Hausa Novels

Juhud Hausa Novels Complete

Juhud Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Juhud Hausa Novels Complete

*(OUM HAIRAN)*

 

 

 

*(LOVE AND ROMANTIC STORY)*

 

 

 

 

*FP ONE*

 

 

*Tunatarwa*

Abubuwa kan faru da yawa mabambamta a zahiri makusantan juna a badini haqiqa qaddara abace dunqulalliya wacce hange da tunanin mai tunani baya iya hasaso abinda zata wanzar tana fadowa ne bakatatan cikin rayuwar mumini, abin buqatar kawai shine ka rungumeta a yanda tazo maka ka godewa Allah a duk halin da kake ciki.

 

Juhud

 

 

*Tsokaci*

A magana ta gaskiya littafin JUHUD labari ne da yake dauke da bangarori na rayuwa banyi don wani ko wata ba duk wanda yaga labarin yayi kama da wani part na rayuwarsa to arashi ne kawai aka samu da fatan zaku fahimceni.

 

 

 

*Farkon Labari*

Dauke da tulun ruwan wata matashiyar bafulatana ce da qiyasin shekaru bazata wucce 16 years ba tafe take tana sassarfa da alamun ruwa ta debo kuma tana sauri ne domin kaishi masaukinsa, tafiya take a hankali cikin yanayin jigata har ta fice daga cikin garin ta shiga daji tana tafe tana sauri hankalinta yayi gaba zuciyarta tana ga abinda ta baro a gida.

Tafiya ce ta kilomita biyu daga cikin garin zuwa rugarsu tana tafe haki harta fara hango rugar tasu taja fasali ta qarasa ta aje tulun ruwan ta shiga bukkar da gyatumar tata take kwance tana kalkade jikinta tace “sannu Innatu ya jikin?” Bude ido matar dake kwance bisa gadon kara da aka dorawa katifar yayi tayi ta zubasu akan yar tata ta daga mata kai alamar jinjinawa. Zama tayi a qasa zama irin na raquma ta dauko kofin silver data zubo ruwa a ciki ta dago haqarqarin Innatu ta kafa mata kofin tasha a hankali saida ta kawar dakai sannan tayi hamdala tace.

 

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

“Yau na dade Burtsatsen dan yobe ya lalace ruwa yayi wahala a cikin gari saida naji gdan maigari sannan na samu ruwa tulun ma ban ciko ba” miqewa tayi ta dauki wata qaramar roba ta nufi inda garken shanunsu yake ta tsugunna a a qarqashin wata shanuwa ta kama hantsarta tana tatsa a nutse, can nesa da ita wani mutum ya nufota da sauri yana balbalin masifa cikin harshen Fullanci fadi yake “shanuwar ta ubanki ce Haro da zakizo kina tatsata dabarar gobe su Lantai su rasa me zasu fidda su sayar su samu na cefane….” Yana zuwa ya fincikota da qarfi ya hau bugunta da hannu da qafa ta miqe da gudu ta nufi bukkarsu tana kuka tana bashi hqr amma mutumin nan bai qyaleta ba har daka yabita yaci gaba da balbala masifa yana cewa “ko uwarki me abin kunyar nan Indo bata isa tayi iko da kayan Haro ba sai abinda mukaga dama muka barta tayi iko dashi bare ke”

 

 

 

 

Rakubewa tayi tana kuka me cin zuciya inda dattijuwar dake kwance bisa gadon cikin halin jinya take matsar hawaye wannan rayuwa da radadi take ba kanta take tausayawa ba face rayuwar wannan yarinya Juhud qara gangarowa hawayenta sukayi lkcn da Juhud ta dora kanta a qirjinta tace “Ayyah Innatu mine kikayiwa su Baffa Ribadu da Baffa Bangel da Matayensu ne da basu qaunar Halwar mu Innatu kowa yana walwala rayuwa cikin jin dadi da farin ciki a Rugar Wand’u amma bandamu Innatu miye aibinmu miye laifin da mukayi musu ne nikam zani na basu hqr su barni na rayu cikin walwala….”

Daqyar Innatu ta daga hannu ta dora bisa bakin Yartata cikin kuka tace “Aradun Allah ban shina ba Juhud tunda Baffanki ya amro ni na tarar da irin wannan rayuwa sukeyi Baffanki baitaba farin ciki a cikin Ahlinsa ba kullum cikin tuhumar kansa yake har yabar duniya nasani kinsan wasu abubuwa da suka hwaru har kawo lkcn da aka kashe baffanki kisan da har yanzu aka kasa gane waye yayishi…..”

Tarine ya sarqeta ta rinqa yinsa tana dafe cikinta harda fitsari saboda azaba bayan ya lafa tace “bansan meye asalin matsalar ba nidai abu daya na sani shine Moddibo Wand’u kakanku shine ya hwara haihar da wagga matsala Juhud babu abinda baki sani ba babu abinda zan fada miki face ince kiyi hqr da yanayin da kika samu rayuwarki a ciki komai yayi farko yana da qarshe kuma komai girman gona zaa samu kunyar qarshe”

 

 

 

 

 

Ajiyar zuciya yarinyar ta sauke ta miqe tana karkade dakin tana gyarawa ta dibi scollar su ta zagaya bayan shingen dakinsu ta fara wankewa har yanzu idanunta hawaye yakeyi saboda ta bugu a gurin Baffa Ribadu, bataji tafiyar mutum ba sai inuwa ta gani a samanta ta dago a furgice tare da ja da baya da sauri tace “Hammah Manga….” Yanda ya kafeta da ido yana lasar lebe ne yasata saurin saita nutsuwarta ta rarumi kallabinta ta aza bisa kafadarta yayi murmushin qeta yace “Oye Aminatu kura kin girma komanki qara tumbatsa yakeyi yakamata fah ace na fara yimiki ban ruwa koda yake alama ta nuna wannan sheqin da kikeyi akwai wanda yake mulmuleki dama Hammah Audi yace ya taba ganinki a bayan kalgo keda dan dauda suna matse maki nono….”

A gigice ta dubeshi tare da zaro idanu tace “aradun Allah ba haka bane cewa sunkayi wai Nono na zaiyi dadi na aza nonon shanuwa sunka nuhi sunkace muje na basu na wazo wazo nabisu kawai suka falkemin riga suka kama shamin nono inajin zahi ina kuka ina kiran Baffana sai Allah ya kawo Hammah Audi shine ya kalbeni a hannunsu yasamin shakwararsa muka taho gida” zubanta idanu yayi tana maganar yana kallon bakinta zuciyarsa na qara kwadaituwa da wagga halitta dake gabansa da gani yasan zatayi ruwan gato kamar yanda yaji kanawa suna suffanta mace me ruwa.

 

 

 

 

Ji tayi yakai hannu ya riqo hannunta yaja wata ajiyar zuciya yace “uhmmm ai zakiyi bayani ne ki gama scollar kizo ki sameni a shinge Yawo zanje shanho idan kinqi kuma yau dake da gyatumarki babu wanda zaiyi baccin kwanciyar hankali” yana gama fadin haka ya juya ya nufi wata siririyar hanya inda yabarta da faduwar gaba a ranta tana maimata taje ta sameshi Shinge Yawo to mi zatayi mashi acan gurin da mutane basu cika biba sunce hanyar yan iskace sannan barayin shanu tanan suke shigowa, numfashi ta sauke tamai da hannunta cikin wankinta ko ita sa’ilin da aka kada shanun Baffanta bayan an kasheshi yanan taga gilmawarsu, shanya kayan data wanke tayi ta juya ta nufi shingensu ta bude ta shiga ta tsugunna tace “Innatu Hamma Manga yace inje in isheshi shingen Yawo nikam banson zuwa” numfashi Innatu ta sauke tace “nima banson zuwanki gareshi idan kinqi zuwa kuma ya fadiwa babayenku su ruhan miki kije amma ki kula da kanki Allah zai kiyasheki mugun ji da mugun gani”

 

 

 

 

A salube ta miqe ta sanya cinyayyen salifas dinta ta dauki sandarta ta nufi siririyar hanyar zuciyarta na cike da zullumi itakam Tana tsoron masifar Hammah Manga duk da cewa ita bai cikayi mata ba amma tasani baya saurarawa kowa Allah shisa ba wani laihi tayi masa ba, a da wannan tunanin ta fara hango hasken wutar yayi a can nesa da ita kadan ta tsaya tana nazarin gurin zuciyarta cike da tsoro Allah ya azawa Juhud masifar tsoro musamman na yanayin dare, ta kasa motsawa daga gurin sai rawar jiki takeyi tunaninta ya gama bata barayi ne tariga ta kawo kanta ance idan suka kama mace a daji tubeta sukeyi suyi cici da ita sannan su kasheta.

Hawaye ne ya zubo mata wannan shine gaba kura baya siyaki gashi tana tsoron idan ta juya irin cin mutuncin da Hammah Manga zai yiwa Innatu tana fama da kanta…… Bata gama wagga tunani ba taji an zungureta da sanda ta baya, warwas ta zube a qasa cikin wani yanayi na mugun tsoro tace “shikenan Hammah Manga kasani nazo gashi zan tahi inda Allah dada waye zashi rinqa kularmin da innatu…..” Wata mahaukaciyar dariya ya qyalqyale da ita ya sunkuya a gabanta yakai hannu ya shafa tsakiyar qirjinta yaja fasali yace “waye ya fada maki mahara ne ai ba yau ce ranar zowarsu ba shiyasa nace kizo nan” sake kai hannunsa yayi tsakiyar qirjinta yace “shekarunki sunyi kadan ki tara wadannan kayan dadin meye yasa kika tarasu da wuri?” Cikin kalamansa babu daya gananne a gurinta sai binsa da takeyi da ido ya kamo hannunta ya miqar da ita yace “muje kigani tsarabar da nayo miki daga Jos harda Riyali na sawo maki na hannu nasan zaiyi miki kyau”

Zungi² ta rinqa binsa tafiya me tsayi har suka isa qofar wani daki ya daga karan gadon ya bude ya shiga yace “shigo” bata kawo komi ba ta antaya ciki yayi murmushi yau tarkonsa na shekaru ya kama masa zaki, bincike ya farayi kamar me neman wani abu yana yar waqarsa har ya cimma qofar kawai taga ya janyo karan gadon ya rufe qofar take wani tsoro ya dirar mata tace “Hamma….” Hannu ya doranta a baki yace “banson surutu sakarya dake kin dauka kawai donna kalleki na kiraki ai tunda akace kina rabawa yan gari nononki to nima sai kin bani nasha nikam ba iya nono ba har gato nikeson ci a yau yarinya……”

 

 

 

 

*THIS BOOK IS NOT FREE… REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566*

 

 

 

 

_*Oum Hairan*_

[10/07, 8:31 pm] +234 810 321 0755: *JUHUD*

 

 

 

 

*(OUM HAIRAN)*

 

 

 

*( Pure love sex nd romantic)*

 

 

 

 

*FP THREE*

 

 

 

*SUBSCRIBE*

_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

 

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

 

 

 

 

 

*TUNATARWA*

Kowa yakanyi maka jaje a lkcn da wani abunqi ya same idan abin farin ciki ya sameka qalilanne sukeyi maka dariya har zuci, kada kasa dariyar mutane a ranka harta rudeka kaji cewa kowa sonka yake masoyin gaskiya shine wanda yake tare dakai a kowanne irin yanayi farin ciki ko akasinsa.🤏🏼

 

 

 

 

*CIGABA*

Inajin ciwon abinda Gwaggo Lami take fada akanki amma ban isa nayi magana ba abu daya na sani shine inayi miki addu’a ki kasance ya ta gari abar Alfaharin iyaye, kwanci tashi girma ya fara zuwar miki komanki abin mamaki ne gabbanki sunada saurin nuna girma hakan yasa tun kina qarama na sabar miki da saka hijjab irin na kanawa, sosai kike ganin tsangwama qyama cikin Yan’uwanki Hasiya Adama da Baraka Amma baki damuwa kodan kin taso kinganmu a cikin wannan qangin ne oho.

Wata rana Naje tallan Nono birni na dawo na tarar dake kina kuka na shige daki kika biyoni nake tambayarki meye yake faruwa sai kike fadamin Asubi ce ta bugeki saboda kunyi fada da Baraka tace miki kilakin birni kin bugeta hakanan na hqr bance komai ba ashe mgnr nan har gurin iyayenku maza taje da dare Baffanki yazo yake tuhuma ta wai waye yake zuwa yake siyan nono a gurina a sulluwa (mota) daga birni?”

 

 

 

 

Dagowa nayi na dubesa nace yaron Alh Idi ne da ka hadamu dashi a kasuwa yake zuwa karbar masa nono” numfashi Baffanki ya sauke ya kira sunana na amsa yace “shin Indo kinasa ido akan Aminatu kuwa?” Sake ware injin idona nayi akansa nace “Wai mekake tunanine Haro nikam bangane inda zantukanka suka dosa ba” sake gyara zamansa yayi ya dafe kansa yace “dazu na dawo daga kiwo na Ishe Ribado da Bangel suna tattaunawa naqarasa domin mu gaisa shine suke cemin wai dazun sunga wani me Sulluwa yazo ya dauki Aminatu a mota sunyi hanyar birni” dafe qirji nayi cikin kidima da gigita nace “aa Haro wlh zancene Juhud yau babu inda taje tallanma nice na fita saboda tacemin batajin dadi” jinjina kai yayi yace “shikenan adai qara kulawa” ashe wasan baa fara ba.

 

 

 

 

Tun daga wannan lkcn suka dora mamu qahon zuqa babu dama mutum yazo siyan nono gurinmu sai suce iskanci yazo ba keba nima a haka nake a gurinsu duk da cewa Baffanki baya bawa abin muhimmanci, tsaka da haka Hammanku Manga ya dawo daga neman kudi yaganki ya nuna yana sonki da murna baffanku yazo min da mgnr domin a lkcn duk anyiwa su baraka aure saura ke kadai kin rasa ko matayi a rugarmu dama maqota saboda sharrin maitar da suka liqa mana.

Duk da zuciyata bataso ba amma banja ba saboda bansan raayinki ba hakanan baffanki ya nemoki ya tambayeki game da Manga domin shi yace ma kun gama daidaitawa nan kikayi tsalle kikace bakiso naso na matsanki ki karbeshi amma sai baffanki yace tunda bakiso babu meyi miki dole ko bayan ransa hakanan naja bakina na tsuke babu kunya yaje yace da yan’uwansa kince bakison Manga nan suka qara sanya masa tsura ashe dama asali ba manga ne yace yanasonki ba sune suka kitsa masa ya aureki sai susan yanda zasuyi su hallaka babanki su kwashe dukiyarki,

Abu kamar wasa gaba me tsanani ta shiga tsakaninsu ko gaisawa basayi watarana da dare har mun kwanta Bangel yazo yayi sallama da Baffanki ya tashi ya fita bansan me suka tattauna ba nidai naga ya dawo yana huci na tambayesa yake cemin Aishatu don Allah ko bayan raina karki yarda ban aminta Aminatu ta auri Manga ba na haramta hakan idan har hakan ta faru bazanyi farin ciki ba” jikina yayi sanyi ya kwanta ranar kwana yayi yana juyi yana hawaye idan na tambayeshi sai yacemin shidai bai aminta Aminatu ta Auri Manga ba a lkcn inata fama da rashin lfy mukaje gun me magani yace cikine dani amma ya kwanta.

 

 

 

 

Ban wani damu ba duk da cewa Baffanki kullum cikin kawomin magani yake hakan baisa cikin nan ya tashi ba wata biyu tsakani sukayi wani gagarumin rikici daya sanya suka qara kullatar juna ashe a wannan dare sukayi taro suka yanke shawarar tunda yaqi basu hadin kai kawai su kasheshi su huta mana inyaso sai manga ya kada shanun yayi kudu dasu kinga zaace barayin shanh ne suka kasheshi.

Maddibo Buba ne yaji wannan shirin nasu a daren kuwa ya kira Haro ya sanar dashi abinda yan’uwansa suke shiryawa yaja fasali tare da murmushi yace “babu komai Allah yafi kowa sanin abindake qarqashin qasa dana ban qasa yafi kowa sanin daidai” daya dawo bai sanar dani ba nidai naga ya tashi cikin dare ya dauko wata qaramar adaka ya bude ya zaro wasu abubuwa masu walwali yabani yacemin Aishatu wannan abin da kike gani ba komai bane face dutsen Lu’ulu’u wanda yan birni suke cewa diamond wannan kuma gwal ne nasan kinsanshi don Allah ki nemi guri kiyi musu mugun boyo asalinsu na Mahaifiyata ne Aminatu naketa ajiyarsu domin Aminatu kada kibari wani yasan dasu a hannunki sunfi shanun can da kike gani garke guda daraja domin kuwa yanzu a duniyar mutanenmu wane da wane ma ba kowane yake iya mallakar diamond ba koda bayan raina zasu qwace komai ya kasance Aminatu ta tsira da wadannan abubuwan”

 

 

 

 

 

Na dade ina tunani kafin na tashi na haqa rami a qarqashin gadona na zubasu a ciki insha Allahu a yau zan baki abinki ki daura a qugunki su zame miki jigida iya wuya kada ki bari su kubce miki kinji” jinjina kai tayi Innatu taci gaba da cewa “washegari da safe na damawa Baffanki fura yasha ya kada shanu ya tafi kiwo nikuma na dauki nono na shiga gari acan suka cim masa da rana lkcn kin tafi kaimasa hura suka sareshi akansa da qirjinsa ya fadi jini nata malala kince kinga shanunsa lkcn da aka kadasu akayi hayi dasu amma bakiga wanda ya kada dinba kina binsu har kika ishe inda Gawar mahaifinki take yashe a qasa kece kika dawo kika fadawa Maddibo cewa an sari Baffanki kuka dunguma kuka koma nidai bayan na dawo na ishe wannan mugun labari shine tunda na yanke jiki na fadi bantashi ba nake zaune a wannan halin tsayin shekara biyu kwatsam sai cikina ya fara motsi nasa kika kiramin Jumme na sanar da ita dake tasan da batun kwanciyar cikin ta sanarwa da Maddibo Shi kadai yayi murna ya rinqa karbomin magani ashe a gefe Bangel da Rubado zargina sukeyi da Buba wai yana shigowa dakina ya dade hakanan sukaje suka kitsawa Jumme tazo har dakin nan tayimin tatas ina zaune babu halin magana a cewarsu ma wai wannan cikin na jikina ba na Haro bane na Buba ne Juhud Allah daya tsakanina da buba daga sannu sai idan ya kawomin magani ko nonon da zaki fita dashi talle.

 

 

 

 

A haka muke rayuwa har kawo yanzu da komai ya qara lalacewa Juhud kullum mutanen nan basu fadin alkhairi garemu kullum cikin yi mana kalen sharri suke yanzu haka kwanaki uku da suka wucce Jafaru makiyayi ya dawo daga kudu ya kawo shanaye guda dari da ashirin yace na Baffanki ne to tun jiya sukebin kaina akan na yarda a daura aurenki da Manga nikuma gashi Baffanki yabarmin wasicin ko bayan ransa bai aminta a hadaki aure da Manga ba a yau bayan kin fita diban ruwa har barazana sukayi min da rayuwata Juhud bandamu ba indai akan burin Haro ne su kashenin ma kansu sukayiwa.

 

 

 

*ASALIN LABARI*

 

 

Jikin Juhud ne ya qara sanyi hawaye na sunturi a kucinta tace “yanzun wadannan sune kadai dalilan da suka sanya Suka kashemin Baffina Amma aka kasa daukar mataki akansu Innatu wannan wacce irin Al’umma muke ciki meson kanta? Shafa nadaddiyar sumarta tayi itama cikin hawaye tace “haka rayuwa ta zama kina gani fah tunda Baffanki ya rasu ko nono sun hanamu tatsa saidai su tatse subawa matansu suje su siyar idan kinga mun samu nono a rugarnan to Moddibo ne ya tatso mana Juhud ya zakayi ne da qaddararka ni yanzu burina a duniya naga kinyi aure kin samu matsugunni saboda wannan rayuwar bata yuwuwa a haka”

Fadawa tayi jikin Innatu tana kuka me cin zuciya itakam da Innatu zata amince da sun bar rugar nan tunda baa sonsu amma tasan bazata aminta ba, da wannan tunanin bacci barawo ya saceta.

 

 

 

 

Washegari da wuri ta dauki tallan nononta ta tafi tasha cike da doki yau tayi niyyar idan tayo ciniki har Balangu zata sawowa innatu ko tsiren quli tana tafe tana yan waqoqinta harta isa gari koda taje yan nonon gurin ya cika batada guri dole ta koma gefe ta rakuye tana wasanninta na quruciya dagowar da zatayi taga wani baqin hadari ya gangamo tana juyawa taga Fulanin duk suna hade karensu gashu batayi cinikin kirki ba donma ta datsa yariman ne ta dibarwa wani na dari biyu shiyasa da haka zata koma.

Ganin hadarin na gangamowa yasata miqewa jikinta a salube tana juya dari biyun ta gama kasaftata tasai mawa Innatu maganin ciwon jikin hamsin tasai mata balangun dari ta riqe hamsin a hannunta ko batirin fitila sa siya, daukar qoranta tayi ta aza aka ta juya kenan zata tafi taji wata mota tayi horn a bayanta ta juya taga me motar ya zuge glass wani matashin saurayi ne me qwarjinin gaske fuskarsa a daure ya bude bakinsa kamar wanda akayiwa dole yace “na nawa ne?” Cikin fullanci yayi mgnr tayi saurin Amsawa da cewa na dubu Uku ba dari biyu” dubanta yayi yace “harke?” Kallonss tayi da rashin fahimta ya daganta gira yace “inaso ki juyemin da sauri” daidai lkcn taji gabanta ya yanke yabads wani dam ta dafe qirji da sauri tana waige² yace “ko bakiji ne?” Da qaraji yayi mgnr taja numfashi ta miqa masa har qoran tace banida ledar da zata dauka duka kaje da qoran ka dawo mani dasu wataran” karba yayi yasa a bayan motar ya zaro dubu biyar ya bata yace “gashinan har kudin qoranki bana shigowa garinnan sai idan wani babban uzuri ya taso” karba tayi tayi godiya ta juya da sauri ga mamakinsa kawai yaga ta take a guje ya saki baki yana kallonta a fili yace “lkc guda nutsuwarta ta gushe ko meye yaja hakan?” Tabe baki yayi ya daki kansa yace “kaima Cornel Rasheed da shiga abinda babu ruwanka kake” cikin kasuwar ya shiga yayi siyyayarsa ya juya da motarsa yabi wata siririyar hanya.

 

 

 

 

Itakuwa koda ta kwasa a guje duk nisa dake tsakaninta da rugarsu haka ra rinqa cin gudu harta fara hango rugar tasu nesa sosai gabanta ya qara yankewa ya fadi ganin wani baqin hayaqi yana tashi ta sashin da bukkarsu take, da sassarfa ta nufi gurin kawai taji an wafci hanunta da qarfi dagowar da zatayi taga Moddibo Buba ne idanunsa sharkaf da hawaye yana janta yana kallon bukkar tasu dakeci da wuta,

Da qarfin gaske ta turje cikin fitar hayyaci tace “Innatuuuu!” Saurin rufe mata baki yayi yaci gaba da janta bai qyaleta ba saida yabar sashin rugar da ita ya tsaya jikin wata itaciya yana sharce hawaye ya dubeta yace “Haka Allah yake ikonsa Aminatu a wannan qarnin babu wani abu dazan iyayi miki face na saki a hanya kibar yankin nan gabadaya Su Bangel basu da Imani Ina zargin sune suka sanyawa dakin Indo wuta suka qoneta ina daji Audi yaje yake fadamin har yana cemin yanzu Hakama Ribadu da Manga sunacan suna nemanki kema sunason kasheki ne tunda uwayenki sunqi amincewa su bawa Manga Aurenki harma suna masa sharrin zai lalataki…………

 

 

 

 

*THIS BOOK IS NOT FREE… REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566*

 

 

 

 

*Shares Please*

 

 

 

 

 

*Oum Hairan*

 Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [ ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

5 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!