Hausa Novels

Kawayen Juna Hausa Novel Complete

Kawayen Juna Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

KAWAYEN JUNA

 

LABARI DA RUBUTAWA

 

*NUSAIBA RABIU*

 

(Mommyn Haneef Ce)✍️

 

 

typing✍️

 

FREE PAGE 1&2

 

🔔📚

*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa}_

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

 

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

 

 

Dasunan Allah mai rahama mai jinkai Allah Ubangiji ina rok’onka da kabani rai da lafiyan sake dawowa cikin wannan sabon labarin mai suna K’AWAYEN JUNA.

 

Masoyana barkan mu da sallah dafatan anyi azumi lafiya Allah yasa mudace da Aljannatur fiddausi.

 

Ya Allah kamar yanda nafara wannan littafin lafiya Allah kasa nagamashi lafiya ameen.

 

Kuma ban yar da wani kowata sujuyamin labariba.duk wanda ya yi dai_dai dalabarin sa to arashine.

 

 

Labarin K’AWAYEN JUNA paid book ne idan kinji labarin yamiki kinaso kicigaba dakaran tawa zaki iya turo dakud’inki ta wannan account number.

0087778987

Nusaiba Rabiu Union bank 500 naira only👌

 

Idan kuma katine zaki iya turo mana da katin mtn ta wannan number 07026368879.

 

 

Wasu y’ammata ne su uku suke tafiya acikin wata k’atuwar mota mai shegen kyau suna tafiya suna hiransu cikin jin dad’i da annashuwa kana ganinsu,kaga man yan y’an mata masuji da kud’i. Amma banda mutun d’aya.

 

Wani katafaren gida suka staya hon sukayi mai gadi yazo dasauri ya wangale musu get d’in gidan,suka shiga a parking space sukayi parking d’in motan suka futo dukan su.

 

Shiga cikin gidan sukayi gaba d’ayansu hannunsu rikeda junansu.Sallama sukayi dukan su”Ammi datake kitchen,ta amma musu da fara’an ta suka shiga duk suka zauna akan kujeran palon sun gaji..

 

Ammi datagama zuba abincin datakeyi tafuto musu dashi tajera akan dainning tadubesu ta ce” Maza kutaso kuzo kuci abinci dan nasan kun gaji.

 

Wallahi Ammi Junaidiya tafad’a ta na mik’ewa suma su Jumaima da Juwairiya suka tashi,dukansu suka nufi kan dainning suka zauna” Ammi dakanta tayi serving nasu nan take suka fara cin abincin komagana basayi saida suka k’oshi, sukasha juice mai sanyi tukun suka mik’e gaba d’ayansu suka shiga d’akin Junaidiyya sukayi alwala sukayi sallan azahar.

 

Ammi ce tafuto taduba ko sungama taga basa parlor tayi d’ayi d’akin Junaidiyya taga har sun idar da sallah suna addu’a ta ce” sarakan ibada Allah yamuku albarka.

 

Suna tofawa suka amsa mata da ameen “Futa tayi takoma parlor suma mik’ewa sukayi sukabi bayanta akusa da’ita suka zauna sai alokacin suka gaisheta.

 

Hararan su Ammi tayi ta ce” bazan amsaba sai yanzu kuka tuna da gaisuwa”Jumaima ta ce” Ammi afuwan dan Allah kiyi hak’uri yunwace ta mantar damu.Suma dukansu suka shiga bata hak’uri suna rik’e kunnansu.

 

Ammi tayi dariya ta ce” To nayi y’an nema nandai suka shiga bata labarin yanda sukaje. “Ammi kam sai dariya takeyi domun ta na bala’in son yaran har ta na jin aranta inama dukansune yaranta datafi kowa jin dad’i Amma yaran ta biyu ne Junaidiyya da Suhaib.

 

Suna zaune wayan Jumaima ya yi ruri ta na dubawa taga Umman tane tad’auka cikin girmamawa, ta ce” Assalamu alaikum Umma ta’amsa da wa’alaikumussalam.

 

Umma ta ce”To kizo ga yayanki yazo yanata tan bayanki bakinan tun d’azu yazo amma baki dawoba yace nakiraki.

 

Jumaima tamik’e dasauri ta ce” Dagaske kike Umma YayaYusuf yazo to ganinan yanzu takashe wayan batama staya jiran mai Umman zata sake fad’aba.

 

Su Juwairiya sukace gamunan dai ba gakinan ba”Jumaima ta ce” to kutashi muje”Mik’ewa sukayi gaba d’ayansu suka futa.

 

Ammi ta ce” Babu ko sallama “Junaidiyya ta ce” Ammi sai mundawo sukamma su Juwairiyya sun jima dafuta,sun manta wani abu waishi sallama.

 

Juwairiyya ita tazauna awajan zaman driver suma sauran suka shiga tafiya suke akan titi cikin sauri_sauri dukansu zuciyoyin su cikeda murna da farinciki har suka isa gidansu Jumaima faking sukayi gaba d’ayansu suka futo dasauri suka shiga cikin gidan.

 

Jumaima ta na kiran Yaya Yusuf kana ina kafuto dan Allah kodai zolayata Umma tayi dan ta nason nadawo gida.

 

Umma ce tafuto bakin ta d’auke da murmushi tadubesu taga kowa fuskansa adame barinma Juwairiyya,Umma ta ce” saboda inason kidawo sai na sharara miki

k’arya ko.?

 

Suna staye saiga Yaya Yusuf yafuto daga band’aki ya’ajiye buta.

 

Jumaima ta ce” La Yayana ashe dagaskene kazo dasauri taje tafad’a jikinsa ta na murnan ganinshi”Suma Su Junaidiyya gaba d’aya murna ta ishesu,suka k’arasa har yanda yake suka had’a baki sukace Yaya Yusuf barka da Zuwa yaya hanya nan dai suka gaisheshi ya’amsa cikin fara’a yana mai kallon sahibar tasa ,waton Juwairiyya sake Jumaima ya yi yanemi waje yazauna yana mai jin dad’in ganinsu,yadubesu yace k’awayen Juna ba’aganin d’aya babu biyu saidai aganku dikanku. Y’angidan Ammi da Mami da Umma duk ansan gar taku..

 

Dariya suka masa suka tanbayeshi starabansu.”Yadubesu yace starabanku nanan karkudamu k’annena ina alfahari daku.

 

Jumaima ta ce” Yaya Yusuf amma kadawo kenan ko.? “Aa nazodai k’anwata amma sauran shekara d’aya na kammala ” Jumaima ta ce” to Yaya Yusuf dagashi sai kuma kadawo gida.?

 

Eh Jumaima “Junaidiyya ma ta ce” Yauwa Yaya

Yusuf gwanda kadawo mudink’a ganinka.Amma kaga Yaya Suhaib yajima bai zoba,gashi da ra’ayi ko magana bayasonyi idan natan bayeshi sai yacemun nacika surutu wai’shi bayason magana.

 

Yaya Yusuf yace to kina damun sane saiyasa to Nima bagashi kunzo kun dameni ananba.

 

Dariya sukayi “Yusuf yad’ago yakalli Juwairiyya yace kekuma baki maganane, Kokuma bakinki yana ciwone?

 

Aa Yaya Yusuf naga kuna ta maganane nayi shuru.”Yaya Yusuf yacema su Jumaima sutashi subashi guri zaiyi magana da Juwairiyya” Suka mik’e suna musu dariya.

 

Hararansu ya yi yace mawaye kuke dariya “Sukace Yaya Yusuf badakai mukeyiba to dawaye kukeyi yamik’e yad’auki muciya zai kwad’a musu ” Suka ruga aguje sai d’akin Umma sunata haki,suka nemi waje suka zauna.

 

Umma tadubesu ta ce” Yanzu haka kunmasa wani abunne zai bigeku.Wallahi Umma wai kawai munyi dariya Junaidiyya tafad’a.

 

Yaya Yusuf kam suna guduwa yadubi Juwairiyya yace Matar Yusuf yadai kina lafiya kuwa.?

 

Lafiya k’alau nake Yaya Yusuf kazo lafiya”Lafiya k’alau Matar Yusuf “Rufe idonta tayi ta na maijin kunya.” Yace sarakan jin kunya gaskiya nafad’a dana dawo za’a fara maganan bikinmu ayi awuce wajan.

 

Yaya Yusuf yace To yaya karatu inafatan dai kuna yinsa yanda yakamata bakusa wasa acikin sa ? “Eh Yaya Yusuf ” To ya yi kyau haka nakesonji,..

 

Juwairiyya yakira sunan ta yace to yaya soyayyata yananan ko anba mawani, an ajiyeni agefe ban saniba nikuwa kullin dake nake kwana nake tashi.

 

Aa Yaya Yusuf aikaima kasan kai kad’aine bazan tab’a had’aka da waniba.

 

Yusuf har cikin ransa yaji dad’in abunda tafad’a kuma yayarda, domun yanayin datayi maganan yagane har cikin ranta tayi. Yace har kinsa naji nustuwa araina. Matar Yusuf ina sonki ina k’aunarki kirik’emun alk’awarina harna kammala karatuna nadawo kinji matar Yusuf..

 

“D’aga masa kai tayi ta ce” Karka damu namaka al k’awarin nima banida wani acikin zuciyata saikai kullin tuna Nina yaushe zakazo naganka.Muryanka baya wadatar dani inba ganin ka nayiba yanzu haka bakasan farin cikin dana shigaba ganinka danayi.

 

Yaya Yusuf tunda tafara magana yake binta da ido yana jin sonta acikin zuciyarsa kice banik’ad’ai nayi rashinkiba kema kinajin abun da nakeji acikin zuciyata kenan.?

 

Bata bashi amsaba tamik’e ta ce” Yaya Yusuf bari naje wajansu Jumi da Juni kar Umma tajini shuru kuma tasan tare muke dake haka suke fad’ama junansu irin wannan sunayen ita kuma suce mata Juri.

 

Yaya Yusuf yace to ni bangaji da ganinkiba zaki tafi “Dan Allah Yaya Yusuf kayi hak’uri zamu sake had’uwa ai tunda kananan.” To jeki

 

Ai dasauri tayi d’akin Umma tasa mesu suna hira da Umma itama tazauna anayi da’ita,…….

 

 

Karku manta damana comments da share dan Allah.

 

 

 

By Mommyn Haneef Ce✍️

[30/07, 6:45 pm] +234 803 192 1625: 👭K’AWAYEN JUNA👭

 

LABARI DA RUBUTAWA

 

*NUSAIBA RABIU*

 

(Mommyn Haneef Ce)✍️

 

 

typing✍️

 

FREE PAGE 3&4

 

🔔📚

*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa}_

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

 

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

 

 

Dasunan Allah mai rahama mai jinkai Allah Ubangiji ina rok’onka da kabani rai da lafiyan sake dawowa acikin wannan sabon labarin mai suna K’AWAYEN JUNA.

 

Masoyana barkan mu da sallah dafatan anyi azumi lafiya Allah yasa mudace da Aljannatur fiddausi.

 

Ya Allah kamar yanda nafara wannan littafin lafiya Allah kasa nagamashi lafiya ameen.

 

Kuma ban yar da wani kowata sujuyamin labariba.duk wanda ya yi dai_dai da labarin sa to arashine.

 

 

Labarin K’AWAYEN JUNA na paid book ne idan kinji labarin yamiki kinaso kicigaba dakaran tawa zaki iya turo dakud’inki ta wannan account number.

0087778987

Nusaiba Rabiu Union bank 500 naira only👌

 

Idan kuma katine zaki iya turo mana da katin mtn ta wannan number 07026368879.

 

 

*********✍️ Su Junaidiyya suka kalleta sukasa dariya Junaidiyya ta ce” to yaud’in ma baza’a saurara bane mutum daga zuwansa yau anfara lik’e masa.

 

Umma mik’ewa tayi tabarsu”Juwairiyya ta zabgawa Junaidiyya harara ta ce” To ina ruwanki y’ar sa ido.

 

Ni idan Yaya Habib yadawo inace mak’ale mishi kikeyi kaman Wanda zaki goyeshi amma kinzo kina fad’awa mutane magana.

 

Junaidiyya ta ce” Eh naji amma badaga dawowansa nake mak’ale mishiba inace amma ke ko hutawa baiyiba.

 

Juwairiyya ta ce” kekika sani.Nan dai sukabar wannan maganan suka Shiga hiran makaranta yanzu sunkusan gamawa dasun gama iyayensu sunce aure zasu musu.

 

Jumaima ce kawai acikinsu batada stayayye kuma batasa abun arantaba itadai ta ce” Allah ne bai kawoba amma dazaran lokaci ya yi komai zai wakana ayi biki.

 

Yanzu karatu tasaka aranta. Suna gama hiransu na k’awaye kowa tayi gida abunta Akabar Jumaima ita da Umman ta.

 

Washe gari da safe dukansu suka tafi makaranta class d’insuma d’ayane wajan zamansu ma d’aya.Suna zama teacher Salis ne yashigo musu, yafara darasi yana gamawa wanima yashiga yafuta.Saida Malamai Hud’u suka shiga kafin aka tashesu hutun rabin awa nan suka futo harabar makarantar. Wani bakin bishiya suka samu suka zauna suna hiransu.

 

Junaidiyya tadubi Juwairiya ta ce” wai najiki shuru baki bamu labarin hiranku da Yaya Yusuf ba.”Juwairiyya tadubeta ta ce” Saidai kiyi dan kuwa bazaki tab’a jiba.Ni mastalata dake kenan gaba d’aya kinason jin gulma..

 

Dariya suka shek’e mata dashi dan sunsan halin Juwaiyya ta na bala’in k’aunar Yaya Yusuf kuma bata iya b’oye sanda take masa.

 

Lokacin dawowan su class nayi suka koma saida teachers uku suka shiga kafin aka tashesu.Saida Junaidiyya tafara kai Jumaima gida kafin ta’ajiye Juwairiyya sannan tawuce gida dayake duk acikinsu itace mai mota.Gida tawuce kai’staye bayan mai gadi yabud’e mata get tashiga cikin gidan parking d’in motar tayi tashiga ciki gidan. Parlorn Ammi tashiga tasamu Daddyn ta zaune shida Ammi sunata hiransu.Ai junaidiyya dasauri ta’ajiye jakan hannunta taje dasauri wajan Daddy. Ta ce” Daddy yaushe kadawo..?

 

Daddy yadubeta yace y’argidan Daddy d’azu nadawo natanbayi Ammin ki ta ce” kina makaranta. ina y’an uwanki naganki kekad’ai.”Junaidiyya ta ce” Sunje gida suna cin abinci sukayi wanka suka huta gidan Mamin Juwairiyya zamuje.

 

Daddy yace to lallaikam to Allah yabaku sa’a yak’ara dank’on k’auna “Ameen Ammi tafad’a ta ce” to maza kije kiyi wanka kishirya “To Ammi Junaidiyya tad’auki jakanta tashiga d’akinta wanka tayi ta d’auro alwala tayi salla tashirya cikin kayanta maikyau tafuto sai zuba k’amshi takeyi..

 

Yanda tatafi tabar Daddy haka tazo tasameshi awajan, zama tayi kusa dashi tagai dashi ya’amsa cikin farinciki dajin dad’in ganin y’ar tashi.

 

Kan dinning taje tazubo abincinta tad’akko tazauna kusada Daddy ta na tan bayansa shikuwa gabad’aya baya gajiya da bata amma.

 

Junaidiyya ta ce” Daddy ina starabanmu.? “Yace kigama cin abincin tukunna sai kik’arb’a muku ko” To Daddy.

 

Ta na kammalawa taje ta’ajiye tawanke bakinta tazo wajan Daddy. Ta ce” Daddy bani nakaimusu kar Jumi tajini shuru”Daddy yadubeta yace jeki d’akina zakiga wani jaka kid’akko mun.”To Daddy tashiga d’akin Daddy tad’akko jakan takawo mishi..

 

Daddy yace bud’e kigani “Junaidiyya da zumud’in ta tasunkuya tajazi d’in jakan tabud’e, tafara d’agosu d’aya bayan d’aya. Dogayen rigunane guda uku mashu stada da turaruka da takalma k’afa uku dakayan kwalliya masu mungun kyau da stada.

 

Junaidiyya tadubeshi ta ce” Daddy yanzu wannan namune nida su sister’s d’ina gaskiya mun gode Daddy Allah yak’ara arziki. “Ameen Daddy yafad’a yana maijin dad’in farin cikin da y’artashi tashiga..

 

Junaidiyya tajuyo tadubi Ammi ta ce” Ammi kikalli kayanda Daddy yakawo mana. “Ammi ta ce” ai narigaki gani “Dariya Junaidiyya tayi tacire ma Juri da Jumi ta d’akko wani sabon laida mai kyau tasaka kayan acikin laidan.

 

Sallama tamusu tafuta wajan motan ta taje tashiga mai gadi naganin tashiga mota yazo yabud’e mata get tafuta bata staya ko inaba sai gidan su Jumi tanayin parking d’in motarta tafuto tashiga gidan.

 

Sallama tayi Umma ta’amsa mata da fara’anta ta ce” y’an uku baku iya juran rashin ganin junan ku. “Ai Umma bazamu iyaba ” To ai shikenan sai kuyitayi itama gatacan ta na ta shiri zatatafi wajanki. ” To Umman mu.

 

Junaidiyya tashiga d’akin Jumi da fara’anta. tasamu Jumi tagama saka kaya ta na kama gashinta da ribbon tayi kyau sosai.

 

Junaidiyya ta ce” iye k’awata kinganki kuwa kinyi kyau sosai wallahi” Jumaima ta ce” nidai karki zageni ina wani kyau anan Juni. Jumi tafad’a.

 

Junaidiyya ta ce ” Wallahi k’awata bawai inason yabanki bane kokuma zaginki gaskiyane kinyi kyau kuma ked’in kyakkyawace ke mai kyauce dan dagani har Juri kinfimu kyau da diri ga gashi gaki fara tas kaman ba y’ar Nigeria ba.

 

Jumi ta ce” Kai Juni jiyanda kiketa gwad’ani to nagode sosai. “Yauwa Jumi albishi’rinki Juni tafad’a ” Jumi ta ce” Goro “Daddy fa yadawo d’azu bayan tafiyan mu makaranta “Da gaske Juni ” Eh wallahi gashi har yakawo mana staraba.

 

Na d’auki nawa wannan nakune keda Juri “Allah sarki Daddy baya gajiya da d’awai niya, tabud’e ledan tacuro dogayen rigunan sunyi kyau sosai irid’ayane babu ban_ban ci itama tad’auki nata da takalmi da kayan kwalliyan da turare,ta’ajiye tasaka himar d’inta suka futo.

 

Sallama sukayiwa Umma suka tafi gidansu Juwairiya hon sukayi Mai gadi yabud’e suka shiga parking sukayi ayanda ake parking d’in motocin gidan. Futowa sukayi suka shiga cikin gidan.

 

Sallama sukayi mai aikinsu ce ta amsa gai shesu tayi suka amsa. ” sukace ina Juri “Lami ta ce” Ta na d’akinta.”Ai dasauri suka tafi d’akin Juwairiya suna shiga suka sameta tayi tagumi ko shigo wansu batajiba..

 

Dasand’a sukaje suka cire mata tagumin datayi ” Ta na ganinsu ta b’ata rai tajuyar da bayanta taki kulasu.”Haba sister mai yafaru kuma kika sharemu duk suka fad’a atare cikin damuwa? “Ganin sundamu ta ce” To tin yaushe naketa jiranku bakuzoba kuma kunsan bama rabuwa da junan mu..

 

Ai ya kiyi hak’uri nine banje gidansu Jumi da wuriba amma kiyi hak’uri Daddy ne yadawo sai yasa kikaga bamuzo yanda muka Saba ba.

 

Juri ai tuni tamanta da wani fushin da takeyi ta ce” Daske Daddy yadawo “Eh mana suka bata amsa. Junaidiyya ta ce” Gastaraban ki muma yabamu namu kuma duka iri d’ayane”Juri tajuye laidan akan gado ta d’aga dogan rigan tagani ya yi kyau sosai tafad’a..

 

Ta ce” Nagode Daddy yakamata muje mumasa godiya. ” Jumi ta ce” Hakane amma kibari sai damu tafi sai muje “To shikenan Juri tafad’a. nandai suka zauna sunata hiransu cikin jindad’i da farinciki.

 

Mami ce taji shewansu tashigo d’akin ta ce” ai saidai kud’in idan kuka had’u ba sauki ko bacci baku barin mutum ya yi. “Dariya sukayi dukansu kai Mami ” Ta ce” to namuku k’arya ne “Aa suka fad’a sukansu, gai sheta sukayi ta’amsa cikin jin dad’i..

 

Itamadai ta na son yaran barinma suka had’u su ukunsu abun yana mata dad’i gaskiya. saiyasa bata tab’a ban_ban tasu da y’arta Juwairiyya, duk wani abunda zata mata to tare take musu suma sunajin dad’in hakan.

 

 

Ammi ma da Umma basu ban_ban tasu saiyasa komai nasu irid’aya ake musu sai dai wani lokaci kala yaban banta.Suna zaune wayen Junaidiyya ya yi ruri ta na dubawa taga my Habib dasauri tad’aga tasaka masa kukan shagwaba.

 

Shikuwa gaba d’aya yarikice dan shi baya k’aunar yaga sahibar tasa acikin damuwa.” Nan dai yafara tan bayanta lafiya mai yasameki,kinsan banason damuwarki dan Allah kifad’amun.?

 

To bakai bane “Nikuma nayi me yau kwana biyu ko kirana bakayiba idan nakiraka baya tafiya.Ok aiya please dan Allah sahibata kinsan haka kawai bazanki kirankiba kinsan mijin naki sojan gaskene to anturamu wani gunda kowayama bata anfani awajan ne saiyasa yanzuma munsamu futowane nakiraki ko Mami bankiraba sai ke sahibata afuwa nake nema.

 

Ta ce” To shikenan inadai lafiya kake dan banason wani abu yasameka “A a baku komai Sahibata.To incedai kina lafiya kuma anmun afuwa ” Eh anmaka.

 

To nagode kuwa kishirya da nadawo zanyima Abbana maganan auranmu. dan idan ba nasamu nad’aukekiba hankalina bazai kwantaba. Kar wani yamun shigan sauri..

 

Kai Yaya Habib ai bashi kai kad’aine aburnin zuciyata “Allah ko Sahibata. Eh mana Yayana yanzu yaushe zakazo ” Nanda kwana hud’u danzo.”To Allah yakawo ka lafiya.Nandai suka gama hiransu suka kashe wayan,….

 

Kuci gaba da mana comment da share domun shi yake bamu kwarin guiwa.

 

By Mommyn Haneef Ce✍️

[30/07, 6:45 pm] +234 803 192 1625: 👭K’AWAYEN JUNA👭

 

LABARI DA RUBUTAWA

 

*NUSAIBA RABIU*

 

(Mommyn Haneef Ce)✍️

 

 

typing✍️

 

FREE PAGE 5&6

 

🔔📚

*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa}_

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

 

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

 

 

Dasunan Allah mai rahama mai jinkai Allah Ubangiji ina rok’onka da kabani rai da lafiyan sake dawowa acikin wannan sabon labarin mai suna K’AWAYEN JUNA.

 

Masoyana barkan mu da sallah dafatan anyi azumi lafiya Allah yasa mudace da Aljannatur fiddausi.

 

Ya Allah kamar yanda nafara wannan littafin lafiya Allah kasa nagamashi lafiya ameen.

 

Kuma ban yar da wani kowata sujuyamin labariba.duk wanda ya yi dai_dai da labarin sa to arashine.

 

 

Labarin K’AWAYEN JUNA na paid book ne idan kinji labarin yamiki kinaso kicigaba dakaran tawa zaki iya turo dakud’inki ta wannan account number.

0087778987

Nusaiba Rabiu Union bank 500 naira only👌

 

Idan kuma katine zaki iya turo mana da katin mtn ta wannan number 07026368879.

 

 

Juwairiyya ce tadubi Junaidiyya ta ce” Haba sister gaskiya baki kyauta manaba yanzu mai makon kibamu mugasaisa kikaki.

 

Junaidiyya ta ce” To kikirashi mana da wayanki.Kalan kikaste mana jindad’i.” Jumaima dai dariya tamusu ta ce” To shikenan yawuce dan Allah, kuma zamu kirashi mugaisa tunda mu’ai Yayan mune ko Juri..

 

Juwairiya ta ce” kirabu da ita zamu rama muma “Junaidiyya ta ce” Inajiranku ma.

 

Nan dai suka gama shan hiransu agidan Mamin Juwairiyya suka d’unguma zuwa gidan Ammi suna zuwa kuwa suka samu Daddy agidan har k’asa suka stugunna suka gaidashi ya’amsa cikin fara’a dajin dad’in shidai k’awancen yaran yana burgeshi dan abun har yana bashi Mamaki sun shak’u da junan su sosai.Yamma nayi kowa tatafi gidan su.

 

*WAYE JUMAIMA*

 

Jumaima iyayen ta asalinsu y’an garin Abuja ne awata anguwa da ake cemasa Mabushi.An guwan talakawa ne duk acikinsa babu mai kud’i amma sunada rufin asiri.

 

Mahaifiyar ta Saratu wanda suke kiranta da Umma amma nagidan su suna cemata Jummai. sai kuma mahaifinsu Malam Usman.

 

Malam Usman shik’adai iyayensa suka haifa,yataso cikin gata dajin dad’i agurin iyayensa Mahai finshi Malam Yusuf sai mahaifiyarsa Jumaima. wan akekiran ta da Inna Jume.

 

Usman ya yi karatun boko amma iya secondary school yastaya.Yafara bin Baban sa gona. Rayuwa yaci gaba datafiya musu cikin jindad’i har Usman yazama saurayi.

 

Baban sa Malam Yusuf yamasa aure da y’ar abokinsa. Baikiba ya yi biyayya wa mahaifinsa, suna zaman su lafiya da k’aunar junansu dan Jummai ta na da biyayya gatada dad’in zama kuma ta na da hak’uri da kaudakai. Akan komai.

 

Tawannan halin taja ra’ayin Usman har yafara sonta. Bayan aurensu da wata uku Jummai tafara laulayin ciki suna zuwa Asibiti aka tabbatar musu ta na da juna biyu Malam Usman murna kaman yagoyata haka yakeji.

 

Maganin da zai taimakawa jaririn cikinta da Wanda zai k’ara mata jini suka rubuta musu.Malam Usman tun a Asibitin yasaya magungunan suka dawo gida.

 

Kuwalawa sosai Malam Usman yakebawa Jummai ko aikin gida baya barinta tayi,shiyake komai nagidan. Har yasamu lokacin zuwa gonar su.

 

Bayan wata tara Jummai tahaifi d’anta kyakkyawa dashi,fari sol dayake sud’in fulanin usuline. Ranan suna aka y’an kawa maijego ragon suna kato.

 

Wanda Malam Yusuf shiyakawo ragon dan Usman yace masa sunan shi akasakawa yaron ya yi murna sosai da farin cikin hakan.

 

Anyi taron suna anwaste mai jego ana kuladasu yanda yakamata. Har sukayi kwana arba’in inna Huwale k’anwar Maman Jummai takoma. Gida dayake taga Jummai d’in da lafiyanta.

 

Malam Usman yaji dad’in tafiyan Inna Huwale dan amatuk’ar dame yake, Yanata murna yau zai angwance. Da matarsa

 

Ayaune suka tashi Allah ya yiwa Malam Yusuf rasuwa Inna Jume tashiga tashin han kali barinma Usman kogai suwa baya iya amsawa.Haka har akayi kwana bakwai.

 

Haka rayuwa yacigaba datafiya musu da dad’i daba dad’i sun cigaba da rainon yaransu har Yusuf yakai shekara biyar suka sashi a makaranta bayan yagama puramare school suka sashi a secondary school shima yana gamawa suka turashi Jami’a,alokacin Jummai ta na da stohon ciki aihuwa yau ko gobe.

 

Bayan kwana biyu Jummai tahaifi y’arta kyakkyawa da ita, Wanda har y’an barka idan sukazo sukaga jinjiran sai sunyi maganan kyanta.

 

Jummai ganin baki yana son yin yawa akan y’ar tata tafara mata addu’a ta na tofeta dashi. Ranan suna akasa mayarinya sunan kakanta waton Jumaima.” Inna June tayi farin ciki da zuwan takwaranta.

 

Ranan suna ansha suna anwaste mai jego ta na farin cikin da Allah yabata y’amace dan tun a cikin Yusuf tayi kwalafaci sai gashi wannan haihuwan tasamu.

 

Umma ta na kulada y’arta yarinya kuwa tayi wayo ta na shekara hud’u aka sata amakarantar boko da islamiya. Jumaima tun alokacin suka had’u da Junaidiyya idan antashesu break Junaidiyya takira Jumaima suci abinci haka har suk saba da junansu bayan wata d’aya aka kawo Juwairiya makarantar. Ana kawota class d’un su Junaidiyya suka kirata tazauna akusa dasu.

 

Nan dai dukan su shak’uwa yashiga stakanin su, idan d’aya bata iya darasin da’akayiba sai suzauna sukoya mata haka sukeyi. Har suka shiga class 4 duk iyayen su sun sanda k’awan censu.

 

Yanzu sun gama class 6 zasu tafi Secondary school dukansu sun rok’i iyayen su asakasu amakaranta d’aya. Haka kuwa akayi harta ajinsuma d’aya aka sakasu iyayensu suna mamakin wannan abu nasu saboda sud’in yarane.

 

Yaya Yusuf yagama Jami’ansa. Har ya yi digiri nafarko.Su Jumaima sun fara zama y’an mata yanzu suna aji 3 a secondary school. Yaya Yusuf tunda yad’aura idonsa akan Juwairiya yaji yakamu dasonta. Duk ranan da agidansu zasu wuni to shima baya zuwa ko’ina shiga cikinsu yakeyi har Junaidiyya da Juwairiya suka saba dashi.

 

Inna Jume ma tasaba da su Juwairiya da Junaidiyya dan wataran sukanje su wuni mata rannan kuwa akwai shan hira dan dukansu sunada surutu sosai amma banda Jumaima.

 

Yanzu Yaya Yusuf, yafad’awa Juwairiya yana sonta itama ta’amince saboda shak’uwan da sukayi itama har tafara sonshi amma batayi yasaniba.Amma su Jumaima sun sani.Saboda su basa b’oyema junansu komai.

 

Sun gama aji 3 suka shiga 4 a secondary school karaunsu sukeyi babu kama k’afan yaro dan baruwansu da k’awayen makarantar sudai su ukun sune suke rayuwarsu amakarantar baruwansu da gurb’atattun k’awaye.

 

Yanzu Yaya Yusuf yagama digiri d’insa nafarko.”Malam Usman yanata fafutukan nemawa Yaya Yusuf zuwa Maleshiya dan yin digiri na biyu.Tun haihuwan sa yasa buri akansa.

 

A kwana atashi Malam Usman yasamu kud’in da zaitura Yaya Yusuf karatu a k’asar Maleshiya.Dan yin digiri d’insa na biyu.

 

Yaya Yusuf yau Allah Ya yi yatafi Maleshiya dan yin digiri d’inshi acan.”Juwairiya bataji dad’in tafiyansaba saboda tasan zatayi kewansa sosai barinma yanzu da soyayyar sa ya yi k’arfi a cikin zuciyarta.

 

Sukuwa yau idan sukaje gidan Mamin Juwairiya gobe kuma gidan su Junaidiyya zasuje. jibi kuma gidan Umman Jumaima. Haka suke rayuwarsu astak’anin gidaje guda ukunnan basuda wani mastala iyayen suma,sunyar da dahakan tunda bawai wani wajan nadaban suke zuwaba.

 

Basu kiran junan su da Paul names.Juwairiya suce mata Juri. Junaidiyya kuma Juni.Jumaima kuma Juri. Haka suke kiran junansu dashi.

 

Haka rayuwa yaketa tafiya astak’aninsu yau gashi suna ajin k’arshe amakaranta Yaya Yusuf ma yanzu saura masa shekara d’aya yagama digiri d’insa na biyu.Sun samu hutune a school d’insu a can yasamu ya lek’o gida.to wannan shine zuwan da ya yi.

 

To kunji labarin Jumaima y’ar gidan Umma da Yayanta Yusuf.Gobe kuma kukasan ce damu zamu tab’o muku Junaidiyya.

 

By Mommyn Haneef Ce✍️

[30/07, 6:45 pm] +234 803 192 1625: 👭K’AWAYEN JUNA👭

 

LABARI DA RUBUTAWA

 

*NUSAIBA RABIU*

 

(Mommyn Haneef Ce)✍️

 

 

typing✍️

 

FREE PAGE 7&8

 

🔔📚

*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION📚*

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa}_

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

 

*⚜️©J.A.W📚🖌️*

 

 

Dasunan Allah mai rahama mai jinkai Allah Ubangiji ina rok’onka da kabani rai da lafiyan sake dawowa acikin wannan sabon labarin mai suna K’AWAYEN JUNA.

 

Masoyana barkan mu da sallah dafatan anyi azumi lafiya Allah yasa mudace da Aljannatur fiddausi.

 

Ya Allah kamar yanda nafara wannan littafin lafiya Allah kasa nagamashi lafiya ameen.

 

Kuma ban yar da wani kowata sujuyamin labariba.duk wanda ya yi dai_dai da labarin sa to arashine.

 

 

Labarin K’AWAYEN JUNA na paid book ne idan kinji labarin yamiki kinaso kicigaba dakaran tawa zaki iya turo dakud’inki ta wannan account number.

0087778987

Nusaiba Rabiu Union bank 500 naira only👌

 

Idan kuma katine zaki iya turo mana da katin mtn ta wannan number 07026368879.

 

*WAYE JUNAIDIYYA*

 

Junaidiyya asalinsu y’an garin Abujane. Mahai finta yana da kud’i sosai,Sunan Daddy Alhaji Muzaffar.Ammi kuma Hajiya Zulaihat.Sun had’une a India yaje yin har k’ok’in kasuwan cinsa.

 

Itakuma Hajiya Zulaihat k’anin tane bayida lafiya akaturasu can itada k’anwanta Fa’iza suke kulada shi.Tafuta shan iska suka had’u da Alhaji Muzaffar.

 

Shikuwa tunda yad’aura idon sa akanta yaji yakamu da k’aunarta har yasamu ya yi mata magana. Yafad’a mata sirrin zuciyarsa. Itama kuwa batawani b’ata masa lokaciba ta amince.”Alhaji Muzaffar ya yi farin cikin hakan nan take yabuk’aci tabashi number ta.”K’arb’an wayan tayi tasaka masa, ya tan bayeta mai yakawota America “Ta ce” masa d’an uwanta Aliyu ne bayida lafiya akaturosu wajan wani kwararran likita .”Ai’ya Allah yabashi lafiya amma mai yasameshi? “Tace” Masa karayane kuma sosai acan gida Nigeria sun kasa suka turomu nan, “To Allah Ubangiji yabashi lafiya Alhaji Muzaffar yafad’a” Ameen Zulaihat tace”..

 

Alhaji Muzaffar yace muje na dubashi.”To Zulaihat tafad’a suka wuce Hospital d’in, suna shiga d’akinda aka kwantar dashi suka sameshi azaune dan yanzu yafarajin sauki.

 

Alhaji Muzaffar, yamasa yaya jiki yacuro kud’i masu yawa yabashi kuma yasaka akamasa magana da likitan akan yanaso akula da Aliyu sosai nan yace masa babu komai yabawa Dr kud’i masu yawa yace amasa duk abunda yakamata. Kar asake karb’ar wani abu daga gurinsu.”Nan Dr yamasa alk’awari sukayi sallama yafuta acikin office d’in Dr Zunnuren.

 

Alhaji Muzaffar yakoma wajan Zulaihat sukayi sallama Fa’iza tamasa godiya,”Yace bakomai.”Zulaihat tarakashi waje yatafi.”Ita kuma tadawo.

 

Hakadai rayuwa yaci gaba datafiya Zulaihat sun dawo gida Nigeria Alliyu yasamu sauki,shikam Alhaji Muzaffar yajima da dawowa.

 

Yasanar da magaba tansa aje anema masa auren Zulaihat. Sunje angama komai anbada sadaki, har ansaka rana abun bai wani d’auki dogon lokaciba. Sabida akwai kud’i.

 

Itama Zulaihat mahaifin ta yana da kud’i sai yasa akayi bikin acikin wata guda. Alhaji Muzaffar yana zaune da matarsa lafiya suna k’aunar junansu.

 

Hajiya Zulaihat tafara laulayin ciki tasanar ma Alhaji Muzaffar ya yi murna da farin ciki,yace suje Hospital. “Ta ce” kamanta da likita kake tare.

 

Ok to shikenan zaki iya duba kanki kenan? sosaima mai zai hanani naduba wasuma bare kaina.Kar kadamu Daddyn baby.”Kai har kinsa naji dad’i Wallahi Allah yasa kihaifomun d’a namiji kyakkyawa mai kama dani.”Ameen Zulaihat tad’ago ta na Murmushi.

 

Haka rayuwa yacigaba datafiya musu yau Zulaihat tatashi da nak’uda Alhaji Muzaffar yasun gumeta suka tafi Hospital bata wani d’auki dogon lokaciba ta haifi d’anta namiji k’ato mai kama da Alhaji Muzaffar.

 

Ma’aikatan suna gama gyara yaro da Uwansa suka futo dashi, “Alhaji Muzaffar kuwa gaba d’aya yakasa zaune yakasa staye. ” nose sunfuto da baby ahannunsu dasauri yak’arasa yace tahaihune’?

 

Eh Alhaji tasamu d’a namiji. Suka mik’a mishi d’an, “Yasa hannu yakarba yana maijin son d’an har cikin zuciyarsa.Yanayiwa Allah godiya dayabashi wannan kyautar.

 

Nan yatan bayeta ya Uwansa take? “Nose d’in ta ce” Dasauki tahaihu lafiya, “Hamdala ya yi yace mata zan iya ganinta “Eh tabashi amsa. Shiga ya yi yadubata.

 

Har ta tashi tazauna.” Alhaji yana mata sannu.”Tadubeshi ta ce” Yanzu kazama Daddy .”Yace tun yanzu, ” ta ce” Eh mana.

 

Nan dai aka sallamesu suka koma gida. Alhaji Muzaffar yakira y’an uwansa da dangin matarsa duk yasanar dasu.

 

Mahaifinsu Alhaji Muzaffar yajima da rasuwa sai mahaifiyar su Hajjo Su ukune agun iyayen su dukansu maza dashi Muzaffar d’in da k’annansa Sani da Ummar suma dukansu sunyi aure yanzu matansu suna da ciki.

 

To Hajjo ma tazo kasan cewar shine jikanta na farko.”Anyi taron suna lafiya, yaro yaci sunan kakansa Suhaibu suna cemasa Suhaib.

 

Bayan shekara goma sha shida Suhaib yagirma har yagama makarantar secondary school Ammin sa tasake haihuwa.Ta ai’fi y’arta maisuna Junaidiya kyakkyawar yarinya.

 

Daddy yatura Suhaib America yacigaba da karatunsa.Junaidiyya kuwa ta nata wayo suna son yarinyar su kasan tuwar itace mace. Tundaga lokacin Ammi haihuwa yastaya mata basuji dad’in hakanba. Yan’zu Junaidiyya ta na da shekara 8 yanzu ta na aji uku apuramare school.

 

Ya yinda suke k’awancen su da su Jumaima har suka gama puramare suka shiga secondary school tazama y’an mata sosai.

 

Suhaib yana zuwa hutu gida. Shikuma gaba d’aya Jumaima bata burgeshi kasan cewar kullun ta na nanike da himar. Shikuma yafison macen data waye ta iya gayu.”Ita kuma kullun cikin himar gashi batadamu da kwalliya afuskanta ba saidai tashafa fauda da man baki sai kwalli.

 

Saiyasa nasu bai tab’a zuwa d’aya da shiba iya kacinta dashi gaisuwa. Shi bayason hayaniya idan Junaidiyya tafara masa hiran k’awayenta sai yadakatar da ita.Yace tafiya surutu.

 

Ita kuma abun baya mata dad’i sanin halinsa sai ta daina. Shikuw bayan yagama hutunsa yakoma America.

 

Junaidiyya yanzu suna ajin k’arshe amakarantar secondary school.

 

To kunji labarin Junaidiyya da iyayenta.Muhad’u daku gobe insha Allah yanda zan kawo muku labarin Juwairiyya y’ar gidan Mami.

 

Karkuman ta da wannan littafin nakud’ine kiyi k’okari kibiya kicigaba da karantawa.

 

 

By Mommyn Haneef Ce

Leave a Comment

error: Content is protected !!