Hausa Novels

Kanin Uba Hausa Novel Complete

Kanin Uba Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

🪂🪂ƘANIN UBA🪂🪂

 

 

🪂🪂 🌼🌼🌼🌼🌼🪂🪂

 

 

 

_Zainab Habib(Mom Islam_

 

 

 

 

Elegant online writers

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Kanin Uba Hausa Novel Complete

Page 1-2

 

DUBAI  4:30pm

 

Nisha zaune kan cinyar Mommah wato mahaifiyarta , wayarta ce ta fara ring tayi banza kamar bataji ba , Mommah na lura da yanayinta tace “Haba Nisha tun ɗazu ake kiranki amma kinƙi ɗauka anya bakya tunanin wulaƙanci babu daɗi?”Nisha da ta hama sauraron faɗan Mommah tace “uhm my Mommah karki wani damu fa  ,bashi da amfani a rayuwata “waye ?”Mommah ta tambaya “Ammar ne” a zabure Mommah ta kalleta kana tace “wato har kanki yayi ƙwarin da  zaki ƙi ɗaukar wayar Ammar ko ?”kin mance waye mahaifinsa ?kin mance wane matsayi mahaifinsa yake dashi a ƙasar nan ?” Nisha dake wasa da yalwataccen gashinta tace ” dont worry my Mommah ,so babu ruwansa da kuɗi mulki ko dukiya “Nisha ta faɗa cike da ƙwarin guwai wa,  tureta Mommah tayi tana cewa “aiko auran Ammar kamar anyi an gama “zata sanya kuka Mommah tace “kar inji ko tarinki”da gudu ta shige side ɗinsu kasancewar su biyu ne mata maza biyu , tana shiga ta sami Pooja a kwance tana chart kan royal bed ɗinsu , faɗawa jikinta tayi tana kuka kana tace ” aunty pooja Mommah tana ƙoƙarin yanke hukunci a kaina ba tare da tayi bincike ba ”  kashe data Pooja tayi tare da mayar da attention ɗinta ga Nisha tace “karki wani damu lili sis because Mommah saboda wani dalili take sonki da Ammar ,amma idan kika nuna mata baki damu ba zamusan inda zamuyi “wow thanks my sweet Pooja “Nisha tace “tare da manna mata kiss a kumatu , Mommah dake bakin ƙofa a tsaye tana jin duk abin da suke tattaunawa akai ta girgiza kai ta koma special palon su ta zauna kana ta zurfafa cikin tunani , a zuciyarta tace “lallai dole in san abinyi sbda da arziƙi a gidan wasu gara a gidanku a gidankun ma a ɗakinku , ta miƙe tana zagaye palon , takai minti hamsin a haka , sallamar Imam wato mijinta ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da take , cikin harshen larabci yace “Asslamu alaikum” walaikumussalam “Momma tace “cikin harshen su mai daɗin sauraro ,Mommah taje gareshi tare da rungumeshi tace “masha Allah cikin harshen hausa har ka dawo ?”eh Imam yace “yana murmishi kana ya zauna , kasancewar suna mu’amala da black tea ,wata ƴar aikin gidan itama balarabiya ta fito ɗauke da small glass cup ta ajiye a gabansu , Imam yace “masha Allah , jiyo kiraye kirayen sallah daga masallatan anguwar tasu duk da bata da yawaitar mutane , Imam ya miƙe tare da ƙara rungumar Momma a karo na biyu yace “idan na dawo zuwa bayan isha’i zamuyi karatu dasu Pooja kowa ya zama cikin shiri , to Momma tace “cikin rashin jin daɗin haɗa kan yaran da yake dan a time ɗin akwai tata manufar da take son shigarwa “to tace “shi kuma ya fice , bedroom ɗinta ta wuce ta shiga toilet tayi alwalah ta fito tare da shimfiɗa sallahya ta kabbara sallah , tana idarwa ta miƙe ko adu’a batayi ba ta tafi side ɗin su Nisha , a zaune da samesu kan sallahya sun idar da sallah ta zauna a bakin bed ta kallesu da murmishi tace “masha Allah ƴarana ina alfahari daku “suma ɗin murmishin sukayi kana suka ninke sallahar suka ajiyeta a drowa suka dawo bakin gado suka zauna a tare ,Imam yace “akwai karatu “cikin farinciki Pooja tace “Nisha mu riga Imaam zuwa palonsa “da gudu suka miƙe suka barta a gurin , tashi tayi ta koma nata side ɗin ta zauna kan stool tana tunani.

Suna shiga Palon Imaam suka shimfiɗa sallahaya kasancewar kiran sallahar isha’i da sukaji  ,bayan sun idar ko wacce tayi adu’ointa suna zaune suna hira sukaji gyaran murya gami da sallamar Imaam, amsawa sukayi cikin nutsuwa ,Imaam yace “yau akwai kyauta mai tsoka duk wacce ta gayamin yadda ake wankan gawa “cikin tsoro da fargaba suka kalli juna Pooja tayi murmishi kana tace “am um Imam nidai zani pharmacy siyo magani na ya ƙare tun jiya “Nisha ce tayi kalar tausayi Pooja ta taɓota tare da yi mata ƙifce da ido alamun itama ta ƙirƙiro tata ƙaryar su fece , cikin in ina Nisha tace “uhm Imaam kai na kamar zai fice dan Allah kayi min adu’a , matsowa tayi Imaam ya kama mata kai tare da kwararo mata adu’oi yace “tabi Pooja su karɓo magani , da gudu ta fice suna murna, murmishi Imma yayi shikam Allah ya zuba masa san ƴaƴansa su huɗu mata biyu maza biyu , kasancewar mazan ba a DUBAI suke karatu ba a egypt ne.

Momma na jin shigarsu side ɗin su ,lokacin ta fito sanye da lifaya mai kyau baƙi ,kasancewarta balarabiya sai ya amshi fatarta , da sauri tabi bayansu ta shiga , tana shiga ta samesu a zaune  suna dariya , Mommah tace “kun yiwa Imaam wayo ko ? dariya suka sa tare da cewa “afuwan Mommah karki gaya masa “Mommah zatayi magana taji wayarta na ring ,  ɗagawa tayi tace “Imaam ina gurin su Pooja gani nan zuwa “da sauri ta fice ta nufi side ɗin Imaam , zaune yake kan wani kyakkyawan kafet daya ƙawata ilahirin palon ,Mommah ta shigo da sallama ,amsawa Imaam yayi kana yace “kin tafi kulawa da yaranki ni kin barni ko “haɗe hannuwanta Mommah tayi kana tace “afuwan ya Habiby”jinjina kai Imaam yayi kana ya janyo wani plet mai ɗauke da dabino da gabaruwa ya miƙawa Mommah , karɓa tayi ta ajiye a gabanta ta dubeshi tace “ya Habiby ,inason magana da kai “cikin fahimta yace “Habibati ina jinki “am dama nace mai zai hana ka bawa yarannan zaɓi su fito da mijin aure ?” jimm Imaam yayi dan har gabanta ya fara faɗuwa tanaji a ranta bazai aminta da ƙudirinta ba , Imaam yace “bana son inyiwa yarana auran dole zan basu time nan da one year ko wacce ta fito da miji , cikin firgici tace “haba Habiby shekara ai tayi yawa wlh gaskiya a rage ina laifin wata biyu “zaro ido Imaam yayi kana yace “a zahiri dai ƴaƴan nan naki ne , ko wani ne yake faɗar haka bazafa kiji daɗi ba “turɓune fuska Mommah tayi kana tace “mutumncin ko wacce mace ɗakin mijinta fa “na sani ya kamata ki gyara maganarki , ko da suka gama makaranta ai ba matsa musu za’ayi ba ƴa’ya mata ne fa “har zata miƙe Immam ya kamota tare da zaunar da ita yace “fushi kikayi daga faɗar gaskiya ? juya fuska gefe tayi dan bai lura bane hawaye ma takeyi ,ɓare dabino yayi yasa mata a baki , babu musu ta karɓa , tunowa tayi ai da kissa mai zai sauko da watan nin da yasa tayi murmishin yaƙe yace “ahh ai Imaam babu komai ya wuce karka damu Allah ya kaimu lokacin”cikin jin daɗi Imaam yace “amin”.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Washe gari an tashi da wani sanyi mai shiga jiki tun bayan sallahar asbah da mutanen gidan sukayi babu wanda ya ƙara fitowa har 12:pm , sai 12:30 Momma ta fito jikinta sanye da rigar sanyi hannunta cikin aljihun ta zauna a palo tana huci , kai tsaye ta wuce side ɗin su Pooja ta samesu suna ta bacci  yaye blanket ɗin da suka luluɓa Momma tayi kana tace “kufa tashi ƙarfe ɗaya saura “da sauri suka diro ƙasa cikin mamaki ,Momma tace “ku wai bacci baya isarku ne ?”murmishi sukayi Nisha tace “Momma ai bacci akwai sweet , ba tare da Momma ta tsaya saurarar su ba ta fice ta tafi side ɗin Imaam ,samunsa tayi yana shirin fita da wani file a hannunsa tace “ya Habiby ina zuwa ?”gurin aiki ne suka buƙaci in tafi da takardun company ɗina ,masha Allah Habiby kace “arziƙi ya kusa bunƙasa “cike da farinciki yace “insha Allah ya rungumeta ya fice ,yana fita itama tayi palonta ta nemi guri ta zauna tana jiran ma’aikatan gidan su haɗa breakfast dan yau bata jin shiga kitchen , ƴan matan ne suka fito cikin riga da wando na Pakistan yayi musu kyau sosai , suka durƙusa tare gaishe da Mommah ,amsawa tayi cike da farinciki ta kallesu tace “ya kamata ace ko waccenku na gidan mijinta “murmishi Pooja tayi tace “Momma ai muna tare dake babu inda zamu “zaro ido Momma tayi tace “lallai kuwa kun ɗako jan aiki ni babu daɗi aka ɗaukoni daga egypt aka kawoni nan Dubai ?”murmishi Nisha tayi tace “Mommah ai ke kin sami mai sonki “da kallon mamaki Mommah ta kalli Nisha kana tace “ke baki samu mai sonki bane ?” Nisha na dariya tace “wlh Mommah samarin yanzu mayaudara ne “shiru Mommah tayi sai Pooja ce tace “tabbas kinyi gaskiya “suna cikin magana wayar Mommah ta fara ring , Ummin Ammar ne ke yawo a  kan screen ɗin wayar , cikin saita murya Mommah tace “Allah ya taimakeki  barka da safiya “daga can ɓangaren Umm Ammar tace “ya big gir ɗinmu ?”a tana lafiya wlh “Mommah ta faɗa ,Umm Ammar ce tace “anjima   ɗanki na nan zuwa fa “okay Momma tace “masha Allah ya kawoshi lafiya muna maraba “cikin jin daɗi Umm Ammar tace “nagode ta kashe wayar “waigawa tayi taga babu Pooja babu Nisha , miƙewa tayi tana zaga side ɗin nata ,ta hangosu kan dining suna breakfast , murmishi tayi ta ƙarasa inda suke tace “inata nemanku ashe kunyo nan , gyaɗa mata kai sukayi ,Mommah ta nemi guri ta zauna itama ta zuba tea ta fara sha , bata kai ga ƙarasa shanyewa ba , ta kalli Nisha fuskarta ɗauke da murmishi tace “ƴar albarka Ammar na hanya “wani mum munan faɗuwar gaba Nisha taji ta kalli Mommah dake murmishi tace “haba Mommah nace bana sonsa ana so dole ne ? nonses karki soshi man wlh idan kikaga ba’ayi wanan auran ba sai dai babu ni”a gigice Pooja ta ɗago ta kalli Mommah zatayi magana sai kuma ta fasa , kuka Nisha ta fashe dashi cikin takaici da muryar kuka tace “Mommah ya kamata fa ki gane yanzu ba time ɗin auren dole bane ,yanzu ko wacce mace ita take zaɓar mijin aure so nidai bazan auresa ba wlh “tasss taji saukar mari a fuskarta , Momma tace “ke ba abin alfaharinki bane ace kin auri ɗan governor ɗin DUBAI ? ba niba hatta Imaam inada tabbacin ,yaji wanan labari zai so hakan ,ƴa ƴanki su taso cikin nera haka ma yayarki , Pooja hawaye na zuba a fuskarta tace “Mommah wanan ba adalci bane “a matsayi mu na yaranki ya kamata ki bamu zaɓi mu fito da wanda mukeso “wani mugun kallo Mommah tayi mata kana tace “naƙi baku zaɓin “da ina tunanin kema bazaki bani matsala ba idan nazo nema miki miji amma tun yanzu kike son taci gaba da bijire min ?”sunkuyar da kai sukayi dukkansu idon Pooja na zubar da hawaye ,Nisha ko ji take zuciyarta kamar an soka mata kifiya , barin shiga kitchen in ɗora masa abinci mai rai da lafiya “duk cikinsu babu  wanda ya kulata bare ya nuna yaji abin da tace “ta miƙe tare da wucewa kitchen , samun ƴan aikin gidan tayi suna hidimar ɗora abincin rana ,ta koma gefe tayi amfani da inda basu ɗora komai ba ,abinci mai rai da lafiya Mommah tayi wa Ammar tare da juice irin nasu na larabawa , da kanta ta dinga fito da abincin tana kaiwa palon Imaam tunda taga Imaam baya nan ,bayan ta gama jerewa ta koma gurin su Nisha ta kamo hannunta tace “tashi kije kiyi wanka ya kusa isowa , ba tare da tayi musu ba suka miƙe a tare da Pooja Mommah tace “Pooja kiyi mata kwaliya mai kyau “murmishi Pooja tayi tace “to a zuciyarta tace “ke har yanzu bazaki gane ba sam , suna shiga bedroom ɗinsu suka zube a gado Nisha ta furzar da iska mai zafi ,zatayi magana Pooja ta rufe mata baki tare da cewa “oya tashi kije kiyi wanka “bata iya yi mata musu sbda soyayyar dake tsakaninsu ko wanne baya son yaga ɗan uwansa ya shiga damuwa , cire kayan jikinta tayi ta ɗaura towel ta shiga toilet ta daɗe kafin ta fara wanka sosai take jin zuciyarta babu daɗi ,brush ta ƙarayi kana tayi wanka ta fito ɗaure da pink ɗin towel ta zauna kusa da Pooja data zurfafa cikin tunani , taɓo ta Nisha tayi amma shiru ,sai data hura mata iska a fuska sannan ta sauke dogon nunfashi tace “har kin fito ?”fuska irin ta mai damuwa Nisha tace “aunty Pooja kina ƙoƙarin sanyani farinci amma a kaina ke kin faɗa damuwa ,to ni taya zanyi inyi farinciki ?rungumota Pooja tayi idonta na zubar da hawaye tace ” yanzu dai tashi kar Mommah ta shigo “Nisha data ɗauka soke maganar hirarta da Ammar tayi rau rau da ido tace “haba anty Pooja kema haka zakiyi min “bamada wani zaɓi daya wuce kiyi kwaliya ki fuskanci Ammar kawai koma menene, gaban mirror taje taja stool ta zauna tare da zubawa mudubin ido , tasowa Pooja tayi ta ɗauki lotion ta shafa mata kana ta shafa mata powder tare da pink ɗin janbaki ta gyara mata gashin girarta kasancewarsu farare kwaliyar tayi mata kyau ,drowa Pooja ta buɗe tare da ɗauko mata sari green ta sanya mata ,kamar dan ita aka yishi sbda karɓar fatarta da yayi , Pooja ta ɗauko warwaro da sarƙa da agogo da takalmi plate tasa mata ita dai Nisha bin Pooja take da kallo , turaruka ta ɗauko tare da fesheta ta kamo hannunta suka fito , babu sami Mommah a palo ba suka wuce bedroom , suna shiga suka sameta tana sanya wata haɗaɗɗiyar sarka ,ga wani tsadadden sari datasa da kallon mamaki Pooja ta kalli Mommah tace “Mommah wanan sari ɗin fa ?”nasan Imaam yana da kuɗi na rufin asiri amma a tunani na wanan Sari ɗin ya kai Lak biyar “zaro ido Mommah tayi cikin ɓacin rai tace “au tambayata ma kike ?”afuwan Mommah “Pooja tace “tare da wayancewa da kamo hannun Nisha tace “kinganta nan Mommah ai tayi kyau ko ?”gaskiya Ammar yazo ya bani kyauta dan na gyara masa amaryarsa , murmishin jin daɗi Mommah tayi kana tace “ai ko zakiga ɓarin kuɗi bari dai yazo nasan dukkan ku babu wanda ya sanshi sai magana ta waya “zata karayin magana wayarta ta fara ring ɗauka tayi tare da sallama Umm Ammar tace “ya iso gashinan zai kiraki ” to to to “Mommah tace “ina jira shugabata “kashe wayar Umm Ammar tayi sai ga kiran Ammar ne ya shigo wayarta , kasancewar tunda suka shirya abun su tayi saving numbersa yasa sunansa ya fito , da sallama ta ɗaga cikin sassanyar muryarsa yace “gani a bakin get “waro ido Mommah tayi kana a fili tace “wanan wane irin siriki ne , ta koma gurin su Nisha tace “an gama gyara komai a ɗakin Imam ga Ammar can a waje “maza ki shigo dashi “Pooja ce ta kalli Mommah kana tace “ba yana gadara da nera ba mai yasa bai zo a mota ba “harararta  Mommah tayi tace “idan kin gama gayamin magana sai ki sake mata hannu ta isa gurinsa “daga faɗar haka Mommah ta juya ta nufi  bedroom ɗinta , tana saƙa da warwara ,batasan lokacin da tace “idan yarinyar nan ta wulaƙanta yaron nan na shiga uku “.

Pooja ce ta kamo hannun Nisha tace karki nuna masa komai ai hira ba aure bace ni nasan plan ɗin da zamu shirya ki bani nan da two weeks “Nisha dai babu abin da tace “suka tafi , yiwa Ammar iso , fitarsu keda wuya suka buɗe  get , ganinsa sukayi a tsaye ya juya baya  Nisha ta taɓo Pooja a hankali tace “my Anty jibeshi fa ,so yake idan munzo muyi masa magana ?”Pooja dake ƙarewa yanayinsa  kallo ta kalli Nisha tace ” lil sis kinsan me , magana tayi mata a kunne wanda ni kaina banji mai tace ba “gani nayi Nisha tayi murmishi tare da ƙarasawa inda Ammar yake tsaye , cikin harshenta mai daɗin sauraro tace “Aslamu alaikum “wlkslm Ammar yace “tare da juyowa sukayi ido biyu da Nisha ,kallon kallo suka fara yiwa junansu ,a ransa yace “Allah yayi halitta a nan gurin tabbas idan na sami wanan tsaleliyar yarinyar na huta  , a fili kuwa yai murmishi kana yace “barkan ki da zuwa gimbiya Nisha “murmishi tayi wanda ya ƙara baiyyanar   da asalin kyawunta tace “muje ciki “tana gaba yana binta a baya har suka iso palon Imaam , tayi sallama ta shiga shima yayi sallama ya shiga , zama yayi a kan sofa tare da ajiye wayar hannunsa a gefe kana ya  mayar da kallonsa  ga Nisha da kanta yake a sunkuye zuciyarta take saƙa mata wani lamari , janyo table ɗin da Mommah ta ajiye abinci Nisha tayi tare da ɗaukar ludayin zuba abinci ta zuba masa, kana ta ajiye masa a gabansa tare da zuba masa juice ,ta dawo ta zauna ,ko wane motsi tayi idonsa na gurin ya kasa ko da ƙiftawa  ,cokali yasa ya fara cin abincin  cokali uku yayi yace “alhmdulilh kana ya kalli Nisha yace “da farako dai sunana Ammar nasan kinada labarin mahaifina ko ?”

eh Nisha tace “ya ci gaba da magana , inason ayi bikinmu nan da sati biyu so banaso a ɗauki long time “wani wahalallen ajiyar zuciya tayi kana tace “ai babu matsala “ba wata hirar kirki sukayi ba shiru yafi yawa a cikin hirarar tasu ,ya miƙe tare da cire wasu maƙudan kuɗi a aljihunsa ya miƙa mata , a’a bazan karɓa ba “Nisha tace “cikin tsoro….!

 

 

*MOM ISLAM*

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Leave a Comment

error: Content is protected !!