Hausa Novels

Jinkirin Aure Hausa Novel Complete

Jinkirin Aure Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: JINKIRIN AURE

 

*_Ƙalubale ga ƴammata_

 

 

 

*By*

 

 

 

*Oum Hairan*

 

 

 

*Dedicated to*

Dr Mass Agadas son so for ever.

 

 

 

*P 1-2*

 

 

Iska ce ke kaɗawa ta damuna me cikakken sanyi da sanya zuciyar da take cikin kwanciyar hankali a nishaɗi, yayin da zuciyoyin da suke cike da zullumin damuwa suke kasancewa da sassaucin yanayi.

 

Saidai a gurinta itan wannan yanayi yafi mata kowanne yanayi zafi, rayuwarta ta ƙuntata hawayenta ya yawaita ƙuncin zuciyarta ya ƙaru a yayin data keɓance kanta ita kaɗai a madaidaicin office ɗin nata me ɗauke da table me kujera ɗaya, gabanta cike yake da files-files na petiant ɗinta na yau data gani inda gabadayan hankalinta yabar gangar jikinta a zaune saman kujerar lokaci zuwa lokaci hawayenta ba diga saman takardar dake gabanta.

 

Ƙwankwasa ƙofar akayi har karo uku dake hankalinta baya jikinta batasan anayi ba, jin shirun ne yasa me neman izinin turo ƙofar tare da sallama ta shigo cikin office ɗin ta tsaya ta zubawa Mamallakiyar office ɗin idanu tana mamakin abinda yake sanyata shiga matsananciyar damuwar da har hankalinta yake gushewa haka.

 

 

 

 

Dukan Table ɗin Dr Zaheera tayi abinda ya dawo da wadda ke zaunen cikin nutsuwarta tayi saurin sa handcap ta share idanunta ta ɗagosu ta zubasu kan Dr Zaheera itama ita take kallo harta isa ga wata kujerar ta zauna suna facing ɗin juna.

Dr Zahira ce ta kawar da shirun da cewa “Kullum kin kasance cikin damuwa kin takuri kanki kin tsawwala kanki Dr Madinah meye yasa hakan ne? Meyesa kike mantawa duk abinda ba’a fareshi akanka ba bazaa ƙare shi akanki ba?”

 

Manyan fararen idanunta ta lumshe ta kwantar da kanta saman kujerar da take kai hawaye na tsiyaya daga kwarmin idanunta tasa tisue ta goge dogo hancinta

“Meye ne matsalata meye ne aibina meye yasa kyawuna ya kasa samar min da mijin aure, meyesa kullum al’umma basamin adalci suke ganin cewar nice naƙi aure bayan Nima nafi kowa son na ganni cikin dausayin sunnar ma’aikin Allah???

 

Tambayar da kullum nakewa kaina kenan”

 

 

 

Cewar Dr Madinah dake ɗagowa tana zuba idanunta akan ƙawarta Dr Zahira, shiru Dr Zahira tayi na ɗan lokaci sannan ta buɗe baki tace.

 

“Dr Madinah ba jama’ar gari da suke ganinki daga nesa ba ni kaina da nake da kusanci dake lamarinki yana bani mamaki gani da sani a damuwa da tunanin meye dalili? Madinah kyawunki yakai ace kina juya ragamar maza a hannunki sai kuma ya kasance maza sune ƙaddararki, ta yaya zan yarda ace mu da bamu kai ba maza na zumuɗi akanmu ke da kika wucce kice babu wanda ya taɓa cewa yana sonki?”

 

 

 

 

Murmushi me ciwo Madinah tayi tana kai dubanta ga agogo ta miƙe ta fara harhaɗa files ɗin ta sanyasu wajen adanasu ta ɗauki jakarta ta dubi Dr Zahira tayi gaba tana cewa “duk sanda na tsaya tuntuntunin abinda kike tunani yanzu Zuciyata zafi takeyi Zahira ni kaina na fara tsoron kaina ina tunanin to ko wani abune ke gareni abin gudu da Ni na kasa ganewa, Zahira shekaruna sun fara tafiya a matsayina na ɗiya mace ba namiji ba ace na zubar da shekaru talatin da biyu batare da aure ba wannan abu da cin rai yake…..”

 

Isa sukayi bakin titin suka tari ɗan sahu suka hau ya fara sauke Zahira a kwanar unguwar su sannan ya wuce da Madinah tasu unguwar ya sauke ta ta fito tana gyara mayafin data yafa saman uniform ɗinta na aiki ta nufi unguwar tasu lokaci zuwa lokaci suna gaisawa da dattijan unguwar dake zaune a ƙofar gidajensu.

 

 

 

Gidansu ta shiga da sallamarta babu kowa a tsakar gidan hakan ya bata damar nufar ɗakin mahaifiyarta ta daga labulen tana cewa “Ammi sannu da gida” Ammi dake zaune a tsakar ɗakin ta ɗago tana duban tilon ɗiyar tata mace tace “Yawwa Munau Jaɓɓama” guri ta samu ta zauna tana yage mayafinta tace “Yau na gaji da yawa Ammi me kuka girka mana?”

 

Numfashi ta sauke tace “Abinda kika tsana” dafe kirji tayi tace “Nashi na Ammi don Allah meye yasa kukayi alale?” Tana maganar tana kwalawa me aikinsu kira Bintalo ta ta rusuna a gabanta tace “meye kikeyi Binta?”

 

Tana wasa da yatsunta tace “bsbu abinda nakeyi Uwarɗakina” fasali taja tace “ki samamin abinda zanci insjin yunwa gashi ku kun tashi kunyiwa mutane Alele” miƙewa Bintalo tayi ta fita bata ba ta dawo ɗauke da tire shaƙare da kwanuka ta ajiye mata a gabanta ta fara budewa tayi murmushi tace “wato wanani Ammi kikayi niyyar yi ashe ma My Favorite kukayi” murmushi Ammi tayi ta zuba mata ido tana kallon yanda take cin abincin a nutse da alama yunwa ta yini da ita yau.

 

 

 

 

“Munau” Ammi ta kira sunanta ta ɗago tana ajiye cokalin ta mayar da hankalinta ga mahaifiyar tasu Ammi tace “Wato Madinah kullum da wannan tunanin nake kwana nake tashi kullum da tunanin lokacin aurenki nake bacci nake tashi Madinah kullum shekarunki tafiya sukeyi girma ƙara sauko Miki yakeyi ke kuma abinda yake aranki shi kikeyi baki tunanin gobenki kin kasa tsayar da hankalinki ki samarwa kanki abokin rayuwa ki inganta kanki, Munau meye ne a gabanki daya danni sunnar ma’aikin Allah da tunaninki baya baki dacewa da cancantarki na kiyi ta? Aure shine martaba da mutuncin kowacce ƴa mace aure shine daraja da ƙimar kowacce mace ke ba iya mace ba hatta namiji aure shine ƙimarsa”

 

 

 

 

Idanunta da suke tsiyayar da hawaye ta sadda ƙasa taci gaba da kukanta me tafasa zuciya, wannan ya tashi hankalin Ammi tace “Ina mamakin yanda da zaran nayi Miki magana akan ingancin rayuwarki kike sanyani a gaba kinamin kuka Munau idan har maganar da nakeyi Miki ce bakiso zan iya tattarawa na daina amma ki sani da gaske ganinki a gabana bayamun daɗi kamar kowacce uwa Nima nafison ki rinƙa zuwar min da yawo kina komawa ɗakinki”

Karanta Littafin Gidan Uncle

Hannu tasa ta tsane hawayenta ta ɗago cikin raunin murya tace “Wlh Ammi kullum ina addu’a mafarki da fatan zuwan wannan ranar amma taƙi zuwa, Ammi ya zanyi wannan rana tazone? Nima na zama matar aure cikakkiyar mace me ƴanci sannan me ji da alfarmar aure, Ammi ki daina ganin laifina kiyimin addu’a don Allah kema gani kikeyi kamar nice banason aure bayan auren ne yaƙi zaɓata Ammi kinsani tun kafin wannan lokacin wallahi tallahi bansan wani namiji ɗaya daya taɓa tarata ya buɗe baki yacemin yana sona koda wasa ba bare da aure, wai Ammi ya akeyi ake samun mijin auren nan ne Nima nayi ko na samu ki daina kallo na a me laifi….”

 

 

 

 

Ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka me gunji tare da kifa kanta a kafaɗar Ammi, cike da tausayawa Ammi ta shiga bubbuga bayanta da sanyin yanayi na mahaifiyar da taga ɗanta cikin halin tsanani tace “Shikenan Munau na fahimceki ki daina kukan haka Allah yanaji yana gani zai kawo mana mafita da yardarsa zanci gaba da yimiki addu’a kema karki gajiya wannan ita ce ƙaddarar mu, yawwa ɗazu baffan ku Sunusi yazomin da maganar haɗin aurenki da ɗan uwanki Khamal…”

 

A firgice ta ɗago tace “Ni kuma Ammi habadai Khamal kin manta waye Khamal Ammi ƙungurmin ɗan taba sannan ɓarawon kaji da awakin unguwa ace shine mijina? A’a nikam wannan zaɓin baimin ba nidai a tayani da addu’a nasan Allah bai manta dani ba Ammi”

Leave a Comment

error: Content is protected !!