KALLO DAYA HAUSA NOVEL
KALLO DAYA HAUSA NOVEL
page 1
0um hibban
Bismillahirr rahmanirrahim allahumma la sahla illa ma jaaltahu sahla waanta taj alal hazhna iza shiita sahla..
Start………..
Qara zuba mata rikitattun idanunsa yayi a karo na barkatai,innalillahi ta qara furtawa cikin qasa qasa da siririyar muryarta,ai ba ta qara tsinkewa da lamarinsa ba sai da taji ya qara daka mata tsawa cikin amonsa me nuna shi cikakken namiji ne yana cewa “wlh sai kin dago kin kalleni yadda nake kallonki dole nima ki biyani kallona ko nayi ta kuka “cikin tsananin mamakin jin furucinsa wai zai yi kuka kmr wani yaaro ta dago manyan idanunta ta sauke akansa amma me ta kasa hada idanu da shi ko na second daya ne ya ilahi ai kmr daga sama ta ji ya fadi qasa yana birgima sosaii tare da kuka kmr ta6ararrun yarannan..ba ta dawo dg duniyar tsoro da tsananin mamaki ba taji muryar hajia mama na fadin “subhanallahi ya akai yusif ya barshi ya fito hasbunallahu,,”cikin er qaramar fusata ta shiga qwalawa yusif kira da gaggawa ya fara hade matattakalar upstairs yana fadin gani mamma …wlh yau duka yake yaqi tsayawa nai masa askin kin ga hannuna cizona fa yayi sai da ya hudamin hannu ya fada yana pointing din yaransa guda daya,itadai deejah tazama statue kawai KALLO n ikon Allah take,ai qara taqarqarewa yai ya zunduma wani ihun da yafi na baya sauti yai kusa da hajia mama yana fadin ,”first luv ki ce ta kalleni zanyi kuka”idonta cike taff da,qwalla ta fara share masa na sa hawayen tana,fadin “yi haquri son zata kalleka amma karbi maganinka tukunna ta fada tana miqa ma yusif hannu da yake riqe da maganin da ya cire yanzun a sachet ba musu ya karba ta kora masa da ruwan gora…tajashi kan sofa tana patting bayanshi cikin sakanni kadan taga yai luf ….hajia mama ta dago tana dan murmushi tace ,”alhmdlh yayi barci ma dan sarara kafiin ya tashi…”KALLO deejah tabi kyakkyawar fuskarsa daita wai dan rigima sai kace wani yaaro wannan qasurgumin qaton ne yake childish character s ganin irin kallon da deejan ke ma sa na tsananin mamakine yasa hajia maama gyaran murya da cewa”
Ku biyoni a shafi na gaba
Pls comment dan samun qwarin guiwa
👀KALLO DAYA👀
Page 2
0um hibban
Start…….kiyi haquri deejay na barki ke kadai sallar dhuha(walha) nake bkm tace ….cikin natsuwa ta gaisheta bkm wlh dama ummana tace na fadamiki ta kammala miki kayan garar kuma ta kikkira number ki akashe shine tace wai ki aiko driven ya dauka…”yawwa” hajia mama tace cikin nuna jin dadin dattakon mahaifiyar deejen Allah yai ma ta baiwar cika alqawari,ba ta wasa da alqawari hajia mama ba ta dawo dg zancen zucin da take ba taji deejah na fadin sai anjima…saurin miqewa tayi tana qara satar KALLO n mutumin da ke barci a cinyar hajia maama wanda duk abinda take tsaf a idon hajia maman da tunda suka fara magana satar KALLO nsa take a fakaice…itama hajia maman ce ma ta tayi touh ki gaida ummar taki dakyau kuma ki ce ma ta wayarce ta fashe wlh son ne ya fasamin ita jiya ina bashi abinci…ki ce ma ta,zan aiko a dauka….ko da yake ma zamuyi waya tunda na ce akawomin Wata ta qarashe maganar tana shafa kwantacciyar sumar son din nata kmr yadda take cewa” a hnkli ta ce touh tana qarasa fita dg falon
A hnkli hajiyar ta mai da kallonta ga dan nata tana mai qare masa KALLO n tausayi a kunnensa ta rada masa” Allah baka lapia daana” kafin t dago kanta ta lula tunanin baya….
Pls comment and share
KALLO DAYA HAUSA NOVEL
Page 3-
0um hibban
Start……da sassarfa deejah ta fada matsakaicin tsakar gidansu tare da sallama a bakin ta umma da ke zaune akan er madaidaiciyar tabarma tana tsinkar danyen zogale ta dago da sauri hade da,sauke 6oyayyiyar ajiyar zuciya ta amsa,da “waalayki salaam”qarasawa kusa da ummar ta ta tai ta zauna tana dan murmushi qasa qasa ganin yadda mahaifiyar ta ta ta zuba ma ta idanu cike da tuhumar me yasa ta dade haka? Cikin boye damuwata tace”ummahta sallah na tarar tanayi sai da na tsaya ta idar”cikin rashin gamsuwa da cewa da wani abin bayan sallar da ta tarar hajja maman keyi tabbas akoi wani abu da ya dan razana diyar ta ta ta dan murmusa da cewa “sai kuma karen gidansu JB da ya koroki ko??”umman ta,qarasa suna er dariya qasa qasa….ta bude baki zata ce a,h malam mahaifinta ya fito dg bandaki hannunsa riqe da buta abinda dauke da,addua ya ajjiye butar yana nufar tabarmar shi ma ya zauna yana er dariya ya dubi deejan da cewa ;qyaleta uwata ai fa yanzun tunda ta gano akoi abinda ke tsorataki shkenan ta samu abin tsokanarki da shi” itama umman miqewa tayi domin duba dambunta da ta dora ta nufi hanyar madafinsu tana fadin”ai ni nayi shiru kuma” cikin er daga murya ta ce “wai tace za ta ayko drivernta ya dauka wayarta ce son ya fasa ma ta”cikin yanayin ko a jikinta ta fadi maganar daga cikin madafar ta ji umman nata na fadin “Allah sarki Mahmoud Allah ya kawo ma sa daukinsa”shi ma malam din miqewa yayi yana ta maimaita kalmar “amiin amiin”…..itadai deejah qarasa shigewarta daki tayi tana jujjuya abinda tagani gidan hajja maama da kuma kalaman ummanta akan son din da sai yanzun ta ji sunana na gsky ….oh ashe ummanta ma tasanshi tunda gashi tana adduar nema masa lpy…tana gama cire kayanta ta fada kan katifarta dan so take ta dan yi barci kafin lkcn tafiya islamiyyar su tayi…amma barcin yana fara Jakarta sai jin saukar ihun qannenta su uku ta ji a kunnenta…cikin masifa ta farka tana fadin” wai me ye matsalarku da ni ne”. Cikin irin shakiyansu su suka hada bakinsu wurin cewa “ZUMUNCI” su ka fada suna qyalqyala ma ta dariya…ai kam pillow ta wawuro tana jifansu da gudu su ka fice,suna kiran ummansu….dariya tayi tana fadin” Allah shiryamana ku” kana ta koma takwanta Amma me???? ta na rufe idanunta hoton duk abinda ya faru tsakaninta da son ke dawo.ma ta fess kmr a majigi…..
Karanta Jinin Abbana Hausa Novel
Cikin wani irin yanayi me wuyar fassarawa doctor isaac ya dago ya zubawa hajia maama ido wadda ta dade da fiddara n samun kyakkyawar amsa dg bakin Dr,…cikin turanci yake ma hajia maama bayanin cewa ba,wani cigaba akan lalurar son din na ta….cikin qwarin guiwa tace”alhmdlh bkm komai AllAh yai mana mai kyau ne”nan sukai sallama da dr ya kwashe kayansa sukai sallama ya tafi hajia ta maeda kallonta ga dan nata da take tsananin so ta shiga tofa masa ayatusshifa………caraf!!! taji ya riqe ma ta hannunta ya na wani zazzare manyan idanunsa akan mahaifiyar tasa kmr zai Daketa…. sai kuma ya hau qyalqyala wata irin daria me ban mamaki yanayi yana riqe ciki kafin daga baya ya hade raiii sosaii ya dawo asalin miskilinsa ya miqe ya shiga cire kayansa hajia maama na ganin hk tace”wanka ko son” gyada mata kai yayi cikin hanzari ta shige toilet ta tara.masa ruwa a bath…amma me kafin ta fito ta tarar yanata shafe bangon dakin da duk wani cream da yake kan madubinsa yanayi yana siririn fito dagashi sai boxer ajikinshi….
KALLO DAYA HAUSA NOVEL
Page 4
Oum hibban
Start……ta fa hannu hajia maama ta shiga yi duk da kasancewar Mahmoud dan ta ne na cikinta za ta iya qirga adadin ganin da tayi masa babu ko shirt ce a jikinka tun bayan balagarsa amma yanzun kalleshi tik!…tasan ma farar saa taci Da Allah yasa duk haukan nasa be taba yin total nudes ba amma da ya zatai dan wlh Allah yai masa qarfin jiki da zuciya tasan ba yadda zaai ta iya mayar masa da tufafinsa tunda duk idan bashi ya ga damar yin abu ba duk gidan ba bu me qarfin danneshi…..sai dai a faki idonsa ai masa allurar barci…..salati ta shiga yi tana fadin”son mene hk”? Ba tare da ya juyo ba cikin muryar asalin shagwababbun yaara ya shiga fadin”ni auren ta zanyi”……😨 cikin tsananin kidima da zaro idanuwa hajia ke fadin ita wa?? “Lokacin ya juyo ya sauke dubansa ga hajia ya shiga janyo hannunta har sai da ya danganata da kujerar da deejah ta zauna jiya…ya wani haye dai dai wurin da ta zauna yana tattakurewa misalin yadda deejah tayi …..sannan ya dago ya zubawa hajia maama idanunsa da yau taga sun dan yi wani ja ja ja….yana dan murmushi yace ,”ina sonta first luv,” ya na gama fadar hk ya miqe ita fa ganin Mahmoud take kmr me hnkli wani lokacin….yanzun wannan wane kalar tashin hnkli ne idan ba rigima ba wai aure a haka??? To ta ji auren yakeso yazaiyi da matar??? Kuma ma wazai dauki diyarsa lafiyayya ya ba ma mahaukaci??? Kuma mahaukacin me duka idan aka yi masa abinda ransa be yi dadi ba…..? Ba ta dawo dg zancen zucin da take ba ta ji sallamar JB aminin Mahmoud ne kafin da bayan haukacewarsa wanda yananan tare da shi be sauya ba yai sallama a karo na biyu yana nufar kujerar Da hajia mama ke zaune yana dan murmushi ya zube a qasa yana gaishe da hajia da ke ta washe baki tana fadin “ga jabiru ga jabiru”ya dan shiga sosa kaiii irin na er.kunyar nan yana fadin”hajia na sameku lpy…? Ya friend yake cike da faraa take bashi amsar ya shiga wanka …..ya miqe yai hnyar dakin Mahmoud din tare da amsawa hajia cewa maman nasa tana lpy…..yana murda handle din dakin ya jishi gam gam a rufe…nan ya shiga knocking yana fadin “friend open d door” jb ne amma shiru kakeji….tun suna zaton abin na wasa ne har hnklinsu ya fara tashi hajia tace wa jb bari mu dauko key’s mu duba na dakin tayi hanyar upstairs kenan yusif yai sallama hamdala tayi da fadin “yawwa yusif dauko key’s din gidannan a bude yayanku yau rikici yakeji ya sa lock a dakin “touh yace ya na hayewa upstairs din da hanzari ya dawo jb ya karba ya shiga gwaggwadawa sai gashi an bude …hakimce kan sofa suka ganshi hankalinsa kwane dagashi sai bathrobe yana ya miqe qafafuwansa yana duban wani bangaren kansa sukayi duk su ukun suna tmbyr menene kasancewar sun san hk yake idan yanason wani abin ….cikin yatsine fuska ya ce ma JB yana pointing hajia “taqimin auren ” cikin zazzaro idanuwa JB yace”aure??? Yusif ma yace” au me? Aure daii hajia mama ta fada tana labarta musu yadda sukai dashi daazun….sakale yayi yana jinsu tsafff…tana ga rufe bakinta ya hau daria sosaiii yanai mata thumb up alamar jinjina…da mamaki JB yace deejan gidan malam Bello limamin masallacin jumaa???? Da sauri hajja maama tace tabbas…..daria ya shiga yi,shi ma JB din yana fadin ba ta fi nihila ba fa ???gabadayanta baxata wuce 15 ba fa….cikin er tai mana yusif yace” idan fa metadata zaeyi bazata cika kofi ba”kafin ya rufe baki yaji wani bahagon naushi…a bakinsu kawai qarar yusif suka ji ba wanda ya kula da lokacin da akai dukan sai jini ta hanci da bakin yusif…JB ya jaaashi toilet yana masa sannu ya na wanke masa fuska yana fadin ,”mind ur tongue….akan kace baza ta fi cikin cup ba ne fa ya duke ka hajia dake bakin toilet din ke fadin “Allah yasa yaron nan ba da gaske yake ba”,”kafin da bayan lalurarsa ba ya fadar abinda ba hk ba”,”kafin yusif ficewa yayi daga toilet din sunai masa sannu ……
Ransa a hade suka dawo suka tarar dashi fuskarnan murtuk babu annuri ya dawo Mahmoud dinsa na asali sa shi suka yi a tsakiya ya wani qara hade raiii sosaii JB ya tsinka shirun da cewa “calm dawn friend za a aura ma ka ita amma da sharadi “mai da kallonsa ya yi ga hajia maama so ya ke ya samu tabbacin batun JB a fuskarta gyada masa kaii tayi dan gaskia bazata iya kantara qaryarnan da bakin ta ba kafin su ankara ya daga hajia sama yana jujjuya ta a dakin …yana wata irin shakiyyar rawa da qyalqyala daria cikin tsawa hajia mama da ta fara juwa take fadin “kai saukeni dan gidanku”…..daqyar ya sauketa da ya hi JB na fadin zaa fasa auren sai gashi ya nutsu tsaaf…
KALLO DAYA HAUSA NOVEL
Kuyi joining na Telegram group domin samun duka littafai https://t.me/joinchat/TWWnWU4L0RqEfWru
Leave a Comment