Sirrin Rike Miji

Kalaman Soyayya Masu Dadi Domin Saurayi da Budurwa Pdf

Kalaman Soyayya Masu Dadi Domin Saurayi da Budurwa Pdf

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Kalaman Soyayya Masu Dadi Domin Saurayi da Budurwa Pdf

Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wacce ta fi tauraro da duk wani haske. Haske a idanuwa na, Ina fatan dai ba fushi kike da ni ba. Zan iya manta komai amma ka sani ba zan iya mantaka ba haka kuma zan iya jure rashin komai amma ba zan iya jure rashinka ba, hakika daga jiya zuwa yau ina cikin kunci mara misaltuwa, bakin ciki y ziyarci zuciya ta wanda har kawo i-yanzu ba na jin zan iya kula wani cikin walwala.

Kalaman soyayya

Idan har na ce zan iya na yi karya domin ni kadai na san irin halin da nake ciki na rashin jin dadin tafiyarka. Zuciyata na tafasa har nakan ji tamkar na fashe da kuka ka sani cewa, wannan sakon duciyata na sanar da kai, hannu aikinsa rubutawa ba wai ina fada ne don tsari ko don ka ji dadi ba.

 

Daga lokacin da ka hada yanaka-yanaka ka yi gaba ni ma daga wannan lokacin na tattara duk wani walwala na da farin ciki na na ajjiye su a can gefe barin da ba za su taba kusanto ni ba. Don haka ina sanar da kai ban yi fushi da abin da ka aikata ba kuma ban kiraka don ka bar abin da kake ba, illah na kira ka na ji laifin ba daga gare ni yake ba. Ka kasance cikin farin ciki ka huta lafiya. Na gode da kulawa, amma ina ga ba ki kai ni shiga kewa da zullumi ba, dama an ce ba a sanin muhimmancin mutum sosai sai a lokacin da ya yi nisa da kai.Hakika jiya na kara gasgata wannan maganar.

Kalaman Soyayya Masu Dadi Domin Saurayi da Budurwa Pdf

Domin nisanta da na yi da ke na yini daya sai na ji kamar shekaru dubu ne, Kin riga kin zama fatar jikina duk wanda ya raba ni da ke kamar ya raba ni da kyauna kwarjini na hade da suturata. Ke garkuwa ce a gare ni mai kare ni daga abubuwa da dama, Hasken zuciyata farin cikin raina, annashuwa da jin dadi na. Ina sonki ina kaunar ki, ba zan iya nisa da ke ba. Ba zan bar ki ba duk rintsi duk wuya, Sai dai in ke kika bar ni zuciya kuwa ba ta fatan ko mafarkin hakan balle a gaske. Ina so ki sani cewa soyayyarki ta yi nisa cikin zuciyata.

 

A hankali – a hankali ina ta ba ki filayen zuciyata ina so in rasa kaina a garin yin hakan ta yadda ba zan taba samuwa ba da sannu sannu dai ina ta mika rayuwata izuwa gareki ya masoyiyata kinzama abar kaunata wannan duk saboda karamcin kine a gare ni a yayin da nake kara kusantuwa dake duk tunane-tunane na suka fara bayyana ya masoyiyata kin zama abar kaunata kamar giza-gizai haka kika zamo inuwa a gare ni kamar ruwan sama haka kika jike ni da farin ciki kamar iska haka kika tafi da tunani na kin sabunta kaddarata ta hanyar samar da sabuwar safiya a rayuwata.

 

Dake kawai nake son kare rayuwata ya masoyiyata kin zama abar kaunata Kada ki taba mantawa da cewar wani na rayuwa ne kawai saboda ke ko ina zaki je ki tuna da hakan wani na rayuwa ne kawai saboda ke a duk inda kike ina miki fatan aminci addu’ar da zuciyata keyi kenan tamkar kyakkyawar abokiyar alaka haka rayuwa take idan kina tare dani a duk lokacin da kika yi nesa dani rayuwar sai ta zame mun ba dadi irin son da nake miki ta yaya zan iya bayyana shi wadannan idanuwan nawa tsahon dare suna tsayawa cur! kuma sunayin kuka duk da kasancewar ina tare dake me yasa nake jin kewarki? na kasa fahimtar miye hakan ki fada mun har na same ki duk da haka ina nesa da ke.

Yayin da kika iso bakin kofar zuciyata na sadaukar da rayuwata ga sunanki na koyi yadda zan rayu masoyiyata ada ban taba koyon yaya zan rayu ba ban taba koyon yadda zan rayu ba tare dake ba, masoyiyata wadannan yabo ne na gaskiya nake miki da zuciyata yayin da na same ki sai duniyata ta kawatu matuka duniyata ta cika burinta duk kanmu ba a ciki muke ba yanzu ne da muka hadu muka zama daya.

 

Ina ma a ce na kasance da ke a duk bugun numfashina, kaunarki ce take kara tasiri a ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarki, ya kuma zamana ni ne sanadin hakan. Bana son Allah ya kawo lokacin da za ki fushi da ni sosai kaina ba zai dauka ba, hakika Allah ya wadata ki da abin da mata da yawa suke nema sun rasa ke kanki kin san a cikin jinsinku, mata irinku kadan ne da a ce na iya rubuta labari da a kan fuskarki zan rubuta littafi mai suna kyauta daga Allah, kuma na san zan samu bayanan rubutu kamar guda uku 1,2 da 3.

Kalaman Soyayya Masu Dadi Domin Saurayi da Budurwa Pdf

Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran kasa na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take da soyayyarki ba ta gushewa kamar yadda taurari ba sa gushewa a sararin samaniya, ba ta kafe wa kamar yadda teku ba ta kafe wa, haka zalika ba ta bushe wa kamar yadda ciyayi ba kamar sukan bushe, soyayyarki dauwamammiya ce a farfajiyar madinan zuciyata da akwai wanda zai tsaga jikina da ya ga jininki yana gudana, a kan kaunarki na manta kaina, kikan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, wannan sunan da kika boye a tafin hannunki idan dare ya yi, ki duba sararin samaniya kin ga mai wannan sunan yana haska duniya masoyiyata, hakika na kasance mai bayyana a mafarkinki kin kasance a fatar lebena. Duk wani taku da na yi a doran duniya sai inji takun na iso ni zuwa gare ki. So marurun zuciya ya yi min saka tun asali so ya shige zuciyata yana min suka.

Ganinki burina, idanuwana ko bacci na farka ki amshi soyayyata abadan kada na koka ba ni barinki cikin kunci yaki zo na yi miki tarba. Daga motsin numfashina kika ziyarci rayuwata a matsayin abokiyar rayuwa a duk zantukana sai na ambace ki. Damuwarki kullum tana cikin tinanina ke ce jin dadina kuma ke ce bacin raina ke kadai ce a zuciyata kalamaina, zabina jin dadina, bacin raina, saboda da ke kawai nake rayuwata, kaunarki ce ke kula da ni take kuma kau da duk wata damuwa daga raina koda a ce babu ni ka san tuwata zan zamana a tare da ke har abada. Kamar yanda baki bai isa ya furta ba haka jiki bai isa ya nuna ba, sannan zuciya ta yi kadan ta kwatanta ruhinki ne kadai ya san yadda nake jinki a sakamakon ziyartar da yake yi wa ruhina a kowane dare ina sonki ba zan daina ba har abada saboda ban isa na daina ba.

Karanta Kalaman soyayya masu dadi

Soyayyata da ke ba ta mutuwa kuma ba ta tsoran mutuwa koda za a yi mana kwace, ko da za mu mutu ko za mu lalace to soyayyar mu za ta kasance a raye na bayar da zuciyata na karbi ta ki na kamu da sonki. Ki tallafi rayuwata da ta tsunduma a kan tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar da ta shagala a kan tsananin soyayyarki ka da rintsi ko zugar mahassada ya sa ki guje ni ko kuma ki rage son da kike min, sonki yana dankare a zuciyata kamar yadda kwakwalwa ke dankare a kan dan’adam da a ce zan samu ikon fito miki da shi da na yi domin ki kara gazgata tsananin kaunar da nake miki.

 

 

Kalaman Soyayya Masu Dadi Domin Saurayi da Budurwa Pdf

Labarin Zainab Da Mubarak (7)

 

Har zuciyarsa ta burge ta sosai don ya iya tsari sai dai kuma ta san ba zai yiyu ta aure shi ba, cikin sauri ta kawar da wannan tunani ta ce “ai na za ta ba zuwa za kai ba, sai dai shi har yanzu ya kasa daina kallonta, shi ma kwalliyar da ta yi ta dauke hankalinsa gaba daya. Wani Material ta saka (Purple) wanda aka ratsa masa (pink colour) a jiki, dinkin riga da siket sai kuma ta dauko (pink) din mayafi ta dora a kai shi ma takalmin ya dace da mayafin jikinta, a hankali ya saki ajjiyar zuciya tare da murmushi ya ce “ Ni na Isa?, kin san ganinki ya fiye min komai” Sai fa ya zuba wa Zeey ido da colour da ke gefen precious wani irin wanda ya sa duk ta bi ta tsargu don kunya, ta sunkuyar da kanta ya ce “’yan mata adon gari, kin yi shiru, ko rowar muryar ake mana?” Ita dai Zeey colour ji take tamkar mafarki take yi, don ta tabbata duk wanda ya ga Seif dole ne ya yaba tsarinsa, precious ta yi gaskiya Saif yana da kyau sosai kuma gashi ya iya kwalliya don duk ya hada komai na kyau wanda ake bukatar a ga da namiji da shi, fari ne kyakkyawa na kin karawa, gashi dogo, hancinsa dogo, bakinsa dai-dai misali, idanuwansa gwanin ban sha’awa, gashin kansa akwance yake irin na Fulani.

 

 

 

Hasali ma ga iya furta zance sai dai kuma abin da ta lura da shi akwai jiji da kai hakan kuwa ba ya daga cikin tsarinta. Ta kale shi ta yi shiru na dan wasu dakiku kanar ba za ta yi magana ba, daga bisani kuma ta ce “Uhm..! Ya kake?, ya kuma hanya?”, Saif ya ce “ Lafiya lau, ina fatan dai kina kula min da baby na ko?” Ita dai Zeey colour har ta kagu tabar wajen ta koma ciki, a ganinta ya fiya kallo, a hankali ta danyi murmushi ta ce “Kamar ka sani, kullum ni nake kula da ita”, Precious kuwa har zuciyarta ji take kamar tafi kowa farin ciki don ganin gata ga Saif , cikin fara’a precious ta ce “ Wannan ita ce kawata Zainab ana kiranta da Zeey colour wadda nake ba ka labari ba ni da Aminiya kamar ta” Saif ya tsura mata idanu yanayin yanda take magana yana burge shi hakan ya sa ya ci gaba da saurarenta tare da bin kallon bakinta da yake motsi.

 

 

KALAMAN SOYAYYA DOMIN ITA KECE ZABI NA

 

 

 

Farkon Sallama Cikin Salamar Samun Sa,a Da Murnar Kasantuwa Cikin Dausayin Ni,imar Sanyin Murmushin Labban Bakinki.

 

 

 

Idan Sautin Zancena Zaiyi Furucin Gaisuwa Agareki Yazama Dole Na Tunkari Gagarumin Murmushin Fuskarki Hakan Shine Zai Tabbatar Da Nutsuwa Acikin Ruhina.

 

 

 

Zahirin Zallar So Shine Yake Addabar Ruhina Shiyasa Zuciyata Ta Kuduri Aniyar Taimakon Ruhina Wajen Isar Da Sakona Agareki.

Kin Zarce Shiga Kinkai Bangon Kurewa Acikin Jerin Yan Matan Dake Takama Da Kyau Shiyasa Idona Baya Gajiya Da Kallonki Ayayinda Murmushina Yake Bayyanuwa Alokacinda Nake Kallonki.

 

 

 

Halittarki Ta Tsaru Kin Kware Wajen Iya Furta Zancen Bakinki Yaya Rayuwa Zata Kasantu Idan Har Banyi Tozali Da Murmushin Fuskarki Ba.

Kalaman Soyayya Masu Dadi Domin Saurayi da Budurwa Pdf

Bude Idanuwanki Kidubeni Tsananin Sonkine Ya Addabi Ruhina Dukkan Rayuwata Tatafi Akan Tsarin Daidaituwar Yawan Begenki.

 

 

 

Kizo Guna Muzauna Cikin Rayuwa Mafi Inganci Nidake Bazamu Rabeba Komai Wahalar Zaman Rayuwar Duniya Bazan Chanja Alakata Dakeba.

 

 

 

Yanayin Rayuwar Duniya Cikin Hikimar Tafiya Da Al,amurran Yau Dakuma Gobe Kullum Ina Kara Tozali Da Sabon Sonki Wanda Yake Shiga Acikin Raina Adukkan Lokacinda Idona Yake Kallon Tafiyarki.

 

 

 

Idan So Asaline Toh Ita Kauna Dolene Ta Zamto Tubali Na Musamman Idan Faruwar Hakan Tafaru Mezai Hanani Tunaninki?.

 

 

 

Sonki Yakai So Har Yakai Bana Ganin Zuwan Mai Zuwa Alokacinda Muka Zauna Atare Domin Kallon Fuskarki Yana Dauke Dukkan Nutsuwa Dakuma Hankalina.

12 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!