Kalaman Soyayya Masu Dadi

Kalaman soyayya

Kalaman Soyayya Masu Dadi

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ga wasu kalaman soyayya masu dadi wadanda zaku iya turawa masoyanku.

 

1. Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina Kinfita daban a cikin mata.

2. Ina son ki zamo mallakina a cikin mafarkina da kuma a zahiri, ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciyata. Fatana a kullum ki gamsu da cewa, Ina Son Ki.

3. Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba.

Sabbin Kalaman Soyayya

4. Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.

5. Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.

6. Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.

7. Burina a yanzu, bai wuce ganin na mallaki tauraruwar da haskenta ke haske sararin samaniya ba, a kowane dare. Wadda nake fatan ta haskake rayuwata da haske mara disashewa.

8. Ke ce dai wannan ɗin nan, wadda ke bayyana a cikin baccina, ko a lokacin da nake farke, da rana ko a cikin dare. Ina Son Ki.

9. A dukkan lokacin da muka yi nesa da juna, na kan ji da ma a ce akwai manyan tsaunika a kusa da ni, da na hau ko zan samu na hango murmushin fuskar nan naki mai taushi.

Na Yi Kewar Ki.

10. Zuwa ga za6in zuciyata, ina fatan ka sha ruwa lafiya? Ina fatan izuwa yanzu nutsuwa ta game jikinka, kishiruwa ta gushe daga makoshinka? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka.

11. Matukar zan cigaba da kasancewa a tare da ke, ba na jin hatsarin da nake ji ana cewa so yana da shi zan gamu da shi watarana. Ke ta daban ce kuma ta musamman a cikin rayuwata. Ina Son Ki.

 

Kalaman soyayya

 

12. Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ka.

13. Da a ce zan iya zama komai, da na zama ruwan hawaye a gare ka, a haife ni a cikin idanuwanka, na rayu a saman kumatunka, na mace a saman laɓɓanka. Ina son ka so mara misaltuwa. Barka Da Shan-ruwa.

14. Irin kulawar da kake nuna min a kullum na saka ni tinanin irin yadda rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Zan zamo tamkar sarauniya a gidanka, kai kuma zaka zamo sarkin da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ka.

Karanta Gidan Uncle Hausa Novel

15. A lokuta da wurare daban-daban ina ganin ka kana yi min gizo, ina ganin ka a lokacin da idanuwana ke a rufe ko a buɗe. Ba na iya yin komai ba tare da tinaninka ba.

16. Haduwarmu ta kasance ne bisa ‘kaddara, zamowar mu masoya ya faru ne bisa za6inmu, na bawa son ki gurbi a cikin zuciyata, ya zama dole ne a gare ni, saboda kin zamo wani ɓ6angare na rayuwata, haka kuma tinaninki ya zama masarrafin sarrafa akalar rayuwa da tinanina.

Ina son ki, so irin wanda gangar jiki take yi wa ruhi.

 

17. Ka amince mu yi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abun da ya kai samun masoyi dad’i, a duk lokacin da na rasaka ban san halin da zan shigaba, daga karshe ina mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin farin cikin ka a koda yaushe.

Karanta Yadda Amarya Zatayi a daren farko

18. So tamkar hasken rana yake da yake haske fuskar da take d’auke a jikin gangar jiki ma’abociyar zuciyar da take ‘kunshe da So. Kasantuwar so a cikin zuciya kan motsa ruhi ya kuma busar da idanuwa daga barin yin bacci a mafi yawancin dare, So kan samar da wasu rassa a cikin zuciya bayan bayyanar sa, wato bakin-ciki da kuma farin-ciki. Zan ci gaba da son ki a cikin kowane irin yanayi. Ina Son Ki.

1 Comment

1 Trackback / Pingback

  1. Salon Kwanciya Salon Gamsar Da Juna | My Novels

Leave a Reply

Your email address will not be published.