Kalaman soyayya masu ratsa zuciya
Tag: Kalaman soyayya masu ratsa zuciya
^Hotonki Ne a Cikin Madubin Xuciya
Shiyasa A Duk Lokacinda Na Kwanta
Bacci Sai Nayi Mafarki Da Kyawun
Surarki.
^Lallai Matuqar Mafarkina Xai Xamo
Gaskiya To Ba Shakkah Sarki Mai
Fadawa Da Rigar Alfarma Baxai Kai Ni
Matsayi Ba Domin Xan Kasance
Sadauki Jarumin Masoya Idan Na
Mallaki Sarauniya irinki.
^Ta Kowanne 6angare a Cikin Jikina
Babu Wata Sai Ke, Sakamakon Gangar
Jikina Tasan Da Xamanki A Matsayin
Inuwar Farin Cikina.
^Mafarkina Wani Babban Sirrin Ne A
Rayuwata Domin Idan Na Bayyana
Shi Kowa Yasan Kece a Cikinsa, Ba
Lallai Bane Masoya Su Barni In Xauna
Dake a Soyayya Sakamakon Kece
Tauraruwa Kuma Malama a Cikin
Fadar Masoya.
^Mafarkina Shine So Da Qaunarki
Dake Bayyana a Cikin Idanu, Idan
Har Kika Gasgata, To Xanyi Alfahari
Dake Matsayin Mai Tausayi Da Tallafi
A Cikin Xamantakewata Dake.
^Mafarki Da Kyawun Surarki Yana
Kore Min Soyayyar Wata “Ya Mace A
Fadin DUniyar Nan, Dan Ina da
Tabbacin Duk Irin Kyawun Wata “Ya
Mace Baxata Kai Kwatankwacin Irin
Naki Ba.
^A Duk Lokacinda Nayi Murmushi To
Mafarki Nake,Sakamakon Babu Wani
Sindari Dake Tunxura Ni a Cikin
Shauqi Sai Soyayyarki.
^Xuciyata Begenki Ne Nishadinta
Kuma Tana Qaunar Duk Wani Mai
Yabonki Wani Lokaci Ma Ina Bada
Kyautar Duk Abinda Na Mallaka Idan
An Ambaci Sunanki.
^Ki Rike Xuciyata Matsayin Amanar
Da Baxa Ta Guje Miki Ba Domin Nayi
Alkawarin Mafarkin Aurena Dake Sai
Ya Xamo Gaskiya Idan Mahalicci Ya
Yarda.
^Xan Rike Alkawari Kuma Xan
Gabatar Dashi Ga Al’umma Dan Kowa
Ma Ya Shaida Cewa Kece Xa6ina Tun
a Mafarkina.
^Yayinda Na Xamo Angonki Babu
Sauran Wani Muhallin Bakin Ciki a
Cikin Xuciyarki Sai Dai Ina Kyautata
Zatona Akan Cewa Xamu Rayu Tamkar
Uwace Tare Da “Yarta.
^Yayinda Nayi Mafarkin Hasken
Kwalliyarki Na Kan Yi Bacci Mai
Tsawo Da Armashi, Sakamakon
Haskenki Wani Mashahurin Abin
Qayatarwa Ne Ga Duk Wani
Ma’abocin Kallo
Inasonki Har a Cikin Rainah.