Juya Hausa Novel Complete

9/27/16, 7:56 PM – Messages you send to this chat and calls are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info.
9/29/16, 2:11 AM – Queen Safiyyert馃憫: “JUYA”
漏 Feenat Ja’afar.
1_A gaban mudubi take tana k’yali,ta shafa
nan,ta shafa chan,ta mudubin kuma tana d’an
k’allon ta cikin shi tana murmushi, ganin yadda
mutuminta ya zuba mata ido ta ciki.
Juyowa tayi,yai d’ai-d’ai akan gado yana
k’allonta, d’uk rashin k’yau na abu,toh mud’in
kana muradin shi mai k’yau ne a wajen ka.
Babban mamakin shi yadda ya kasa ganin munin
Matarshi a kullum, yakan shafe “seconds” dan
gano ta inda “Prettyn”shi ta gaza, kai ya girgiza,
dan shi baiga makusa ajikinta ba ko kad’an.
D’uk a kullum dangin shi suna mishi gorin d’uk
k’yawawan garin nan,amma ya rasa wacce zai
jaju6o sai Fulera,ga ta “JUYA”,ta bare suce ko
dan haihuwa taci darajar so,,d’uk ta tare gaba,ta
tare baya, ta hanashi ganin d’uk wani makusa
tata a gare shi,balle yai tunanin gazawarta na
zama “JUYA”.
Asalima shi in d’ai zai tozali da Fureran
shi”Pretty” toh yakan manta komai.
“Pillow” ya sake jawo wa,lokacin da ya g’yara
k’wanciya yana cigaba da k’allonta, d’ai- d’ai da
dak’ika d’aya baya fatan yaga “Pretty” ta
barshi,yana matukar k’aunar ganinta kusa dashi.
Bai aune ba ya ji ta hure mishi ido da bak’inta
tana murmushin nan wanda ke sashi murmushi
ko da bai shirya ba,, kamshin “lestrine” ya buge
shi, had’i da kamshin alawarta ta kullum,”splash”.
Take ya sau ajiyar zuciya, kan ya k’allota.
Hakika yana kara godiya ga Allah mad’aukakin
sarki da ya bashi “Pretty” a matsayin “Matarshi”
kuma “Sanyi ga Idanunshi”. Tabbas yana daga
cikin maza masu t’sant’sar sa’a a rayuwa na
samun “mace ta gari”,wacce ganinta kad’ai, ya
isa wanke maka bak’in cikin rayuwa,har yai
hamdala da mahaliccin shi,dan ya mishi
baiwa,irin wacce ba Kowanne namiji ke da ita ba,
a ganin shi,dan ya hanashi “D’a” bazai zamu ya
masa butulci ba.
Murmushi ya sakar mata,kamar kullum ya fara
yaba mata wankanta. “Kinyi k’yau sosai pretty, a
kullum ranakun duniya kamar ana dad’a kawata
min ke ne,kamar ki zauna nai ta k’allon ki kawai.
“Ko zaki fasa zuwa sunan?
Murmushin jin dad’i tai,gashi d’ai kullum irin
kirarin nan tana shan su,amma baya hana taji
dad’in jinsu.
Zama tai, tare da ruko hannunshi ta kai baki
tai”kissing” take k’wa ya sauke ajiyar zuciya,tare
da d’aura d’ayan hannunshi kan nata..
Tsaf ta riga da ta gama samo abinta cikin ruwan
sanyi, ta riga da ta gama sanin d’uk wani “week
points” nashi akanta, mai lafazi mai k’yau ce ita
da sanyin murya, takan ko’k’arin tauna
zance,sannan ta ya6a mishi”gold” da “lu’u-lu’u
kan ta bashi.
Cikin salon ta da wata irin murya ta fara magana
tana lumlumshe mishi ido da d’an lallashi. Ji yake
mar rad’a take mishi a kullum.
“Kar kaji kom “Nawan” ni taka ce ai,k’walliyar ma
taka ce, zan rintse ta ga ganin kowa,sai d’ai in
mata y’an uwa na, badan sanin mahimmancin
sunan nan a gare ni ba,da zan ta zama,kai ta
k’allo na,har sai kace na ishe ka.. Ta karasa tana
fari da idonta, take k’wa ya sau ajiyar zuciya.
Unguwa ko bai niyar barin prettyn shi ba,da
kalam kawai zata sa ya firta “Toh”.
Kai ya girgiza kan ya tashi ya zira rigarshi.
Ita kuma ta sa hijab da Nikaf dan rufe k’walliyar.
Tafe suke a mota,suna ta faman firar duniya
cikin nishadi,har ya faka a kofar gidan
sunan,wanda matar K’aninshi take gare shi.
Hannunshi na cikin nata,tambayarta yake sai
yaushe zai zo d’aukan ta? Ganan wasu na
shiga,wasu kuma na fita a gidan sunan,sai d’ai in
sun fito,maimakon su tafi,sai suja su tsaya
k’allon su prettyn.
Tana shiga ta tsaya ta cire nikaf d’in, kan tai
bangaren mai jego.
Da sallama ta shiga d’akin fuska sake, fal cike da
jama’a, kowa ya zuba mata ido, ta samu gefen
gad’on ta d’an dosa na,tana kula da hararar da
wasu ke sakar mata,”ina yinin ku.. Fuska mai
jegon ta yamitsa,kan tace”sai yanzu? Dad’i Miji..
Murmushi tai,dan tasan da ta tofa yanzu za’a
fad’a mata magana. Cigaba tai, “shidai cin tuwon
kishiya ramako ne,ehee. Kai ta k’ada, lalle
mutum.
K’anwar mijin tace ta amshe,”ba Kowanne tuwan
bane na ramako..kar ma kisa a ka,a yadda tai
shirim d’in nan ne zaki sa rai? Baki ta ta6e,kan
tace suna ga wata wai “JUYA” tashi tai “parlour”
tana hararar prettyn,wacce ke mata murmushi.
By
Feenat Ja’afar.
9/29/16, 2:12 AM – Queen Safiyyert馃憫: “JUYA” 漏 Feenat Ja’afar. 3_Asalin su y’an
Kaduna ne,a karamar hukumar Zaria,Baban ta
Muhammad “mechanical engineer ne,Matar shi
d’aya,Mama Dije,da yaran su takwas, tun samun
aikin shi ya dawo cikin garin Kaduna da zama da
iyalen shi,a lokacin yaran biyu ne rak!, Suleiman
shine babban d’anshi,sun dan jima kan su samu
Aisha,sai Furera,Maryam, Hassan da Husaini da
k’annen su. Tun su Furera suna yara Abban su
ya shiga “missed call” sai ya zamo baiya aikin
Gomnati sai makanikanci, rumfa ya bud’e dan
wannan harkar, ko dan burin shi na sai yaran shi
sunyi karatu, da taimakon Allah,da taimakon dan
uwanshi dake Zaria ya kafu,, sosai ya iya g’yara,
dashi yake samu ya biya ma yaranshi karatu.
Tun tashin yaran yai musu sa6on dad’i, sai kuma
akazo ya rasa aiki,d’uk da haka yana iya kok’arin
shi yaga ya wadata yaran shi da d’uk wani abin
jin dad’i, ta yarda bama zasuyi kukan baida shi
ba,d’uk an neme shi daga baya yace ya d’aina
bautawa Government, g’wada yaci da gumin shi.
Mama Dijee itama takan yi su su6o da sauran
kayan sanyi. Sosai suna k’wata ma yaran su
tarbiya,kuma sun taso ba laifi, d’uk dunsu ba
masu son k’warafniya bane,in banda d’aya da ta
fita zakka cikin su,wato “Fure”. Tun tashin Fure
sam bata d’aukar wargi,ita sha yanzu ce,magani
yanzu,sam bata barin ta k’wana. Gidan haya na
biyu kenan suna yi,yanzu su biyu ne aciki,sai d’ai
shi baban su sai ya kewaye bangaren su da
langa-langa, d’uk ba jin dad’in zaman suke,d’an
fa d’ayar matar sam batta kirki, d’uk hakurin
Mama Dijee sai da ta kaita bango,a kan yaranta
t’saf sai taci damara. Ga yara zagi a bak’insu
kamar ruwa. ” Fure ki wuce mu tafi yanzun nan
kan na had’a ki da Umma. Kara chakumar wuyan
y’ar gidan matar tai, “wallahi bazan cikata
ba,mey yasa zata zagi uwata? Sa’ar ta ce? Jin
kok’awar fad’an ne ya fito da Larai daga daka,
tuni Aisha tai gefe,dan tasan ba abinda zai hana
ta rufar musu a ka. Zaune ta samu Furera akan
y’ar tana nad’a kamar Allah ya aiko ta, sarai
Umma naji, amma tai kamar bataji ba, Larai batai
wata-wata ba ta rufar wa Fure,tana dukanta ita
kuma tana narkar y’arta, wanda a zahiri ta fita
girma da komai,amma ihu take a taimake ta a
hannun Fure. Ganin zatai wa y’arta illah yasa ta
bar dukan Furen ta hau ko’k’arin fincike ta akan
y’ar. ” uwata Sa’ar ta ne,ai dama na fad’a mata
wataran sai na fasa mata baki agidan nan, shegu
dangin maguzawa… Da gudu ta zuba, ganin larai
taiwo kanta tai zaure, g’walo tai ma yarinyar, da
tana kuka tana kuwa k’wararowa iyayen Fure
wasu mugan zagi ba ko dad’in ji, tana daga
zauren tace “oho d’ai, ko banza na koya miki
hankali, kuma zamu had’u anjima. Umma dake
d’aki suna jin ruwan ashar din da Larai da y’arta
suke watso musu.. tai shiru ita da Aisha da
sauran k’annen ta. D’a ne ka haife shi baka haifi
halinshi ba,ko ta hana Fure kula Larai da yaranta
sam bata jurewa,barin in suka zage ta,amma abin
na yau yafi k’arfin ta,dan d’uk tsiya sai d’ai suyi
chachar baki,amma yau Fure harda dam6e. Tana
zaure har taga shigar Larai da y’arta d’aki kan ta
arto da gudu tai kewansu. Harara Umman ta
sakar mata, uffan bata ce ba tai shiru, amma
dole yau asan nayi, dan sam zaman gidan nan ba
nasu bane, dan tsaf Larai zata gur6ata musu
tarbiyar yara, musamman Fure, zama da Larai
bak’inta yai masifar kara bud’e wa,ga fad’ar
magana kamar y’ar makafi. Da dare kuwa Abban
su yana dawo wa ta kora mishi bayani, kamar
kullum ci kanki bai cewa Fure ba,wanda ita
Umman ta zata zai ja mata k’unne. Tun daga
ranar jaraba ba kama hannun yaro tsakanin
ya’yan Larai da Fure, sam bata ko shakkar
girman su, haka zasu kamata su mata taran
dangi har uwar amma uffan Umma bazata ce ba,
kuma inda zasu k’wana dukanta sai ta rama
kuma ba ko hawaye, tana zuwa d’aki Umma ta
kara mata wani. Ba shiri Abba yasai fili ya kuma
ta dasu a gidan Larai kan suka samu lafiya.
Gidan su kad’ai ne a ciki,mai d’aki biyu da
baranda, yanzu burin Abban su kawai ya tara
kud’in gini, dan k’warai ya gaji da bin haya,in
yaso ko na kasa ya gina musu. K’wance tashi su
Fure har an shiga secondary, day d’uk yaran
suke,yayinda Yayan su Suleiman ya kammala
secondary sai jami’a. Sosai y’an gidan suna da
K’wak’walwa, barin Fure uwar rawar kai, Kasuwa
kam ta bunkasa wa Abban su, dan har ya bud’e
wa Ya Suleiman shima wajen g’yaran kan ya
samu g’urbi a A.B.U Zaria. Anyi hutu suka
tarkata sukai Zaria ziyara, anan ta samo yaran
kawunsu sa’aninta suma sun dawo a Queen
Amina, yadda suke bata labarin makarantar da
“boarding school” kawai tai sha’awar zuwa,,
Uncle d’in nasu achan yake aiki d’ayan, tuni Fure
ta tada bal’li ita sai Boarding. Da taimakon
Kawun ta biyu da Abban su ta samu g’urbi a
makarantar Queen Amina College. Haka Abba
yake fafutukar nema kodan biyan makarantun
yaran. Fure a Boarding, k’warai rayuwar ta
mata,d’uk da tana k’ewar gida wataran, nan ido
ya kara bud’ewa, daga “Furera” ta koma “Pretty”.
A d’uk dabi’ar ta bata nuna cewa ita y’ar wani
ce,asalima ita irin k’aryar nan ta y’an boarding
sam bata d’ad’a ta da kasa, dan sosai tana alfari
da Abbanta, kuma bata 6oye mazaunin ta d’uk
fafar ta. K’wance tashi ba wuya a gun Allah,ga
nan su Fure har an shiga SS1, Cikakkiya ce
Pretty,ta bun kasa,d’an ba ramammiya bace ita
sam, t’sirinta da tsabar iyayinta su ke boye
muninta, bata sahun farare, sai d’ai sahun
bak’ak’e, sai d’ai a cikin bak’ak’en ma iya kiranta
wankan tarwada, a fuska kam ba wata
k’yak’yawa ta azo mu gani bace, d’an karamin
k’yau gare ta, sai d’ai a jiki a dire take. Babban
sirrin k’yaunta” gashi” dan ko a fuska “eye
lashes” d’inta da girar ta sunfi d’aukar ta tazamo
mai k’yau. Yadda k’wa take far-fara su in tana
zance, kai kace da ga’iya take,dan tamkar tai
“fixing”. By Feenat Ja’afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Apr 10
Feenat Ja’afar Novel’s
“JUYA” 漏 Feenat Ja’afar. 4_A jiki “Full option” ce
kam,abun da a yanzun tafi jin haushi a kira ta
dashi kuwa shine “Fure”. Yana d’aya daga dalilin
da yasa a school suka k’ak’aba mata” Pretty ”
dan kam ita k’yau ce da wanka. D’uk yanzu y’an
unguwa yawanci da Pretty suke kiranta, a gida
ne kawai sunan ya gagara k’arbuwa gun su
Umma,dama shi Abba bai san da sunan ba.
Ak’wai lokacin da Abban ta da ya Suleiman suka
je musu Visiting, shaf sai suka manto visiting
card d’in a gida. Da alfarma aka kira wata mate
d’in su Fureran kan su fad’a mata sunan ta kira
ta da y’anuwanta. Sunan ta tsaya tana maimaita
wa, halamar tama rasa mey shi, sai da yasa
sunan uba da unguwa kan tace”au Pretty ce, bari
na kira ta,, da d’an gudunta ta tafi tun daga
wajen ta fara k’wala mata kira, Abba ya girgiza
kai, kan ya k’alli yayan nasu,”yanzu wai kaji Fure
har sunan k’arya ya shafe na gaskiya? Murmushi
yai,kan yace”Abba makarantar kenan,sai a
hankali. Tana hango su Abban da gudunta ta
nufo su, har ta baro sauran a baya,”da gaske
k’wa kaga ita d’in ce suleimanu, dariya yai,
lokacin da ta karaso tak’wa tukuikuye Abban,kan
ta koma kan Yayan nasu. Bayan sun gaisa yace,
“Yanzu Fure ke ce kika koma pretty saboda
Allah? Da sauri ta matso tana marairaita mawa
baban kan ya d’aina cewa Fure,sai wai school ta
d’auka. Yace” ungo naki, shi dai ya Suleiman
dariya kawai yake musu. “yasu Umma? Yaya ya
makaranta? Yai murmushi, “suna gaida ku, ” yaya
ka kusa gamawa ai? Kai ya k’ada mata,”InshaAll
lah, murna take kan yayan ta shima zai zama
engineer. Sunje hutu sun dawo,wanda a shine
suka shiga ss2,anyi sabin coppers, yayin da
iskancin su pretty ya motsa. Sun bala’in raina wa
coppers hankali, d’an su kam mayun mata ne.
Ranar d’aya ya shigo ajin,Hausa yake d’auka, sai
fafa yake musu shi nan a dole yana gaban y’an
mata. Bayan ya gama darasi ya k’allo su, dariya
kawai suke mishi, amma shi ko a jikin shi, sai ma
wage musu baki da yake. “If you hv questions
queshh” or additional information… Haba wa,mai
su Pretty zasuyi inba dariya ba. Har aka buga
“next period” ya bar ajin ba wanda ya kula shi
sai shakiyancin su suke. Yana fita su pretty ita
da y’ar desk d’inta suka fito k’waik’wayar shi,, ta
d’au alli”if u hv questions quashhhhh… Or
additional information. Yadda kasan shine a
gaban allon. Fad’i suke in banda malam,mey ya
kai turanci kai da kake koyar da hausa? Tuni sai
suka fara tariyo na d’ayan coppern da yai musu
mathematics, dariya Fure take harda rike
ciki,d’an yin irin in’inar da d’an NYSCn yake.
Tsitt! Ka ke jin ajin sai dariyar Fure da Adama ke
tashi. Zungurar ta Adama ta fara,lokacin da tai
ar’ba da abinda yasa class y’in shiru. Hard’e
yake da hannu a kirji,rike da “text book” an
rubuta”chemistry” a jiki,sanye yake da fara sol
d’in rigar NYSC da siririn farin glass a
fuska,fuskar nan sam ba annuri,, tunda suke ko a
malamai basa jin da wanda ya ta6a musu
k’warjinin wannan, balle a wanda suka raina. Ajin
ya shigo,har lokacin idon shi nakan Fure da ta
kame a gun baki sake, tuni ita Adama tasan
nayi. A gabanta ya tsaya tamkar wani soja rai a
had’e. Takarda Adama ta nannad’e,sai ta seta
Furen ta hulla mata, a tsorace tabar K’allonshi
tai gun zamanta. A t’sanake ya karewa ajin
k’allo, tabbas nan Garba ya shigo dazun,dan daga
iskancin su yasan sune, yana jin lokacin da
malamin Hausa yake sanar da sauran iskancin
da suka masa. Ya kai a k’alla minti biyar yana
karantar ajin su Furen,yana k’allo takadiran cikin
d’aya na zungurar d’aya. Kai ya k’ada, kan ya ju
ya kan allo ya fara rubutu. “Chemistry” Shine
abinda ya rubuta. Fure ta ta6e baki. Juyowa
yai,kan ya bud’e baki cikin murya mai sanyi.
Cikin turanci yace sunan shi “Ahmad Abba
Ahmad”, shi zai na d’aukan su Chemistry daga
yau. Bayani yake musu,wanda tsit ka ke ji kamar
anyi ruwa an d’auke, dan d’uk iskancin su nasan
kure Malami a turanci yau sun gamu da bokan
turai. Class mastern su har zuwa yai leken ajin
dan jin yau shirun su da yai yawa, a tunanin shi
discipline master ne a ajin,da mamakin shi sai ya
ga Ahmad. Kai ya k’ada, lalle wai gaba da gaban
ta,Aljani ya taka wuta. Ko da aka tashi gulmar
Uncle Ahmad suke ta yi,daga suce mai girman
kai,sai su ce ya had’u amma. Suna hanyar tafiya
“hostel” suna ta shakiyancin su, kasancewar ss3
suna “practical” a “hall” yau su suke cin karan su
ba babbaka. Ko “lunch” basu tsaya k’ar6a ba
suka taho. A bak’in “gate” suka tsaya, ganin
Baba mai gadi na d’akin shi bai kuma gate d’in a
datse da “key”, maimakon suce ya bud’e musu
su shiga,kawai sai suka hau mishi wakar su ta
kullum,wanda har ya riga ya gane su Fure. ”
Baba a bud’e “gate” ko mu taru mu 6alla “gate”…
Shima kamar mai wakar daga d’akin nashi ya
basu amsa, “Ku taru ku 6alla,tunda gate d’in na
uban ku ne… Dariya su Fure suka sa, lalle ashe
mutumin su ne ” on duty”. Kawai sai suka bashi
amsa dan kawai suyi ta deban shi,, “K’warai na
uban mu ne,tunda Gomnati ta siya.. Da gora ya
fito daga d’akin yana bam-bami,” yau zan kawo
karshen iskancin nan naku,, “au Fure? Nasan
kece gandi lida, yau za kuyi bayani.. Dariya suka
sa mishi,” Baba namu,mukwa na Allah, muga
Annabi… Da gudu suka zuba, ganin ya bud’e gate
d’in yai Kansu da gora,, wuuu sukai “gate” d’in
kamar zasu 6alla suna mishi dariya,tun daga nan
aka fara yin d’ai-d’ai da kaya, daga su sai
underwear suka isa hostel. Washegari kuwa da
safe sai ga kira daga principal tana kiran Fure da
y’an Eysla d’ukansu.. Principal kam tasu ce,ba ko
shakka suka nufi office, sun san bazai wuce
fad’a akan surutun aji ba. Masinja ne yai kiran
Furen ita kad’ai zuwa ciki, yana zaune su biyu a
kujerar da ke gaban principal d’in, da ladabi ta
gaida principal, kan a ciki ta gaida su,d’ayan ne
kawai ya amsa,yayin da d’ayan ya d’auke kai.
Dagowa principal d’in tai,ganin Fure ce yasa ta
k’ada kai,”Furera” kai sunkuye ya ta k’warai
tace”Yes Mom, kai ta k’ada, kan tai murmushi, ”
Trouble marker” kenan,ai tunda naji SS2 ne nasan
sunan ki sai ya fito ciki. “Wai zaku 6allawa Baba
gate koh? Kai ta kara kasa dashi, “sorry Ma, kai
ta k’ada, ” ai kinfi kowa rashin ji, sannan kinfi
kowa tsoro. By Feenat Ja’afar.
9/29/16, 2:13 AM – Queen Safiyyert馃憫: “JUYA” 漏 Feenat Ja’afar. 5_Tuni tai narai-narai
da ido kamar zatai kuka tana k’allon PCn, “Momy
kiyi hakuri, kai momyn ta k’ada, ” last warning ”
kar na sake jin haka daga gare ki “Fure” kai ta
k’ada, kan tai godiya tai waje tana murnar ba ko
“punishment”. PC ta k’allo su Ahmad, wanda
suke k’allon yadda momyn ta bi Fure da k’allo
tana murmushi, ” yaran sun matukar shiga raina,
tun jss1 d’insu aka kawo ni, tun a sannan nasan
dasu,fitina, tsokana,ilimi d’uk yan su ne. Kai su
Ahmad suka k’ada, tare da mamakin saukin kan
principal d’in. An dawo a break yake da su, d’ane
wasu suke akan desk a zaune, wasu sun had’a
group ana shewa, chan ya hango Fure a tsakiya
tana ta zuba k’wainane, kofa ya buga,da sauri
kowa ya nemi waje ya zauna. Kamar jiya,yau ma
ya kare musu k’allo, magana principal ya fara tan
tama na anya yaran suna da kok’ari? Akan Fure
ya dire idon shi wace ke fito da irin “Text book”
d’in shi a jaka. Ciki ya shiga,kan zasu gaida shi
ya zaunar su. Daga inda ya tsaya jiya ya
tashi,suna tsaka da karatu ya k’allo desk d’in su
Fure, ture-ture suke kamar wasu yara kanana.
Alli ya saita su dashi ya hulla musu, da hannu
yace su mike, kan ya tambayi sunan su, “Fure”
ya kira ta, da sauri ta daga tana k’allon Y’an aji
da har sun fara kunshe dariyar su, tuni ta kicin-
kicin da fuska kamar zatai kuka. Gaban allo yace
ta fito. Hannu ya hard’e tare da zuba mata ido
cikin glass,ita tuni hankalinta yai kan y’an ajin,
bata zata ba ta tsinci tambayar shi gare ta. “can
you name the first 20 elements of the periodic
table pls?” Tsayuwa ta g’yara,dan yasan dak’yar
in ma ta sansu bare ta rike su.. Sai d’ai kan ya
karasa zancen zuci ya tsinci muryar ta cikin
sauri-sauri tana jero su kamar ma ita wasan yara
ta d’au ka. “Hydrogen,Helium,Lithium, Beryllium…
Ba ko shan numfashi ta dire masa su tana du6en
shi. Kai ya g’yada, kan ya sake jeho mata wata
tambayar,kiris yake jira ya sata kneeling. ”
electronic configuration of firs…. Da sauri ta
katse shi tare da karanto mishi, “Boron,carbon,
Nitrogen… Suma ta dire cikin sauri ba tare da ta
bari ya gama maganar ba,dariya y’an ajin suka
fara,tun itama tana dake wa har suka sa ta yi,
ajin ya k’alla, sai sukai tsit,itama ta kunshe tata,
bak’in kofa ya nuna mata da hannu, da mamaki
take k’allon kofar,wai tai “kneel down” ta daga
hannu ta rufe ido, tuni kuma ido sai ya raina
fata, dan taki jinin punishments,ga ya had’e rai
ba damar bada hakuri. Daga yin minti 5 ta fara
raki, shikam dalibai ya cigaba da koyarwa,jefi-jefi
yana d’an k’allo ta. Hawaye ta fara,da gefen
hannu take gogewa,gaba d’aya hannunta ya fara
sage wa, sai motsa K’afa take halamun ta gaji,
ya juyo da zummar kara k’allonta yaga tana
kuka, sai ya d’auke kai, y’an aji tuni aka shiga
taitayi,ganin Fure na kuka,dan sosai sunsan abin
da zai sa Pretty kuka babba ne. Ba’a fi minti uku
ba ya kara k’allo ta, ta cikin glass d’in ya d’an
rufe ido,bai so ta kaishi bango ba,kawai ya ki
jinin rawar kan nan na Fure ne. A hankali ya kira
sunanta ta bud’e ido, tuni har sunyi ja, d’aurewa
yai yace ta tashi taje ta zauna. A shag’wa6e ta
tashi tana d’an dingisawa, koh zama bata gama
ba aka k’ada, ya tattare kayan shi tare da d’an
k’allon yadda ta d’aura kanta akan desk hawaye
na zubowa. Da sauri ya d’auke kai dan kar su
gane yai waje, ai kamar jira suke sukai kan
Pretty suna lallashi. Har akazo k’wanciya in ta
tuno sai tai k’wafa, ita sam bata ga mey tai ba
da har ya sa ta kneeling. Shima d’ai Uncle
Ahmad d’in yana a d’akinsu dake cikin “staff
quarters” d’in, a ganin shi raini ne zaisa Fure yin
hakan,sai d’ai shi mai tausayi ne, tuno da yadda
take hawaye dazun d’uk sai ya ji ba dad’i. Ihun
y’an makaranta ne da ke “hostel” yasa shi tashi
da sauran y’an d’akin, tun zuwan shi wannan ne
na farko da akai ihun gardi,waje suka fitu,ganin
wasu malamai nayin hanyar hostel d’in yasa suka
bisu,ba kad’an ba yara ke gudu,wasu na fad’uwa,
d’uk anjijji ciwo wasu na kuka,kawai Fure ce ta
fad’o mishi,sai d’ai bai isa fidda ta cikin yawan
daliban ba. Washegari da safe a “area classis”
sai zancen jiyan ake, yana jin lokacin da aka ce
dayawa sunji ciwo,wasu na “dispensary “,kawai
sai ya samu kanshi da leka ajin su Fure,suma
d’ai maganar jiyan suke tayi,suna ganin shi suka
nutsu tare da g’yara zama. Juyawa yai,dan ganin
ba Fure a ajin,sai yai hanyar dispensaryn.
D’ang’walolo,tana k’wance sai wash! take tana
y’arfe hannu ana mata “dressing” d’in kafarta.
Murmushi yai, ganin dan ciwan amma take
wannan wash! d’in. Yana tsaye yaga an zaro
allura,Furen ya k’alla, ai kam ido ta zaro,”Allurar
mey za’a min? Tab! Baya ta ja kan ta mike tsaye,
“nifa na warke malam, na d’aina ma zazzabin,
mai allurar yace” kiyi hakuri kawai ki ju ya, dan
fa sai na miki. Kawai da mamakin shi yaga ta
6are baki tana kuka,kuma ba koh hawaye, dayar
y’ar “mate” d’insu tace”haba Pretty,allurar? A
masife ta k’allo ta,” eh din ina ruwan ki.
Murmushi yai,kan ya k’ada kai ya shiga cikin
“dispensaryn”. By Feenat Ja’afar.
9/29/16, 2:15 AM – Queen Safiyyert馃憫: “JUYA” 漏 Feenat Ja’afar. 6_Tana ganin shi ta
juyar da kai tare da d’aina kukan, ya koma gefen
da take, bata nufa ba taji yace “sannu Furera..
Da sauri ta dago,sam batai tsammanin bahaushe
ne ba, yafi mata kama da y’an chan kudu,fari
ne,dan sosai ya fita haske,mai sage siriri,da
tsayin shi,dan ya kere ta da kusan kai uku,da
gani mai hakuri ne, sai d’ai bai d’aukan raini.
Sosai yake da k’warjini, musamman agun y’an
mata. A hankali cikin sigar lallashi yace tai
hakuri a mata,kai ya k’auda, sai ta samu kanta
da d’an daga wa, gefen nashi yake take k’allo,
halamar bai son ganin abin,ido ta lumshe,lokacin
da taji tsinin allurar, “shikenan fa an gama, ido ta
bud’e, tare da sauke rigarta tana k’allon Uncle
Ahmad da har yanzu yaki k’allon ta, magani aka
zuba mata,dispensarern yace gobe ta dawo,
juyowa yai,lokacin da take k’ar6a. Tare suka
fito,tana d’an dingisa K’afa, shi kuma rike da
maganin da k’walin lemon da y’an k’wanarsu
suka kawo mata, mamakin ta yadda ya zamu mai
saukin kai,har aji ya rakata, a bak’in kofa ya
tsaya,tare da kiran Adama tazo ta k’ar6i kayan,
sudai y’an aji da ido suke binshi,sam ba wasa a
fuskar shi bare su tanka,tana zama ta k’allo shi,
hannu ya dago mata yana murmushi, itama sai ta
murmusa,baki sake suke k’allon su har ya juya
ya fita. Da sauri y’an class suka zo jin
gulma,wasu na Sonta yake Allah,harara ta basu,
“wani irin so? Ku fa baku kai. Ina,sukam y’an ajin
har aka tashi suna pretty ta uncle Ahmad. Tun
tana masifa har ta fara binsu da ido. Sai d’ai fa
ana zuwa bacci ta kasa sukuni, dan har yamma
sai da yazo duba ta,harda drinks d’inshi mai
sanyi da cake. Takan yawaita murmushi in ta
tuno shi,wanda ita kam a nata wayon bata san
meye ba.m Sai ya zamo Uncle Ahmad sun d’inke
da Fure sosai,d’uk da bai ce yana son nata
ba,asalima in yana ” teaching” yi yake kamar bai
san kowa ba a ajin,,dama kuma itace “class
captain” ta y’an iska,d’an ita d’uk randa akace ai
”noise maker” ranar take cewa kowa yai surutu
son rai,randa ba’a ce ai ba kuma zata chunkune
kaji aji tsit,tari kai sunan ka ya shiga. “Records”
na exams nasu suke su da uncle Ahmad, suna
karanto mishi ita da Adama,ga nan wata na musu
firfita,har Adama ta gama nata pretty ta fara.
Yadda take fidda lafazin cikin murya mai dad’in
sauraro kai kace tun daga “primary” ta samu
“good foundation”, sosai yake jin muryar ta har
tsakar kanshi, yakan rasa mey yake ji a game da
” pretty” in dai zai tsinkayi muryar ta. Jim
tai,yana jiran ta fad’i “next” tai murmushi,
“Furera muh’d, murmushi yai kan ta fad’a mishi
mark itama tana murmushin, Adama ta zunguri
mai firfita suna gulmar su. A zahiri kowa na son
kowa,amma sun kasa gano hakan,shi d’ai uncle
yasan yana yawan tunanin Pretty, amma sam bai
kawo so ba. K’wance tashi har sun kusa gama
service d’in su,a dalilin uncle Ahmad Fure ta
nutsu sosai,har d’aurin karatun addini yake musu
ita da K’awayenta,da nusar su yanzu sun girma
su daina kaza da kaza,,sosai kamar K’anwar shi
haka yake ji da ita,randa yai k’wanan waje in
bata ganshi ba d’uk sai taji kamar tana jin
zazzabi, d’uk a tunanin ta ba d’an KD bane. Ana
gobe zasu tafi lokacin su Fure na ss3,kuma ”
Head girl” Duk tabi tai laushi, a kofar aji suke a
dandamalin a zaune, kowa ya zuba musu na
mujiya,k’allonta yake ba ko kiftawa, ita kam kai
d’uke kamar ta sau kuka, a dan karatun littafin
soyayyarta ta zata sonta uncle d’in yake,ashe ba
haka bane,gashi har yau zai tafi bai furta mata
ba. In d’ai batai k’arya ba ita kan tasan ta rufta a
son shi,murmushi yake,”Furera” kai ta dago,da
dan murmushi a fuskar ta,”ki kula sosai,kinga kun
fara “practical”, kiyi karatu ko d’an ki fita da
result mai k’yau. Kai ta k’ada mishi, wayan shi
ne ya k’ada kirar” Blackberry” da murmushi ya
daga kan ya ambaci sunan “Mama” sai ya d’an
tashi ya matsa, sai da ya gama ya dawo
fuskarshi d’auke da murmushi, “Mama na gaida
Furera, murmushi tai kan ta k’ada kai,” ina
amsawa. Har address d’in Fure ya k’ar6a, da
alkawarin zai kawo mata ziyara har gida in sun
gama makaranta. K’warai ta d’aure ganin batai
kuka a gaban shi ba, sai d’ai yana tafiya ta k’ar6i
“pass” tai ”Hostel”. Kuka take wanda da
biyu,itama d’ai ta zurma d yawa, amma irin su
Uncle Ahmad tasan ba ajin su bane,wai k’warya
tabi k’warya, yadda yake da aji da k’yau tasan
yafi k’arfin ta, zuciya kawai ke yaudarar ta. Tun
tana damuwa da son Uncle Ahmad har ta jingine
shi ta hau karatun ta. In har da rabon zasu gana
kila ta ganshi. Sun gama “exams” kowa ya tafi
gida da k’ewar juna da dunbin k’yaututtukan
ta,sa6anin Adama da suke kusan unguwa d’aya
da Pretty. K’allon Fure Umman su take,d’uk ta
rame kibar nan ta dawo y’ar chas da ita,”har yau
ina mamakin ramar nan taki Furera,ko A’i batai
rabin ramarki ba data gama makaranta.
Murmushi tai,kan tace”Umma karatu ne, zai
maida kiba ta har da k’ari, kai ta k’ada, sai dai
har yau tana mamakin yadda Fure ta nutsu gaba
d’aya, ta zama wata irin sassanya,a zaton ta d’uk
makarantar ne, sai d’ai gashi har sun shafe wata
1 da gama makaranta Fure na yadda take,kawai
sai ta bada girma ne ya shigi Fure. Abu d’aya ke
ci mata tuwo a k’warya yadda shiru ba labarin
Uncle Ahmad, ga yadda tsabar tunanin shi ke
hanata sukuni,takanji zuciyarta na wani iri in ta
tuno shi, gashi ko numbern shi bata rike ba,
dabara ce ta fad’o mata,fatan ta Allah sa Abban
su yai saving numbern, dan tana yawaita kiran
shi da ita. By Feenat Ja’afar.
Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Apr 14
Feenat Ja’afar Novel’s
“JUYA” 漏 Feenat Ja’afar. 7_Da dare Abba ya
dawo a wajen aiki ta d’au wayan da nufin zata
kira k’awaye, d’akinsu ta kule,kan ta hau duba
“contact” “Fure schl” taga sunan wani contact,
tasan kenan numbern da take kiran Abba dashi
ne a makaranta, gabanta na fad’uwa tasa
numbern a “private” kan tai “dailing” g’yara
k’wanciya tai,tana sauraron yadda wayan ke
“ringing” bugun zuciyarta na k’aruwa, sai da ta
kusa yankewa har ta sadddak’ar ta sinkayi
sallamar shi da muryar da ke sata cikin nutsuwa.
Ido ta lumshe tana sauke numfashi da sauri,
hannu tasa a d’ai-d’ai zuciyarta dake mata
barazanar fitowa fili. “Da wa nake magana pls?
Sai a sannan ta bud’e ido,tama manta da ya
d’auka,sai da ya kara sallama kamin a hankali ta
zare wayan a k’unnenta tana hawaye ta kashe.
“Ashe ita kad’ai ma ta damu dashi? Kila ma shi
ya manta kashin wata Fure a wani gu, zatan ta
baya ma kasar, dan yasha sanarta “England” zai
je masters, ashe yana kasar a garin amma bai ko
neme ta ba har tsawan wannan lokacin… “Fure
lafiya? Umma ce ta katse ta,da sauri ta goge
hawayen tare da k’ak’alo murmushi, “ba komai
Umma,, da mamaki Umman tace “ba komai ki ke
kuka? Jin dad’i komai? Kai ta k’ada,tare da
kawar da zancen da cewa “yaushe Aisha zata
dawo Umma? Zama Umman tai,kan tace” a satin
nan zaki ganta, ai tasha hutu kusan wata biyu
kenan,amma Furera tun dawowar ki na fuskanci
kin sauya, kin zama shiru-shiru, kodai ba ki lafiya
ne? Kai ta k’ada kan a hankali ta zame ta
k’wanta cinyar Umman, “Umma ba komai,
makaranta make ma son shiga Umma. Kai ta
k’ada mata,” yana da k’yau, Allah shige
gaba,amma sai kin tsaida tunaninki waje d’aya,
gashi har yau kin kasa maida jikin ki,sai ma wata
ramar da naga kina yi. Kai ta k’ada mata,kan tai
ko’k’arin had’iye kukan ta. Gaba d’aya ta tattara
Uncle Ahmad ta jingine shi gefe,har numbern shi
ta ma goge,dan in d’ai ta motso mata in ba
muryar shi taji ba bata samun sa’ida, yanzu kam
Alhamdulillah, ta samu ta fara manta so,sai d’ai
“memoryn’ baya yana a K’wak’walwar ta. Yanzu
karatun ta kawai tasa a gaba,a bangaren
”catering”. Yaya Suleiman ya kamalla karatun shi
har an bashi aiki,yanzu burin shi aure,sai dai har
yau bama budurwar,babban burinshi kamin na
yanzu bai wuce ya tara kud’i ya tada ginin Abban
shi ba,dan sosai yake da murad’in iyayenshi suyi
nasu su huta da haya. InshaAllahu zaya hutar da
Abba aikin makanikanci bada jimawa ba,yai
alkawarin ji da iyayen su da y’an uwanshi dad’i
na duniya in har Allah ya bud’a. Albashin shi na
farko Abba da Umma ya direwa,a ganinshi su yafi
kamata su fara ci kamin kanshi, musamman
Abban su mai arzikin zuci,ya sani da Abban su
mai jajircewa ne mai kuma nema da guminsa,shi
yasa yake kara alfari dashi yake kuma neman
koyi da dabi’un shi. Zaune suke da
yamma,dawowar shi a aiki kenan suna zaune a
katuwar darduma a tsakar gida shida Umma da
sauran k’annen shi,yakan yi nishadi in ya ji shi
cikin gida haka da d’uk Familyn shi,Abba kawai
ya rage baya a cikin su,tad’in bikin Aisha suke da
Umma, yayinda Fure ke zaune tana taya su
Hassan da Hussaini “Assignment”,sai d’ai jefi-jefi
yayan nasu na sako ta cikin zancen. Ka gansu
g’wanin ban sha’awa, gidan su ba k’yara bare
hancini, kowa yana nan-nan da juna. Adama tai
sallama, cike da murnar ganin K’awarta ta shigo
gidan. Wani ihu da suka zuba kan Furen ta tashi
suka ruk’unk’umo juna, daga Umma har yayan
baki suka saka suna k’allon su,toh g’wara Umma
dama tasan halin Adama da Fure,amma shi da
mamaki kawai yake k’allon su musamman
Adama, sai da suka gama rawar kansu tukun
cikin kunya ta gaida Umma,kan ta sauke
k’allonta akan Ya Suleiman,da halamun kowa d’ai
yai katari da ” soul mate ” d’in shi, dan kasa tai
da kai,lokacin da ta gano waye shi,shikam
k’allonta kawai yake da murmushi,kai duk’e tace
“ina yini Ya Suleiman, Fure ce ta katse shi,”
Adama ce fa Yaya,ta girma koh? Murmushi yai
kan ya amsa,”ai sam ban gane Adama
ba,”2years” d’uk sun kara girma,koh Umma?
Murmushi ita d’ai Umma tai,da halamun ta gano
bak’in zaren. By Feenat Ja’afar.
Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Apr 14
Feenat Ja’afar Novel’s
“JUYA” 漏 Feenat Ja’afar. 8_D’aki suka shige,
suna firar yaushe gamo, “kawai ki kaje kikai
zamanki a Abuja abinki? Murmushi tai, kan ta
ware “pashminan” kanta, “k’awata Abuja tayi a
rayuwa, ke! Bari kawai, Allah kamar kar na dawo,
naci fa na k’wanta, hatta kayana wanken ake.
Hannu ta bata suka tafa tana “shege Ada,kinyi
k’yau ke kin ganki? ” ke d’ai bari, zama ta g’yara,
“kai k’awata yayan kun nan fa Allah sai had’uwa
yake kara yi, d’uk yafi y’an gidan nan k’yau fa..
Dariya ta tuntsire mata dashi, kan ta bata suka
tafa, ” dad’ina da k’awata ba fulako,ki ce munyi
kasuwa? Hannu ta kai bak’inta halamar tai a
hankali,”Allah dama ranar yace nai mishi
budurwa a unguwar nan,sai kuma naga shima
kamar ya zurma. Wasa-wasa d’ai zance ya
tabbata tsakanin Adama da Ya Suleiman, har
magana taje gidan su Ada, sosai ba wanda yakai
Fure son wannan had’i, sai kuma su da suka
k’ulla abunsu. Biki kam ya karato, d’uk da yazo a
lokacin da Fure ke shirin y’in Exams a school.
Tafe suke ita da Aisha da k’awayenta su biyu
daga saloon,ganan g’wagg’waran su a leda da
aka nad’a musu, k’awayen suka tsaida ‘Taxi”
suna sanar da Aisha sai goben, sauri suke, ganan
magriba ta wuce amma hanya d’uk “go slow”, sai
sunyi kamar zasu t’sallaka sai Fure ta
r’unkumota har wata motar ta taho, t’saki Aisha
tai,” wallahi kamar tashin k’auye kekam, da tuni
mun wuce sai wani rirrike ni kike. “A ke,rai d’aya
ne, a yadda kowa yake saurin nan muje wucewa
da garaje kawai sui ciki damu? Kai Aisha Amarya
ta k’ada,” toh ni kam zan t’sallaka, dan kinsan
Abba in ya dawo ya tarar bamu dawo ba fad’a
zai,in yaso randa mutane suka d’auke K’afa sai
kizo. Hijab d’inta ta rike,”wallahi baki isa ba.
Yanzun kam mota suna d’an nesa, hannun Furen
ta kama”ki biyo ni toh yanzun. Da d’an gudunta
Aisha tai gaba,sai jin Fure ta zame hannunta tai,
“tsaya ledar mu, ina, A’i har ta wuce,da sauri ta
ju ya da nifin ta t’sallaka t’saut’sayi, ashe wata
jar CRV ta kuts’o,da gani kuma sauri su ma suke,
gashi tazo t’sakiyar k’walta,ga ihun Aisha na tai
gudu ta karaso. Ga ihun “horn” din motar,d’uk sai
ta kasa gaba ta kasa baya,suka had’u da tsoron
k’walta suka rikita Fure,ido ta rintse,tare da
sakar ledar kayan a kasa ta rufe k’unnenta da
hannunta d’uk biyu, tasan ba makawa sai motar
nan tai ciki da ita. Jin shiru ba ai ciki da ita ba
saima hasken motar da ya dalle mata ido da dan
jin hayaniya yasa a hankali ta bud’e ido jiki na
ka’r-ka’rwa. “Da ke! ke da asara wallahi bamu
ba, so nai a yabimin ta kanki tunda kin gaji da
duniyar shi kuma ya tsaya.. Babbar mace ce,sai
d’ai da ka ganta zaka san isassiya ce mai ji da
kanta, k’allo d’aya zaka mata kasan naira na inda
take, fara ce mai kiba ba chan ba. Sam ita bama
ta lafiyar Furen take ba. Masifa take ma Fure
kamar ta rufeta da duka,gashi ita Furen ta tsaya
kem! Kamar an dasata a gun,har yanzu jikinta na
ka’r karwa, Aisha data karaso ita kad’ai ke bawa
Hajiyan hakuri,tare da ko’k’arin janye Fure. Wasu
da suka gaji suka zame bi ta gefe. Haka take ga
wanda yake ” driving “,tunda ya taka birki yake
k’allon wacce yaso ya bige, kamar wani wawa ya
sau baki yana k’allon Fure ba ko kiftawa, ganin
suna neman tafiya yasa da sauri ya 6alle murfin
mota yai gunsu, Hajiyan ta zata k’addamar musu
zai yi sai taja baya,yace”Momy shiga mota in zo
yanzu. Sai da yaga ta shiga mota yai gunsu
Furen,” Aisha. Da sauri Aisha ta dago,wanda
Fure itama tai saurin dagowa lokacin da zata
d’au ledar, “a pharmacy? Ba d’ai kai ne a motar
ba? Idon shi akan Fure yake yana murmushi,
yayin da itama Furen ta zuba mai ido ba koh
kiftawa. Tabbas itace,ya fad’a a zuciyar shi,sai
da Aisha ta kara magana kan ya juyo gare ta,
“kuyi hakuri amaryar mu,sam ban zata ku bane,
kan Fure ya dawo, ” Furera da fatan bakiji ciwo
ba?….Momy ce ta katse shi da cewa “Kai dare
fa na kara mana a titi, kabar wannan yaran dama
y’an titin ne daga gani mu tafi. Wai waya wa
yai,” toh Mom,coming. “Ku kara hakuri pls
Amarya, ya dubi Fure,da itama shi take k’allo ba
ko kiftawa, Aisha ma da mamakin ina yasan Fure
take, sai kuma mamakin uwar shi bala’e’iya,
Tana nan a haka har sukai sallama amma ita ta
kasa furta komai. Har ya shiga mota shima yana
waiwayen ta. Ko da suka je gida su Umma suna
ta tambayar su ina suka tsaya har haka? Furen
Aishan ta k’alla, “Umma amare ne sukai yawa a
garin,ga gidan mai kunshi ma acike. ”Toh ita
Furen mey ya same ta? Koh yunwar ce? Da sauri
Aisha ta k’ada kai, dan tasan in d’ai ta sanar da
Umma abinda ya faru yanzu zata rikice. Juyi
kawai take a katifa, har yanzun ta kasa
t’ant’ance murna take ko akasin haka? Ga Aisha
ta dameta da tambayar ina Ahmad yasan ta? Kai
kawai ta k’ada mata, kan tace itama bata sani
ba. Juyi ta kara yi,sai ga hawayen da tun dazu
take bidar su zubo sunki sai yanzun. “Dama
uncle Ahmad na garin nan har yanzu? Lalle
yanzu ta kara tabbatar da ihu kawai take bayan
hari, tunda har address ta bashi in yaso zai neme
ta. Haka ta lulluba tai mai isarta kan ta sa a
ranta indai tana da zuciya toh tabar tuna uncle
Ahmad. Suma chan su Momy tun a mota take ta
kara zagin su Fure,shi d’ai yai shiru,tunani ne fal
ranshi har suka zo gida. K’wance yake yana
k’allon” A.Cn d’akin nashi, kawai yanayin Fure
yake tuno wa, ashe Allah zai sa yaga Fure a
fad’in garin nan bayan rasa address d’inta da
wayar shi? Murmushi yai,a hankali ya
furta”Pretty” sai kuma ya gintse. Tabbas Fure na
matukar kama da Aisha,sannan sosai yasan
yayan Aishan a A.B.U,toh meye had’in su da
Fure? Dan tun dawowar Suleiman a dalilin auren
Aisha sau biyu yana zuwa gidan su,amma bai
ta6a ganin Fure ba… Gaban shi ne ya fad’i
sakamakon tunawa da zanchan su na jiya da
Suleiman d’in, kan wacce zai aura makarantar da
yai service tayi,kuma shekarun d’aya.. Kar fa ace
Furera ce wacca Suleiman zai aura? Kila koh
y’an uwa ne shi yasa suke kama… Cewar wata
zuciyar. Tashi yai zaune,dan tuno da g’yaran
amaren da suka sha ga uban lalle da kayan
g’wag’gwaro da suka fad’i kasa. By Feenat
Ja’afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com
9/29/16, 2:17 AM – Queen Safiyyert馃憫: [4/16, 12:30 PM] Feenat Ja’afar: “JUYA”
漏 Feenat Ja’afar.
9_Washegari “10am” a kofar gidan su Aisha ta
mai,a kofa ya same su, da halamun daga wani
waje suka dawo,tsaye suke da Ya Suleiman suna
ta nishadin su da dariya,tun a nesa kawai ya
bada hasashen shi ya zama gaskiya,toh amma
ita Furen wace tasu? Ina ne gidan su?
Tun tsayuwar shi Fure ta tsagaita dariyarta tana
dub’en motar,tabbas ta jiya ce, k’allonta Yayan
nasu yai,kan ya k’alli inda take k’allo, tuni fara’ar
shi ta karu tare da furta”A’a, AAA.. Kan yai
wajen shi,Aisha ma ta fara fara’a, ita kam kasa
tai da kai,dan ganin suna yin wajen su da Uncle
Ahmad d’in.
Idon shi na kanta,ganin yadda Yayan nasu ya
shiga t’sakiyar su ita da Aisha,da fara’a suka
gaisa da Aishan,kan itama tace”Uncle ina
k’wana.. Damm! Ya ji zuciyar shi ta buga,a
hankali ya amsa,tare da d’auke kai a kanta,
shikenan Pretty ta fita a rabon shi? Ido ya dan
rintse,”kai zurfin ciki bai ba a rayuwa, gashi yana
k’allo k’wado zai mishi K’afa.
Ya Suleiman ya k’allo shi, “nasan dama zaka
sansu, sai ya k’allo Fure da murmushi, itama ta
k’akalo murmushin dole. “she’s my.. Da sauri ya
tare mashi numfashi da fad’in” I know, sai yai
murmushi a takaice, kan ya k’allo Furen, Ya
Suleiman yace”ok,kun ta6a had’uwa a gidan ne
hala? Kai ya k’ada, duk sai ya ji tsayuwar ta
gundure shi,Aisha ce ta katse shi da fad’in
“Ina Angon ka barmin shi? sai kuma ta rufe fuska
ganin yadda Yayan su ya kafa mata ido, ” iyee!
Lalle fitsaru. Shikam murmushi yai kan
yace”yana a masaukin shi,zai zo bada jumawa
ba.
“Zan wuce, dama Ilyass ne yace na tabbatar da
lafiyar Madam d’in shi,sai mun had’u a ” Dinner “.
K’allo su Fure yai,”toh amare zan wuce,sai mun
had’u anjima, kai Fure ta k’ada mishi, kan ta d’au
ledar su ta shige gida,da tsabar takaici,ashe ma
ba dan ita yazo ba? Ajiye dilkar tai da suka
k’ar6o, tai ciki ta bar y’an biki a t’sakar gida.
Shikam a mota d’uk ya rasa sukuni, Fure ita ce
mace ta farko da ya fara jin ” feeling” akanta,
hatta Maman shi tasan da zancen Furera,yau da
ya sanarta yaga Furera k’warai ta tayashi
murna,har yaje gida sukuku yake jin kanshi. Sam
baida kuzari.
D’akin Maman shi ya zu6e, wanda indai maganar
mace ne toh dole sai wajen ta,amma sauran
lamari Momy ce ja gaba sama da Maman tashi.
Mata biyu ne ga Baban shi, Momy itace Uwar
gida,yayinda Mama ke amarya, d’uk a zankuwa
aka haife su, sai d’ai lokacin su Ahmad na yara,
kamin suka dawo Kaduna da zama gaba d’aya.
Baban su Alhaji Abba Ahmad “costom” ne kan
yai “resining” ya zama d’an k’wangila.
Sosai yana da kud’i, sannan da dattako, Momy
nada fad’a, sam taki jinin talaka,dan baban ta
babban “costom” ne lokacin da Alhaji Abba ya
aure ta.
Ga matukar dagawa da raina mutum,ga son fasa
taro,komai ita ke ju ya shi son ranta a
gidan,yaranta 3,Hauwa(Aunty Jidda), itace babba
a gidan,sai Nasir,da Huwaila, sai y’ar K’anwar ta
da take ruko Rukayya.
Kan aka auro Mama, d’uk itama gidan su ba
laifi,gata mace ce har mace,mai hakuri da
t’sabar sanin ya kamata,tana da kawaici, kullum
zaka samu fara’a k’wance kan fuskarta, da fari
Momy ba taso zama da kishiya ba sam ita,
sai d’ai kuma wani had’in Allah, kawai sai tasu
tazo d’aya, dan komai ta sakar mata ta
mallake,hatta yara in ta haifa toh sun koma
zaman d’akin Momy,ita kam dake mai hakuri
ce,d’uk sai ta sallama mata su, yaranta
shida,Usman, wanda shine mijin Aunty A’i, sai
Aunty Maryam,Ahmad,da Ummi autar ta rasu.
Amma d’aya kawai ta rike wato Ummi.
T’sakaninta da sauran sai gaisuwa koh in taje
bangaren Momyn,sai ko randa ta motso musu
suzo bangaren ta,dan ita k’wa6arsu take matuka,
amma a d’akin Momy sunan ka”kai komai ba
komai na”.
D’uk da mugun hali irin na Momy sam batai ma
yaran Mama mugunta,batta da mitar ta,hakan ne
yasa ita maman sam bata damuwa,sai d’ai abu
d’aya, duk yaran kad’an ne basu kin talaka da
raini,wannan dabi’ar ita kad’ai ke ciwa Mama
tuwo a k’warya.
Dan tamkar fad’an Allah d’uk yaran gidan sai mai
kud’i, in maza ne sai ya’yan manya masu k’yau.
Hudubar Momy kam tai aiki,Ahmad shine ya fita
daban,wanda sam baiya burin auran y’ar masu
dashi,sannan kuma k’yak’yawa.
Asali ma tun tashin Rukayya Momy tace itace
Matarshi, shikam fur yaki, dan ka’f ba abinda ta
bari a halin Momy,tamkar ita ta haifo ta.
Gadai k’yau har k’yau, amma sam ba hali. Shi
yasa ko dariya Ahmad bayayi a gaban ta,
asalima ita d’uk gidan shi tafi tsoro.
Takanyi ma Momy kukan sam Ahmad bai kula
ta,sannan ga hancinin tsiya. Momyn takance ta
k’wantar da hankalinta,Ahmad kamar ya zama
nata an gama.
Haka kowa yana da burin fita kasar waje yai
karatu a gidan amma banda Ahmad.
Rayuwa mai sauki shi ya za6arwa kanshi, kuma
a zahiri kowa a gidan naji da Ahmad, har sukan
kira shi da mai “ra’ayin kanshi”.
Anan ya had’u da Ilyasa,yayinda shi Ilyass yake
abokin Ya Suleiman. Nan suka k’ulla abota, duk
da kowa bangaren shi daban,sannan ba yadda za
ai ya nuna maka shi d’an wani ne,dan ko mota
bai ya zuwa da ita cikin A.B.U.
Ko Abban ne a yanzu d’ai da Ahmad yake yawo
ko ina zashi,tunda sauran manyan yaran kowa ya
kafu da K’afarshi.
Sosai Abban su yake son yaran shi,haka bai son
takura musu,yai musu sa6o da jin dadi,d’uk da
shi d’ai bai kin talaka,sannan baida wulakanci.
Mama ce ta k’allo Ahmad,” ya d’ai? Har ka dawo
a gun Fureran? Kawai sai ya k’wanto cinyarta
“Mama aure zatai go6e..” Ya Salam! Shine
kalmar da maman ta fad’a.
Kamar ya k’urma ihu haka yake ji.
“Ita ta fad’a maka? Kai ya girgiza, ” A’a, Aboki na
d’ai zata aura.
Kanshi ta shafa cikin sigar lallashi, “kai hakuri
toh,Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi, Amma
sosai nima d’uk da banga Furan nan ba ta shiga
raina. Nan tai ta bashi baki,kan matar mutum
kabarin shi.
By
Feenat Ja’afar.
[4/16, 1:44 PM] Feenat Ja’afar: “JUYA”
漏 Feenat Ja’afar.
10_Da k’yar ya iya shirya wa zuwa wajen
“Dinner”. Sosai yai k’yau cikin manyan kaya yau
da ya shige su,dan shi ma’abocin kanana ne.
Farar shaddar ta matukar k’ar6ar shi, ga hular
nan ta kama,sai kamshi yake kamar Angon ba
wai abokin Angon ba.
Parlourn Momy ya shiga,don sanarta ya fita.
Rukayya ce kawai a parlourn tai d’ai-d’ai a kujera
tana ” 2go”. Tana ganin shi ta mike da rawar kai
harda ce mishi yai k’yau, baki ya d’an ta6e kan
ya had’e rai”ina Momy? Da dan harara ta nuna
mishi d’aki ta koma ta k’wanta a ranta tana”ka’r-
ka’ra a d’aura mana aure ne,zaka shigo hannu.
Sukuku ta gama shiri tun jiya batta kuzari,
hakanne ma yasa Y’an uwan suke d’an sata
nishadi,amma da anjima zata dawo gidan jiya,su
sun d’auka koh rabuwa da Aisha ke sata haka.
Tsaye suke a gaban madubin su na katako a
d’akin su,kanta kawai take k’allo, matuka tai
k’yau tamkar wata k’yak’yawar. Tabbas in kana
da k’yau ance ka kara da wanka.
A d’uk k’walliyar k’ewayen idonta yafi ko’ina
d’aukar hankali.
Ma’abociyar ita gashin ido ce dana gira sune
tushen k’yanta. Yau sunsha” Mascara” da “eye
liner”. G’yaran jikin da fatarta ta samu ita ta
fidda ta zama ” Black Beauty”,
net ne “gown” “combination” d’in fari da “pink” a
jikin ta.
Daga sama aka sa farin zuwa chan g’wiwa,
kasan aka mishi tattara da “pink” d’in, da “head’
na “pink” da k’yali-k’yallin “silver”.
sosai tai k’yau ainun kamar itace amaryar.
d’uk da su masu karamin k’arfi ne amma ak’wai
zuciyar yi,dan sosai sun fitar da kansu
kunya,d’ai-d’ai g’warg’wadon hali Abba da Ya
Suleiman sun fitar su kunya.
Kawun su na Zaria shi ya d’au nauyin gado da
kujerun Aisha y’an zamani,sosai y’an uwa ma
sun musu kara abin sai son barka.
Adama ma tasha lefe Ya Suleiman kamar ba
go6e,ranar albashi yai rana da taimakon
makanikancin.
Aisha ce ta shigo ita ma sanye da” net”
“brown”.. Sosai tafi Fure k’yau,amma a yau d’uk
sun had’u sunyi k’yau sosai.
Gaban madubin taje tana murmushi, kanta ta
d’aura akan kafad’un Furen, ” y’ar uwa tamkar
kece amaryar kinyi k’yau ainun,, murmushi Fure
tai d’uk tai laushi, “ku nake tayawa k’yau tunda
kunyi k’yau kuma. Tai murmushi, “dan Allah
Furare mey ke damun ki? Tun randa abin nan ya
faru d’uk kin dawo wata iri, kinyi sanyi sosai,
“dazun naji kince ma “pharmacy” Uncle, amma
kince min baki sanshi ba,bayan Ya Suleiman yace
anan yai “service” a school d’inku,mey kike 6oye
min ne? Murmushi tai kad’an kan ta juyo, gaskiya
ta fad’a mata kan ta sanshi sosai.
Ido kawai ya zubawa kofar ” Hall” d’in dan jin
ana sowar ga Amare nan, Asha da Angonta ne a
gaba,sai gata ita da Ya Suleiman, sai dai shi ya
ju ya waje lokacin da ya gane Adama ta tsaya.
Ido ya rintse dan ganin lokacin da Ya Suleiman
ya rad’a ma Furen wani abu tana d’an tushe baki
da dariya. Tsayawa su Aishan sukai,har ta
karaso bai daga kanshi ba.
Tana daga kanta tai ar’ba dashi ido rufe,da sauri
ta d’auke kanta jin wani abu na taso mata a
zuciya wanda tuni ta rufe bab’in shi.
Sowar daya kara ji ne yasa ya bud’e ido,sai ga
Adama sun shigo da Ya Suleiman, da sauri ya
k’alli wajen su Aisha yaga Furen na tsaye tana
d’an murmushi tare da d’an had’a hannu tana
musu tafi a hankali.
Wata ajiyar zuciya ya saki tare da sakar
murmushin farin ciki.
“Dama Adama ce matar Eng.Suleiman? Kai
amma ansha dashi k’warai. Tashi yai Shima yana
d’an tafa musu da murmushi a fuska,kan a
hankali ya ju ya ga Fure, wacce itama da sa’a ta
k’allo shi,murmushi ta sakar mishi wanda kamar
dak’yar ya fito,kan ta d’auke kai a hankali.
Sosai ya famo mata wani ciwo,ga wani uban
k’yau da ya mata cikin manyan kaya yau d’aya,
dak’yar ta saita kanta.
Chan inda aka warewa abokan Ango da na Amare
ta nufa kai d’uke, kujerar da ke k’allon shi kawai
ta rage” empty ” shikam har yanzun k’allonta
yake har ta zauna.
Ana gabatar da abubuwa shikam Fure kawai ya
zubawa na mujiya,sosai tai mishi k’yaun ban
mamaki, ga wata nutsuwa da yaga tai bala’in
mishi, kamar ba Fureran da ya sani ba. Kowa ya
tashi,na taka rawa suna yi,na yawo nayi, sai ya
rage daga Fure sai Uncle Ahmad.
Kai duk’e ta gaida shi da sanyin murya,jin bai
amsa ba yasa ta dago,murmushi yake yayin da
idon shi ke k’anta. Sai ta samu kanta da kunyar
shi.
Da k’yar ta samu ta zame da wayyon Adama na
kiranta.
Binta yai da k’allo, yau d’aya Fure ta kara
mamaye zuciyarshi, bazai kuma kara sakacin ta
ku6uce mishi ba. Wa yaga “real Love’.
Daga ita har shi har aka tashi fara’a suke, ita
kam batasan tata ta meye ba.
Maimakon yadda suka zo su koma tare ita da
Amare,kawai sai mazajen su suka d’auke su,Ya
Suleiman yace ya had’a mishi da y’ar K’anwar
shi da wata cousin nasu.
Ba dan taso ba suka shiga motar,wata “civic”
baka mai k’yau.
Baya Sadiya tai saurin shiga,wai ita ta shiga
gaban. Haka tai sakare,kan ta bud’e ta shiga,ya
ja su.
A hankali yake tuki cikin nishad’i,ya kan d’an
k’allota kad’an kan yai murmushi, itama takan
d’an satar k’allon shi ta gefen ido, fuskarta
sake,sai d’ai ba walwala,kowa y kasa ce wa
kowa uffan.
“A.C ya kara,kan ya hankali ya kai hannu ya
k’unna wakar da in d’ai zai ji ta toh Fure ke fad’o
mishi, sai d’ai yau gata gare shi, a hankali ya d’au
“remote” ya d’anna “play” sai ga nan wakar
“Nothing gonna change my love you ta shigo.
Tsam ta nutsu, tare da sauraran b’aitin cikin
wakar,sai ta samu kanta da lumshe ido kamar
mai bacci,tare da jingina kai a kujerar motar.
k’allo ta yai,kan shima ya jingina a kujerar yana
tukin shi cikin nishad’i,tamkar ance an bashi
Fure.

See also  Bazawara Ce Hausa Novel Complete

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top