Kasar Dubai zata gina cibiyar kasuwar Crypto
Tag: kasuwar Crypto
Cibiyar Kasuwancin Duniya ta kasar Dubai (DWTC) zata kaddamar da wani babban sashe da za’a rika hada-hadar kasuwancin Crypto haɗe da kula dashi.
Kasar Dubai dai a cigaba da fadada iyakokin kasuwancin ta a duniya, yanzu dai itace kasar da tafi kowacce kasa a duniya mu’amalantar yan crypto kuma muma yan crypto muna son Dubai.
Mai girma CZ shine kusan mutum na farko a duniya daya fara murna da wannan cigaban kasuwar Crypto da kasar Dubai ta kawo a shafin sa na Tuwita, dama shi CZ tuni ya sharewa wannan al’amari hanyar shiga farfajiyar duniyar Crypto domin a watan October ya sayi katon gida a Dubai din.
Ina tunanin ta wannan fagen dai Dubai zata zama zakaran gwajin dafi ga dukkanin sauran ƙasashen duniya, mutanen kasar El Salvador za’a sha shagalin taron bude (W-CTH).
Mustapha Gfatu
(Dan Fafutuka)
Pingback: Harajin da Ellon Musk ya biya a 2021 ya kai Tiriliyan 4 - My Novels