JININ ABBA NA COMPLETE HAUSA NOVEL
KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…
Zazzau ne suke shida mahaifinshi da mahaifiyar shi , suna hira cikin jin dad’i momyn Haruna ta mik’e ,domin d’auko plet a kitchen, fitarta keda wuya ,su dady suka jiyo k’arar alamun ana harbi , da gudu momy ta dawo ,dady yace ”barin lek’a momy na kiranshi amma ina yatafi ,yana zuwa aka harbeshi a k’irjinsa , daganan ya kwanta ciwo tundaga ranar yazamo bashida lafiya.”
Gidane babba kai dakaga gidan zakasan nera ta zaune , 6angare biyu ne a cikin gidan kuma duka komai nasu kala d’aya ne, wa da k’ani ne a cikin gidan ,wato da Alhaji Haruna da Alhaji Bashir ,suntaso cikin kulawa da tarbiya mai kyau , Alhaji Haruna shine babba yaro ne ga Alhaji muntari shikuma Alhaji Bashir d’ane ga Alhaji Yusif , Alhaji Muntari yayane ga Alhaji Yusif , y’a y’an nasu suntaso cikin wadata da k’aunar junansu a fili kenan ,komai ‘iyayen zasuyi tare suke yimusu haka iyayensu mata ma basa ban banta komai nasu a tare suke yimusu , wata rana Alhaji Yusif ya kwanta rashin lafiya ashe cutar ajali ce , Allah ya k’ar6i abinsa , yabar Haruna ,a hanun Alhaji Muntari , kulawa Alhaji Muntari kebawa y’ay’an duka biyu , sai dai ‘iyayen mahaifiyar Haruna sun ,buk’aci da koma gida tunda ta tafi bata sake wai wayar gidan ba ,dukansu suna zaune a Kano unguwa uku , Alhaji Muntari yanada budurwar y’a fara kya_kyawa da wuya ta wuce bataja hankalin jama’a ba y’ar gata kenan kome ta fad’a shiza’ayi babu tangard’a , mahaifin Haruna yafi na Bashir kud’i dan haka ,maman Haruna da rasuwar mahaifinshi ta dank’awa Mahaifin Bashir komai hakan ba k’aramin dad’i yayi masa ba saboda yana facaka da dukiyar d’an uwan ‘nasa.”
Tun da mahaifin Haruna ya rasu rayuwa tayi masa k’unci bashida walwala a cikin gidan bare yasake suyi wasa da Bashir , tsangwama harara kyara babu wanda bai saba dashi ba , shine yake yiwa wanan budurwa mai suna Fauziyya wanki ko pants da bra ta cire shine meyi mata wanki tun yana kuka haryazo ya saba , lokacin da yacika shekara goma yafara bijirewa umar ninsu, a lokacinne daga uwar har y’ar suka tsiro da wata azaba ta musamman da suke gallaza masa.”
Yanzu kam banbanci ya wanzu tsakaninsa da d’an uwansa yasan ba d’aya suke ba , yafara sanin hankalin kansa ,shiyasa yafara ja baya da komai na gidan baya zuwa inda ba’a kirashi ba ,hakan da yakeyi yasa suka fara kiransa magulmaci a cewarsu yayi gadon munafurci , bashida bakin magana sai dai yabisu da ido ,hatta makarnta an ban bantasu boko da islamiya kowa da tashi .”
Alokacin da Haruna ya cika shekara goma sha takwas ,baya barin bashi ,amma ya maida hankalinsa ga karatunsa , baya wasa ko kad’an gashi Allah ya hore masa ilimin islama dana boko ,bashida mugunta ko k’an amma yanzu yafara koya kasancewar ya taso cikin rashin jin dad’in rayuwa..]
KU SAUKE CIKAKKEN LITTAFIN ANAN KASA👇👇👇
Name: | Jinin Abbana |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML |
Uploaded By: | MYNOVELS.COM.NG |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books |
Groups/Writers: | Billyn Abdul, Benaxir Oumar, Eyshat, Nadia Buhari, My Novels, Zamani Writers Association, Exclusive Writers,Alheri writers,Best Hausa Novels |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | July, 2021 |
Leave a Comment