Sirrin Rike Miji

Kalaman Soyayya Na Kwanciya Bacci

Kalaman Soyayya Na Kwanciya Bacci

 

 

 

 

 

 

 

 

Kalaman Soyayya Na Kwanciya Bacci

Zuciyata ta riga ta saba da kai, ta yadda nake iya jin tamkar na zamo cikin jakarka a dukkan lokacin da ka tashi fita. Da tinaninka nake wuni idan ka fita, sai kuma ka dawo nake samun sukunin yin murmushi. Ina Son Ka Mijina.

 

 

 

HM! HMM!! HMMM!!!

 

 

 

Karda ka so 1, kuma karda ka so 2, amma dai ka ci-gaba da son 1 wadda ta mace a kan son ka. Mijina kai ne abun alfaharina da kuma ‘ya’yana. Ina Fatan Dawowarka Gida lafiya.

 

 

 

WANNAN SAK’ON ZUCIYATA NE ZUWA GA MALLAKINTA.

 

 

Kalmomi na kasancewa ma’abota sau’ki wajen furtawa a dukkan lokacin da SO ya kasance shi ne harshen furtawar. Zuciyata na yin haske a dukkan lokacin da muke tare, na kan shiga damuwa idan ka nesanta da ni. Duk da ka zamo mallakina amma zan so ka kasance mai kare min kanka daga harin da sauran mata zasu ke kawo maka a duk inda kake. A dawo lafiya.

Kalaman Soyayya Na Kwanciya Bacci

 

 

Zuwa Ga Matata:

 

 

 

KIN HASKA DUNIYATA.

 

Hotunan Yadda Ake Kwanciya Da Mace

Samuwarki a rayuwata ne ya koyar da ni har na san zahirin siffa ta SO. Sai bayan da muka yi aure na ‘kara fahimtar soyayya ta gaskiya. Ina fatan mu kasance a tare da juna na tsawan rayuwa har zuwa gidan Aljanna. Ina matu’kar son ki matata. Amma a lokacin da na dawo gida za ki ‘kara tabbatar da hakan. Hmm! Ina nan cike da zumud’in son zuwa cin girkinki mai dad’i.

 

 

 

‘DAYA TAMKAR DA GOMA.

 

 

 

Da akwai wata mace a cikin wannan duniya, wadda ta yi daban da sauran matan dake a gidajensu na aure. Ita ta kasance ta daban ce, halayanta kuma ababen so ne. Ba kowa bace face ke, a saboda haka nake ‘kara son ki a kullum. Ki kula min da kan ki, har zuwa lokacin da zan dawo gida kulawarki ta dawo hannuna. Ina Son Ki Matata.

Reference https://hausanovel.org.ng/kalaman-soyayya-na-kwanciya-bacci/

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!