Kaddarar Sumayya Hausa Novel
ƘADDARAR SUMAYYA
ƊANDANO
…Duk da ganin cewa zan bankaɗo wani babban sirrina ne, amma hakan bai dakatar da ni daga faɗin abun da mutane ke son ji ba. Duba da yadda mutane su ka zura min ido don jin yadda ta kaya, amma ban yi ƙasa a gwiwa ba don na san wannan babban lamari ne da ya haɗa da ƙwatar min haƙƙina, wanda aka zalunce ni wasu shakaru da suka gabata, matuƙar Nabila ta tabbata ƴarsa. Take na yi ajiyar zuciya, sannan na yi gyaran murya, ba tare da tsoro ko wata fargaba ba na juya na kalli lauyata wacce ta ƙura min ido tana jiran martanin da zan ba ta, na ce, “ku saurara”, sannan na dubi kotu na fara:
A zahirin gaskiya ban kasance mai tsallake maganar iyayena ba, ba kuma don in yabi kaina nake faɗin cewa ina iyakar ƙoƙarina waje faranta musu ba, a’a sai don in nuna cewa tabbas iyayena suna alfahari da ni a matsayin ƴarsu da na kasance mai jin maganarsu da kuma biyayya a gare su daidai gwargwado. Bisa ga wannan dalili iyayena suke min duk abun da nake so matuƙar bai saɓa wata ƙa’ida ko doka ko kuma cin karo da addini da al’adunmu ba. Daga cikin manyan abubuwan da iyayena suka yi ƙoƙarin cika min buri a kai shi ne ci gaba da karatu a makarantun gaba da sakandare, jami’a.
Lokacin da na shiga jami’a na ga abubuwa daban da yadda na saba ganinsu a makarantar sakandare, kodayake daman an ba ni labarin abun da zan je in tarar. Cikin ikon Allah ban tsaya ɓata lokacina wajen shiririta irin ta ƴan bana-bakwai ɗin nan ba, sai na mayar da hankalina kan karatuna saboda kada na ba wa iyayena kunya, sakamakon irin sadaukarwa da soyayyar da suka nuna min wajen ganin na yi karatu, duk da hakan wani sabon abu ne a danginmu, wato ba a barin mace ta yi karatu, amma daga kaina aka fara. Don haka, sai na ƙudiri aniyar jajircewa don kasancewa abun alfahari a wajensu da sanya su farin ciki, da kuma kore shakkun mai shakku game da abun da na je yi jami’a.
Allah Sarki buwayi gagara misali, Shi kaɗai ne gatan bayinSa a duk inda suke. Shi Ya halicce su kuma Ya ke kula da su, sannan Ya jarabce su ta inda Ya ke so kuma Ya kare su daga dukkan sharri. Kwance tashi har Allah Ya kawo mu aji uku, kuma cikin ikonSa na kasance abun kwatance a ajinmu. Hatta malamanmu suna kwatance da ni wajen mayar da hankali kan karatu da kuma cin jarrabawa. In taƙaice muku dai, tun daga aji ɗaya nake cin ta-daya a ajinmu, abun da a bokonce ake ƙira First Class har zuwa aji uku. Tabbas godiya ta tabbata ga Allah Madaukaki.
Haƙiƙa da bawa ya san abun da zai faru da shi a wasu wurare, da ko za a fitar da ransa ba zai taɓa tunkararsu ba. Amma an ce ƙaddara ta riga fata kuma babu yadda bawa zai yi da ita. A wannan shekarar da ta kasance shekarata ta uku a jami’a a fuskanci tashin hankalin da ban taɓa fuskanta ba a tarihin rayuwata. Na shiga damuwa matsananciya, na yi kuka na zubar da hawaye, amma babu wanda zai share min. Na shiga damuwa, amma babu wanda zai rarrashe ni. Na yi kukan zuci, amma babu wanda ya san zafin da ke ruruwa a cikin zuciyata.
A cikin jerin satukan da ba zan taɓa mantawa da su ba cikin rayuwar da nayi a jami’a, na ke ta fama da ƙananun ciwo a tsaitsaye sai dai ban samu na je asibiti an duba ni ba tunda wasu lokutan idan na sha magani na kan ɗanji dama-dama, a gefe guda kuma hidimar karatu ta bada gudunmawa da ban samu damar zuwa asibitin a kan kari ba. Sai wata safiya da na tashi da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai, na sha magani amma abin ya ci tura don haka a wannan ranar na yanke shawarar zuwa ganin likita, duk da cewa nima ɗaliba ce dake karantar fannin lafiya ce amma na na yanke wannan shawarar musamman ganin yadda na ba wa kaina duk wani taimakon gaggawa da nasan zan iya amma na kasa jin daɗin jikin nawa. Don haka cikin dauriya na kimtsa sannan na yiwa abokan karatuna sallama tare da shaida musu inda na nufa, duk da wasu daga cikinsu sun so na jira su dawo daga karatu su rakani amma na tubure, don haka fatan dawowa lafiya kawai suka min na tafi.
Sai da naje ƙananun asibitin cikin unguwa guda biyu kafin daga baya na yanke shawarar tafiya babban asibiti, saboda sakamakon da suke faɗamin hankalina bai ɗauka ba, sai dai na danganta hakan da rashin sanin makamar aiki da kuma rashin kwararrun kayan aikin da muke fama da su a wasu daga cikin ƙananun asibitinmu.
Tamkar ɗaukewar ruwan sama haka duk wata jijiya da ke jikina ta tsaya cak da aiki na wucin gadi, abin alfaharin mujiyana ƙyam abkan Magidancin likitan da na ke zaune a gabansa, maganar da ya kuma yi ce ta dawo da ni daga duniyar ɗimautar da na tafi, har a lokacin nutsuwata ba ta dawo ba sai dai na yi ƙoƙarin buɗe kunnuwana don na saurare sa.
“Madam sai kin kula sosai da ƙa’idojin da na faɗa miki saboda gujewa duk wata matsala da za ta shafi abin da ke cikinki. Allah ya raba lafiya” Ya faɗa da murmushi a fuskarsa yana miƙomin farar takarda.
Cikin dauriya na yi murmushin yaƙe cikin jarumta da son warware abinda ya naɗe harshena Na ce, “Nagode Likita, zan kiyaye Insha Allah.”
Na miƙe da ƙyar a ƙoƙarina na son barin ofishin likitan tunda dai ya sallameni, na sake ware idona saboda yadda na ke gani kamar wacce ke yanayin maye, a wannan lokacin ƙwaƙwalwata na ƙoƙarin tantance gaskiya da akasinta don har yanzu wani sashi na zuciyata ya kasa gamsuwa da cewa ina da shigar ciki har na wata uku a jikina, to a wani dalili zan yarda da hakan bayan ni ba aure na taɓa yi ba, ban kusanci zina ba kuma babu wanda ya taɓa keta haddina.
Taku ɗaya, biyu, ban kai ga na ukun ba ƙafata ta riƙe tsam! kamar bishiyar da jijiyoyinta ke ƙarƙashin ƙasa. Sharaff! Na yanke jiki na faɗi kamar tsuntsu da aka harbo daga sama, ban sake sanin halin da na shiga ba sai bayan wani lokaci.
A hankali na ke buɗe idona har na buɗe su gabaɗaya, jina da nayi a kwance yasa na fara addu’ar Allah yasa mafarki nayi ba gaske bane. Sai dai kash! Hasashena bai tabbata ba saboda zafin da naji a hannuna na dama wanda hakan ya tilasta ni kallon hannun, ɗaurin ƙarin ruwa na gani, hakan ya tabbatar min cewa a gadon marasa lafiya na ke kwance. Lokaci guda kuma na shiga tariyo abin da Likita ya faɗamin wanda nasan ko shakkah babu silar da ta sa nake kwance a nan kenan, domin na tuna cewa na miƙe zan bar ofishin Likitan sai dai ban kai ga fitan ba, hakan ya ba ni tabbacin cewa lallai suma na yi.
Juna biyu! Kalmar da ke wa zuciyata barazanar fiddo ta ƙasa kenan, ta ya ya zan samu shigar juna biyu? Ta ya ya ? Na kasa samun amsar tambayar da zuciyata ke aikawa ƙwaƙwalwata.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” Na ji harshe na ya taimakawa laɓɓana wajen furtawa. Kamar tsuntsun da ya fita a tarko haka na ci gaba da ambaton kalmar da faɗar ta ke rage raɗaɗin da zuciyata ke yi. Na ɗau tsawon lokaci a haka kafin na ji nutsuwa ta fara samuwa a jikina, sai a lokacin kuma na shiga nazarin maganganun Likita a gareni, ba shi ne wanda na fara ziyarta ba, na ziyarci likitoci biyu kuma irin sakamakon da suka faɗa ya maimaita min, sai dai bansan me yasa na shi ya girgiza tunani na sosai ba, amma na danganta hakan da sakamakon gwajin hoto da ya sa aka min. Abin da ya ɗauremin kai shi ne ya aka yi a matsayina na ɗalibar da ke karantar kiwon lafiyar mata a jami’a na kasa fahimtar juna biyu a tattare da ni har tsawon wannan lokaci, na karanta hanyoyin da ciki zai iya samuwa a mahaifar mace kuma na tabbata a duka waɗannan hanyoyi babu wanda na aikata. Ko me ya ke shirin faruwa da ni?.
“Kaicona! Ni Sumayya, Ya Allah wani laifi na aikata mai muni haka da wannan rikitacciyar ƙaddara ta same ni.” Na faɗa lokacin da wani kuka me ciwo da ya daɗe yana ɓoye kansa cikin zuciyata ya fito fili, hakan ya ba wa ma’aikaciyar jinyar da bansan da zamanta a ɗakin ba damar ƙarasowa gaban gadon nawa tana jera sannu a gare ni tare da bani baki…
N400. Ga me buƙatar PDF WhatsApp 09041186879.
Jiddah Bint Muhammad
Mohiddeen Ahmad
Sumayyat Musa Abubakar
Ummi Aliyu
Ina gaisua