JININ HAILA: ABUBUWAN DA SUKA KAMATA KI SANI KAN AL’ADA DA DAUKAR CIKI
KASHI KASHI HAR KASHI BIYAR 5
GA KASHI NA DAYA (1)
A wasu lokutan matsalar rashin haihuwa ga ma’aurata na samo asali ne daga rashin fahimta kan batutuwa daban-daban da suka shafi yanayin jikin mace, ciki har da ovulation, wato lokacin da ƙwan haihuwar mace ke ƙyanƙyashewa.
Galibi mutane sun san lokacin jinin haila wanda mace ke yi a kowane wata, sai dai kalilan ne kawai suka fahimci lokacin da ƙwan haihuwa ke ƙyanƙyashewa, wanda hakan na faruwa ne kwana 14 kafin zuwan jinin haila.
Ovulation shi ne fitar ƙyanƙyashewa.wai daga mahaifar mace zuwa wuyan mahaifa wanda ya ke ƙyanƙyashewa idan ya hadu da maniyin namiji a lokacin jima’i.
A cewar ƙwararru kan haihuwa, ovulation shi ne lokacin da mace ke ɗaukar ciki a lissafin lokacin ganin hailarta.
”idan namiji da mace suka sadu kwana guda zuwa biyu kafin ovulation, mace za ta ɗau ciki.”
Kamar dai yadda kowace mace ke da lokacin ganin hailarta, haka zalika kowace mace na da lokacin da take fitar da ƙwan haihuwa.
*KASHI KASHI HAR KASHI BIYAR 5*
*GA KASHI NA BIYU (2)*
Misali, idan kina ganin jinin haila bayan kowane kwana 26, sannan hailar na zuwar miki ranar 2 ga watan Agusta,(2021) ki sake ganin wata ranar 29 ga watan Agusta, to ranar fitar ƙwanki ko ovulation shi ne 15 ga watan Agusta.”
”Wasu mata na ganin jinin haila bayan kwana 26, wasu kuma 32.”
”Macen da ke ganin haila bayan kowane kwana 24, ƙwanta na fita a ranar ta 14, yayin da su kuma masu ganin haila bayan kwana 32, ƙwansu na fita a rana ta 18.”
Da fari, kowace mace ana haifarta da ƙwayaye miliyan daya zuwa miliyan biyu.
Idan ta kai lokacin balaga, ƙwan na fita a kowane wata a matsayin haila idan macen ba ta sadu da namiji ba.
wasu mata na ganin digon jini, rikewar mara ko zugi na miniti 1 zuwa sa’o’i 24 amma dai baya wuce sa’a 24.”
Wata mata da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida cewa ”a lokacin fitar ƙwaimamana na kumbura da nauyi.”
Sai dai ba duk mata ke fuskantar abu iri guda a lokacin fitar ƙwai ko yanayin ya zo musu guda ba ko kuma lissafin lokacin fitar ƙwan ya zo daya.
*KASHI KASHI HAR KASHI BIYAR 5*
*GA KASHI NA HUDU (4)*
3. Amfani da abin gwaji
Akwai abin gwaji da za a iya amfani da shi wajen lissafi a lokacin da mace ke tsintar kanta cikin sauyin ƙwayayenta ko fitar su. Wannan yanayi idan an gwada ana iya ganewa sa’o’i 12 zuwa 36 kafin ta saki ƙwai.
A cewar wani likitan mata, Olusegun Akeredolu, amfani da abin gwaji, ”kana iya gwada fitsari ko yawu domin duba lokacin fitar kwai.”
”Idan ka ga ya nuna layi biyu kamar yadda yake nunawa a lokacin gwajin ciki, hakan na nufin kina kan lokacinki,.
4. Fitar ruwa daga gaban mace
Daga lokacin al’adar farko zuwa na gaba, yanayin fitar ruwa a gaban mace ya kan bambanta.
A cewar wani shafi da ke bincike kan lafiya, MedicalNewsToday, al’adar mace na iya zuwa kwanaki 1 ko biyar kafin lokacinta.
Abin da ke fitowa daga gaban mace galibi jini ne.
Bayan kammala al’ada da kwana 5 zuwa 10, ba a samu fitar ruwan a gaban mace.
A lokacin fitar kwai (kwana na 14), ana samun karuwar jikewa da fitar ruwa mara kauri da kala.
Idan ruwan da ke fita a gaba ya kasance mara kauri, ruwa-ruwa to ya kamata ki gane cewa lokacin ovulation ɗinki kenan.”
Bayan fitar ƙwai akasari daga rana ta 14 zuwa 22, gaban mace na ɗan bushewa. Fitar ruwan na kasancewa kaɗan amma daga baya yana ƙaruwa.
Haka zalika a wasu lokutan mace na fitar da ruwa kwana daya ko biyu kafin ganin jinin ala’adarta.
Sai dai kuma duk da waɗannan hujojji, cututtuka irinsu Maleriya da sanyi ko gajiya na tasiri ga fitar ƙwan mace.
*KASHI KASHI HAR KASHI BIYAR 5*
*GA KASHI NA BIYAR (5)
Dalilan da suka sa lissafa lokacin fitar ƙwai ke da muhimmanci
Rike lokacin fitar ƙwai ko ovulation na taimaka wa ma’aurata sannan lokacin daya dace da daukan ciki, don haka sai su tsara yadda saduwar su zata kasance a wadanan ranakun.
Idan mijinki baya nan ko kuma kina auren mai mace sama da guda, akwai bukatar ki tsara yadda saduwa da miji zai zo daidai da wannan lokaci.”
Idan ba haka ba, ma’aurata da ke rayuwarsu su kadai, ma’ana babu kishiya suna iya sadauwa akalla sau uku a sati, da kuma tarar lokacin fitar ƙwai idan suna neman cikin,
Hakan na kuma taimakawa da tsarin ƙayyade iyali kuma ma’auratan da ke gudun haihuwa suna iya ƙauracewa saduwa a lokacin da mace ke cikin wannan yanayin.
Sannan, lissafa ovulation na taimaka wa mace sanin lokacin zuwan al’adarta na gaba don haka tana iya shiryawa saboda gudun abin kunya kamar ɓallewar jini a cikin mutane.
_Manufar Mu A Kullum Itace Domin Wayar DA Kan Al’umma.
Leave a Comment