Hausa Novels

Kauyen Yar Kade Hausa Novel Complete

Kauyen Yar Kade Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Kauyen ‘yar kadde wani garine dake ‘kasarmu ta Nigeria, garine dake jihar nasarawa, garine da ya had’a mutane daban daban. Ya had’a yaruka da dama, ‘karamin garine wanda ya had’a mutane musulmai da arna, garine mai tattare da zaman lafia, ga tarin ni’ema. A kwaisu da noma iri iri.

 

A cikin garin yau na yada zango, gani tsaye a ‘kofar wani d’an ma dai-dai cin gida, gida ne dai irin namu na ‘kasa, kusa da gidan kad’an akwai wani ‘karamin asibiti, gaba dashi akwai wani ‘karamar primary school.

 

Shiga gidan nayi domin d’ako muku rahoto.

 

“”Joy yau dai kinsan cewa a kwai Church ko?”” Shiru tayi kamar bada ita uwar take ba, “” Joy ina magana kina jina, baki tashi tsiyarki sai Sunday, da zarar ance yau Sunday ne shikenan sai ki kama nu’ku nu’ku, to maza ki shirya ki tadda ni can, time nata kurewa, saura kuma ki’ki zuwa”” tai ‘kwafa tare da tale mata kai.

 

Har uwan tabar wurin bata tashi ba, tana nan zaune inda ta barta, bata tashi a wurin ba sai kusan hour1.

 

A kuma wannan lokacin ne na’kare mata kallo, yarinya ce ‘yar karama da ita, shekarun ta bazai wuce 16 years ba, farace doguwa yanayin fuska kuwa ita ba mummuna ba haka zalika ba kyakkyawa ba, wato tsaka tsaki kenan.

 

Tana da diri mai kyau, yanayin ta mai cike da natsuwa, tana sanye cikin kayan barci Wanda suka zauna d’as a jikin ta.

 

Cikin natsuwa taje kitchen, d’iban d’umamen shinkafa jallof tayi a kwanan miya kamar Wanda za’a bawa d’an shekara biyu, koma wa tayi d’aki taci ko gama cinyewa batai ba taje ta aje tare da sake ruwan wankan a bokiti tayi bayi.

 

Ta’bata lokaci sosai sanan ta fito, ta shiya cikin wata ‘karamar riga da dogon wando, rigan tad’ame ta sosai wanda ya fito da shape d’in ta.

 

Gara gashin tada yake ba’ki, mai Kyau dashi tayi Wanda ya kwanta a gadon bayan ta.

 

Babu wani kwalliya a fuskan ta tad’au Bible d’in ta ta rufo gidan nasu ta nufi hanyan church, shima Church d’in ba nisa yake dasu ba.

 

Tafiya take a hankali cikin natsuwa, komai nata masha Allah.

 

A haka tazo wuce wata wurin wasu samari da talura kullum safe wurin zaman su kenan koda ana sanyi damuna .

 

Wani daga ciki tunda ya hango ta yafara had’iye yamu, yana lashe le’be, har tazo ta wuce su duka zuka zuba mata ido kamar zasu lashe ta.

 

Lumshe ido yayi saurayin tare da cewa “” gayu al’kur’an yarinyan nan tayi, komai yaji wallahi ta zata yadda dani hmm da abin ba’acewa komai. Kai dana more””.

 

Wani cikin su ya sake cewa “” yarinyan badai kaya ba, sai shegen miskilanci da jijji dakai, ni da zata yarda wallahi da auren zanyi, kaji baza wawa shashsha madace fah kuma arniya, meye gamun buri da kada? ina laifin mu lalla’bata mu kwashi ra’ba?”” Wani wanda bakin sa ba’ki’kirin dashi yake cewa haka.

 

“” Ah Allah yarinyan zatai taurin kai, guma kawai na aura domin na bari ta su’buce min hmm inaga sai na kusa zaucewa. Wa zai yarda ma har ka aure ta?, ai duk tsiya indai yarinyan ta yarda ai angama””.

 

Haka dai suke ta zancen ta, itako bata San ma sunayi ba.

 

Koda ta’karisa church har an tashi, domin mutane har sun fara fita, da murna ta saki wani murmushin dake saka kuma tunta lotsawa, hakan kuma na’kara ‘kawata fuskan nata.

 

Da mamaki nake kallon ta, tana tsaye kusa da church d’in saiga maman ta tafito ita da wata ‘kawanta.

 

Da mamaki suke kallon ta uwan ta fusata domin gani ta ganta bata ko tsorata ba saima kafeta da ido da tayi kamar yadda tayi.

 

Don haka cikin zafin rai ta nufeta tana cewa “” yanzu don ubanki sai yanzu kika zoko?”” Tai mata ran’kwashi, taji zafi domin harda runtse kyawawan idanuwan ta.

 

“” Joy mekike so?, meke damun ki? bansan wata irin yarinyan gareni ba Sam baki maida addinin ki abakin komai ba, baki da hankali sam “”.

 

‘Kwanta tace “” madam Gloria kenan ai na fad’a miki indan baki raba yarinyan ki da watanan musulman ba sai kinyi kuka watarana””.

 

Haka maman tai ta mata fad’a ko damuwa batayi ba, itako ‘kawar maman sai faman zugata take.

 

7 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!