Hausa Novels

Karuwar Miji Na Complete Hausa Novel

Karuwar Miji Na Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Page 1 & 2

 

Federal college of education gombe . A nutse Mr nurain yake tafiya, daga ganin shi zaka ga cikar zati da kuma kamala a tattare dashi, nutsuwar shi bazai sa ka gaza gane tsananin izza da kuma miskilanci daya ke fama da shi ba domin kuwa mutum ne shi wanda baya son hayaniya ballanta Kuma shiririta, haka zalika shi ba mutum bane mai son a zauna ayi ta hira na banza da wofi domin kuwa, time yana da mugun muhimmanci a rayuwar shi..

 

“Kehh Layla ga mutumin naki ya faso fa”

Ae Ni wlhhh kamshin turaren shi ne yake mugun tafiya da imani na, kinsan Allah da zai bani dama daya ga wani abu wai shi love..

 

“kai Layla” wani love har zaki nuna ma wannan mutumin mai shegen girman kai, kina ganin malamai mata ma ya suka ƙare da wannan shegen girman kan nashi ballanta ke student

“hmmm”

feenah kenan, up to now ba kisan waye Ni Layla Usman bah, buh a sannu a hankali zan wayar miki da kai….

Kamar anyi ruwa an dauke haka sukayi tsit domin kuwa takun shi sukaji a daff dasu yana ƙoƙarin shigewa ta gefen su ya wuce office…

 

Dariya sosai feenah ta kece dashi “ke da kike cewa zai ga love”, sai gashi kin yi tsit daga jin takun sawon shi kusa dake.

 

Bazaki gane bane, ina ɗan shakkan shi, amma dai idan ya sake ya faɗa tsarko na hmmmm, ke dai kawai ki taya Ni da addu’ar Allah ya bani sa’a…

Amin layla na Allah ya baki Sa’a musha kallo.

 

 

Da sallama ya shiga cikin office din nasu dayake dauke da table guda biyar, a mutunci suka fara gaishe da junan su shi da sauran malaman dasuke zaune a nasu table din su hudu.

bayan sun gama gaisawa ne ya bude system dinshi domin ya karasa recording test din student din shi da bai k’arasa ba, hira ne yake gudana tsakanin sauran malaman dasuke cikin office din.

takaici ne ya turnik’e shi kamar kullum yadda yaga Malama A’ishah ta zage sai hira take yi da sauran malamai maza, Allah wadai yayi da rashin kishi irin na mijin Malama A’ishah da har yabar matar shi cikin maza da sunan tana aiki…

 

 

*****

Faty ina cikin matsanancin damuwa na rasa ina zan sa kaina, miye na rasa a jiki na da har zai sanya mus’ab ya fara neman matan banza fisabilillahhh, so yakeyi baƙin cikin shi ya kashe Ni ne dan Allah, haka jiya ma yana dawowa ya faɗa toillet yayi wanka kuma wlhhh wankan tsarki yayi, daya fito na nuna mishi ina buƙatar ya kusance Ni cemin yayi wai ya gaji bazai iya ba, kinga yaje ya ci wata karuwa a titi dole Ni yak’i Ni ina matsayin matar shi ta sunnah _cikin shehshekar kuka mai tab’a zuciya zainab ta k’arashe maganar ta_

 

“Hold on zainab” plss kibar kukan nan, kinsan miye matsalar mu matan yanzu?

_Cikin kuka zainab ta amsa mata da a’a_

 

Toh ba komai bane illa yawan zargi ki kwantar da hankalin ki, idan ma neman matan yake yi shi da Ubangijin shi, Ni banga abin D’aga hankali ba wlhhh.

 

Baza ki gane miye nakeji bane faty, saboda ke Kinga mr nurain bai da matsalar neman mata ne shiyasa har kike ganin laifi nah.

 

Ba wai ina ganin laifin ki bane, amma kinsa miye ya kamata kiyi?

 

_gyada kai zainab tayi alamar a’a_

 

Akwae wata mata me suna Maman hishma inaga ita ce zan baki Number ta, sai ki fada mata dukkan matsalar ki insha Allah zata Sending miki a grp dinta koma zasu baki shawarin da zai amfane ki da izinin Allah.

 

“Uhmm” sai yanzu nad’an ji dai dai a raina toh shi knn nagode, amma wlhhh wannan lamari na mus’ab abin yana cimin rai wlhhh, auren shekara 4 yara 2 kaɗai amma duk ya zama wani abu daban.

 

Allah dai ya kyauta, kinga Ni kam zan tafi zainab, sbd kar mr.nurain ya baro wajen aiki bai tadda Ni a gida ba..

 

Toh shi knn faty Nagode sosae ki gaida min da zuhriyya ta idan ta dawo daga school.

 

Toh shi knn zataji sai anjima.

 

Zuciyar zainab ya danyi mata sanyi domin kuwa tana kyautata zaton idan tayi ma Maman hishma magana dukkan matsalar ta zai kau, guntun murmushi ta sake sannan ta furta, in Allah ya yarda komai yazo karshe..

 

 

“Ohhhh” Ni faty karfe biyu da rabi na rana amma koh shara banyi ba, bayan nasan 4 sweet zai dawo.

 

Cikin sauri faty tah hau gyaran gida tare da daura girki..

 

“Kehh” laylah ga fa mutumin ya fito, maza kiyi sauri ki gwada sa’ar ki..

 

” Haba” feenah, ki yarda dani tinda nace miki mr. Nurain zai sha zuma na a kyauta ki yarda mana.

 

Ae Ni wlhhh bazan yarda ba sai naga kin aiwatar, kin tsaya sai aikin cika baki.

 

Kalaman feenah sunyi mugun fusata laylah, cikin azama ta tashi da niyyar ta tunkare mr nurain, dan kawai ta shaida ma feenah ita din ta cika mace.

 

Cikin sassarfa Layla ta fara tafiya bata tsaya ko ina ba sai dai dai gaban mr nurain, jiri ta fara yi na karya juyi takeyi kamar zata fad’i, yararaf ta fad’i a kirjin shi, dukkan nauyin ta tasauke mishi tare da manna mishi kirjin ta wanda Koh brezia Bata sanya ba.

 

Lumshe ido mr. Nurain yayi daya shek’e daddad’an kamshin turaren ta, amma dakewa yayi tare da furta, _whats wrong with you_ cikin Muryar sa mai dauke da tsananin izza da kuma aji..

 

Mannuwa ta k’ara yi dashi tare da ƙara furta jira nakeji sir, lumshe ido tayi tare da cije leb’en bakin ta ta gefe daya idanun ta tini suka sauya zuwa red, zai yi wuya cikakken namiji ya kalli cikin idanun laylah baiji sha’awar ta ya wanzo a zuciya da gangar jikin shi ba…

Gah wani daddad’an kamshin daya fito daga bakin ta a lokacin da takeyi mishi magana .

 

Ita kuwa feenah tana gefe tana kallon dramer nasu, mamaki ne ya kamata tare da furta, shegiya laylah ta iya maza wlhh……

 

Raba ta yayi da jikin shi sannan ya furta, sai kije ki nemi magani bawai ki tsaya kina buge mutane a hanya ba..

 

Sake baki laylah kawai tayi tana kallon yadda lips dinshi suke motsawa koh fahimtar me yake fad’a batayi ba.

Wucewa yayi ya barta baki sake tana nazarin kalaman shi.

dafa ta dataji anyi tare da furta kai kinya k’ok’ari laylah shine kalmar daya dawo da ita cikin tinanin ta..

 

“Hmmm feenah” aradu guy dinnan duniya ne wlhhh, kuttttt hmmm abin ba a cewa komai har na hangu mu muna ehhh, ae kin gane.

 

Kwashewa sukayi da dariya tare da furta sai mun lashe zuma.

 

 

Cikin sauri faty ta kammala ayyukan ta, ta fito daga wanka ke nan da ga ita sai towel a kirji taji Muryar mr nurain a kofar palour yana sallama.

 

Buɗe mishi kofar tayi tare da furta oyoyo sweet, sannu da dawowa.

 

Cikin murmushi ya amsa mata da sannu babyn sweet.

 

Rage kayan jikin shi yayi ya rage daga shi sai boxers, zama yayi a wajen dayake cin abinci domin jiran faty ta gabatar mishi da abincin shi..

 

Aekuwa sai ga faty ta k’araso gaban shi da tray din abincin ba tare da ta sanya sutarar kirki a jikin taba.

 

Haba! Baby, yanzu sau nawa zance miki ki daina kawo min abinci a tub’e, hala ma koh pant baki dashi ta cikin towel din, gaskiya Ni bana son Wannan dabi’ar naki.

 

 

Haba sweet dan Allah, daga wanka fa na fito, ballantana kace wari nakeyi, Ni wlhhh dad’i na da kai yawan mita,.

 

cikin fushi ta wuce daki ba tare da ta kawo mishi ruwan sha ba, kwanciya tayi akan gado bayan ta sanya doguwar riga mai kyau da ɗaukar hankali a jikin ta….

 

 

_shin laylah zata ci galaba akan mr nurain kuwa?_

 

_toh shi mus’ab miye ya kaishi bin matan banza, toh ma dagasken matan banzan yake bi ne?_

 

_Anya yadda faty take tafiyar da lamarin gidan ta daidai ne kuwa?_

 

Muje zuwa taku ceh oum zuhriyya

 

_Ku daure ku siya plss bana Allah ya isa domin kuwa iya rabo na zan samu, kuma fans din gaskiya siya sukeyi_

 

_gah mai bukatar *ƙaddarar zuciya ta* zai iya samon complt a 300, idan kuma harda *karuwar miji na* duka biyu zaku iya samu a 400_

 

Ina godiya da kulawar ku fans, comments dinku Yana Kara min karfin gwiwa

Leave a Comment

error: Content is protected !!