Kada Ki Kuskura Ki Riqa Yin Irin Wadannan Abubuwan Agaban Mijin Ki
1)yin tusa agaban mijinki zaisa ya rinqa ganin rashin kunyar ki yayi yawa
2) Kada kirinqa yawan sakatar hakora da tsinke sai ya rinqa gani qa zamtar hakan
3)Kada kibari mijinki yagane kina da masifar cintsiya
Mezai Hana kici abinki kamin yazo
4) Shan rake domin Yana canja Miki kamanni ko da anyi Miki magana bazaki iya maida amsa cikin kintsi ba
5) taunar qashi agaban mijinki qaqaqas qas saikace wata kura inama Ace kibari inya fita kici abinki cikin natsuwa
6)kwantar Kai agaban mijinki domin mafiyawan cin Maza basasun ganin gashi ahargitse
7)soshe soshen jiki ko Kai da yawan cin cingam cakal cakal
8) yawan zama da dauran qirji agida matukar ba wanka Zaki shiga ba
9)yawan zagi da ashar agaban mijinki
10)yawan Karya Kada kikuskura ki rinqa yima mijinki Karya Dan wataran ko gaskiya Kika fada baiza yarda ba
SIRRIN LAFIYAYYAR MACE
Duk macen da take fama da qarancin ni, I’ma yayi wannan
hadin
Domin wannan hadin Yana qyara jiki Kuma idan kina shayarwa Yana qara Miki ruwan nono
Idan kina fama da yawan ciwun Mara Yana magani Kuma Yana maganin Rama da macerwa fata
Kuma idan kina Shan wannan hadin akullun Zaki tsufa da
ni,I’ma
Hulba
Madara ko nono
Zaki Sami garin hulba babban cokali 2 kizuba atukunya Kisa ruwa kofi2 ki tafasa idan ya tafasa sai ki sauke ki tace ruwan zaki raba biyu ki dau daya ki hadashi da Madara ko nono maikyau Kisha Rabin Kuma sai da dare shima Zaki hadashi da Madara ko nono inda har kina Shan wannan hadin Baki ba qarancin ni, I’ma
Allah yasa mudace Amin BY Mmn WALIDA
HADIN DAN MANNAU
Ya,Yan Kankana
Ya,Yan kabawa
Zuma
Zaki niqa ya,Yan Kankana tareda ya,yan kabawa kiyi garin su sai ki Sami Zuma Mai kyau Kamar Rabin karamin Kofi sai ki zuba cokali goma na garin ya,Yan Kankana da kabewa acikin zumar ki jujjuya Shi ya hade sosai
Sai ki riqa laqata kina ci akai akai harki canye wannan hadin yana Kara Miki Dan,dano Kuma yanasa Mai gida yarinqa yawan ziyararki akai akai shiyassa ake Kira wannan hadin Dan mannau
Allah yasa mudace AminBY Mmn WALIDA
GERIMAH