Kamin Ki Nemi Saki Ki Samu Amsar Waɗannan Tambayoyin Da Kanki

Matsalolin Maaurata

Kamin Ki Nemi Saki Ki Samu Amsar Waɗannan Tambayoyin Da Kanki

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Matsalolin Maaurata

Sau tari wasu matan suna zakewa akan a sake su ba tare da tsayawa sunyi tunani ko nazari mai zurfi da zai hanasu yin kuskuren da zasu yi dana sani ba.

 

Ana samu wasu matan da tabbas ya dace su nemi saki. Wasu kuwa kwata kwata bai dace ba amma kuma sai su nemi yin hakan saboda rashin tsayawa sunyi dogon nazari.

 

Kamin ki biyewa zuciyar ki daya raya miki neman saki, to fa ya kamata ki yiwa kanki waɗannan Tambayoyin kamar haka:

 

 

Matsalolin Maaurata

1:Kina son mijin ki? Wannan shi ne abu na farko da ya kamata ki soma neman amsar sa da kanki domin ta hakan ne idan kin saku bazaki yi danasi ba.

 

2: Wani Irin Laifi ne? Dole ne ki duba nauyin laifin da kike tuhumar mijinki da shi ya kai ki nemi saki ko dai kawai ranki ne ya baci.

Sau dayawa wasu matan suna neman saki ne akan yar karamar matsalar da za a iya hakuri dashi a zamantakewa na aure.

 

3: Yaya iyayyenki zasu ji? Kamin ki nemi saki ya zama dole ki samu amsar yadda iyayyenki zasu ji bayan mutuwar auren naki.

 

Iyaye ko waliyai suna iya hanaki jin dãɗin zaman zawarci muddin basu goyi bayan mutuwar aurenki ba. Don haka ya zame miki wajibi ki soma samun amsar wannan matsalar kamin ki nemi saki.

 

4: Makomar yaranki? : Idan kuna da haihuwa a tsakanin ki da mijin naki, ya zama wajibi ki samu amsar Makomar ya’yaki da wannan mijin naki kamin ki bukaci ya sake ki.

 

Akwai mata da yawa da suke neman saki bayan an sake su kuma matsalar yaran da suka bari ya zame masu matsalar rashin kwanciyar hankali. Don haka dole ki samo amsar Makomar ya’yanki kamin ma ki cewa miji ka sake ni.

 

5:Sabuwar Rayuwa? Kamin ki buɗe baki kice a sake ki, ki samu amsar yadda zaki fuskanci sabuwar rayuwar da zaki shiga ba kuma bayan an sake ki ba ki rike bin tsohon mijin naki kina neman taimakon sa.

 

Dole ne ki samu amsar yadda zaki ci gaba da daukar daeainiyar kanki koda kina da masu miki bazasu miki yadda miji zai miki ba.

 

Matsalolin Maaurata

Dole ne ki samu amsar wajen da zaki zauna ko da kuwa kina da mazauni zai bambamta da zaman gidan miji.

 

Dole ne ki samu amsar yadda zaki ci gaba kare mufuncinki wanda aure ya rufa miki shi.

 

 

Matsalar bushewar gaba

Wadannan sune wasu daga cikin tambayoyin da ya kamata duk mace mai neman saki ta soma samun amsar su kamin tayi azarɓaɓin neman a saketa.

 

Shi dai zaman aure da hakuri ne da kuma kau da kai. Duk matsalar da kike fuskanta a gidan mijinki da har kike neman saki akansa, wata na can tana hakuri da matsalar data fi taki.

 

Ma’aurata a rika hadawa da hakuri. Mata a daina neman saki cikin fushi ba tare da duban abubuwan da zasu je su dawo ba. Allah Ya bamu haƙurin zama da juna.

 

 

Matsalolin Maaurata

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.