gidan nan sannan zaki kuka cewar dayan wallahi kija masa kunne duk da sunaji su wasune to muma mungaji tunda bafinmu yai ba suka juya suka fice
Kuka take ganin wannan tashin hankalin a gidan yayar tata duka satin su biyu da aure yau kwananta uku saboda yayar tata tayi waya cewar yana aikin dare kwana biyu tazo tadinga tayata kwana tunda ita batasan yar aiki taci karo da wannan damuwar tayi tayi ta kashe ta kasa kiyi hakuri ki koma ciki shika daine yake iya kashewa sukuma sun dauka kece matar gidan kuci gaba dayi masa addu a
Ta juya ta koma parlour din ta ganshi ya Zara belt yabata kilar nafeesa ta kwalla kara tayo kansa ya juyo a fusace ya fada jikin ta da niyyar itama ya jibgeta sai zame ya dinga shara amai banda kuka ba abunda nafeesat keyi yagama me masifar wari wanda duka sai da suka toshe hancinsu
To Dan iska wallahi kayi kadan ka Kara aure sai nayi abunda nasaba tafita ni nazame ma jaraba matar jaraba Kai dan iskan duniya ne nima haka dan haka lawan kayi kadan cewar matarsa ummi inmaji da wannan shedancin naka mana idan baniba waze zauna Dakai
Ya sheke da dariya sai naja atu itama yar hannuce Dan nayi shi sosai kuma da kudi a hannunta sosai wajen aikinmu daya albashin ta yafi nawa kinga zamu huta sosai wallahi baka isaba bazaka aureta idan ko ka nace wallahi kaga wacchan rigiyar ciki zan fada nabarka da yaya biyar kasan yadda zakai dasu aure ba fashi wallahi sai dai kifada Dan sai nayi yarako zata rike tunda ta dade batai aureba itama yarinya muzuba mugani yasa Kai ya fice
*MASOYANA WANNAN SHINE SABON NOVEL DINA WANDA DA NA KUDINE AMMA SABODA DARUSAN DAKE CIKINSA NAFASA ZAN MUKU SHI FREE AMMA IDAN YAI MUKU ZAN CI GABA NAJI RUWAN COMMENTS KAWAI*
*MASOYANA KUTAYA MY BASH DA ADDU A ALLAH YA KARA BUDA MASA YA BIYA MASA BUKATUNSA DAYASA A AGABAALLAH YA CIKA MASA BURINSA DUK ME KAUNATA DAN ALLAH YAI MASA ADDU A BANSAN BAKIN WANIBA SHIYASA NAI MUKU FREE KU FADAKU DA DARUSSAN DAKE CIKIN NOVEL DIN SABODA NA FARANTA MUKU KUSA SHI A ADDU ARKU NIMA ZANCE NAGODE MY LIFE ALLAH YA BIYAKA YA KARA ARZIKI DA BUDI*
*Yawan comments yawan typing nice taku a koda yaushe*
*FEEDYN BASH*
DAN ISKAN NAMIJI
*NA*
*FAREEDA ABDULLAHI*
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
*BISSIMILLAHIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI GODIYA TA TABBATA GA ALLAH (SWT) DAYA BANI IKON SAKE KAWO MUKU WANNAN BOOK DIN INA FATAN ZAKU AMFANA DA DARUSAN DAKE CIKINSA*
*MASOYANA NAGODE SOSAI NAJI DADI DA YADDA KUKA NUNA KAUNARKU GA DAN ISKAN NAMIJI ALLAH YASAKA MUKU DA ALKHAIRINSA IRIN ADDU OIN DAKUKE MANA NIDA MIJINA NAGODE SOSAI ALLAH YA BAR KAUNA YASA MU AMFANA DA DARASIN DAKE CIKIN LITTAFIN*
*INA GODIYA AGAREKU ARNAN DAJI FANS 1-4 YADDA KUKE MUN ADDU A GAME DA CIWON HANNUNA NAGODE SOSAI ALLAH YA BIYAKU DA MAFIFICIN ALKHAIRINSA NAGODE*
3-4
A guje Lawan kejan motor yana tukinsa yadda yaga dama a kwalta kamar shi kadaine a titin a bakin asibiti yaja wani mahaukacin burki ganin wata tsaleliyar budurwa ya samu waje me kyau yai parking Yana Danna Mata horn ta lura da ita yake tana zuwa Bata wani yi Masa maganaba tasa Kai cikin motar ta kwame a gaba sai Ina baby
Tai Wal tana kallonsa inda zaka ya sheke da dariya harda buga gaban mota wow nice baby Ina kallonki nasan ke Yar hannuce Dan haka baki da matsala dani beb hankali kwance yake driving dinsa basu zame ko inaba sai kano club Yana parking aka Fara ihu sai Dan iskan namiji Ana tafi Yana daga musu hannu yaja hannunta suka shige ciki
Nan waje ya Kara dinkewa ga yayan iska Nan Nan aka Fara cashewa Ana watsa daloli Ana zuba ihu manyan yayan hutu suka sa gasa suka wulla key din mota duk wacce ta cafe ta Zama tata haka aka dinga rawa a club saboda club ne na manyan mutane ba na yara ba sai daya uku saura lawan ya kamo hannun beb dinsa wadda ta tafi da maza dayawa amma bame Kai farmaki saboda ta lawance kowa yasan iskancin lawan bari muji waye lawan
Iyayen sa duka sun rasu tun Yana karami yataso Cikakken Dan iskane na bugawa a jarida tun Yana karami nayaji ko kadan iyayensa bakin haurene ba asan garinsuba andai ce Yan Niger ne buzayene bayan gobara ta hallakasu dukansu lokacin lawan Yana makarantar dare gobara ta tashi da iyayensa makocinsu mallam Isa shiya karbi lawan ya tsaya Masa ya cigaba da karatunsa har yaje Jami a ya gama Amma Sam bayaji ko kadan tun malam namasa fada har ya gaji karshe malam u a kwanta dama iyalansa suka koreshi daga gidan dama ya Fara taka leda sannan yafara aikinsa nan yafara neman aure
Ya auri matarsa ta farko ta Haifa Masa da daya duka da tantagaryar iskanci yasa suka rabu daga baya ya auri ummi sunyi auren soyayya tana sansa sosai Amma ita ba Yar iska bace kaddara duk da batasan Yana Shan giyaba ta dauka kawai Dan yawace yawacene Ashe da sauran kallo bayan ta aure shi tagane zallar halinsa irin shedancin sa da iskancinsa haihuwarsu uku Amma tana zaune dashi lafiya Dan tun farko dayake jibagarta sai ta Dena fitowa idan ya dawo Dan tasan a makensa yake duk unguwar baya ganin mutuncin kowa ba Wanda besan lawan ba
Lawan Dan iskan namijine a tsakiyar unguwa yake Shan giyarsa hankali kwance saboda yana da daurin gindi manya yasan manya saboda indai zaka Sha giya Dole zakai rayuwa da manya shiyasa baya tabuwa har bindiga gareshi da ankwa kamar ma aikaci kuma ba Wanda ya isa ya kamashi sun hadu da Laila a wajen aikinsu Laila tayi karatu me zurfi Amma ta rasa mijin aure
Hakan yasa tafara Dan taba yawo daga baya shine tasamu aiki a company inda lawan ke aiki to ta fishi matsayi Amma yafita kurda kurda da sanin mutane zuwanta wajen lawan ya Fara shigemata saboda ta Masa gaskiya Wasa Wasa suka Fara shakuwa har takai ga suna Shan romon democradiyan juna ta Masa ta ko Ina shedan na karara zuzuta musu wutar San juna tasan lawan tantirin Dan iskane Amma a haka ta daure ta ce siyi aure shima ya yarda da haka dan albashinta me tsokane yadinga karbewa
Tajewa iyayenta da maganar auren lawan Sam basu amince dashiba saboda mutanene na gari Amma ta rantse idan basu Bata shi ba komai ze iya faruwa har ruwan ta daga itama tana musu tanbele Allah ya shirya iyayen sukaga tunda hakane gwara a aura Mata shi antsaida ranar bikin da komai inda hankali kwance da zuciya daya zatai auren ta saboda tadena sabo tayi alkawarin Zama da kishiyarta lafiya
An dawo labari lawan be zame ko inaba da wannan budurwar sai darbur hotel anan suka yada zango suka dinga murzar juna kamar ba gobe Dan lawan ya iya sarrafa mace haka yadinga lasheta Yana Shan gabanta ko Ina sai da ya side a jikinta yagama tafiya da ita Dole ta like Masa koba ko sisi haka suka kwana suna shedancin sai da safe sannan suka samu damar rintsawa ba sallah ba salati
Karanta Littafin Matar Yaro Hausa Novel Complete
Maryam na kuka ta ringume nafeesat anty lafiya me kikai Masa yadinga jibgarki haka Maryam arfan mashayin giyane ya cucemu ya cuci rayuwarmu Ashe Dan giya aka aura mun iyayenmu mutanen arziki basu dau duniyar a bakin komai ba sun bashi Ni saboda Allah badan dukiyarsuba saboda San da mukewa juna Ashe Dan giyane kuka take kamar ranta ze fita dakyar Maryam ta rarrasheta kiyi hakuri anty jarrabawace kowa da kalar tasa kitai Masa addu a
Kamashi mukai shi dakinsa sai na gyara wajen mu kwanta Taya ya barci ze yiwu Maryam kinajin wannan muguwar karar motar me Shirin fasa dodon kunne naji anty Nima tadameni Amma yazamiyi ya muka iya Dole hakuri zami zuwa wani lokaci tukun idan ya farka ya kashe
Haka suka kinkimeshi suka kaishi dakinsa Yana wani mugun wari jikin nafeesa rudu rudu da duka haka Maryam takai ta daki ta kwantar tabata paracetamol duk da tasan cewa bazata taba iya bacci ba saboda wannan karar motar ga Kuma tunanin halin da mijinta ya fada ta kasa cewa komai kawai saida safe tace ta dawo parlour ta kwashe Aman ta goge wajen tana tausayin yayar tata gaskiya gida zata koma gobe bazata iya wannan rayuwar ba
Alhaji ghali ya kamata Kai aure kodan idon mutane saboda a dinga ganin Ana shiga da zuka zukan maza Yara matasa gidanka za a zargi wani abun za adingaima wani kallon duk da kaidin kwallon Dan iskane me basaja me sadaka me zakka me kula da marayu Amma daga gefe Kai kwallon Dan iskane basu saniba basusan duk da kudin Haram kake hidimta musu ba suka kwashe da dariya suka tafa shege alhaji atiku ai duk jirgi dayane ya debomu
A a da bambanci danni inada iyali Kai kuwa duk wadda ka aura sunanta sorry Dan baka taba yarda ka haihuwa ba Dan a ciki sawa a burgeshi Kai da mace sai kallo Ni kuwa inada Yaya na Amma dai duk kanmu Yan iskane ko waye nagari a cikinmu suka sheke da dariya suka tafa
*ANAN ZAN DAKATA SAI NAJI COMMENT DINKU YAWAN COMMENT YAWAN TYPING NICE TAKU AKODA YAUSHE*
*FEEDYN BASH*
[DAN ISKAN NAMIJI
*NA*
*FAREEDA ABDULLAHI*
*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
*TALLA TALLA TALLA*
*AKWAI SABON BOOK DINMU WANDA ZEFARA ZUWAR MUKU BADA DADEWA BA ME SUNA ANNOBAR SHEKARA ANZUBA ILIMI DA FASAHA WAJEN TSARA WANNAN LABARI LABARINE IRIN WANDA YA SHAFI ABUBUWAN DASUKA FARU ADA KARKU SAKE ABAKU LABARI*
*~RUBUTUN MUTUM BIYUNE KARKU SAKE A BAKU LABARI DA ANFARA TYPING DINSA KUYI HANZARIN FARA KARANTASHI LITTAFINE DAYAZO MUKU DA SABON SALO NA MARUBUTA MUTUM BIYU~*
*FEEDYN BASH & HAFCY SMART*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI*
5-6
Arfan ne yafarka yagan shi kwance akan gadon dakinsa na kasa ga masifar Kara da motarsa keyi waya kawoshi Nan da sassarfa ya fice yaje ya kashe motarsa ya kulle hankalinsa ya tashi yaja wani shegen tsaki mtswww wallahi beb yau sainaci ubanki tunda kika sa nai wannan muguwar buguwar nazo gida ahaka bayan mata ta bata san ainihin halina Ba dole kici ubanki yau duk san danake miki kuwa cike da kunya ya shigo yana sanda Ba kowa a parlourn da Sauri yahaye samansa
Duk iskancin arfan yana sallah Koda ba akan lokaciba da hanzari ya shiga toilet ya tsarkake jikinsa ya fito ya zira jallabiya ya tada sallah da ya idar ya koma ya kwanta Dan baze iya sauka kasa wajen nafeesat Ba bayan jiya taganshi a ainihin halinsa daya boye Karin takaicin ma ga kanwar ta a gidan mtswww tsaki yaja yama kasa baccin tunani kawai yake gaskiya beb kin cuceni amma dole kici ubanki yau saida nagaya Miki bazan shaba kozan Sha kadan zansha sai da Kika yaudareni nasha meyawa
Jiyai an bude kofar rintse ido yai bayasan suhada ido kunyarta yakeji duk da yasan shi cikakken Dan iskane wanda kaf garin kano ansan dazam alalace indai yarone Kai me tashe kana chilling Dole kasan alalace ko mace ko namiji amma matarsa kamilace ya sameta cikakkiya dole zeji nauyinta na boye mata ainihin halinsa da yayi ta zauna kusa dashi Tai Masa magana yai shiru kawai ta fada Kansa tanata kuka menaima haka meyasa kasha giya bayan kasan haramunce har ka dakeni duka ya furta eh kadakeni jiya kalli jikina ta bude masa yasan yadake ta amma besan yai tsamari hakaba
Ya kamota ya matseta gam a jikinsa dear kiyi hakuri bansan cewa giya bace ni bansantaba kawai muna meeting ne sai aka kawo mana kinsan manya sun dauketa tamkar ruwa bansan ita bace sai bayan nagama sha naji suna zancen shine nafita daga hankalina kawonima akai (kuji karya fans waibema santaba Allah ya kyauta) amma kiyi hakuri haka bazata sake faruwaba kinji dear nan yayi ta shirga mata karya yana kalallameta da dadin baki ta yarda dashi bata Kara cewa komai Ba a haka harsuka sauka tahada musu break sai 12 yafita kasuwa
Lawanne kwance a daki yanata sharar bacci shida yarinyar daya samo a kwararo kiran wayar shine ya tashe shi laila ce ke kiransa tagaya masa yagayawa ummi zata aika kannenta sukaiwa su ilham kayan data siya musu cike da murna yace to Ba matsala zangaya mata nan suka danyi hirarsu yarinyar ta motsa yai Sauri yai mata sallama ya kashe wayar chan laila tayi kasake da waya a hannu cike da zargi Anya Ba’a hotel yakeba taji dakin yana amsawa tunda sun Saba zuwa gata da dankaren kishi itama chab amma tabasar kawai tarabu dashi Tafarka ya jawota jikinsa yanata shafata bari nakira uwar gida ko zan gaya mata sako
Ya Kira ummi yagaya mata zatai baki begaya mata ko suwace Ba Itama bata tsaya tambayarsa ba Dan acike take dashi iskancin yadawo kenan yadena kwanan gida tunaninta be kawo komai Ba ta dauka kawai irin Matan abokan sane ko kuma da abokansa zezo nan ta hau girki harda siyo kankara ta hada lemonta me dadi lawanne yaja beb dinsa me ruwa da dadi suka Kara komawa ruwa sannan ya dauke ta suka fita yabata kudi me kauri ya sauke ta a bakin asibiti ta gangara unguwarsu zage shima yaja motarsa zuwa mazauna yana zuwa yatarar ummi tagama komai Sai gidan nan tsaf sai cin kunu take
Mtswww sai yanzu Kaga dama kadawo yau me kwanace kenan to a ina ka kwana kedai bari kawai abokinane ya rikeni na kwana a wajensa matarsa ba lafiya a asibiti muka kwana kwafa tayi ta wuce daki cike da takaici Dan tanada masifar kishi ita iskancinsa baya daga mata hankali kamar neman mata kamar bunsuru ita kuma ga kishi daze hakura yaita shaye shayen ita bata damuba Tunda tana sansa zatai tai masa addu’a har ya shiryu dakinsa ya wuce bacci ya kwanta yadingayi Ba sallah Ba salati sai wajen 3 saigasu rahma da amira sunzo kawo kayan da laila tasiyawa yaran
Cike da farin ciki ta fito jin sallama Tasan bakintane turus tayi ganin yammata kyawawa su biyu ku lafiya meya kawoku gidana gabanta na faduwa saboda lawan na nan tasan mugun Dan iskane yana kyalla ido yaga wayannan sai ya bisu sukai dariya aikomu akai Ba angaya miki zamuzoba jin sunce aikosu akai yasa tadan saki fuska suka shiga dakin ta kallesu yammata daga ina suka gaisa rahma ce tace mu kannen laila ne wacce fa bangane taba wadda megidan nan ze aura aikomu tai mukawowa su ilham kaya zuciyarta kamar zata fashe har wani dagawa take
Suka bata kayan ta karba ta bude kayane masu kyau da tsada kayane da takalma gaskiyane nagode ina zuwa ta shiga dakin lawan cikin sanda ta dakko dorinar dukanta ta boye yanata bacci besan metakeba ta koma dakinta ta dakko almakashi ta zauna abakin kofa ta jawo kayan tadinga tsargasu Tana yankasu guyin guyin Ta faffarke takalman kallon kallo ake tsakanin rahma da amira toko bata da hankaline mahaukaciyace Basu saniba tasan tsadar kayan kuwa suka zuba mata ido kaf na yara biyar dinnan saidata gama lalatasu sannan ta mayar Leda
Ta mike ta dakko dorinar data boye a waje ta rufe kofar tafara jibgarsu nan suka fara ihu ga bame ceto a bacci yaji ihu kamar na manya bana yaransaba ya fito yaga ta kulle dakin tanata jibgarsu Tana bala I nizaku kawowa kayan asiri nizaku asirce nida yarana a auren miji zakuci ubanku kuje kugaya mata gidana yafi karfinta gidana nakabarta ne agareta Idan tasake ta shigo sai dai buzunta idan Tana musu tashigo da hanzari ya daki kofar ta bude ya riketa tahaukace ko gani bata yi sosai saboda masifa da kishi Da gudu suka fito ta kwace a jikinsa ta dauki ledar da gudu da takalmansu ta bisu kofar gida ta watsa musu ku kaimata kugaya mata huKuncin danai muku ku kanku kannenta yan aike bare ita idan tazo
Alhaji ghaline tafe a mota yanata sake sake yazo dai dai round din baban gwari yagansu su biyu a tsaye dayar ce taja hankalinsa medan jikin yar duma duma yai parking yammata ina zakune da Sauri siririyar zamuje party din candy dinmune nan bokabo ok Ashe Ba nisa kozan iya rage muku hanya sosai kuwa dama munrasa abun hawa munyi tafiya me nisa tundaga kofar mazugal mun gaji sai dai ke ki shiga amma nibazan iya shigaba haba kawata daure muje kinga Ba nisa ke kika Ki yadda mu karasa da kafa kikace kingaji daure kawata
Wuf ta bude motar ta shige gaba abunma mamaki ya bashi Da dariya dakyar ta shiga sai daya sa baki ya lallabata sannan ta shiga baya yaso itace agaba amma hakanma yayi tunda tayarda ta shigo yammata meye sunanku ne ni sunana Alhaji ghali ina zaune a rijiyar zaki danbare charaf tace ni sunana nauwara ita kuma kawata maimuna wow nice name gaskiya nauwara kin burgeni yadda baki da wahalar sabo allah ko ta fada tana wani kada ido allah hakane amma gaskiya nakamu da san kawarki tunda nai mata kallo daya gashi bata magana Kuma nasan ba kurma bace kan uba tafada a ranta wallahi baze yiwuba Kayi kadan kasota gani tafada a ranta
Au maimuna wai ai tanada wanda suke soyayya shikadai take kulawa shiyasa kaga bata kula kowa ansa musu rana ne a’a andai kusa angama zanje na nemi izini Kawai a gidansu nan nauwara ta hade rai tacika tai dam saboda bakin ciki da hassada wallahi bazata taba bari ya auri maimunaba sai dai ya aureta ita itako maimuna jitai ta tsane shi tundaga kallon farko datai masa mezatai dashi wani bulele dashi ga uban tumbi ya ajiye tsaki taja lafiya maimuna inji Alhaji ghali tai masa banza Bunden nasauka kwagama maganar idan nasauka maganar ai takice bakiga tun dazu nai parking ba inajiran mugama magana na sallameku kidaure kiban number dinki
Motar ta bude ta fice ta barsu shida nauwara kitemaka mun nauwara zan iyayin komai saboda kawarki ta tafi dani gaba daya mekike tunanin zefaru idan na rasata Zuciyata zata iya bugawa shiru tayi zuciyarta na Kuna yimin kwatancen gidansu nan tahau yimasa na gidansu zuciyarta cike da hassada da kyashi rafar dubu Dari ya bude Jakarta yasa mata gabanta ya fadi haka yake da kudi zece yanasan wata kawarta wallahi basu isaba dukansu kidena mamaki ban miki komai ba indai kika shawon kan kawarki to tace masa kawai ta fita ungu kibata itama rafar dubu Dari ce gaba daya mutuwar tsaye tayi takasa gaba takasa baya haka ta tsaya kamar gunki yaja motarsa yai gaba yabarta.
Jikina ya keso
E
Wow
Wow
hausa novel
DAN-ALLAH.GOBARAR.GEMU
pls inaso asani grp whtapp idan akwai 08161536075
Dan allah dangi daya
Masha allah
Good
masha allah
Masha Allah
Nice one
Masha Allah
it clear
Mekikaganine
NICE THANKS U
ASlm
A
MUNGODE
Nice
YAYI KYAU
Tnx
Gaskiya mugodae
Wow
Aslm Dan Allah inaso Miji Babata
Aslm allah yakara basira
Allah ya karrabasera
KAZA MAI EYEEY ETA KI SURUN SHERWA